RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 14 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 14 BY HALIMA K/MASHI

 

 

 

Kaka ta fusata matuka don tana ganin

raini mai tsanani ya shiga tsakaninta da Shatima, kuma tana ganin laifin uwarsa ne, domin ita ma ta dauke Kafarta daga gidan, amma tana nan tana zaman jiransu.

Nafisa tana shirya su Ashrafzuwa

islamiyya, sai ta ji sako ya shigo wayarta. Tana

dubawa ta ga Maman Nana, gabanta ya fadì ta sani in ta ga sakon Maman Nana, to zancen

mijinta ne. da sauri ta karanta gajeran sakon.

“Yanzun na ga mijinki ya sauke Zinatu a

bakin layi, da alama siyayya suka yo, don na

ganta da ledoji, kuma shi ma yanzun zai shigo’. Nafisa ta mike cikin tashin hankali, sai taji shigowar Shatima. Tabbas babu karya, domin da leda ya shigo.-Daga irin kallon da ta yi masa ya san akwai sabuwar matsala, domin ko da suke takun saka tana yi masa sannu da zuwa, kuma tana gaida shi. Ya mika mata ledar hannunsa taki amsa ta juya ciki. Shatima ya dauki yaran yakai su islamiyya, yana dawowa inda ya bar kayan a nan ya same su. Ya dauka cikin bacin rai ya shiga.

‘”‘Kin ce kina bukatar abubuwa na siyo na

kawo sai ki watsar min a nan gurin?” Ta ce,

“Ka kai ma wadda ku ka je tare ta hada tunda kai ka yarda ka zubar min da mutunci

Ya yi shiru yana nazari, sannan ya ce,

“Sai yanzun na fahimta da ma a kan wannan yarinyar kike ta wannan haukan?”‘ Ta ce,

“Au hauka ne ma? Ai dama nasan ka santa kake yi min alaye, duk motsinku ina sani kuma na gaji zan fada ma Hajiya kila inta maka fada za ka ji Ya sani Nafisa za ta aikata, in ko ta fada bai san ya zai yi don wanke kanshi ba, don haka ya shiga raba idon inda zai ga wayarta. Saman kujera ya hango ta sannan yaje ya dauka da sauri ya nufi fita. Ta ce, “Ni ka ba ni wayata”.Bai ko kula ta ba, ya yi tafiyarshi.Da mota ya fita ya shiga layin yana

dubawa ko zai ga Zinatun, layin ba kowa sai

‘wasu matasa biyu zaune a kofar gidansu. Ya san yan layin ne, don suna sallah a masallacin nan layin. Ya same su suka gaisa, yace,Ina ne gidan su wata yarinya fara haka, mara

kamun kai?”Kafin Shatima ya rufe baki dayan ya ce,Zinatu”. Shatima cikin gamsuwa ya ce, “Ita ce, don Allah inane gidansu?”Daga nan suka kwatanto masa gidan, ya kama hanya. Babu maigadi, don haka ya yi ta

buga gidan, cikin sa°a ita ce ta nufo kofa tana

fadin,Wane ne don Allah kar a karya mana

gateTana budewa ta ga Shatima, ba za ta iya

fassara abin da ke tattare da zuwansa ba, don

fuskarsa kamar yanda ta saba ganinsa. Ta turo dankwalin kanta gaba tare da fadin, “Na sani sai ka zo har gida Ya ce,Bismilillah zo mu Ta kalli jikinta”Ban minti daya da rabi in

dauko mayafina”Bai ce komai ba ya juya mota. Har da turare ta Kara, ya dauke ta a mota tana ta kaudi.Cikin mamaki taga ya karya kwanar shiga gidansa. Har za ta yi magana, sai kuma ta yi tunanin ko matarsa ce ta fita shine ya dauko ta. Ya aje motar ya fito, sannan ya ce mata, “Fito”Ta bi shi suka nufi falon, ta shiga ta samu guri ta zauna ta dora kafarta daya kan daya. Shatima ya nufi ciki, Nafisa tana zaune bakin gado ta zabga tagumi duk abin duniya ya ishe ta.Ya shigo ya dube ta, Taso mu je” Ta mike ta bi shi babu musu. Tana ganin Zinatu ta zaro ido cikin tashin hankali,Me wannan ta zo yi gidana? Me ya kawo ta?”Shatima ya ce,Ke kina da damuwa, ki tsaya ki ji abin da ya sa na kawo ta

Ya ja kofar falon ya kulle, ya zare

makullin ya dawo ya dubi Zinatu,

“Ki fada mata alakar da ke tsakanina da ke”

Shatima ya yi maganar cikin daga murya.

Zinatu ta tsorata ta dubi Nafisa, sai kuma

ta dake ta ce,Soyayya Ya nufi kanta tamkar zai rufe ta da duka, ya ce,Da wa ki ke soyayya? Na taba cewa ina sonki?”

Ta kankame guri daya tare da fadin,

“Nike sonka Ya ce, To wallahi ko ki fadi yanda aka yi ki ka shiga motata, ko kuma in sa a Batar da ke. Daga, nan in na yi waya aka z0 aka dauke ki kin tafi ke nan!”Nan take Zinatu ta soma rawar jiki tare da rokon Shatima kan ya yi hakuri, sannan ya ce, ai sai ta fadì gaskiya. Nan ta shiga rero zantuka tana maida yanda aka yi, har zuwan Nafisa

gidansu. Shatima cikin mamaki da takaici ya

dubi Nafisa ya ce,Ai kin ba ni mamaki da har ki ka kasa shaidar halina, zuciyarki ta yarda zan

iya neman kamar mace irin wanna da kowane

Kazami ke zuwa gurinta”Ya jefi Nafisa da

makullin,Bude mata kofar ta fita”.

Ya nufì ciki rai a bace. Zinatu ta mike

cikin sauri tana share zufa, Nafisa ta bude kofar tana fadin, “Fita nan banza masharranciya*Sai da ta tabbatar ta fita sannan ta ce,Oho dai ko ba komai na gwara kanku, kuma kinci sa’a da in nayi muku wani kullin Karyar ne ki kwance shi”Nafisa ta samu Shatima tana ba shi hakuri,

ya ce Na san ajin da na aje ki daga yau kawai,

tunda ba ki bincike kike yanke hukunci”

Ya ciro wayarta ya mika mata tare da

fadin,Kina iya kiran Hajiyar yanzun ki sanar da ita sannan na gode ma Allah da ya haska min wasu abubuwa sakamakon wanna kazafin

Nafisa ta yi ta kokarin fassara zancen

nashi, amma sai ta kasa.Amna ta kalli Maman Afra, sannan ta kalli kofin hannunta, “Me ki ke nufi da wannan?”Ta ce,

“Ki amsa ki sha domin na gaji da

korafin da ki ke kawo min, ba ni da isassun

kalaman da zan ba ki shawara akan matsalolinki”.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *