RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY HALIMA K/MASHI

 

 

fuskarshi daure, su Salma suka soma gaida shi”Sannunku”Kadai ya ce ya kauda kanshi.

Salma ta dubi Salma,Mu dan matsa can

ko?”Shatima ya katse mata maganar da cewa,

“Shiga mota mu je”Ta dauke kai gefe. Ga mamakinta sai ta ga ya fito ya nufo ta, ta lumshe ido ta saka ran cewa zai tsinka mata mari ne, sai kawai ta ji ya kama

hannunta. Ya bude motar ya tura ta ciki, ya dubi su Dankasa ya ce,Ku je gida abinku”

Ya figi mota, Salma tana zaune tana tura

baki Sai da ya figi motar sannan ya ce,

«Ina miki magana kin banza, daga ina ki ke?”

Ta ce,Ni gaisuwa na je”Ya Ce,Da izinin wa?”

Ta kauda kai zuwa titi. “Kaka mana”Ya ce, “Kaka take aurenki?” Ta yi shiru. Ya ce,

“Kina ganin zaman da ki ke yi

gidan Kaka shine ya fi miki ko?” Ta ce,

“Eh” Bai zaci amsar ba, har ya taka burki babu

shiri. Sai da suka yi gaba dukkansu, Aliya tace,

‘”Mu dai kada ka zubar da mu”. Bai bi ta kanta ba, ya ce,Salma kina nufin kin fi zon zama da Kaka a kan zama dani?” Aliya ta sake fadin,

“Don Allah ka kai mu gida” Ya dube ta,

“Don Allah ki tsaya min, ina zuwa Ya dubi Salma. Ta ce,Dole zan fi son zama da kaka,

domin ita tana sona’Ya ce,Ni kuma bana sonki ne?. Salma ta ce,Ai na san ba ka sona tuntuni

Ya tausasa murya,Salma, ina sonki. Waya fada miki bana sonki?”Salma ta dago ta dube shi, ta ji kalmar har tsakiyar kanta. Ta lumshe ido,Yanzu ka fara sauke ni in shiga mota, za muyi, maganar nan gaba kadan- Ya ce,

“Mu tafi gida, sai mu je da ke mu

ba Kaka hakuri”A ranta ta ce,

“Tab! In ko na yi hakan na bada Kaka”

Ta dube shi,Ka bari mu bi a hankali”

Ya tada mota ya nufi garejin Kawo da ita.

Shi da kanshi ya sauka ya je ya samar mata mota, saura mutum biyu ake jira ya biya kudin

duka, ya ce ta fito. Kafin ya dawo daga gurin

masu mota Aliya wadda takaici ya isa, sai tsaki take yi. Salma ta ce, Gara ma da ya fada a gaban masu min gorin. Ni ko ba sonshi nike ba, ya gama rawar kan ya ba ni takarda ta’ Aliya tace,Kar dai ki min rashin

kunya”. Salma ta yi yar dariya ta maimaita abin da ya fada ma Aliya,Don Allah ki tsaya min ina zuwa” Aliya za ta yi magana ta ga Shatima ya nufo su, Salma ta dube shi, in har ya sa kananan kaya suna matukar yi mishi kyau. Ta ce,In ka iso ka bude min kofa

Tamkar ya ji yana zuwa ya bude mata,

“Fito ku taff?”Ta dubi wurin Aliya,Sai anjima

Aliya ta yi mata banza, Shatima ya dubi

Aliya,Tana miki sallama Aliya ta ce,

“Uhum sai anjima, ban ji bane Ya sake raka ta har gurin motar. Sai da ta shiga ya ce,

“Za mu yi waya anjima?” Ta dubi cikin idanunshi,Za mu yi” Ya yi murmushi ya juya. Ta bi shi da kallo har ya shiga motar, ya tada ya dube ta, tare da daga mata hannu, ita ma ta daga mishi don tura

wa Aliya haushi. Suna tafiya a titi tana ta murmushi ita kadai, ba ta san dalilin ba yau ta ji zuciyarta fes, ko don Shatima ya furta mata kalmar so? Kuma a gaban Aliya? Gaskiya yau Shatima ya burge ta. Aliya kuwa da suka isa gida kosawa ta yi Shatima ya fita, don ta kira Hajiya. Tana kiran Hajiyar ta daga, suka gaisa, ta ce,Dama kiranki na yi kawai mu gaisa

“Shatima ya zo wannan satin?” Hajiya ta

tambaya. Aliya ta ce, Ya ZO, yanzun nan ma muka dawo daga kai Salma gareji tare da shi”

Hajiya ta ce,Salma kuma, gidan ta koma?”

Aliya ta ce,A’a mun fa dawo duba

abokin aikinshi ne daga asibiti, sai kawai muka

tsince ta ita da wasu kawayenta. Shi kenan ya

hau rawar jiki yana ta lallashinta wai ta dawo. Da yake ta samu dama har ni ta dankara ma magana, saboda ta ga ya yi min tsawa Hajiya ta ce,Lallai! Ki ce ni aikin banza

ma nike yi. Kenan zirma ni yake yi da ya ce zai

sake ta?” Aliya ta ce,Addu’a kawai yake bukata. Don na jima ban ganshi cikin irin wannan walwalar ta yau ba” Hajiya tace

“Na gode, zan kira shi yanzun Aliya ta ce,

“Hajiya, kar ki kira shi. Ki dai

masa addu’a, zai ce ni na fada miki, dama

rannan yake ce min bai san wane ne ya ke kai

sirrinshi gurin Hajiya ba Hajiya ta ce,

“Sai na masa magana tunda

ba ubana ba ne shi Kafun Aliya ta yi magana har Hajiya ta katse wayar. Aliya ta tsure kar dai Hajiya ta fada masa. Salma kuwa sai ta kasance cikin jiran kiran Shatima, har ta yi kamar kada ta kira shi, sai kuma ta fasa. Ta yi shirin kwanciya, zuwa lokacin ta cire rai da cewa zai kira ta. Idanunta suna lumshe tamkar mai bacci, Maryama da ke kwance kusa

da ita tuni ta yi bacci. Gunjin

wayarta ta ji don ta cire mata Kara tuntuni saboda in Kaka ta ji karar waya sai ta tambaya waye ke kira? Wani lokacin ma har sai ta nemi jin dalili.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *