RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY HALIMA K/MASHI
Shatima ya yi dan tsam, amma sai ya cije
ya ce,”Safwan ai dama wauta na yi zan ce ko
shirme? Domin sai daga baya na gane ina
mutuwar sonta, so mai tsanani”*Gaban Safwan ya fadì, ya ce,Kuma?”
Shatima ya ce,Ka yi mamaki ko? Ni
kaina na yi matukar mamaki sosai”.
Safwan ya daure yace,To kayi
gaggawar maida ta dakinta”Ya ce,
“‘Insha Allah, dama Hajiya ta ce ta rike wuta, Gashi an kunno wa Badi’atu wuta a
gidanta Wace irin wuta?” Safwan ya tari
num fashin Shatima. Nan Shatima ya ba shi labarin komai. Safwan ya ce,Kuma shi kenan an barta ta mutu a can?”Ya ce,Jiya dai Alhaji ke fada min tun a ranar su Anty Momiyo suka maido ta gida, amma wai surukar ta ce ba zasu zo ba, kuma ko wando na jariri ba su saya ba”.Safwan ya ce,Subhanallahi! Gaskiya zan sa a daure mijin Badi’atu. Ai tafi karfin cin
mutunci, ya san wace ce ita kuwa?”Shatima
ya ce,Ka barsu da halinsu,yanzun dai bari mu yi ta lafiyarta da Baby din”. Safwan ya ce,
“Yanzun zan bar Lagos zuwa Kano da zan kwana, amma na fasa, zan tafi Zaria yau dole in ga halin da Badi’atuna take
ciki?” Shatima ya ce,Allah ya kai ka lafiya”
Kamar yanda Safwan ya ce, sai kusan
taran dare ya sauka Zaria. Kai tsaye ya sa
direbanshi ya wuce da shi gidan Hajiya. Badi’atu tana kwance a doguwar kujera ta gama cin abinci ta sha magani, tana kallon talabijin Safwan ya yi sallama ya shigo falon. Badi ‘atu ta tashi zaune cikin mamakin jin muryarsh. Ya tsaya a gabanta tare da rike kugu yana kallonta cikin mamaki, bai lura da Hajiya da Alhaji da ke zaune suna
kallon talabijin din ba, sai da Alhajin ya ce,
“Safwan ne da daren nan?” Cikin mamaki ya dubi Alhaji,Garin yaya yarinyar nan ta dawo haka?”Hajiya ta miqe tare da fadin, “*Aima ta yi kyan gani, kafin a kai ta asibiti?”Safwan yace,Ai kamata yayi a ce kwance take karkashin kulawar likitoci” Alhaji ya ce,
“‘Ta yi kwana daya suka sallamo ta Safwan yace, Hajiya, ku shirya yanzun
ku koma asibiti”Ya ciro wayarshi ya soma kiran layin likitanshi, ya ce,Dokto kana gari
Yace,Ina nan”Safwan ya ce,Don Allah ga Kanwata nan za a kawo ta yanzun za mu z0 tare ne”.Alhaji ya ce,Kana ganin a kai ta asibiti
kuma don tana da magani da wancan asibitin
suka ba ta”Safwan ya ce,Alhaji kwararru ne wadannan” Badi’atu ta kasa tashi
kuma ta kasa magana don kunya, kanta na kasa ta sunkuyar. Hajiya ta mika mata hijabi da takalmi, nan da nan ana kai ta likita ya duba ta ya ba ta gado, domin ya ce, akwai ma alamun nakuda a tare da ita. Da ma tun safe ta ke ciwon mara, tana daurewa ne don ta ga yanda iyayenta suke ta kai kawo a kanta. Safwan ya tambayi likita ko me ake bukata? Ya ce,Kayan haihuwa. A daren suka tafi nema, amma dare ya yi duk an tashi, sai
dan abin da ba a rasa ba. Badi’atu ta sha wahala har gari ya waye
ba ta haihu ba, kwana Safwan yana kiran waya,amma zancen daya ne. hajiya har da kuka domin ta soma cire rai da Badi’atu. Karin abin haushi ta kira mijin ta sanar da shi, sai ya ce, Allah ya sauke ta lafiya bai ko kara kira ya ji ba, har garin Allah ya waye. Likitan ya ce, mijinta ya zo ya sa hannu za a mata aiki
Hajiya ba ta yi fushi ta sake kiranshi ta
sanar da shi, ya ce, shi kam ba zai zo Zaria
yanzun ba, gurin aiki zai tafi. Safwan da ya ji yayi ta fada a kan me Hajiya za ta kira shi? Ya tafi gurin likitan da kanshi ya saka hannu aka shiga da ita dakin aiki. An yi nasarar ciro yaron, sai dai babu rai,ya sha ruwa. Ita kuma ta sha wahala, suka karbi dan suka tafi da shi, ita kuma aka ci gaba da kula da ita. Ranar Shatima ya diro, ya ji bakin ciki
sosai game da abin da mijin Badi’atu ya yi, don haka ya kira shi ya fada masa danshi ya zo babu rai, sannan kuma lallai ya zo suna son sanin abin da yake nufi da Badi atu. Ya ce, shi kenan tunda ya zo babu rai an huta, sannan gaskiya zuwa sai in ya samu lokaci.
Hajiya da sauran mutanen da ke dakin
suka dau salati don a murya ya saka wayar.
Shatima ya kashe wayar tare da fadin,
“Lallai wannan yana da kyau a koya amsa hankali, amma bari ta samu lafiya”
Aka je aka rufe yaro. Badi’atu ta warke sarai, kwananta goma aka sallame ta. Ranar Kaka ta matsa lallai a kawo mota su je su duba Badi’atu tunda ta dawo gida. Salma dama ta jejje asibitin. Suna shiga
suka samu Shatima da matansa, har Nafisa ta zo tunda Salma da Maryama suka shiga falon suna turo keken kaka Shatima ya kashe Salma da idanunsa. Duk da hijabi ne a jikinta bai hana shi gane jikinta ya ginu ba. Kaka ba ta amsa sannun da Hajiya take yi mata ba. Ta amsa gaisuwar su Amna da su Aliya da Nafisa, har ta kama hannun Abulkhairi tana fin kai sannunka, kai ne Aminu ko, uwarka ba ta taba kawo ka na ga kalarka ba sai yau
Aliya ta yi dan yake tare da fadin,Zaizo ne kaka Ta ce,A,a ya barshi bana nemansa. A
duniya da wanda ke yinka ka keyi Tace,
“Salamatu tura ni gurin maijegon in
mata sannu, mu zo mu wuce ko? Salma ta gaida SU Hajiya da sauran
mutane. Ta ji mamakin yanda Hajiya ta amsa
mata da sauri, har ma ta yi zaton ko don ganin
Kaka ne? hajiya ta yi wa Badi’atu sannu tare da ba ta hakuri bisa abubuwan da suka faru da ita a gidan auran nata na rashin dadì. Ta kuma ba ta shawarar yin addu’a Allah ya yi mata abin da yafi zama alkhairi tare da yi mata addu’ar Allah ya
- Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe