RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 26 BY HALIMA K/MASHI
Amna ta ce, “in Na yi magana sai ya ce shi bai san ya ce ba, mantuwa ce
“Tabdi yarinya ta tsare muku Maman Jafar
bacci ku ka yi ne haka! In fada miki ni nan ba ni da kishiya, amma na yi kishiyoyin waje. Da baban su Afra kwararren dan neman mata ne, ni ma farkon haduwarmu da haka ya zo na nuna mishi ni fa ina da
tarbiyya, shine ya Billo da batun aure, da yake ina sonshi ban Qi ba na amince.
In fada miki anyi aure muna ta soyayya daga
samun cikin Afra sai wulakanci ya shiga. Ai ko ya shiga neman matanshi har ba ya shakka in sani. Ina haihuwa Yayata ta hadi ni da wata mai saida maganin mata a Kaduna. Kafin in yi arba’in ta yi min gyara tare da shawarwari yanda ya kamata.Ranar ko da ya dawo ban da tona sirrin aure babu
kyau da na ba ki labarin yanda muka kwashe kin sha dariya.
Mutum ya koma tamkar soko, ko inCe bawana, Ni ina sonsa tsakani da Allah haka bai sa na
wulakanta shi ba. Cikin hikima dubara da addu’a Allah ya taimake ni ya bar duk wata macen waje,sannan in na yi magana yana karba, duk abin da nace ina so in yana da hali yana mana. Daraja da Kima
ta ta dawo idanunsa, Ke shawararsa wadda ba ta shafe ni ba ma sai ya kawo min ita. Ni ko in ba shi iya fahimta ta sakamakon ina karance-karance
littafan Hausa ina samun kaifin basira”Amna ta tabe baki
“Ni fa duk wannan
karance-karancen na Hausa bana yin su, gara English Novel, sannan wadannan abubuwan ban yarda da su
ba. Ga likitoci kullum suna gargadin shaye-shaye da matse-matsen nan”
Maman Afra ta ce,
“Ina mamakin irinku”yan
gayu masu karatun al’adun wasu ku bar naku.
Hikima da basira ai tanaga marubutanmu cikin
hikima da basira, kuma kin san wannan matsalar da ki ke fadì da kina karatun da tuni kin magance ta batare da kowa ya sani ba kuma game da kayan gyaran
jikin nan, sai dai in ba ki nemi ingantattu ba kuma basu baki shawara daga masu saida kayan ba. Kin san cewa ni ma na yi irin abin da ki ka yi?”Amna ta tabe baki,
“Ni fa ban iya wannan
aikin, ko da aurena ban sha sosai ba, ko yanzu na fi ga dan irin na waje din nan Maman Afra ta ce,Ai wannan ba su zama a
jiki in za ki dawo hanya ki dawo kawai”
Amna ta ce,Mu bar wannan zancen, ni muyi wanda nike miki
Maman Afra ta ce,
“Mun bari. Amma in kin
canza shawara kina iya tuntuba ta zan kuma hada ki
da ita. Don kullum ina fada ma mata sai sun gyara zasu ga daidai Amna ta ce,
“Yanzun ni ya zan magance
wannan matsalar, yanzu haka fa ita tana Abuja gaba daya mu sai dai ya zo ya yi mana kwana daidai don ita Karamarmu ma da yake ya maida ta sakara, sai yayi zuwa ka ga bai kwana gurinta ba
Maman Afra ta sheke da dariya tareda fadin,
“Lallai na jinjina ma wanna Nafisar, har ta burgeni” Amna ta ce
“To mene ne abin dariya a nan.
Maimakon ki taya ni bakin ciki miji yana tare da ni,kuma yana ambatar kishiya. Akwai ranar da har kuka na yi saboda kiran sunan Nafisan, na yi wai sai ya ce
min wai sun yi fada ne shine abin yake ransa
Maman Afra ta sake shekewa da dariya har
da kwalla. Amna ta mike za ta tafi tana fadin,
“Tunda abin dariya ne bari kawai in tafi”
“. Ta yi maganar cikin fushi.
Maman Afra ta riko ta,
“Tsaya ki ji kawata,
rainin hankalin da namiji nike yi wa dariya. Ya rasa lokacin da zai tuna sun yi fada da ita sai irin wannan lokacin mai tsada a gurinki?”
Maman Afra ta dafa kafadar Amna,
“Yi tunani da kyau ki gani. Yarinar nan tana matukar gyara jikinta, inda za ki tambayi sauran kishiyoyinki
Kila su ma yana kiran sunanta a gurinsu. Ai bai san lokacin da zai yi barin ba
Amna ta ce,
“Kin ganta ne, busasshiya. Na fi
ta komai fa! Har na fara zargin ko ta yi masa asiri ne” ta ce,
“Ba wani asiri in fada
miki isassun mata yanzun ba sa zuwa gurin bokaye, kayan gyara suke siya suna gyara jikinsu, ki ga mace
birtintin amma ta isa’ a gurin miji, kuma ita ma har bushewarta ta fi ku a idonshi. Shawara ta daya ku dage kawai ki gyara, amma fa tushi babu inda zai kaiki”
Ita dai Amna har ta tafi ba ta gamsu ba. Cikin dare nakuda ta kama Aliya, ranar
asabar ce Shatima yana dakin Amna, Aliyar ta yi ta kiran layinshi ba a daga ba. Haka ma layin Amna tayi ta kira, wayoyin duk suna falo su kuma suna cikin
daki, sam ba su ji kiran ba. Karfe biyar na asubahi Aliya ta haifo danta santalele shi ma mai kama da
Babansa. Cikin bacci Shatima ya yi mafarki wai Aliya ta haihu. Da sauri ya farka, falo ya nufa ya ciro
wayarsa a caji da nufin kiranta tunda likita yace
lallai tana fara nakuda a kai ta asibiti, domin ta gota lokacin da ake saka ran za ta haihu. Adadin kiran daya gani nata a wayarsa shine ya sa shi ficewa daga
dakin babu shiri, ya nufi sashen Aliyar, Ya same ta tana numfarfashi a gefe ga da
yana ta tsala kuka. Da alama ba ta jima da haihuwar ba. Ya kai hannu ya kama ta tare da fadin, “Tashi”Ta ce.
“Ka bani reza a cikin can in fara yanke
mishi cibiya”
Ya dubo ya ba ta, ta yanke cibin, sannan ta ce
ya ba ta zani. Ta nannade yaron, sannan ta ce ya kwantar da shi. Ta ce ya taimaka mata ta shiga wanka. Ya tara mata ruwan zafi ta shiga wanka, layin Amna ya kira da wayar Aliya, ba ta daga ba ya
Nufi dakin da sauri ya tashe ta, ya fada mata
haihuwar Aliya.Juyi ta yi tar da fadin, Allah ya raya Ta maida kai ta kwanta.
Yace Ki tashi ki taimaka mata’ Amna ta ce, “Me ni gaskiya ba zan iya zuwa wani taimako ba Ya ce, “Ita kadai fa ta haihuTa ce, “Ina asibiti ne Can ya kamata ka kai ta Ya nufi dakin Salma da sauri, ya taso ta, ya
“ce ta zo ta taimaka wa Aliya. Suna shiga suka samu° Aliyar zaune tana goge jiki, ta fito wanka. Salma ta ce, “Sannu Anty Ya nuna mata gurin jinin, “Ki gyara nan Salma ta nufi gurin zuciyarta ta tashi, amma
haka ta daure ta kwashe ta kulle uwar a ledar da Aliyar ta ce ta dauko a store, ta goge ko ina tsaf da Detol sannan ta fesa turaren daki; ta koma dakinta zuciyarta a tashe, ta shiga ta yi wanka, sannan ta yi sallah,”Da safe Shatima ya dauki maijego da danta ya kai su asibiti don likita ya duba lafiyarsu. A ranar
– dangin Aliya suka cika gidan daga Zaria, Amna sai da ta tashi fita zuwa shago sannan ta shiga don yi wa
‘Aliya barka. Kusan tunda take a gidan wannan ne karo na farko da ta shiga gurin Aliya, gara ma gurin
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe