RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 24 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 24 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Nafisa tana cikin yan kai amare, sai dai ya ce yasan gidan ya ragu da jama’a bari ya shiga ya yi sallama da su Mama ta sun yi waya. Cikin sa a da ita ya fara cin karo a falo, tace

“A’a Baban Ashrat?’Ya ce,

“Na’am, kin gama shiri ko?

Tace Wane shiri kuma?”

Ya ce To mu je inda babu mutane mu yi

magana Nafisa cikin mamaki tace Shigo nan

Ta tura akin su Hamida. Wasu yara ne a

ciki, ta ce, “Kuje falo

Ta kakkabe mishi bakin gado tare da fadin, Zauna  Ya zauna yana cewa,

“Ina yaran?”Ta ce,

“Ashraf ya makale wa Babata tun da

muka zo. Babanmu kuma yana bayan Mama

Shatima ya yi murmushi, “Ai dole ya makale ma takwaransa?Ta dubè shi, *Ina yini?”Yace Lafiya lau,tunda an kai amare ai biki

ya Kare saimu tafi ko, don gaskiya gobe da ke za mu nafisa ta yi yar dariya, “tace gobe fa za,a yi budar kai, ka ga ya dace in tafi?”

Yace an  gama budar kai tunda an kai

amarè dakinsu, kuyi musu addu,ar zaman lafiya-kawai”Tace yaya gaskiyal ba zai-yiwu ba, kannai na har biyu na kasa halartar budar kan kansu Ya ce,

“To na ji, zan jira ki goben ki taho da

wuri na fada miki Abuja za mu wuce, jibi office

Ta ce,Wai ni Yaya me ya sa ba ka min

adalci? Ni kadai ce matarka? Ga Salma ai tana htun ba makaranta take zuwa ba, kuma ga Amna in ma Aliya tana da ciki. Amma ko yaushe sai a kace dani zakaje Abuja, kuma

ni anki saka ni makaranta,Fisabilillahi adalcin kenan?”Shatima ya yi

shiru yana kallonta, har da

kuka. Gunjin kukanta ya sa Anty Maimuna ta leko tare da fadin,A’a bayan an gama kukan daukar amaren wa muka samu yake gunji a nan?”Ganin Shatima da Nafisa sai ta ce, “Au dama ku ne?”

Shatima ya gaida Anty Maimuna, ta ja kofar

ta nufi dakin Mama, ta kira ta gefe, tace

*Mama? Nafisa ce mijinta ya z0, sai kuma na ga tana kuka Mama ta ce.

“Suna ina?”Anty Maimuna taCe,

“Suna dakin Su Hamida Mama ta ce,

“Nafisa da ki ke gani sarka ce

sarkin rikici. Bari in je in ji mene ne kuma

Bakin kofar ta tsaya tana jin muryarshi yana

fadin,Karatu dai ko ina ana yinshi ba sai Zaria ba,kuma in kin kwantar da hankalinki Abuja zan nema miki. Inma da za ki yarda akwai wata makaranta da

wata mata ta bude irin ta koyan sana’o’in nan kayan yara da zannuwan gado, da rigunan aure. Na yi magana da matar Nafisa ta ce,

Tab! Nizallar karatuna zan yi”

Yace Kin fi so ki koma baya? Kina ganin

Amna a waje tayo karatunta tana da kwalinta na digiri, amma me ta yi da shi? Yanzu gata kasuwanci ta koma.

Ta ce,amma dai iliminta yana kanta ko?”

Shatima ya ce,

“Shi kenan, yanda ki ka so.Amma ina fada miki Abuja za mu tafi gobe, don haka goben lallai ki taho da wuri

Ta ce, “Ni fa ba zan dawo gobe ba.

Ta yi shiru ganin Mama ta shigo. Kamar an

jeho ta, Shatima ya rusunar da kai yana yana gaida Maman. Yanda ta amsa gaisuwar yasan ranta a bace yake. Ya dago ya dube ta, Nafisa take kalla, ta ce,

*Duk da ban ji zantukan ku duka ba, abin da na ji ya gamsar da ni. Ban san lokacin da za ki san darajar mijinki, ba, yana ga abin da za a yi kina ke ba shi kike so ba. Wannan ba tarbiyya ta bace, ban san kuma

A ina ki ka samo su ba Nafisa cikin kuka ta ce,

“Mama wai a ce mu hudu ne fa amma kullum Yaya ni yake dakilewa karatu, sai dai in bi shi Abuja. Marin da Mama ta sakar mata ne ya sa ta dafe bakinta, shi kuma Shatima bai san lokacin da ya rike hannun Mama ba, yana fadin,Don Allah Mama kiyi hakuri abin bai kai haka ba Mama tace

“ta tashi ta hada nata ya nata ta

bi mijinta.Yace a’a ta bari sai gobe ta zo, Mama ta ce

“Kai ka fi ba ni haushi, ka tsaya kana lallabata tana botsewa, maimakon ka shasshara mata’ mari, mata sun sa ka canza daga Shatiman da na sanka Ya ce,

“Mama ai ba za a biye ba a yi ta

rigima, a barta sai zuwa goben’Ya mike;

“Mama ni zan je in yi sallah mu

wuce”Mama tace

“Don Allah ka yi ta hakuri daSu

Shatima ya ce,Babu komai”Yayi godiya ya fita.

Anty Maimuna tana gain fitarshi ta shiga

dakin tana tambayar abin da ya faru, Mama ta fada mata komai.

Nan suka rufe ta da fada, Anty

Maimuna ta ce Sokuwar banza, cikin ku hudun harda ‘yar yarinya wadda ba ta kai ku shekaru ba, ya za6e ki kece fa tauraruwarshi, ya taba zuwa da sauran?”Tace

“Sau daya ya je da su, Salma kuwa bai

ta6a zuwa da ita ba Anty Maimuna ta ce,

“To kin gani? Gyaran

da ki ke yana amfani, kuma wannan shigar da ki kasamu a gurinsa ta fiye miki duk wani karatu da za kiyi”. Mama tace

“Kuma da za ta shiga makarantar

koyon sana’ar sai tafi mata karatun, tunda na gasa ne za ta yi karatun ba na ra’ayin kanta ba ne”Nan dai suka bar fadan, suka dawo bata shawara da nuna mata abin da ya dace

Washegari tun karfe Daya Mama ta tattara

Nafisa da yaranta direba ya maida ta. Lokacin

Shatima baya gida suka dawo, da ya zo ya same su murmushi ya yi tare da kara ganin darajar mama,matsayin suruka ta gari. Sai dai ya san sai ya yi lallashi game da marin da Mama ta yi mata. Lokacin da suka shirya tafiya Salma ba su dawo daga Katsina ba, don haka ya bar abin da yakan dan-ba ta na nama a hannun Aliya. Salma ta samu nasarar zana jarrabawar share

fagen shiga jami’a (jamb), suna jiran Samun

sakamako. Wani yammaci maigadi ya yi sallama a kofar Aliya ya tambaye ta ko Alhaji yana ciki? Ya yi baki. Aliya wadda ta kumbura saboda cikinta ya ma fita a watanshi, ta ce,

“Yana nan, bari in fada mishi,

ko da sai sun dan jira yana wanka

Shatima ya fito sanye da jallabiya ruwan

madara, ta yi kyau sosai a jikinsa duk da bai sa ta don kwalliya ba, sai don shan iska: Wata mota ce a gefe ya gani, Danbaba maigadi bai bari sun shiga ba,

tunda sun ce bai san da zuwansu ba. Samari matasa

sa’annin su Mustapha ya gani sun fito daga motar sun nufo shi, duk suna sanye da dogayen kaya da huluna,

shigar mutunci. Suka gaida

shi cikin girmamawa, Shatima ya sake dubansu, sam bai sansu

ba, ya ce, “Samari daga ina?”

Suka ce,Daga cikin gari”

Ya ce, “Kuma ni ku ke nema?”

Suka ce “Eh, yayan Salma dai muke nema”

Shatima cikin mamaki ya ce Salma?”

Suka ce, “Eh” Ita

Ya ce, “Ni ne, lafiya ko?”

Daya cikinsu ya ce’

“Eh to gaskiya dai lafiya

lau Ya nuna Yusuf,

“Wannan abokin namu ne

dama yake sonta, to amma ta ki saurarenshi shi ne wata kawarta ta ba mu shawara a kan muzo gurin yayanta

Duk da wanka Shatima ya fito sai da ya ji

wata zufa ta keto masa. Cikin matsanancin bacin rai ya ce Amma ita Salma ba ta fada muku cewa tana da aure ba?”

Yusuf ya zaro ido tare da dafa kirji, gami da

fadin,Dama da gaske take yi?”

Ya cire hular kanshi yana fifita, nan da nan

idanunsa suka yi jajir. Yana fadin,

“Na shiga uku, da

ma da gaske Salma tana da aure? Wallahi ina

tsananin sonta Shatima ya daka mishi tsawa,

“A ina ka ganta?

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *