RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 23 BY HALIMA K/MASHI
Salma ta amsa tare da godiya, suna
tafiya Salma ta mika ma Kaka kudin, Kaka ta
ce, “A’a kudinki ne naira ba zan amsa ba”?
Salma ta ce, “Kaka ina da kudi fa wanda
Safwan din nan ya turo min”Kaka ta ce,
“Ba na fada miki yanda za ayi da kudin ba? Ki ciri dari biyu a sai ma iyayenki dan fili, ko ke ba ki samu damar gina shi ba, yayanki sai ya gina. Mahaifiyarki ta wuce haya”Salma ta ce, “Ni da sai a yi amfani da sauran a tada gini ko da ciki daya ne” DA Kaka tace A’a ke maki gyara dakinki
tunda kin jima ba kya nan dakin dai kin san ba
za ki gabshi da gado Salma ta ce,To ni dai rike wannan Ta ce, Raba biyu to dubu biyar ne, don haka ta ba Kaka uku ita kuma ta dauki dubu biyu. Kaka ta ce,TO Salma yau sai a kasa bacci don murna maimakon darare da ki ka Bata cikin damuwa.Sallar da kike ta Allah ya maido miki mijinki, yau kuma sai ki yi ta godiya ga Allah”
Salma ta sunne kanta a cinya tana dariya,
Kaka ma ta yi darijya tare da fadin, “Ja’ira ina
hankalce da cewa ke ma kin kosa ki koma ga
mijinki. Amma duk da haka ga shawara, kada
ki nuna masa dokinki, ki bi a sannu, kuma ki
sani yanzun tamkar sabuwar rayuwa ya kamata
ki kafa, ki canza daga wancan zaman da ki ka
yi, kin san kowace mace da irin nata salon, ki
je da sabon salo ke mace ce ba ki bukatar sai
nace ga yanda za ki yi”.Salma ta ce, “To Kaka, insha Allahu zan kokarta” Kiran Shatima ne ya katse hirar tasu. Salma ta dubi Kaka, “Kin ganshi ko har ya ji ne?” Kaka ta Ce,Daga mana”
Salma cikin salon karya harshen da ba ta
san tana yi ba a duk lokacin da za ta yi waya da
Shatima ta daga tare da sallama, Ya amsa tare
da fadin, “Salmata ba Kaka tukunng in yi
godiya”. Ta ce,Ga ma ta nan a kusa”
Ta mika mata, Kaka ta amsa suka gaisa
yana ta yi mata godiya. Kaka ta ce, “A’a daina godiya zuwa zaka yi ka biya diyyar jinin da ka zubar mata Ya ce,Zan zo in biya Kaka, ban da aiki
da ya min yawa da gobe zan zo, amma juma’a
ina tafe”.Allah ya kawo ka”Ta mika ma Salma wayar, Salma ta tashi ta nufi cikin daki, daidai lokacin da yake fadin,
“Tashi kusa da Kaka .Ta ce, Ga ni na shiga daki”
Ya ce,Yauwa Salma, yau ina cike da
farin ciki, na san ba zan, iya bacci ba. Ina zuwa
fa zà mu dawo?Salma ta ce, “MU dawo ina?”
Ya ce,Gida manaTa ce,Sai na gyara dakina
Ya ce,Salma ai gidan gaba daya zan sa
a yi fentinsa, zan sa a gyara miki tun kafin in
dawo”Ta Ce,Zan sai sabon gado da sauran
abin da ba ni da shine da kudin nan”• Ta fada
mishi yanda suka yi da kaka.Shiatima ya ce, “Hakan ya yi”.Sun jima suna hira Shatima yana nuna zakuwa tare da kosawarsa ga kasancewarsu tare. Duk matan Shatima sun sha mamakin ganin an tashi gyaran gidan tare da gyara duk wani abu da ya lalace. Ranar alhamis Salma suka zo Kaduna ita da Yaya Hadiza da
Maryama, suka samu Salma inda wata
‘yar Salma ta yi musu jagora, Salma ta sai dan
gadonta na dubu dari da hamsin, ta sai talabijin
da karamin firji. Sai dan sauran tarkace irin
wanda ba a rasa ba, suka je suka gyara
dakunan tsaf? Na Shatima, ta sa sabon gadon ta
dora katifarshi a kai, dayan dakin ta sa kafet.
Nata gadon suka maida shi sun gyara komai
sannan suka wuce, har Sálma.
Washegari juma’a Salma gidan kitso da
lalle aka wuni, annashuwar da take ji tamkar
yau ne ranar aurenta, ga wani son Shatima da
take Kara jinsa a zuciyarta. Sai bayan juma’a
ta dawo gidan tana fitowa wanka kaka ta miko
mata wata kwalba tare da fadin, “Hura gawayi
ki zo da kaskon nan. Wannan turaren ina son ki
tsugunna a kanshi a qalla sau bakwai yau za ki
karar da shi” Salma ta yi yanda Kaka ta ce, Ramshin turaren duk ya bide jikinta. Ta idar da magriba tana shafa mai kafin a kira isha, suka ji sallamar Shatima. Nan ya zauna gurin Kaka suna hira,don ta ce Salma tana wanka. Salma ta fito cikin bakar doguwar riga da mayafinta, tun kafin ta karaso Shatima ke jin kamshin Salma na ratsa
shi. Cikin girmamawa ta gaida shi, Kaka ta ce,
ta kawo masa abinci, ya ce,Kaka na koshi, naso ne tazo mu tafi kawai?”.Kaka ta ce,
«Ku taf ina ba ta sallami Innarta ba? Ka je dai sai gobe ka zo”Ya ce,Ni ma zan kwana a nan kenan?”
Kaka ta ce, “Bana son muna musu, ka koma cikin iyalinka ka kwana, ina Kaduna ina
Zaria?” Dole Shatima ya tafi bayan ya ci abinci,
kuma yana kallon Salma bai samu damar
kebewa da ita ba. Bayan tafiyarshi ne da ma
Kaka ta hana ko rakiya ta masa, ta ce, “Ai ba ki
gama turarenki ba, kuma ka’idarshi sai kin
gama ba a son ko hannunki namiji ya rike”Washegari tun asubahi Salma ta soma
turaren, sai sha biyu ta gama. Kaka ta ce,
“TO ko yanzu ya zo sai a yi ta tafiya. Kudì na kashe a ka kawo min turaren nan’ Tunda Salma ta idar da azahar bayan sunci abinci ta sheka kwalliyarta ta sa sabuwar
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe