DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
bakaken maganganun da ta gayawa Faruk ya
fado mata, ta tuna yanayin fuskarsa lokacin da
take gaya masa. Take ta ji wani gumi yanko mata, tuni ta yaye bargon duk da haka gumin bai bar diga mata ba tamkar wanda take labour room, duk da A.C da fanka da ke aiki amma gumi sai Karuwa yake.Kuka take shabe-shabe da hawaye,
“Yaya faruk ka yi hakuri, wallahi ina sonka! Wallahi ina sonka’Idonta a rufe suke hawaye ko sai Bul bula suke tamkar an Balle famfo.
Duk da dare ya yi amma ya kasa hakura
sai gobe ya z0 yaga Fatin, a wannan tsohon
Daren ya kamo hanya, abunka da dan gida kai
saye ya wuce dakin Fatin.Sai ya ci sa’a Kofar ba a sa mata key ba,Bude Kofar ya yi ya hango ta kwance rigingine’ a tsakiyar gado idonta a rufe, ga kuma hawaye ya wanke mata fuska,
sunan shi kawai ke fita a bakinta,. Kura mata ido ya yi, Subhanallahi!” A gaskiya ba zai iya hakura da Fati wani ya aure taba, kyan jikin Fati ba Karamin ruda shi ya yi ba,duk yadda yake tunaninta ta wuce nan.Bai san lokacin da ya isa kan gadon ba, kwanciya ya yi kan cinyarta, a hankali ya soma shafar lallausan jikinta.
“My dear please ki aure ni, wallahi ba zan
iya rayuwa da kowacce mace a rayuwa ba sai ke,
duk kokarin da na yi don in iya hada jiki da
Maryam na kasa Nan ya yi ta fadan maganganu
cikin shauki, so, Kauna da sha”awa, daga ganinshi ka ga wanda ya kamu da ciwon so.
A firgice ta bude ido cikin matsanancin tsoro
Da fargaba, ganin Faruk din bai ba ta mamaki ba kamar yadda ta ganshi kwance kan
cinyar ta yana aiwatar da abin da bata zata ba.
“Faruk kana da hankali kuwa?”Fati ni mahaukaci ne bani da hankali ko kadan, na haukace a ciwon sonki, Don Allah ki taimaka ki warkar dani, don Allah Fati ki aure ni, wallahi in ban aure ki ba ina ga mutuwa zan yi,in kuma ban mutu ba zan gwammace mutuwa da rayuwar da zan yi.
Ki taimaki dan’uwanki ki aure shi”
Ta riga data san maganar Faruk ba wasa,ya riga da ya gama haukacewa, don haka inba
dabara tai mishi ba yadda za a yi ya tashi a
kanta.Ta ce,To Yaya Faruk na ji tashi muje
falo ka ga in Umma ta z0 ta ganmu a haka zatayi fada Cikin hanzari ya tashi, “To muje Fatina,
wallahi dama na san kina sona kuma za ki aure
Ni Gaba ya yi tana binshi a baya, sai da taga
ya fita ta yi sauri ta rufe Kofar tasa key. Da karfi
ya juyo ya turo kofar yaji ta rufe, bugawa ya yi
ta yi tamkar zai Balla kofar.Kasancewar Kofar gilas tana ganin shi shima yana ganin ta, tsugunawa ya yi yana hawaye shabe-shabe.
“Fatina don Allah ki bude, Fatina rayuwata zata nakasa in bake, don Allah ki taimake ni ki bude Ita ma kukan take amma sai ta tashi ta ja
labule ta rufe. Ya yin da ya ci gaba da magiya
Fati kuma sai kuka. Umma dake daki ta fito ta samu Faruk cikin mummunan hali, don kuwa
ya dawo tamkar tababbe, sai surutai yake.
*Fatina without u life is impossible to
spend my love. I found it very tough, I can’t
even breath properly. Please do me a favour”.
Ki bude kofar nan ki z0 muje ai mana aure
Umma ta dafa shi,Haba Faruk, me yasa
baka da hakuri da kuma tawakkali?”
“Umma ya zan yi da sonta, nima ban san
ya zan yi in daina sonta ba. Umma ko kina min
addu’ar abin da ya fi alheri. kar ki min
addu’ar Allah yasa in daina sonta, don wallahi
bana so in daina sonta. Wallahi Umma ina sonta
da yawa,ina sonta sosai. Ummana inason
Fatina”Umma ita ma hawaye take na tausayin
danta, bare uwa uba Fati da ta rasa yaza ta yi a
daki, don a gaskiya yadda ta dauka Faruk na
sonta har ta wuce yadda take tsammani.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe