RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 22 BY HALIMA K/MASHI
Salma tace
“Kash! Da ma ta yarda ga shi
mai kyau. Wannan ko ga shi har da mata da yara biyu”
Aisha ta ce,
“Ai kowa ya ji haushinta bare
Hajiya. Babanshi shine babba a dakin su Hajiyan fa,
kuma ya rungume su kamar me, komai shi yake musu don shi ma dan kasuwa ne. yana da kudi, da
dan ne ya taso sai ya fi uban kudi”
Salma ta ce,Allah ya yi wannan ne mijin
nata Aisha ta ce,
‘Kuma haka ne, Allah ya ba su
zaman lafiya Sunanta da ta ji Imran ya kira ne ya sa Salma
waiwayawa da sauri. Imran Kanin Aisha ne, ya ce,Anty Salma wai ki zo Ta ce, ‘In ji wa?”Ya ce,
‘Ke dai ki zo”
Ta bi shi ta ga sun
nui fità waje. Tana
mamaki sosai ko su wane ne? dan Yaya Hadiza da Inna su ne za su zo mata, amma sai gobe gidan daurin aure. Har Kosawa ta yi sukai ta ga ko wanene. mamaki ya kamata ganin Yusuf. Da sauri ta isa
gurinsu tana fadin,
“Na shiga uku, wa ya ce ku zo
nan? Me ya kawo ku?”
Tana yi tana waige-waige. Duk ta firgice.
Ya ce,Kwantar da hankalinki mana, mene
ne don na zo miki biki? Salma kawarki ita ce ta bani katin bikin yayarki, Tun yamma muka zo ni ma ina
da yan uwa a Kaura, can muka sauka shine na ce bari mu zo Dinner, gobe mu je miki Daurin aure daga
nan ma sai ki gabatar da ni”
Salma tace
“Yusuf ka taimake ni., wallahi ni
matar are ce, ina da mijina fa”
Ya ce.Salma sai dai kawai in ba ki sona
kawai ki fada min, amma Salma kawarki ta tabbatar min cewa ba ki da wani miji”:
Salma ta ce,
“Ai ba ta sani ba ne. to na ji din
ma bana sonka, don Allah ka tafi mijina yana nan gurin auren kanwarsa ake yi fa”
Ya ce, “Ni dai ban yarda da zantukanki ba, ki
kai ni kawai yanzun gurin danginki”.
Abokinsa da suka zo tare kuma ya ce,
In kina jin kunya ko tsoro fada mana gurin wanda zamu, sai mu je da kanmu. In kuma sun fi son ganin magabatanmu sai su zo”
Ganin
mutane sun fara fitowa daga dakin
taron sai Salma ta yi baya da gudu, jikinta yana bari
ta nufi cikin dakin taron. Karo ta ji sun zabga da wani, a rude take fadin,
“Subhanallahi»
” Domin wanda suka yi karon yana kokarin fitowa ne, yana
yin waya. Wayar ta fadì kasa, cikin sauri ita da shi suka kai hannu da nufin dauka. Salma ta riga shi kai
hannu ta dauki wayar kirar Samsug ce wadda ake
yayi, karshen tsada a wannan lokacin. Ta juya wayar
a hannunta bayan wayar ya yi kwatsa-kwatsa dai shi
ma bayan gilashi ne. da sauri ta dago ta kalli mai wayar da nufi ba shi hakuri, sai ta kasa ganin wanda
ya yi wa Anty Badi’atu ruwan kudi ne. ga shi ya
zuba mata ido yana kallonta, bakinta yana rawa tace
“Don Allah ka yi hakuri. Bai ce Kala ba sai kallon Salma yake yi
Ta mike da sauri ta nufi ciki tana yi tana
waiwayenshi, shi yana tsaye yana kallonta mamakin barnar da ta mishi ne yake yi mata irin wannán
kallon, ko kuwa mene ne dalili? Gurin da su Aisha
suke ta nufa, ta ce,Ina mayafin kuma?”
Ta taba kafadarta,
“A’a ina to mayafin?”
Ta soma waige-waige, ta kalli Aishan,
“Bana baki ba? Tace,
“A ina ki ka ba ni?»
Salma ta ce,
“‘Tun da za mu yi hoto”
Aisha ta ce,
“Kuma da aka zo kiranki bakin
karba ba”
Salma ta ce,
“Allah dai ya sa ba na yar ba
Ta soma dube-dube, ba ta ganshi ba ta soma
duban inda za ta hango Shatima. Ta kasa tashi daga
inda take zaune duk ta tsani taron ta kosa a tashi. Ta mike tare da fadin,
“Bari dai in duba gurin can da na
buge ma mutumin nan waya”
Ba ta ga mayafin ba sai su Shatima da ta
hango shi da wannan da suka yi karo suna magana a gurin motocinsu,
Muryar Yusuf ta ji yana kiran Salma. Da
sauri ta dubi gurin su Shatima don ta tabbatar bai ji kiran sunanta da aka yi ba, kuma cikin sa’a Shatima
ya ji kiran tunda tsakaninsu babu nisa, domin ta ga ya kai dubanshi gurin Yusuf din, sai ta yi sauri ta
juya cikin addu’ ar Allah ya
sa Shatiman bai ganta
ba. Bayan an tashi ta bi ayarin amarya zuwa cikin motoci suka nufi gida ranar dai gidan Anty Momiyo
ita ma ta kwana
Tun Karte goman
safe suka dawo gidan
Hajiya kaka domin nan za a daura aure, duk amaren ma nan
suka hadu. Ana ta wanka da kwalliya.
Salma ta makale ana gama yi wa amare kwalliya ita
ma aka rangada mata, suka sha ankon daurin aure
ana ta hotuna. Aliya da Amna sai ga su, Salma tace
“Da ma Yaya a daren nan ya koma Kaduna kenan!”
Sai ta ji Aliya tana fada ma Nafisa wai
Mustapha ya je ya dauko su. Salma ta dauki Jafar
yaran Amna tare da fadin.
“Zo mu yi hoto”
Ko don ganin mutane ne ya san Amna fadin
wannan katon za ki dauka? Salma da ma sau daya ta
taba daukarshi lokacin da suka dawo ta je ta yi musu
barka. Salma ta amshi wayar Aisha tana yi musu
hoto, Aisha ta ce,
“Ke dai don Allah Anty Salma ki
sa Kawu Shatima ya sai miki waya, wayar kowa cike
da hotunanki
Salma ta Ce,
“Kuma don Allah kar ki goge
min ko daya anjima duk zan tura su a wayar yaya Aliya ta kalle ta,
“Shi kuma sai ya ba ki
wayarsa babba ki masa wasa”
Salma ta Ce,
“Ai ba wasa zan masa ba, in ya
hana kuma sai in amshi ta Anty Badi atu in nayi
Waya sai ta turo min ko ta whatsapp ne
Su Inna da Hadiza sun zo ta kawo su gurin
Kaka suka yi mata murna. Sun ci waina sannan suka
bari su je can gurin Hajiya da kuma gidan su
Nafisa su yi ma mama murna ita ma.
Bayan an gama daurin aure Shatima ya shigo
yana neman daya daga cikin matansa, Amna ya iya
samu a waya, ya ce, suna son abinci shi da abokansa.
Ta ce,
“Ni ina zan je nemo abinci?”
Aliya kuma tana Zaune
turus tana
son gwaninta ga ciki ya yi nauyi, ta ce,
“‘Amna ta yi wa
Anty Momiyo magana”
Amna tace
“Ni fa gaskiya ban iya surutun abinci ba
Salma ta gama saka dayan yadinta, ta yi kyau
sosai riga da siket an sha Dauri ta fito kenan
Mustapha ya shigo, ya ce,
“Kai su Anty na an sha
kyau. Yaya na son abinci shi da abokansa’
Salma kuwa ta je har dakin abinci ta debo
kaloli, tuwo, waina, shinkafa dafa duka da nama da
abin sha, tire biyu.
Mustapha ya dau daya, ita ta dauki daya.
Shatima ya amshe ta tareda fadin,
“Sannu Tace
“Yaya ina wayarka?”Ya dube ta,
“Me za ki yi da ita?”
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe