RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 30 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 30 BY HALIMA K/MASHI

 

 

kasuwanci mana. Na tabbata in ka samu irin su Yaya Safwan zai ba ka shawara tunda shi din dan kasuwa ne

Shatima ya zuba ma Salma ido,

zancen kasuwancin ya ratsa shi. Ya ce,

“Amma ke ba kya ganin kasuwa sai da jari?”

Ta ce, Wannan ko su Hajiya da Alhaji za su

Iya juya maka Ya ce,

“Kice gobe in tafi Zaria kenan. ZanJe inyi shawara da su Hajiya Salma da Sa’ida da kuma Saddika S. Tata suna tafe zuwa gurin motar Sa’ida, duk suka jingina

jikin motar hirar dai ta karatu ce. Salma ta ce,

“Jikina ni har ya soma sabawa da suntirin Kaduna zuwa Zaria din nan kullum, ga shi duk na rame Saddika ta ce,

“Humm, ai karatu fa babu sauki”

Sa’ida tace

“Bari in tafi dama na zo na duba kune Har ta shiga mota, ta ce,Au? Na manta,

Salma Yaya Safwan ya ce in ce miki ya gode, amma na ba shi lambarki dazu da safe. Wai menene ma?”Salma ta yi yar dariya,

“Sako ya ba Yaya Shatima ya kawo min, shine ban masa godiya ba”Saida ta yi murmushi,

“Kai Yaya manya, to sau nawa yana kyauta ba ya waiwayawa? Na zaci wani abin kirki ne ma, don na ga shi ba mutum ba ne mai son shiga shirgin wasu”Salma ta yi ‘yar dariya, sannan suka juya.

Shatima ya tallauna da mahaifanshi biyu kan

batun kasuwanci, amma bai nuna musu cewa ya gaza da gidanshi ba. Sun ji dadin shawarar kuma sun yi alkawarin

taimaka masa da jari. Sun kuma goyi

bayan ya tuntubi Safwan. Ya kira Safwan ya sanar da shi cewa yana son ganinshi, Safwan yace babu matsala, in ya samu lokac zai zo har gida a cikin

ranakun karshen mako. Wani dare Salma tana shirin kwanciya sai ga kiran yayarta Hadiza, ce suka gaisa, tace Salma kina

lissafin bikin Auwal kuwa?” Salma tace

“Ina lissafe Yaya, saura kwana

ashirin ko?”Ta ce, To cikon dubu biyuna ki Kokarta ki samo min. to ke me za ki masa?”

Salma ta ce,

“Dubu biyunki suna nan aje, ki

bari zan fada wa Yaya gobe in na zo makaranta in karaso gidan Inna sai mu yi magana a tsanake, don

kam mu nan sai a hankali, Yaya Shatima abubuwa sun yi masa yawa

Hadiza tace

“Mun ‘yi maganar da Inna da ta

ga wannan karon kudin haya da guntu-guntu ya biya musu Salma tace

“Allah sarki Yaya, bai ma fada

min ya biya kudin ba. Allah ka ba ni ikon gama

karatun nan, ka albarkace ni da samun aiki, zan taimaka masa da dukkan abin da zan iya sannan in taimaki iyayena”Suka yi bankwana a kan sai gobe.Hajiya ta dubi Momiyo.

Ni fa Allah tunda

Aliya matar Shatima tazo lokacin da ta yi arba’ in din nan take ba ni labarin irin kudin da Shatima ke kashewa kan konanniyar yarinyar nan du tsanarta ta karu a raina, ga iyayenta shine cinsu da shansu, shi ne kudin haya

Momiyo ta ce,Karatun jami’a kam da kashe

kudi, amma tunda shi ya ga zai iya ke ki daina

damun kanki mana Hajiya taCe,Allah dole in

damu. Shekaran jiya Aliyar ta sake kirana tana fada min,wai ga shi har ya kai matakin kasawa da su. Duk da albashinsa mai tsoka da yake dauka, har bashi yaci

na abincin gida Momiyo taCe Bashi kuma?

Wane iri? Shatima gaskiya gara a san abin yi Hajiya ta ce, Ba ina fada miki ba ya z0 da son

shiga kasuwanci ba, har kina murna? To na fasa bashi kudina, karshe ni zan kwana ciki a bashi ya kashe musu anty Momiyo ta ce,

“Kar ki hana shi, amma ki masa kashedi, kuma

ki nuna masa kin. san me gidan nasa yake ciki” Tace Ai in na nuna masa na san abin da

gidan nasa yake ciki sai ya yi mata magana, kuma daga nan zan daina jin komai. Zan dai san yanda zanyi in ga na raba su, don bala’I ita ba haihuwa ba ba komai ba sai tsatsibar kudi kawai suke yi” Momiyo tace

“Kaka dai tana yinta sosai” Hajiya ta ce,

“Ta yi ta yinta din, ni dai dole

ya rabu da ita ba zan iya ba. Na soma yi wa Alhaji mitar yayu  tsalle ya ce kar ya kuma jin haka Momiyo tace, “Allah dai ya kyauta, amma

dai Hajiya ki bi a hankali”

Shatima yana tafe cikin motarsa gida ya nufa,

don shi ba shi da dabi’ar yawo babu dalili.

Kyakkyawar yarinyar da yake yawan gani a kusa da gidansa ce ta sa mishi hannu alamun ya tsaya. Kamar

ya wuce, sai kuma ya tsaya. Ta iso da dan saurinta gefe da ba kowa ta kalle shi, “Don Allah Baban Ashraf gida za ka?”

Ya dauke kai daga dubanta, don wani salo da

ya ga tana yi da idanunta, sannan ya ce, “Eh”

Ta ce,In shigo ka taimaka min, na rasa abin

hawa Ya ce,Bismillah”

Ta bude ta shiga tare da fadin, “Na gode”

Bai tanka ba ya figi mota.

Ta dube shi, hankalinsa yana kan tukinsa, ta

ce, “Ba ka yi mamaki da na kira sunanka ba?” Ya dube ta, fara ce tas ga kyau, ya maida kai

Kan titi Ban yi wani mamaki ba gaskiya, don an fada min haka Ta ce,

Ka san ni to, da ba ka ji mamaki ba?”

Ya ce,Ban sanki ba gaskiya, amma na taba

ganinki a layin da nike”Ta saki wata yar dariya,

«Tunda nike ban taba ganin mutumin ddaya ganni  sau daya ya

kuma ganina bai gane ni ba. In na tambayi dalili sai ace kyauna ne sila’Shatima ya sake kallonta cikin mamakin maganarta. Ya maida kai titi, “Hakika kina da kyau. Ta ce, “Kai ma ka yaba kenan?”Ya ce,A’a, na dai fadì abin da yake zahiri”

Ta dan yi shiru kamar mai nazari, sai ta sake

dubanshi.Kusan kowa ai yana yabawa da mai kyau, musamman ku maza Ya ce,

“Haka ne, amma kowa da ra’ayinsa ba

a komai kyau ke burge ni ba, musamman ga mace.Don bana son abin yayi da kuma wanda kowa ke so. Ina ki ke ganin yanda Kuda sukan taru a kan alkakin da ya ji suga Maganar ta shige ta, don haka ta ce,

“Ai kuma irina ba kowa nike ba fuska ba?”.

Daidai lokacin ya tsaya a kusa da gidansa,

“Kina iya sauka zan shiga gida”

Ta bude, “Har mun iso?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *