RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 1 BY Fateeyzah mbs✍️
Www.bankinhausanovels.com.ng
*ALHERI WRITERS ASSO.*
*A.W.A*
https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/
https://chat.whatsapp.com/FqpYwmmbahRLaZHssfLpfu
*_RAYUWAR CAMPUS_*
_(rayuwar ‘yanci)_
*_Na Fateeyzah mbs✍️_*
Fzahmbs.blogspot.com
*_Fateezah@watpad_*
_*Marubuciyar*_👇
*_Gidan nagoggo_*
*_Doctor zahrah_*
*_Yakin mata(Aure)_*
*_Kuda wurin kwadayi_*
_____________________________________
* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ *
*Page 01*
Security light din daya haska wurin ya bani damar ganin
abunda ke wanzuwa , duk girman filin dake bakin girls
hostel din nan cike yake taf da motoci na alfarma, wanda
zakayi tunanin dinner party ake awurin saboda yanda mata
keta fashion parade a wurin, ko wacce ka ganta taci
kwalliya sai kace zata red carpet, kallon agogon wayata
nayi na ga karfe sha daya na dare, wanda a
ya kamata ko wacce macen kirki da tasan darajar kanta
tana dakinta, amma sabanin nan da zaka dauka rana ce,
*RAYUWAR CAMPUS* kenan mai cike da ‘yanci, babu mai
kwaba maka ko ya maka nasiha, kowa zaman kanshi yake,
sannan kowa karatun gidansu yake biyawa.
Daga can gefen dama, ‘yan mata ne kyawawa su biyu suke
tsaye ko wacce fuska tasha smoky make up, sanye suke da
wasu fitunanni kimono wanda suka sha kwalliya da stones,
sannan ga wani uban takalmi high hill da sukasha, bakajin
komai, sun yane kansu da wani siririn gyale da yasha
stones, sai kas kas na taunan cingum da sukeyi cike da
fitsara.
Daya daga cikinsu ce ta kalli agogon hannunta tare da sakin
tsaki, sannan tace ” wallahi meena na gaji da jiran sumy,
tun tuni ta tafi taje tayi zaman ta, tana can yana kwakuleta
mu kuma ta barmu a tsaye, wannan ai tana zubar mana da
class ne duk wanda zai wuce sai ya kallemu”.
Wadda aka kira da meena tace” haba hibba kiyi hakuri
mana, kinsan in muka tafi muka barta baza taje ba, sannan
itace pass dinmu in mun dawo, kinsan securities din nan
basu da mutunci in ba wani abun kabasu ba, ba za su taba
barinka ka wuceba, kuma kinsan sumy ce kadai bata
kyankyamin su a cikin mu, ga tacan ma ta fito” ta karasa
magana tana nuna bakin wata mota kirar prado.
Kai duba nayi, wata kyakkyawar budurwace da baza ta
wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwai ba take tsaye
da wani tsoho wanda akalla zai kai shekara sittin a duniya
yana ta washe mata wawulan bakinshi, hugging dinshi tayi
tare da mai kiss, sannan ta nufo su meena, dogon wando ne
na jeans a jikinta wanda ya matseta sosai ya fito da shape
dinta na figure 8, sai wata armless top data matse ta breast
dinta, hannunta rike da kimonon ta, sannan kafarta sanye
da wani uban high hill wanda yafi nasu meena tsawo.
Karasowa tayi wurinsu, sannna cikin zakakkiyar muryarta
tace” sorry friends, wallahi sugar ne ya tsayar dani kunsan
madam dinshi na on, shine nadan taimaka masa ya rage
ruwa” ta fadi tana mai tura hannunta cikin riga.
Tsaki Hibba ta ja tare da banka mata harara sannan tace” ai
ga alamanan bra dinki tayi kasa, sai ki gyara mu tafi don
dare ya fara yi Allah ma yasa mu samu Napep” ta karasa
magana tana mai duba agogon hannunta.
Marairace fuska tayi tare da cewa” don Allah ku kareni in
gyara, kunga mutane na wuce mu”.
Wata uwar shewa meena ta yi tare da fadin” ta baya ta
rago, san da kika je wancan tsohon najadun ya matse miki
kayan cowbell baki ji kunya ba sai yanxu zakice kina jin
kunyar masu wucewa, zo badan dai halinki ba mu kareki,
kuma wallahi kar ki bata mana lokaci don nasan ana can an
fara sakin masu zafi”.
Bubbude kimononsu su kayi suka rufa mata, dukkansu
shigan dogon wandon jeans ne a jikinsu da armless top
kamar yanda sumy tayi, cikin kankanin lokaci ta gama
gyarawa, sannan tace musu “muje na gama”.
Ba tare da sun tankata ba suka gyaygyara sannan suka dau
hanya, suna tafe ba wacce ta tanka ma ‘yar uwarta, sai da
suka kawo dai² building din S.U.G (student union
government), sannan sumy tace” wai naga kuna karawa
gaba, ba zamu kira salma bane”.
Yatsina fuska meena tayi tare da cewa” tace baza taje ba,
don yau suna da meeting a S.U.G karfe sha biyu, inaga ma
anan zata kwana in an gama meeting din”.
Wata dariya sumy ta kece da ita sannan tace “shegiya
salma, kice yau su presido zasu kwashi gara, don dai nasan
baza su barta haka ba”.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa” kuma dai kunsan Salma
taxi no garage ne, bata gamsuwa da namiji daya, tafi so taji
kamar uku akanta, shi yasa ni ban sata akaina don ko wani
gaja salma bi take”. Ta karasa tana mai yatsina fuska.
“Shi yasa in akayi hutu take shan wuya, kinsan gidansu
kulle ake musu” cewar meena dai² sun karaso bakin gate
din fita daga makarantar.
Daga gefen gate din, wani matashi da zai kai shekara
hamsin da uku,wanda yake sanye da uniform din security
yace” Allah ya tsare kannina, a dawo lafiya”.
Hada baki suka yi wurin Amsawa” Allah ya yadda
yayanmu”.
Bakin gate din a cike yake da motoci wanda suka sha bakin
tint, kasancewa ba a barin mota mai tint shiga.
“Shegiya Rufy ashe ta dawo” cewar sumy tana nuna wata
‘yar duma² da ta fito daga cikin wata camry.
Meena ce ta murmusa tare da fadin” Ai Rufy ta ji dadi
wallahi, saurayin nan nata na ji da ita, tun level one fa suke
tare, amma kinga har yanxu tare suke runs dinsu”.
Hibba ce ta yatsina fuska tare da cewa” Don Allah kubar
wannan maganar, in mun dawo kwa dasa, kuzo mu nemi
napep sha biyu fa tayi”.
Tare napep sukayi tare da fada masa wurin da zai kaisu, ba
tare da sun tsaya ciniki ba suka shige, mai napep ya ja.
A can bakin hostel kuma, securities ne kebin kowacce mota
da sunan koransu, saboda sha biyu tayi, wanda shine
lokacin da Dean yabada domin kulle hostel tare da koron ko
wanne student dake bakin wurin, sai dai abunda zai baka
mamaki shine yanda maimakon kora sai dai karban kudi da
sukeyi a matsayin cin hanci a wurin masu mota da student,
wanda in ka bada ka zauna, in kuma baka bayar ba, ka kara
gaba.
A bangaren su Sumy kuwa, sabon gari suka nema, inda mai
napep ya saukesu a kofar club din *BUBBLE PLUS* ba kajin
komai sai tashin disco, sallamar mai napep sukayi tare da
bashi dubu daya, haka ko ya wuce yana mai sa musu
albarka tare da neman musu shiriya wurin Allah, don duk
wanda/wacce ka gani a wurin yana/tana bukatar Addu’ar
shiriya.
Tsayawa sukayi a kofar wurin tare da cire kimonon jikinsu
da gyale, Suka ajiye a wani boxes da akayi don ajiye
muhimmin abu, nan danan kamannin su ya sauya zaka
rantse irin karuwan nan ne na kudu, domin bazo da kitson
attach din da suka yi har gadon bayansu, sannan suka
kutsa kai cikin wurin.
Katon hall ne, wanda akayi decoration dinshi da yadi black
and red, sai kujeru leather seat, da taburan roba, sai bulb
din wuta mai kala² wanda sai wal wal yakeyi, daga hannun
dama kuma giya aka jera akan tabur kala kala yayin da
saman gurin aka rubuta *BAR* da manyan baki.
Gaba daya wurin Ya mutse yake da maza da mata, yayin da
wasu ke rawa, wasu na shaye² dangin su giya, codien da
shisha, wasu kuma suna rungume² da shafe² , gashinan
dai abun ba kyan gani, don duk matan wurinnan babu mai
sanye da wata sutura ta kirki.
Suna shiga kowacce ta kama gabanta, yayin da sumy ta
nufi bar, Hibba ta nufi masu rawa, sai meena da ta ke kutsa
kai cikin jama’a, tana tafiya kamar mai sanda.
Sun kwashe kusan awa daya da rabi a wurin sannan naga
Hibba da meena sun nufi wurin sumy wacce ke zaune a
*bar* tana busa shisha, dago kanta tayi ta kallesu yayin da
idonta yake jajawur, kyafta ma juna ido sukayi, take sumy
ta taso ta nufosu tana tangadi, saurin kama ta sukayi suka
nufi waje.
Napep suka kuma tarewa inda Hibba tace mai” Eleganty
zaka kaimu, basu jira cewar shi ba suka shige.
*Don’t miss any single page*
*_Fateeyzah mbs_*✍️