💖RAYUWARMU AYAU 💖💖💖💖💖💖💖
Story& Writing
By Salmeert (Autar Mama, Yar lelen royal star🧚♂️🧚♂️🧚♂️)
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
“`MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊAN TARWA GAMIDA WA’AZANTARWA HUNMM WANI ABU SAI ROYAL STAR’S WRITE’S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITTE’S EVER💖 “`
*ALƘALAMINMU ƳANCINMU*
(Bisimillahir rahmanur’ rahim) zanfara wannan litafinawa dasunan allah mai rahama mai jinkai..
Shafi na 1_2
Free page
Wata yarinya nahango wace ba zata wuce shekara goma zuwa sha uku ba kyakyawa amma balalle ne kai ya gane kyan da take da shiba saboda yan da wahala da tashin hankali da kuma talauci da suka samu gurin zama ajikinta Salmeert kenan wadda RAYUWAR MU ta YAU tajuya masubaya
Wani gida na hango tashiga Wan da gidan kallo d’aya zaka masa kasan ma zau na gidan bak’aramin talauci sukedashiba Wan da akallon gidan kadai Zaka gane cewa basu da abinci yau bare na gobe.
Wani matashin yaro na hango mai ji da naira da mulki da kuma kud’i kyakyawa ne ajin farko sai dai ba shi da yawan fara’a Ammar Kennan soja maraimari daga nesa yana tsaye bakin wani shopping mall da alama dai shiga zaiyi ciki shi da wasu yan mata guda biyu Ayshat da Ameera kennan..
Salmaeert na shiga gidan naga tashiga wani d’aki da ko labulen arzik’i babu sai buhun siminti da sukasa amatsayin labule sai wata yamulalliyar tabarma dake gefe da wata mata take zau ne sama wada kallo d’aya zakamata kaga muguwar kamarda sukeyi da Salmeert da hakan zaisa ka gane cewa mahaifiyarta ce da sauri matar ta ta shi ta tarbo Salmeert jikinta narawa tanacewa “Yar albarka ya baki” Salmeert taduk’ar da kai tayi kasa tace “Mama bai bayar ba” matar tasaki salati tace bari naje gurinshi da kaina killan Allah yasa ya bani” matar tafita ta d’auki wani yalolon gyale tayafa akanta Wan da bashida maraba da tsumma tafita taje gurin mai shagon dake kusa da gidansu tace “Assalmu alaikum Malam Bala na Aiko Salmeert gurinka tace wai ba zaka bani garin ba dan Allah kabani zuwa anjima insha Allah zan kawoma kud’in da kaina” wani ban zan Kallo ya aiaikamata da shi yace “Hadiza da kikazo da kanki k’wata za kiyi koko? ta sadda kanta k’asa tana hawaye “Aa Malam Bala ba k’wata zan yiba amma dan Allah dan Annabi kabani Wallahi anjima zan baka kud’in” Malam Bala gani hawaye a idonta saiya karya masa zuciya yace to shikennan zan baki amma kikawomin kud’ina anjima edan bahakaba ba zan kara baki kayanaba ta dago kanta da sauri tana murmushi tace “nagode Malam Bala..