RAYUWAR MU A YAU CHAPTER 2
Wannan saurayin mai suna Ammar na hango zai shiga ciki shopping mall hakan yasa nabisa da sauri saboda kar ya b’acemin yana shiga naga ya yi gurin turaruka yana zubawa cikin kwan don shopping turaruka yake zubawa masu tsada kamar bai san Ciwon kud’iba chan kuma na hango waenan ”yan matan Suwa suna dibarkaya sun kusa awa biyu suna ebar kaya sai chan naga sun nufi gurin biyan kud’i kafin nakaraso har sunbiya kud’in sunfita haka na ringa binsu abaya har naga gidan da suka shiga gida ne babban gida da kuma ya ansa gida gida ne gari guda gakuma sojoji birjik suna gadin gidan ban samu da mar shigaba sana dawo da zummar gobe insha allah zan koma..
Chan kuma fannin su Salmeert Mama ta anso garin harta fara tan kad’an tuwon mama tace ”Salmeert kawo aikin kije gidan kawunki Aminu kice nace dan Allah yataimakamin da dubu biyu zanja jari insha allah zan mai da mai kud’in”
Haka Salmeert ta d’auki hijabinta ruwan milk tasa wada sai karatse da Allah ruwan kasace tsabar dati
Haka tafita tana tafiya tana tunani har tafito titi ta tsallaka gidan kawunta tagayamasa sakon mamarta
Ba musu ya d’auki kud’in ya bata saboda yana matukar tausayinsu tun da wannan eftila’iln ya rutsa dasu na garin yola suke cikin wani hali sukakoma abin tausayi gashi sunyi rashin uba gidan da suke cikima na hayane …
Washe gari.
NA koma gidan su Ammar domin naga wata wainar ake toyawa sai
Gidane babban gida da narasa ta ina zanbi saboda girman shi dakuma part_part d’in da ke da’akwai
Natsaya Ina tunani sai naji karar horn d’in mota ena juyawa naga ashema Ammar ne kawai sai nabi bayan shi muka shiga wani part wan da yafi kowa ne part tsaruwa agidan da muka shiga part d’in sakin bakinayi da hanci ena kallon tsarin part d’in da zamu eyakirada aljannar duniya dumin babu ceka dai babu cikin falon chan ena kalle kallena idona tasauka akan wata hamshakiyar mata tana zau na cikin wata luntsimaimir kujera tad’aura kafa d’aya kan d’aya tana ganin Ammar naga tasaki fara’a tanace your welcome son sannu da dawawo sai yan zu Ammar yasamu guri kusa da eta ya zau na yana kwantawa saman cinyarta yana kwabe fuska rinta shagwababun yara yace “washhhhh momma I’m tried” tace “sannu son bari nasa Ameera takawoma ruwa da abinci” takwallama Ameera kira tace kawowa yayanku abinci da ruwa ba’ajimaba sai ga Ameera d’auke da wani d’an madaidaicin tray d’auke da abinci da lemo ta’aje gaban shi tana kallonshi tace yaya ga abinci wata irin uwar harara yawatsa mata yana yamutsa fuska yace “barnan kona mammareki “aidasauri tabar gurin tana kunkuni kasa_kasa
Tashiyayi yanacin abinci suna hira da momma d’inshi
Sukaji sallama dukansu ansawa sukayi suna kallon maishigowa fallon
Alhaji nasir mai dala neyashigo d’akin yakali Ammar yana cewa “kai baffan kayadawo amma bakaje gaishe shiba maiyasa? yace sorry Daddy yan zu dama zan je abinci natsaya ci….