RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

               WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

MUN TSAYA 

Sultan ne zaune a Katon dakin taron gabansa kudadene masu yawa, a cikin wata ‘yar akwati. Ya kafe kudin da kallo yana sauraren jawabin manya-manyan mutanen da suke son a kashe wani Case wanda shi yake jagoranta, haka yaga da damar da zai iya kashe Case din, Ogansa da kansa da suka shaKa masa kudi, ya amince za su wargaza Case din musamman yadda yake shirin taba mutuncin su. Yanzu Sultan ne ya rage, duk da suna tunanin Ogansa ya isa ya gaya masa ya ji, amma da Ogan ya yi masu bayanin wanene Sultan sai suka tsorata ainun, don haka suka yi shiri sosai, sannan suka tunkare shi. Kalaman Nasreen sun taimaka masa Kwarai wajen sake cusa masa tsanar damin kudaden da suke gabansa, “Allah ya makantar da kai daga haramun.” A bayyane ya ce, “Ameen Nasreen.” Ya dube su sosai yana nazarin su, “Gaskiya ba zan karbi kudinku ba, wai don kawai ina son in faranta maku in Kuntatawa wasu. Allah ya riga ya amsa addu’ar matata ya nesanta ni ga Haram, ya makantar da ni ta yadda bana iya ganin kudaden da ke zube a gabana. Ku yi haKuri gaskiyata ta kawo ni kujerar nan, bana jin abinda ban aikata, tun ina Karamin dan sanda ba, zan iya aikata shi a yanzu da nake jin kaina na kai. Ku yi hakuri mu bi wannan case din a hankali har mai gaskiya ya yi nasara, amma ba ta wannan hanyar ba. Ina da abubuwan yi a gabana, ban yi tunanin wannan dalilin ne zai sanya a

ZAMU TASHI 

raboni da iyalaina ba, da babu abinda zai sa in fito.” Sultan ya ture kudin gefe guda ya mike ya sara wa Ogansa sannan ya juya Zai fita.

Muryar Ogansa ya ji a tsakiyar kansa yana cewa, “Sultan kana da taurin kai, kana da kafiya. Ban san yadda kake yi da iyalanka ba, Ka kwantar da hankalinka, ka ceci rayuwarka da ta iyalanka ka amsa wannan maganar. Ina sama da kai, na baka umarni ka ki bi, mutanen nan shuwagabanni na ne, sun bani umarni ni kuma na baka, amma saboda taurin kai kaqi kallona a “ matsayin Oganka. Shin haka dokar aikin mu ya ce? Ka da ka yi wa Oganka biyayya?” Sultan ya dinga kallonsa wani iri, haka kawai yake jin kamar ya make shi kowa ya huta, “Sorry Sir! Dokar aikin mu ya ce in yi maka

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
biyayya, a lokaci guda kuma ya hore mu da kada mu ci hanci, har ya tanadi laifi mai tsauri ga wanda ya yi hakan. Ni ba Barawo bane, bare kudin haram ya burgeni. lyalaina kuma idan ina numfashi babu wata barazana da za ta firgita su, akwai kariya daga Allah, haka ni ne bangon su. Bana tunanin akwai barazanar da za ta sanya idanuna bude wa akan Haram. Kai ma kuma kaji tsoron Allah, domin,,,,,,, talakawa ne ba wakilcin shaidan aka turoka ba Ogansa ya daga hannu cikin bacin rai zai mari Sultan, fuskarsa dauke da murmushi ya riKe hannun Ogan yana yi masa wani shu’umin kallo, sannan ya watsar da hannun ya daure fuska a lokaci guda yace “Aiki nayi na sami wannan matsayin ba siyan kwalin nayi ba, haka ba ta sama na biyo ba, training na shiga nayi kafin insanya unifoam. Ba Karamin jarumi ne zai iya sa hannu a jikina ya zauna lafiya ba. Ka da ka ‘sake gigin taba tsaftataccen jikina, yin hakan zai jawo maka kuskuren da babu shakka sai ka cire wannan kakin da kake taKama da shi. Ba a fada da ni a ci riba. Ina fatan za ka rufa wa iyalanka asiri da rayuwar da kake yi a lullube cikin Kazantar haram ka fita a cikin sabgata.” Ogan bai yi mamakin dukkan irin taurin kan da Sultan yake da shi ba, domin kuwa kowa ya san shi, kaifi daya ne. Mutanen suka yi shiru suna dubansa cike da tsoron lamarinsa.Sultan ya fice abinsa, hakan ya sa daya daga cikin mutanen ya ce, “Haba Me zai sa ka yi masa haka? Mutumin da ya kamata ka lallaba shi? An gaya maka irin wadannan mutanen barazana tana damun su ne? Baka gansa a tsaye ba? Ai mammakeka zai yi ya karya ya watsar. Ya zama dole a bi shi a hankali maganar fushi ba namu bane. Yanzu dai a daga masa Kafa zuwa kwanaki biyu mu ga abinda Allah zai yi. Sultan yana dawowa gida ya zauna a nan falon yana cire safa, yana gama wa ya fara cire maballin rigarsa ya rintse idanunsa yana Kara gode wa Allah da irin ni’imar da ya yi masa wajen guje wa haram. Hafsat ta fito idanunta jajir. Allah ya dora wa yaran Hajiya Salma wani irin sonta, da kuma shakuwa da ita. Musamman_, ma ‘yar auta Hafsat. Sultan ya kafe ta da idanu yana neman Karin bayani. Ta yi masa sannu da zuwa bai amsa ba, ta ci gaba da cewa, “Anti Zakiyya ce ta sa ruwan zafi a hanya wai saboda Nasreen ta tsoma Kafafunta, shi ne Umma ta sa Kafafun ba tare da ta sani ba, yanzu haka Umma tana can Kafarta ta saBule.” Ta Karasa da wasu WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG hawaye. Sultan ya sake kallonta cike da mamakin dalilin da zai sa Zakiyya ta ajiye ruwan zafi saboda Nasreen. Mike wa ya yi cikin fusata, ya tabbata yau abinda zai hana shi kakkarya Zakiyya sai ya ganshi. Nasrecn ya ci karo da ita a bakin Kofa tana rike da hannunta da ke dauke da gocewar Kashi. Yanayin tsayuwarta kamar wacce take iya kallon komai. Sassauta bacin ransa ya yi yana gudun kada ya sake ji mata ciwo. Hucin alamun wucewarsa ta ji, hakan ke tabbatar mata da sai ya aikata abinda ya yi ninya akan Zakiyya. Kara ta sanya ta riKe hannunta , tana fadin “Wayyo hannuna.” Ba Sultan ba, hatta Hafsat sai da ta Karaso wurinta tana riKeta. Sultan ya kama ta, ya kai cikin daki yana mata sannu. Hankalinsa yana kan Zakiyya ji yake kamar za ta gudu kafin ya Karaso. Rike hannunsa Nasreen ta yi hakan ya sa ya dan dube ta, “Nasreen sakar min hannu ina zuwa,” Hannunta ta kai Kirjinsa tana Karasa cire masa maballin riga idanunta cike da hawaye ta ce, “Idan ka yi fushi kada kayi magana, domin kuwa ba kai bane shaidan ne. Fushin da ka yi shi yasa ka watsar da ni, har na sami wannan matsalar, kayi wa Anti Hafsat duka wanda daga baya ya zame maka danasani. Me kake zaton zai ci gaba da faruwa idan har baka iya kaucewa irin fushinka ba? Me kake tunanin zai ci gaba da faruwa idan har kullum sai kayi fushi ka aikata barna daga baya ka dawo kana danasani? Hannunka ba shi da kyau, ko yaya ka taba mutum sai ka ji masa ciwo mai wahalar warkewa, da za ka daure ka nema natsuwa a daidai lokacin da kayi fushi da baka zabi wannan hanyar a matsayin hanyar daukar mataki ba. Anti Zakiyya matarka ce, idan ka daki Kanwarka kana nufin har matanka ma dukan su za ka dinga yi? Gidanka cike yake da ma’aikatan da suke aiki a KarKashinka, idan suka ji ihun matarka, shi kenan sunanka ya lalace, yadda kake da zafi a Office har a gidanka ma zafin gareka, dukan matanka kake yi. Daga nan duniya za su fara yi maka addu’ar yadda kake dukan ‘ya’yan wasu haka za a daki naka, saboda ba su san dalili ba, haka kuma babu uzuri ga mai iya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG dukan mace. Na yarda Anti Zakiyya ta yi kuskure, amma banda mu da muka sani waye zai je waje yana gayawa duniya dalilin dukan da kayi mata har a saurare shi?” Hannunta ta tura a cikin rigarsa tana murmushi, “Idan ana son a Kuntata min a zagar min miji. Idan aka zageka ji nake kamar in cire zuciyata daga jikina in huta da radadin da nakeji. Ka sauya hanyar hukunci, amma banda duka, idan kana dukan wata ina kallo, ina jin dadi watarana kaina za ka juya, saboda ina da tabbacin dole watarana insaba maka. Duk dan adam tara yake bai cika goma ba. Kayi mata haKuri don girman Allah, kayi mata nasiha ne a maimakon duka.” Sultan ya dade yana duban Nasreen, yarinyar a haka kamar ba za ta iya furta magana mai tsawo ba, amma dubi yadda take tsara kalamai daya bayan daya ba tare da ta ci tangarda a hanya ba. Ji ya yi kamar ankwashe masa. bacin ransa, idanunsa sun bude haka ya janye maganar dukan da ya yi niyyar ya yi mata, sai dai fa za ta sha fadan da sai ta gwammace ya daketa din. Hannunta ya kama saboda abinda take yi masa yana jinsa har tsakiyar kansa, “Nasreen na gode da tunatarwa. Amma kuma dole zan dauki mataki akan Zakiyya. Bata jin tausayinki ne? Kina dauke da lalura sai ta Kara maki wani? Idan na Kyale Zakiyya gobe rushin wuta za ta samo ta sanya maki akan hanya. Wallahi makantar nan naki yana damuna, ko jiya na kira Al-amecn akan matsalar nan.” Fuskarta tana nan manne da murmushi tace “Duk duniya babu wanda ya isa yayi wa bawa abinda Allah bai rubuto ba, ka Kaddara Allah ya rubuta sai hakan ya faru. Ni dai ka zauna kusa da mi har sai ka sami natsuwar zuciyarka WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG sannan sai ka fita, bana son aikin danasani.” Yadda ta marerece tana maganar abin sai ya burgeshi. Ya manna mata sumba a gosh yace“Ko a yanzu zuciyata fes take. Ganinki kadai yana faranta min rai, bare har inzauna kusa da ke inshaki daddan Kamshin nan mai rikita ni. Shi dai Jafar din nan ya huta, yana kuma taimakon ‘yan uwansa maza sosail, musamman yanda yanzu mata kuka lalace da Kazanta, wata kuma ga tsaftar har tsafta amma babu Kamshi, kin ga babu mace kenan.” Nasreen ta dan shiga duhu, don haka ta ce, “Ban gane ba? Waye kuma Jafar?”
Sultan ya shafi gashin kanta ya ce, “Na Je gidan Yumnah nabi diddigin Kamshin nan da laushin fatan da kike dauke da shi, duk ta yi min bayani. Yanzu haka idan naje Kaduna gobe insha Allahu zan biya ta Zaria din, don na kira shi a waya ya tabbatar min zan same shi, amma matsalar akwai mutane sosai ne a shagon. Kin ga idan naje Zaria, akwai wata ‘yar uwar abokina Hauwa’u Dan Borno ita zan aika ta siyo min komai. don naji an ce Fatima Dan Bornon ma nan take siyayyan su Humrarta.” Nasreen ta ji dadi sosai, haka za ta so ta je wurin idan idanunta sun bude, Kila ta samu ganin Fatima Dan Bomo a wurnin tana da tarin tambayoyin da ta tanada za ta yi mata, haka ta amince da ingancin kayan Jafar, da ke sabon garin Zana. Tunda har su Fatima Dan Bomo suke zuwa siyayya a wurin, uwa uba ita kanta ta yi amfani da kayayyakinsa ga shi duk ta sauya, kamar yadda ta ji mijinta yana fada. Bata son ta nuna zumudinta ya tambayeta ina ta santa? Domin bai san ta yi karatun littafan Hausa ba. Firgigit ta yi, a lokacin da ta ji anjawo babbar yatsan Kafarta, ta ce ‘Wash! Za ka karya ni ne?” Mikewa tsaye ya yi yana son fice wa, “Ina na isa inkaryaki? Idan na karyaki wurin wa zan je in sami natsuwar barci?” Cike da zolaya ta ce “Wurin Anti Zakiyya.” Har ya buda baki zai ce wannan Kazamar? Sai kuma ya tuna idan yaci gaba da nuna rashin mahimmancinta  Za ta iya raina shi, don haka ya wuce kawai yana cewa, iyya lallai ‘yar yarinyar nan ta yi baki kwana biyu, amma na kusa rufe bakin nan.” Kai tsaye wurin Umma ya ‘ shiga, bai yi zaton Kunan har haka ne ba, don haka ya ware idanunsa yana jin zuciyarsa tana WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG jagulewa, da Karfin nasihar Nasreen ya daidaita natsuwarsa. Duk da haka sai da ya dubi Umma
yace, “Umma sai na hukunta Zakiyya.Umma ta dube shi cike da takaicin yadda ya je wurin Nasrcen ya kuma dade a wurinta, a maimakon ya fara zuwa ya dubata. Ta ce, “Babu abinda za ka yi mata dan rainin hankali. Ni za ka . raina? A ce maka matsala ta same ni shi ne ka wuce ka fara duba Kanwar uwarka ko?” ;
Sultan ya yamutsa fuska, ransa ya sosu Kwarai, sai dai wacce ta isa ce take magana a gabansa, don haka ya KasKantar da kai, ba shi da abinda zai iya kare kansa. “A yi hakuri Umma. Ina ganin Hafsat ta shirya ki mu je a kaiki babban asibiti.”
Umma ta tabe baki tana yi masa wani kallo hadi da girgiza kai, “A’a bawan Allah ni kuma a wa? Ka duba tsaf ka gani, an duba min Kafafuna har ansa magani, don haka kaje ka dauki makaunoya ka kaita babban asibiti a bata lafiyar idanu, ba ni Salamatu ba. Ka tashi ka ba ni wuri.
Ina nan zan sa ido idan ka san ka cika mara kunya in sake ganin Kafafunka a hanyar dakin Nasreen wai ka je dubata. Na gama kula ka raina ni sosai, saboda ina zama a gidanka ina kuma yi maka dariya.Sakaran namiji, yarinyar da ka rena da hannunka yau ita ce kake jin tsoron ka batawa, kake yi mata biyayya, ka zama sai yadda ta ce da kai. Ka zama mijin tace.”
Sultan ya shafi kansa yana jin bakinsa yana masa daci. Ya ce, “Umma kiyi hakuri. Gobe naso zuwa wajen Abba, amma tunda ba ki jin dadi zan bari ki warware tukun.” Umman ta saki baki tana duban danta, wato ba zai tanka wa maganarta ba, sai dai ma ya sauya wata magana. Ajiyar zuciya ta yi, tana son Sultan ya je ya binciko mata gaskiyar lamani, don haka ta ce, “Ina ruwanka da jin sauKina? Ko ka zauna baka tafi ba, ai goben fice wa za ka yi a gidan sai an ganka. Goben ka kama hanya ka tafi ina son jin gaskiyar abinda ke faruwa, kaina yana cikin duhu Sultan. Idan mahaifinka ya yi hakkun ai na kusa dawowa. Ni da nake son ka raba matanka, Nasreen mu koma Kaduna da ita, Zakiyya ta zauna a nan, saboda idan daya tana Kaduna zamu dinga ganinka sosai.” Sultan da yaji kansa ya yi mugun sarawa, ya kafe muahaifiyarsa da idanu babu ko Kyaftawa. Umma ta dube shi da mamaki, “Lafiya kake yi min irin kallon nan? Ko ba za ka bari Nasreen ta koma Kadunan bane?” Sultan ya mike ba tare da ya iya furta koma ba, yana jin lallai a wannan karon Umma sai dai ta yi haKuri idan ma za ta tafi da daya sai dai ta dauke Zakiyya. Ya so Kwarai ya koma dakin Nasreen sai dai gargadin Umma yana nan maKale a kansa, don haka ya koma falonsa ya kwanta shiru a dogon kujera. Yana son zuwa Kaduna da Nasreen, amma yasan hakan ba mai yuwuwa bane.
Zakiyya ce ta shigo falon cikin zuciya ya mike kamar zai mareta, suna hada idanu gabansa ya fadi da WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG Karfi. Kokarin addu’a yake yi, amma hakan ya gagara, kamar an riKe bakinsa da cingam. Zakiyya ta ci gaba da yi masa gizo tana sauya masa daga macen da ya tsana, zuwa macen da yake jin sonta yana ratsa shi. Haushinta da yake ji gabadaya ya kau. Bai san lokacin da ya mika mata hannunsa ba. Kamar jira take ta kama hannun tana jifansa da wani shu’umin murmushi. – Ya kasa sarrafa kansa, ya rasa me ke shirin faruwa da rayuwarsa. Ko ma mene ne » mahaifiyarsa ta taimaka Kwarai wajen wannan aikin. Haka ta kama hannunsa suka shiga daki. A ranar sai da dukkan Karfinsa ya Kare wajen Zakiyya, ya sha wahala fiye da tunaninsa. Haka ya kasa ko da motsawa. Ita dai Nasreen ko da ta ji shiru bata damu ba, saboda ta riga ta san da wahala Umma ta sake barinsa. Duk da zuciyarta tana gaya mata sai ya san yadda zai yi ya shigo. Shiru-shiru babu Sultan babu dalilinsa. Tun tana iya jurewa har hawaye suka fara aikin su. Har bayan Sallar isha’i babu wanda ya sa Sultan a idanunsa. Umma ta gaji ta aika Hafsat ta dubo shi. Hafsat tana shiga sashensa ta tsaya tana Kwankwasa Kofa. A lokacin Nasreen ta fito falo, haka itama Umma tana zaune da Kafarta, tana addu’ar Allah yasa lafiya Sultan bai fito ba, gaba daya ta shiga damuwa. Hafsat ta jima a tsaye, sannan Zakiyya ta bude Kofar ta tokare tana dubanta sama da Kasa. “Lafiya kike Kwankwasawa mutane Kofa?” Mamaki yasa Hafsat Kare mata kallo, sannan ta ja tsaki ta ce, “Malama ba wurinki na zo ba, gun Yaya na zo.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *