RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 13 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 13 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Shatima dai ya yi shiru, don rigima zai

hada iyayenshi in har ya ji cewa Hajiya ta hana.

Salma ta kasance cikin tunanin hirarsu da

Shatima, haka kuma ta samu kanta cikin yawan murmushi. Maryama har sai da ta tambaye ta.Anty Salma kina ta murmushi yau?” Salma ta ce,Ina tunawa ne za mu je

Katsina an ce Anty Badi’atu tana da ciki”

• Ta fadi hakan ne don ta ga Kaka tana kallonsu. Maryama ta yi dariya, tun kafin ta haihu za ku je?” Salma ta ce,Ai don makaranta ne da na tambayi Kaka na je Kaka ta ce,

“Allah dai ya raba ta lafiya.

Cikin yana ba ta wahala, ai ke ina ga har

maganin haibuwa za a nema miki, shekaru nawa shiru? Innarki ma ta iya shiririta, shi ko namiji ne ina ruwansa bare ya ga ya samu

*ya ya daga sauran matanshi? Ai ko haka ma ya yi miki wulakanci kin san wasu mazan sai su ga kamar in mace ba ta haihu dasu ba zama da ita ma ba dole ba ne”Salma dai ta yi shiru, Kaka ta ce,Lallai in kin fita kibi ki ce ina neman Innarki” Shatima ya shiga

super market don siyayyar kayan masarufi.

gurin biyan kudi yarinyar ta ce,Sannu Baban Ashraf”Ya dube ta,Yauwa sannunki” Ya ci

gaba da bada kudin da ya kirga. Yana saka

kayan a kujerar baya, yana bude mazaninshi

yana shiga, ita ma ta bude dayan bangaren. Yana zama ita ma ta zauna, ya dube ta,

“Ya ya, lafiya, daga ina?”Ta kafe shi da idanunta,Taimakona za kayi. Layinmu daya, sai ka barni ina jiran abin hawa?”Yace,Me zai hana tunda ba ni na kawo

ki ba, ko na ce ki zo?”Ta gyara zama tare da kau da kai,Masu kamun kai irinka suna burge ni sosai. Taimaka ka kaini” Ya figi mota ba tare da tsayawa ba ta amsa taba. Duk da ta yi ta dan jeho maganganu, sam bai tanka ba domin yana tuno zantukan Nafisa na zarginshi da take yi. Matsawar taganshi za ta ce lallai halinsa ne, shi ya sa kafin ya shiga kwanar layinsu ya ce,To sauka nan Tace Haba ina laifin inda muka karasa?” Kiran Salma ya shigo wayarsa, kafin ya yi magana sai ya kalli fuskar wayar. Ganin kiran Salma ya dauka cikin sauri,

tare da fadin,Masoyiyata”Salma ta dan yi

tsam don tana cikin makaranta ne ta ji tana son jin muryarsa, ta ce,Yaya dama na ce ne ina son zuwa Katsina, zan duba jikin Anty Badi’atu”.Ya ce,A’a ki bari sai innazo juma’ a sai muje asabar mu kwana a can”Ta ce,

“A gidanta za mu kwana da kai?”Ta tambaya cikin mamaki.Yace,A’a, hotel za mu je mana” Ta ce,Tab! Ina tsoron Kaka. Sannan

kuma har yanzun ba ni da tabbas a kan cewa

kana sona ko a’a”Ya ce,Ya kike maganar nan? Allah ina sonki Salma, kullum cikin tunaninki nike”.Ta ce,Ni nace sai in ka fata ma wadanda ka fada ma cewa ba ka sona” Ya ce,Ai na fara don wallahi na fada ma Alhaji”Salma ta saki

‘yar dariya, sannan ta ce,Yanda ka fada a cikin mutane haka nike son ka sake tara su ka fada musu” Yace Salmata gamida kwantar da

murya,Haba taya zan tara wadannan

mutanen?” Cikin shagwaba ta ce,

“Ni ban sani ba. Amma in bakayi haka ba, ba zan bi ka zuwa Katsina ba”

• Ya ce,Amma za ki yarda da son da nike

miki?” Ta ce,A’a ba zan yarda ba

Ya ce,Shi kenan, zan ga yanda zan yi

hakan. Kuma za mu yi magana da dare”

Ta ce,A’a, sai anjima”Ya ce,Jira ki ji Salma”

Ta ce, Katina zai kare, kuma bana cikin

wadanda ka ke saka ma kati duk sati”

Ya ce,Na gode Allah da gori ni Jafar.

Zan sa miki anjima”Zinatu wadda ke zaune tana sauraronshi tace,Baban Ashraf ka manta da nine wai?”Cikin sauri ya dube ta, har ga Allah ya manta da wata a kusa da shi, ya ce,

“Ke fita mana, zaman me ki ke yi a nan?”

Cikin sauri ta ce,Au haka ma za ka ce?”

Ta yi maganar cikin daga murya ko don Salma taji. Fahimtar hakan ya sa yayi saurin katse layin na Salma. Ya bude kofar,

“Fita na ce da Allah”. Zinatu ta fita tana fadin,

” Amma ba a taba yi min abin da ka yi min ba”

Ya fisgi motarsa ya yi cikin layinsu. Salma

bata zargi komai ba game da muryar da ta ji da suna wayar. Zatonta Nafisa ce

don haka ta tabe baki tare da fadin,

“Kamar mai tsoronta?”Wasa-wasa haka lokaci ya yi ta tafiya, lamura suna canzawa har cikin Badi’atu ya kai wata bakwai. Tun daga lokacin Badi’ atu ta soma nacin za ta koma gida ta haihu a can. Abin da ke ba ta haushi, sai ya dinga nuna mata za su yi shawara da matarsa. Ta kuma sha tambayar akan cewa, matar ce take auranka ko shi? A duk

lokacin da ta yi wannan tambayar sai sun yi

rigima. Sam auren ya fice a zuciyarta, wannan yasa kullum ta ke cikin kuka da bakin ciki. Salma kadai ta san cewa tana cikin matsala, don suna chatting. In ta fada ma Salma ne take jin dadi, sannan Salmar tana lallashinta da cewa, ibada ce take yi ta yi ta hakuri. Amma ta ba ta shawara da cewa, in ta haihu ta zo wanka ta sanar da halin

da take ciki don a nema mata ‘yanci.

Sai dai shi Shatima in ya kira Salma za suyi magana, amma ya yi ya yi ta fito su hadu taki, domin shi ma yaqi zuwa ya samu Kaka.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *