RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 1 BY HALIMA K/MASHI
Cikin zafin rai Shatima ya isa gurin da Salma
_ke tsaye tana cika tana batsewa. Ya zabga
mata mari, ya sake zabga mata a dayan
gofen. Salma ta gigice, ta ce,In ba ka sona
iyayena suna sona ba sai ka kashe ni ba. ka
sake.Ya sake kai wa bakinta kwabda, ta fadi
Kasa bakin ya fashe jini ya soma tsiyaya. Shatima ya ce, “Kin dade ba ki tafi ba, kin ji ko? In ki ka sake magana sai na sumar da ke
Ya fice bai bi ta kan kayan da ya zube a
kofar daki ba, ya nufi dakin Aliya yana huci cikin tsananin bacin rai.
Aliya ta tare shi da sannu, amma ganin ya
kasa amsawa sai ta fahimci yana cikin bacin rai, don haka sa ta aje ruwa a gabansa ita ma ta samu guri ta zauna.
Salma kuwa tana tashi ta shiga bandaki ta
sa ruwan dumi ta wanke jinin da ke zuba.
Lebenta ya kumbura suntum, jini kuma bai tsaya ba, ta ce,Ai yau komai dare sai na tafi”
Ta dauki jaka da akwatinta daidai an tada
sallar magriba ta san Baba maigadi yanzu ya tada sallah, ta yi ficewarta. Ba ta yi nisa a layin ba ta samu dan acaba ta tare ta nufi titi. Ta dan jima kafin ta samu motar zuwa Zaria. Da ta sauka ta sake daukar dan acaba zuwa gidansu.Maman Nana makociyar Nafisa ta shigo gidan da sallama, Nafisa ta amsa tare da fadin,Har kin dawo?”Maman Nana ta ce,
“Ai kin san asibitinbabu layi, kana zuwa za ka ga likita, ina su Nana suna ta yi miki rashin ji ko?” Nafisa ta ce,Suna can falo suna kallon
carton da su Ashraf”Ta ce,
“To bari tunda ba su ji zuwana ba
in je in gama aikina”Nafisa ta ce,
“To ga makullin can”
Ta nuna mata shi a windon kicin, har ta
juya sai kuma ta dawo tana cewa,
“‘Au! Maman Ashraf ina ta zuci-zuci in
fada miki wata
magana, amma ban san yanda za ki dauki abin ba Nafisa ta ce,
“Haba Maman Nana, inda zaki fada min ko mene ne kawai ki fada min”
Ta ce,Ban fada miki da wata manufa bá,
sai don ki yi saurin daukar mataki, amma cikin
nutsuwa da hikima ba wai tashin hankali ba”
Nafisa ta zaro ido,Mene ne don Allah?
Ki fada min”. Maman Nana ta ce,
“A’a kar ki daga
hankalinki, shekaran jiya waccan na dawo gidan Maman Sabir naga mijinki ya sauke wannan yarinyar Zinatu shine nike son ki fada masa ba yarinyar arziki ba ce. Duk namijin da ta dafe masa sai ya yi kamar ya zauce don sonta. Ta yi aure sau biyar duk wanda ta aura sai ta sa ya rabu da iyalinsa sannan ta ki zama, sai ya sake ta. Yanda ki ka san annoba haka ta zama a layin nan”
-‘ Nafisa ta ce, “Na shiga uku, to ni Baban
Ashraf in ya ce zai so ta ai mun bani, mu hudu
ne fa, wa zai saki?”Maman Nana ta ce, “To nan bala’ in yake,ko mutum ba ya neman mata in har ya hadu da Zinatu zai fara. Tana da kyau kamar aljana, ga ta fara tas, ga diri ta iya gayu sosai. Sai dai fa akwai shiga malamai”
Nafisa jikinta har rawa yake, ta ce,
“Ya je Kaduna zan ma jira ya dawo kuwa? Ina jin a waya zan kira shi”‘.Maman Nana ta ce, “A’ a ki dai bari har ya dawo din sai ki nutsu ki yi masa magana cikin lumana” Nafisa ta ce,
“To shi kenan, na gode
Maman Nana”
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe