ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE END by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE END by Sumayyah Abdul-kadir

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Fa’iz ya ce, “Hajjah me ya sami wayarki ne? In an bugo bata shigowa”.

Ta ce, “Kai don Allah rabani da wayar nan, kubi ku ishi mutum da kararraki, ko sallah yake ba zaku barshi yayi ta cikin nutsuwa ba. Ku dai ku kira mutum kiranma maras dalili. Na bude na cire batirin don ku kyaleni na huta ku da ubanninku da uwayenku”.

Yayi dariya ya ce, “Haba Hajjah, ai muna jin muryarki cikin koshin lafiya dadi muke ji musamman in muna nesa. Hankalin mu na kwanciya mu cigaba da fafutukar rayuwa cikin kwanciyar hankali Hajjah”.

Hajjah ta ce, “Idan ta zama dole ku kira Barau, sai ya kawo min muyi maganar a tashi amma ni ba zan iya ba. Tunda na cire batirin nan na jefa bayan gado kunnuwana suka huta na samu nutsuwar gabatar da ibadu na”.

Ya ce, “Talbijin fa? Don me ba’a kunnawa alhalin abar taya hira ce? Kina kallon mutane koyaushe suna gilmawa kina kuma jin muryoyin su yafi zama shiru”.

Ta ce, “Rediyo na ta isheni, in murdo tashar Kaduna in koma sashen Hausa na BBC, duk abinda ake fadi ina ji na kuma san ‘yan uwana ne Hausawa Musulmi ba wadannan jajayen fatar da ba jin me suke fada nake ba”.

Da alama ta bashi dariya amma bai yi dariyar ba, ya ce.

“Shi kenan Hajjah, yadda kike so haka za’ayi”.

Ta ce, “Yo dama mana? Ayi ba yadda nake so din ba a gani in zan yarda, ga jikoki ashirin, tattaba kunne goma sha biyar, kullum suna zagaye dani muna hirarmu, kuje ku ku kadai nake jira ku karo in roki Ubangiji na Ya dau raina haka. Duk wani burina da na marigayi na cika shi,  da taimakon Allah da taimakon babanninku ‘ya’yan albarka, wadanda har yawun bakina ya bushe ba zan daina sanya musu albarka ba. Bana jiran komai sai fatan cikawa da imani”.

Ta mike cikin dafa bango da taimakon Ya Fa’iz, ta nufi uwar dakinta tana fadin.

“Yau tunda na tashi da safe jikina yake bani zaki zo gareni Fa’izah, don haka na sanya aka yi miki dambun naman kaza cikin katuwar samira, aka kuma yi miki gashin naman rago irin yadda kike so da ruwa-ruwanshi, yana nan cikin magashi (oven) bude ki dauko, dambun na kai daki na boye don in Na’ibi ya shigo ya gani sai ya kwashe rabi”.

Ina dariya cikin jin dadi na ce, “Allah ko Hajjaty? Sakallahu khairan”.

Ta dakata a kofar dakin nata tadan yi murmushi.

“Irin wanda nayi miki ranar kamun ki, ranar da kika ja kafa kika gujeni baki kara  waiwayata ba”.

Tausayin Hajjah ya kamani, na mike na bita na amso dambun cikin samira. Muka zauna a tare a gefen Ya Fa’iz mun sanyashi a tsakiya, na bude na diba na kai bakina ragowar nace.

“To bude wawulon bakinki in zuba miki”.

Ta bude bakin tana dariya na sanya mata lomar dambun naman mai dadin da baya misaltuwa.

“Nayi-na yi kimanta kin ki ko Hajjaty? Ni fa ban gudu na barki ba, naje inga Momi ne”.

Ta harareni ta ce, “Nono kika je sha ba ganin Momi ba”.

“Kenan baki yafe min ba Hajjah? Baki yarda kuskure ne ba? Idan baki yafe min ba Hajjah ina zani? In samo irin sanyin da nake samu a cinyoyin ki? Baki yarda ina son Hafizin ki ba kamar koma fiye da yadda nake son kaina? Yaya Fa’iz don Allah ka fada mata ‘how much I love you'”.

Dauke kai yayi ya cigaba da danna wayarsa kamar bai san bikin da muke yi ba. Wani tunani yazo min, ya zanyi in goge wannan tabo a zuciyar Hajjah na cewa ina son Hafizin nata yanzun? Wata zuciyar ta ce.

“Show her in another way”.

Sannu a hankali na tashi daga mazaunina na koma gaban Ya Fa’iz. Na zube gwiwoyina na sumbaci goshinsa zuwa labbansa, sumba mai tsayi da zurfi. Ya bude ido cikin barazana yana zazzare su.

“Ke Fa’izah, meye haka? A gaban hajjahhh?”

Hajjah ta fashe da kuka, wanda a cewarta, “Na farin ciki ne”.

“Na yafe miki Fa’izah, Allah Ya yafe mana baki daya”.

Muna takawa a hankali a harabar gidan zuwa bakin mota, Hajjah a tsakiyarmu ta yo mana rakiya muna ‘yan hirarraki wadanda duk akan ‘yan uwa ne, masu haihuwa, masu aure da masu karatu. Su Indo, Inna Kubra suka biyomu da tsarabar Hajjah (dambun nama) basu barni na rike ba. Don haka da muka fito kofar gida nayi musu ihsanin da zasu jima basu manta ba.

Har mun kai jikin mota zamu bude Hajjah ta ce,

“Au, Hafizi?”

Fa’eez ya juyo ya dakata da bude motar.

“Na’am Hajjah”.

Ta karaso garemu. Sai ta kama hannuna ta kamo nasa, ta hada ta dunkule. Da wani irin murmushin kauna a gefen bakinta, ta ce.

“Sai ina kuma kuka yi yanzun?”

Ya ce, “Gida zamu koma Hajjah. Gobe da safe kuma zamu bi jirgi zuwa Lagos wajen su Yaya Aliyu. Da mun dawo za muyi kaura zuwa (Wales) can inda nake aiki don jaurar tayi min sauki, in samu nutsuwar gabatar da ayyuka na Hajjah da Fa’izahta a gefe na, duk karshen shekara zamu zo mu ganku kuma ku ganmu. Ko in aikowa Baban Giwa tikiti ya kai min ke duk lokacin da naji son ganinki. Hakan yayi Hajjah?”

Murmushi tayi, wani irin murmushi da ban taba ganin Hajjah tayi irinsa ba.

“Nayi ta zama a duniyar kenan Hafizi kuna ganina kuna jin dadi? Ai mun iso gangara, me yayi saura Hafizi bayan fatan cikawa da imani?

Ga amanar Fa’izah a hannunka, na roke ka ka kyautata mata muddin rayuwar ka. Baku sani ba, kuma ban taba fada ba koda ga iyayenku, yadda nake sonka haka nake sonta ko a cikin jikokina ku na daban ne. Ina rokon ku ku hada kanku, ku kaunaci juna saboda Allah!”.

Fa’iz ya sake damke hannuna cikin nasa, ya lumshe idonsa.

“Na yi miki wannan alkawarin Hajjah”.

Har muka shiga motar ya tayar, Hajjah bata koma cikin gida ba. Ta sake matsowa jikin tagar da yake ta russuna dai-dai kunnensa, ta ce.

“Kayi tukin a hankali”.

Sannan ta dago ta dubeni nima, “Fa’eezah ga amanar maigidana, Hafizina Abubakar Saddiku, ki bishi, ki yi masa biyayya kinji Fa’izah? Ki dawo min da mai sunansa in kin tashi dawowa ko mai sunana. Ina kulafucin ganin ‘ya’yanku wanda nasan DA KYAR NE…”.

Jikina yayi wani irin sanyi da al’amarin Hajjaty a yau. Magana take kamar mai yin wasicci kuma kamar mai hango gobe. Ko dan yatsana na kasa motsawa haka shima Hafizin. Na kasa amsawa sai kallon Yaya Fa’iz, shi kuma sai ya sadda kai kasa bai ce komai ba.

Da kyar na iya na ce, “Insha Allah Hajjah”.

Ya yi ribas da motar gate din A.B Houses Hajjah na daga mana hannu. Ni kam mai raguwar zuciya sai nasa kuka, kuka nayi ta yi ba dan kadan ba. Kalaman Yaya Fa’iz ya kara tunzura kukan nawa, cewa yayi.

“Yau Hajjah duk ta kashe min jiki da kalamanta, ban san me yasa ba, gata dai lafiyarta kalau… Don Allah ki daina kukan nan Fa’izah, kina kara tayar min da hankali, kina sawa inji tamkar Hajjah mutuwa zata yi kafin mu kai Kaduna”.

Na tsagaita da kukan amma ban daina ajiyar zuciya da sauke numfashi ba har muka zo gida.

A daren shima bai yi wani isasshen barci ba. Sau uku yana bugawa Aunty Maryam Maman Yaya Aliyu da Baba Na’ibi waya yana tambayar yadda Hajjah take har suka yi mamaki. Suka ce lafiyarta kalau, yanzu haka girki take yi wai zata yi sahur dashi, sannan ya samu ya rintsa sama-sama.

***

Jirgin ‘Aric’ muka bi zuwa Lagos a washegari, ‘already su Zanirah sun san da zuwan mu. Don haka muka same su a filin jirgin saman sunzo tarbar mu da yaransu Fa’izah da Amra mai sunan Hajjah.

Yaya Aliyu yayi kiba har da tumbi tabbacin hutu ya zauna, kazalika itama Zanirar, Zannura inji Hajjah tayi kiba mul-mul da ita, tayi haske na tsabar hutu, daliba a jami’ar Lagos (UNILAG) tana karantar likitancin kashi.

Suka tarbemu da farin cikin da baya misaltuwa. Ni da Zanirah muka rungume juna, haka Fa’iz da Yaya Aliyu. Tun daga (Airport) labari ke cin kowannenmu har cikin gida bakinmu bai yi shiru ba ni da Zanira.

Na kasa shiru da irin daular da naga yaya Aliyu da iyalinsa ciki, na ce.

“Shin wai Zanirah ba aikin      kamfani       Yaya Aliyu ke yi ba?” Zanirah tayi dariya ta ce, “Da kenan. Ai Yaya Aliyu likkafa ta mugun ci gaba. Yana daya daga cikin mamallaka kamfanin sarrafa gilashi tsura dake Japan. Sannan yana safarar tagogi da kofofi na gilashi daga kamfanin         zuwa gida Nigeria”.

Na ce, “Na fahimta. Allah Ya kara arziki mai albarka takowanne fanni”.

Anyi zumunci wanda aka dade ba’ayi ba. Diyar Zanirah ta biyu mai sunan Hajjah da suke kira Amrah kamar Ya Fa’iz ya haifeta saboda kamanninsu.

Kwananmu uku a Lagos muka juyo gida Kaduna, muka fara shirye-shiryen tafiya Wales.

***

A CARDIFF (WALES)

Gidan da Abubakar Mukhtar Giwa yake zaune yana Cardiff, wata irin rayuwa ce muka tsinci kanmu, wadda ba zan iya bayyanawa ba. Ubangijin da Ya halicce mu, Ya kuma yo mu jini daya, Ya sanya wata irin soyayya da shaquwa a tsakanin mu da biro ba zai iya rubutawa ba. Abinda zan iya cewa kawai shi ne aurenmu tattare yake da albarkar iyaye wadda ita ce komai. Ita ke haifar da komai, ita ke bude hanyar kowanne alheri cikin rayuwar dan Adam.

Ko wata uku bamu rufa a Cardiff  (Wales ) ba Yaya Fa’iz ya samar min ‘admission’ a jami’ar Cardiff University of Cardiff ). Ala dole na sauya layi kasancewar turai basa yin ‘course’ dina. Na soma karantar (Civil Law).

Watanninmu Shidda a Wales muka ji kira daga gida Nigeria. Wani irin kiran waya mafi muni a rayuwarmu da dukkan zuri’ar Abubakar Bamalli. Wato mu zo gida Hajjah babu lafiya, jikinta ya rikice kuma mu kadai ne a bakinta.

Haka Ya Fa’iz ya tattara hidimomin nemansa ya ajiye a gefe muka taho gida. A lokacin ina da cikin fari dan wata hudu.

Ashe Hajjah sa’i yayi, kwananmu uku a Giwa Allah Ya yiwa Hajjah rasuwa tana mai sa mana albarka da mu da iyayenmu baki daya, da alfahari da haihuwar su. Tana addu’ar da rokon su ko bayan ranta, su cigaba da daura igiyoyin data bari na aurarraki a tsakanin jininta.

Mutuwar Hajjah ta girgiza ta kuma dimauta baki dayan A.B, wata irin girgizawa da ba’ayi irinta ko lokacin mutuwar Abubakar Bamalli ba. Babu wanda bai gigice ya fita hayyacinsa ba, kada Abubakar Fa’iz ya ji labari. Wanda sai da aka yi da gaske kafin ya koma bakin aikinsa. Hatta abinci yasan Hafizi ya rasa Hajjah, tunda shima ya rasa Hafizin na lokaci mai tsawo.

Watanni biyar da rasuwar Hajjah na haifi yaro namiji, Fa’iz ya cika burin Hajjah ya mayar mata da maigidanta kuma takwaransa muna kiransa Sadiq.

Bayan haihuwar Sadiq da shekaru biyu na haifi Mukhtar, a lokacin karatuna yayi nisa sosai. Ahmad ya biyo baya muna kiranshi (Khazrajy), sai haihuwata ta hudu ne Ubangiji (S.W.T) Ya nufe ni da cika burin Hajjah na samu ‘ya mace. Gaba daya daga mu har ‘yan uwa HAJJATY muke kiranta. Allah ya dauki son Hajjaty ya sanya a zuciyar Yaya Fa’iz. Su Mukhtar sai suka zama ‘yan kallon sha’anin Daddy da Hajjaty. Gashi ta yo kamannin Hajjah sosai da dan banzan wayau.

Haihuwar Hajjaty ta zo mana da sabon sauyi. Rana daya naga Yaya Fa’iz yana tattara ‘belongies’ dinsa daga kasar Birtaniya, ya aje aiki da ‘British Airways’ akan kashin kansa ba da son ransu ba, a cewarsa lokaci yayi da zai bada gudummuwarsa ga jiragenmu na gida Najeriya wanda rashin kishin kasa namu na ‘yan Nigeria yasa har gobe suke koma baya, British Airways suka yi mishi tukuici mai yawa wanda koda bai koma aiki ba nan da shekaru ashirin a gaba, a rayuwa dai ta dan Nigeria, Nigeriar ma Arewa, kuma dan asalin garin kauyen Giwa, ta ishe shi shida iyalansa su kasance cikin rufin asirin Ubangiji.

Gidanmu na Malali aka sabunta aka fadada shi don walwalar yaranmu. Muka dawo Kaduna ina dauke da cikin kanin-ko-kanwar Hajjaty.

Ya debi samarin dukkaninsu ya zuba a British International School dake Lagos, Yaya Aliyu ke kula dasu a can. Gidan daga ni sai Hajjaty, itama da cikina ya shiga watanni takwas Maman Kaduna ta dauketa.

Ranar da na haifi MAIMUNATU ranar Yaya Fa’iz ya fara aiki da ‘Aric’.

Duk yadda dan Adam ke burin rayuwa zan iya cewa mun sameta. Ba zamu gushe ba face muna masu godewa Ubangijin Halitta. Mai azurta wanda Yaso, a kuma lokacin da Yaso. Ya talauta wanda yaso, ba don baya son shi ba sai don ya jarraba imaninsa. Rayuwa mai cike da so da kauna, irin wadanda basa ‘fading’ (kodewa) har muka fara furfura. A lokacin da nake da mukamin babbar Lauyar Gwamnatin Tarayya a Federal High court reshen jihar Kaduna, ina rokon Allah Ya kara soyayyar juna a zukatanmu, yarda, aminci da arziki mai albarka, ya raya mana yaranmu cikin tarbiyyar islama har zuwa ranar da muka daina numfashi.

MASHA ALLAHU LA-QUWWATA ILLA-BILLAH!!!!

Nan na kawo karshen littafin ZUMUNTAR KENAN! Da fatan za’a dauki darussan da littafin ke koyarwa muyi amfani dasu cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Taku har abada  Sumayyah AbdulQadir  (Takori ).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *