RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 12 BY HALIMA K/MASHI
Ta dauki wayar ta sauka zuwa falo bayan
ta bi Kaka da kallo wadda ke lullube a kan katifa. Sai da ta kwanta kan kujera, sannan ta daga.Ya ce,Na yi tunanin ma ba za a daga
ba?” Tace, Saboda me?”Ya ce,Ana fushi dani”Ta ce,Humm. Ina yini?” Ya ce,Lafiya ba lau ba’Ta ce,Me ya faru?”Ya ce,Rashinki mana’
Ta ce, “Yaya kenan. Rashina me zai hana?
Ni da dama ba wai ana sona ba ne?”Yace,
“Salma ki daina wnanan maganar”Ta ce,
“Ai ko ba zan iya daina ta ba, ko, ince ba za ta gogu a raina ba, domin ban san iyakacin mutanen da ka ce ma ba ka sona ba”.
Ya ce,Wai yaushe na fada ne? Ta ce,
«Ka tuna ka fada gaban su Hajiya da kishiyoyina, sannan kuma ka fada ma Aliya,
sannan akwai wasu yan uwanka da kayi
maganar da su”.Ya ce,Ban yi maganar da Aliya ba. Na san na fada gaban su Alhaji gaskiya lokacin ban fahimci cewa ina sonki ba. To amma ke ki fada min inda ki ka ji bana sonki, har ki ka fusata kike son in rabu da ke”
Ta ce,Ba zan taba fadin inda na ji dayan
ba. Amma ko a ranar Anty Aliya ta goranta min
zancen so da haihuwa, ba ta san ni ba su ba ne a gabana ba’Shatima ya yi shiru, Aliya ta canza hali yanzun kenan. Jin ya yi shiru ta ce,
“Na san ba za ka yarda da abin da na fada ba, sai dai lokaci na zuwa za ka sha mamaki”
Ya ce,Mu bar zancen kawai, ni dai nasan na fada a gaban su Hajiya din nan to sai dai Safwan wata rana da muka yi maganar da shi
Salma ta ce,Au? Har shi ka fada masa ba
ka sona kenan?”Ya ce,Yanzun fa zan iya fada ma duk wanda na fada ma bana sonki da cewa, ina sonki”. Salma ta dan yi dim,
“Na kasa yarda” Ya ce,Kin kasa yarda cewa ina sonki?” Salma ta ce,Eh” Ya ce,To me ki ke son in yi da zai sa ki yarda cewa ina sonki?” Salma ta ce,Abu uku za kayi Ya ce,Fada min su”. Ta ce,Da daidai da daidai za ka yi.
Yanzu dai ka fara sanar da duk wanda ka san kace ma ba ka sona, cewa kana sona. Shine mataki na farko” Ya ce,Hajiya tana son ganina gobe. Zanzo Zaria ki fito mu hadu Salma ta Ce,Hajiya Kaka ba za ta bari ba. Ince mata naje gurin wa?”Ya ce,Gurin Inna Ta ce,
“Kada ka koya min haka, in na iya kuma kai ma watarana in maka? Ka zo dai in ka
matsu”Ya ce,Za mu yi waya”Ta ce,
“Shi kenan, sai da safe kenan?”Ya ce,
“Za ki yi mafarkina?”- Salma ta yi murmushi, “Ban sani ba ko zan yi?”Sai dai ta ji ya sumbaci wayar kai tsaye, cikin kunnenta. Tsigar jikinta ta tashi har ta dauke wuta, ba ta san ya kashe wayar ba.
Hajiya ba ta zauna ba saboda ganin Alhaji
yana gidan. Ta yi ta aiki a kicin don son Alhajin
ya fita, sai aka yi rashin sa’a Alhajin ya ki fita,
kuma da ya tashi fita sai ya ce, Shatima ya kai
shi gidan Alhaji Nadabo ya samu Hajiya a kicin, “Zan tafi ne daga can in na sauke Alhaji, ga shiba ki ce komai ba’ Ta ce,
“Ma yi waya, ko ka zo sati mai zuwa don maganar bana son yinta a gabanshi”.
Shatima ya ce,Wai mene ne Hajiya don
Allah?”Ta ce, “Tunda yau zaka koma Abuja in ka isa ma yi waya da dare Ya ce,
“Allah ya kai mu daren. Ina son inbi in gaida Hajiya Kaka’ Ta ce,
“Na haramta maka zuwa har sai
Salma ta bar gidan, saboda ita na kunshi bakin ciki kala-kala” Shatima ya ce,
*Bakin cikin me Hajiya?” Ta ce,
‘Ban ta6a fada maka ba ka ji ba,
sai a dalilinta. Ko, wannan kadai kalubale ne ina tsoron nan gaba ma sai ka guje ni a kanta”
Shatima ya ce,Hajiya, ki kwantar da hankalinki, Ki yi addu’a kawai Ta ce Ina alkawarin da ka yi min na sakinta? Alhaji ya kwala masa kira,Babana, fito mu je mana, kace yau za ka Abuja kuma ba a
jirgi ba”Ya ce,Hajiya za mu yi wayar”.
. Ya fice cikin sauri. Alhaji ya ce,
“Ungo mika mata wannan kudin da ka bamu tayi cefane”Hajiya ta ce, ya barshi. Alhaji yace,Kuna fada ne da uban nawa ne?”
Bata tanka ba, Alhaji ya ce, “Mu je”.
Suna fita, Alhaji ya ce, “Ka yi hakuri fa Babana, na rasa abin da ke damun Mamanku Ta damu a kan maganar yarinyar nan. Yanzun ina maganar ta tsaya tunda Kaka ta ce lallai in cire bakina a maganar?” Shatima babu dama ya ce Hajiya ta gindaya mishi kalma a kan zuwa gidan, sai ya ce,Kaka ta dage sai na sake ta, kuma ni ina son matata Alhaji ya yi
“yar dariya,Ka fara sonta kenan? To kaka ta yi namijin kokari da ta sa muka san haka, da ba ta rike ta ba kila da kai ma ba ka san ko kana sonta ba ko?” sai’ Shatima ya shafa kansa, ya san Alhaji yana tsokanarshi ne, ya ce, “Ni dai da za ku sa baki matata ta koma gida Alhaji yace,Babu ruwana. Amma zan
ba ka shawara, ka je ka ce mata kana son
matarka, iyaka ta maka fada ta ba ka matarka. Amma kaki zuwa”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe