RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 28 BY HALIMA K/MASHI
Wankan da bai yi ba kenan ya dauki makullin
mota ya fita, dole ya tabbatar da wannan zancen. Ya kalli agogon hannunsa, karfe nawa yanzu Biyu da rabi, yace
-Ina da lokaci”
Layin Shatima ya kira, “Kana gari kuwa?” Ya
tambaya bayan sun gaisa.
Shatima ya ce, “Karfe uku dai zan taso zuwa
Kaduna yace Dama gorin da ka ke min ne zan
wanke laifina Bros”
Shatima yace Ni fa da na ga kiranka sai da
na yi mamaki, har na yi zaton ko wani ka je kira wayar ta danno sunana’
Tare suka sa dariya, ya ce,
“Da yanzun na so da zuwa, amma bari na jira in shigo gobe”
Safwan dai ranar bai samu barci ba, yana ta
tufka da warwara. Bai san ya zai yi ba in har ta tabba matar Shatima ce. Salma ta kalli Shatima, Yaya ina zan samu
café a nan unguwar ne?”
Ya ce.Me za ki yi a gurin? Ta ce,
“Akwai wasu takardu da za mu yi
kwafinsu, sannan akwai wasu tambayoyi da zan duba a yanar gizo
Na so siyan miki waya yau, abubuwa
ne suna da yawa. Amma bari mu ga zuwa gobe” Wayar Shatima ta sake yin ruri, ya kalla,
“Safwan ka iso?’ Yace
“Ga ni a gate”
Shatima ya mike, “Koma tukunna in Safwan
zai fita ma hada hanya sai in kai ki
Shatima ya fita suka shigo da Salwan, dakin
Amna ya kai shi da ma ranar ya hana ta fita, ya ce tunda zai yi bako daga Zaria, Aliya batq nan, Nafisa
tana Abuja. Salma tana kwashe shanya ta hangi bakon a fili ta ce, Wannan ai wanda na fasa ma waya ne
Ta dan makale har suka shige zuwa gurin
Amna, Shatima da Safwan suka gaisa, sannan suka soma hira. Amna ta zo suka gaiva, Shatima ya bi ta
daki, ya ce ta kawo masa abinci mana. Ta ce, bari tasa masu aiki su kai.
Ya ce, “A’a bari”. Ya kira Salma
Tamkar kada ta fito, amma ba ta da damar
gaddama. Ta saka mayafi sannan ta nufi dakin. Ta rusuna ta gaida shi, ya amsa jiki babu kwari, domin
gaskiya ya kamu da tsananin son Salma. Shatima ya dube ta,
“Shiga kicin ki kawo masa abinci
Salma ta nufi kicin, Safwan ya bi ta da kallo.
Sai da ta bace, sannan ya maido kanshi ga Shatima, wanda shi kuma yake kallon Safwan din. Ya ce, Wai wannan ma matarka ce?”
Shatima ya yi dan murmushi,
“Ita Ce karamarsu Safwan yace
“Sauran ba su nan kenan?” Shatima yace
Daya tana Abuja, daya ta
haihu tana Zaria
Salwan yace Kana KoKari, na yi zaton kafin
shekara biyu za su tsular da kai da matsalolinsu, sai naga har yanzu kana nan a gayenka Suka sa dariya, Shatima ya mike don kunna talabijin, lokacin Salma ta fito da tiren abinci ta aje.
Taje ta turò teburin da ake dora abinci in ba a bukatar
hawa teburin. Ta Dora masa a kai, sannan ta koma kawo abin sha.
“Amna ta fito tana cewa Shatima,
Jafar bari in Dauko shi a islamiyya.
Shatima yace
“Kada ki jima Tace
*Yanzu zan dawo
Salma tana gama jerawa za ta fita, Shatima yaCe Wai ke da Allah yaushe za ki daina tsoron mutane? Dawo to in gabatar miki da shi, ba bako bane, dan gida ne, zumunci ne ba shi da shi. Kin san
“gidan Alhajin G.R.A?
Ta ce, “Ba mun jeba, gidan su Sa’ ida ko?”
Shatima ya ce, Yauwa, to shine babban
yayan su Sa”ida. Da babanshi da Hajiyarmu uwarsu daya ubansu daya, shine babbansu
Shatima ya kalli Salwan,
“Don Allah ka yi aure
Ya kalli Salma wadda ta zuba ma talabijin ido.
Shatima ya ce Kin ganshi tare aka yi
goyonmu, amma ina da yara hudu shi har yanzun ya
ki aure’ Salma ta kalli Satwan suka hada ido, gabanta ya fadì, tayi saurin dauke kai saboda wani irin kallo da ta ga ya yi mata.
Muryar Safwan ta ji yana cewa. “Lokacina ne
baiyi ba. kuma mu ture batun wasa bana sa’a ne akwai masu sona da yawa, amma na lura suna son abin hannuna ne. Su kuma wadanda nike son sai a samu
matsala Shatima yace
“Ban da Badi’atu wa ka so?’
Safian ya tsiyaya ruwa a kofi ido ya kurba,
“Yanzu haka akwai wadda nike tsananin so, amma ina zaton ita ma na makaro
Shatima ya dube shi, “A ina take?
Safwan yace
“A nan Salma ta kalle shi da sauri, daidai lokacin da
Shatima ya ke cewa, “Nan Kaduna?”
Safw an ya ce, “Eh”
Shatima yace Yar gidan waye?”
Safwa- ya girgiza kai,
“Ban san mahaifinta
ba” Salma to dubi Shatima a
sanyaye ta ce,
“Yaya wayarka tana ringin tun dazu.
Ya mike ya nufi cikin dakin Amna, tare da
fadin,Ina jin ringin din tun dazu. Ki zuba mana
abincin Salma ta mike ta nufi gaban teburin ta
tsuguna tana
zuba musu dafa-dukan taliya
da dankalin turawa. Safwan ya ce, “Na zone ki biya ni wayata Ta zaro ido,
“Don Allah kada ka fada ma yaya
“To fada min lambar wayarki”
-Ya dauko wayarshi yana dannawa, kanta na
Kasa ta ce! “Ba ni da waya
Ta mike da sauri cikin mamaki ta koma kan
kujera, me kuma zai yi da lambarta?
‘ Shatima ya dawo ya zauna tare da fadin,
“.Ashraf ne wai ya matsa wa Mamansa sai ta kira masa ni
Safwan ya ce, “Mu ma dai bari mu zo mu aje
yaran nan Salma ta kalli Shatima,
Yaya zanJe islamiyya
Yace
“To ki je in mun fita da wuri zan sai
miki wayar*
‘Ta ce, “Café din kuma fa?”
Shatima ya dan yi shiru, yana son ya ga ya ya
ma zai mata, Safwan ya katse masa tunani da cewa,Ba ka da computer a gida?”Yace,
“Ta amfanina dai akwai, amma ai ba
zan bata ta bata ba, ko ta goge min abubuwa
Safwan ya yi yar dariya,
“Sai ka ce wata
mara wayo, ko kuma wadda ba ta san computer din ba?”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe