RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 27 BY HALIMA K/MASHI
Salma ta kalle shi da murmushi, tare da “A ce ina gaisuwa musamman ga , yarana” Kai ya daga alamun ya ji, sannan suka ci gaba da zancensu. Ya ce, a ba shi Ashraf. Suna gaisawa sai yaron ya ce,Daddy ba ka ce Momi ta daina shiga gidaje ba?”Bai jira amsa ba ya ce,To jiya ma ta
shiga, kuma ta bar mu a gida Shatima ya gane nufin yaron da ya je jiya, yana nufin dazun. Nafisa ta amshe wayar tare da dadawa yaron duka, tace, Mai surutun tsiya Ran Shatima ba ya son dukan yaranshi, don haka nan take ya bata rai, ya sake kiran Nafisa don ta kashe wayar. Tana dagawa ya ce,Ba Ashrat” Ta mika masa, yaron cikin kuka yake fadin,Daddy ta duke ni”
Ya ce,Ka daina kawo Karan mamanka,
ta fada min Ashraf ya ce, To na daina
Ya ce,To ina Babana?” Ashraf ya ce, “Ga shi nan a kan gado’ Ya ce,To ba shi”‘ Ya yi magana da su, sannan ya ce su bata wayar, ya ce ta ce su fita ko ita ta fita, don baya son magana a gabansu, dubi yanzu bai san lokacin da yaron ya ji kashedin da ya yi ma uwar tasu ba, amma ga shi ya kawo karaR Ta katse mishi tunani da cewa,
“Sun fita” Ya ce,Me ya sa ki ka fita ba tare da
izinina ba?”Ta yi shiru, ya ce,Na raba ki da matan
layin nan banan son huldarki da su, amma kin
kasa bari ko?” Ta ce,To fa haihuwa aka yi”.
Ya ce,Ko uwar wace ce ta haihu na hana ki na ce ko? Sannan kuma abu ba abu ba
ki kama yara da duka kin san ba zan dauka ba
ko? To tunda kin kasa jin maganata za ki baro
Abuja ke ma ki dawo nan, in don yara ne
makaranta ko? Zan canza musu wata”
Ta ce,Gaskiya to ni zanin gadona da
nike yi ya za a yi kum.Ya katseta,
“Wannan ba matsalata bace, domin ribarki ce babu wani abu da nike amfana daga cikin sana’arki. Kin ga don kinbar inda kike kasuwa ba damuwata ba ce, don ni damuwata in na ce a yi, to a yi. In kuma nace a bari, nan ma a bari. Tunda na lura ba damuwata ce a gabanki ba, to ki je ki yi ni nasan matakin da zan dauka”
‘ Ya kashe wayar tare da jefa ta kan kujera.
Salma ta yi tam tamkar ita yake yi ma
fadan, ta san kuma ya gama cin abincin. Ta
tashi. ta wanke hannu don ita ma tuni abinci ya
ginshe ta. Ta koma kusa da shi ta sa hannunta a
gefen kumatunsa,Yaya ka yi hakuri”. Cikin
sanyin murya ta yi maganar,Bana son
ganinka a damuwa ga shi fushin ba ya yi maka
kyau. Dan yi murmushi don Allah” Niide Ya kalli fuskarta, ta ce,Ka yi murmushi
mana yaro mai kyau”Dariya ta kwace masa, “Ni ne yaronki?” Ta ce,Ah sosai ma, ga shi nan ma ina
lallashinka””. Cikin dariya ta yi maganar,
“Zanma siyo maka fida dama kuma ai ina ba ka”.
Ya sa hannu ya rufe mata baki cikin dariya ya ce,
“Salma kin zama mara kunya ko?”Ta ce, “To ai ni don kai Da wadannan dabaru ta mantar da shi
fushin da yake ciki, sannan ta kawo zancen
Nafisa kan batun dawo da ita Kaduna,
musamman da ta san cewa in har ya dawo da
Nafisa to kila ita za ta, karatunta ya sha ruwa
tunda ya yi ta zancen da dama, shi kuma bai ki
sauraronta ba domin yana ganin cewa tana da
baiwa.Ta ce”Yaya zan yi karambani a kan
maganar Maman Ashraf, dawo da ita ba shi ne
zai zama mafita ba, kenan kana son ta tabbata
ba ta jin maganarka? Tai kuma yi ta yin abin
da zai bata mata rai kyakkyawan zamanku zal
lalace. Anty Nafisa tana sonka sosai, na tabbata
in har ka bi hanyoyin da suka kamata gurin
sulhunku za ta yi abin da ka ke so. Ban da haka
ma ai sigar. Shatima ya ce,
“Ke tunanin ki ba lallai ya zama irin nata ba. Amma ban san hanyar da take son in biyo mata ba, tundas na zauna da ita na ce mata bana son yawo Salma ta ce,To tunda wannan karon ka
yi fada sosai na san za ta tsorata musamman da
yake ba ta son dawowa sai ka nuna mata wanna shine karo na karshe da inta ketara
dokarka za ka dauki’ matakin dawo da ita nan.
Sannan ka shimfida mata dokoki ba masu
tsauri ba, na san za ta kiyaye”Shawarar ta shige shi, amma ya nuna wannan shiririta ce, don baki ya tabe tare da fadin, Wannan zancen naki ba lallai yayiwu ba, amma na san ya ya zan mata
Ko da Salma ta shiga debe kayan da
suka ci abinci Shatima mamakin baiwarta yake
yi, don in bai manta ba ita ce ta ba shi shawarar
kasuwancin da yake yi da Safwan, ya zuwa
yanzu yasan kasuwanci yana sama da aiki
Ta katse mishi tunani da cewa,Yaya
don Allah ka daina cewa sana’ar matarka ba ta
kara maka komai” Ya ce, To duk abin da yake a wuyana ina yi mata” Salma ta ce,
“Shine burgewar kowane namiji, kuma na san dole kudinta ya kare ka koda kuwa yaranka ta sai ma dan takalmi” Ya Ce,To na ji sarkin jawabi, a zo a yi
min tausa, duk jikina ya yi nauyi Ta ce,
‘”Mu je gado to yanda zan lallaba
kayi bacci yaro mai kyau”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe