RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 11 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne?
Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su

ZAMU TASHI 

Nasreen ba masu dadi bane. Sai gashi dukka abubuwan sun taru sun dawo cikin gidanki. Baba Mu’azzam you’re under arrest!”
Abba ya gyada kai, “Na ba ka izinin ka hukunta duk wani mai laifi. Bana goyon bayan zalunci, Aikinka ne kayi dukkan abinda ka gadama ba zan hanaka ba.”
Mahbub ya sarawa Sultan sannan ya nufi Baba Mu’azzam. Shi kuwa ido ya raina fata, sai duban su Nasreen yake yana jinjina Karfin ikon Allah. Nasreen da Naufal suka Karaso gabansa suna dubansa, “‘Kai ba mahaifinmu bane, ba zan taba ambaton sunanka a matsayin ubana ba, ba * zan taba kallonka a Www.bankinhausanovels.com.ng matsayin mahaifi ba. Sultan shi ne gatanmu,.a duniya, Abba shi ne uban da muka budi ido muka sani, amma ko da alama ba zamu taba danganta kanmu da kai ba. Wayyo rayuwa! Me ya sa

rayuwarmu bata tafi a duhu ba, da in ga wannan mutumin a matsayin uba? Me yasa kuka bari nasan wacece ni?”
Nasreen ta zube Kasa kuka ya ci Karfinta ta daya hannu sama tana magana cikin kuka, “Allah na roKeka, ka hukunta wannan bawa naka tun a gidan duniya, ka hana shi kwanciyar hankali, ka aiko masa da masifu iri-iri ka wulakanta…” Sultan yana jinta ya share ta, sai Abba ne ya hanata Karasa addu’ar da take kwararowa mahaifinta. “‘Nasreen! Uba ubane, ba a taba canzawa tuwo suna. Kada ki sake yi wa mahaifinki irin wannan addu’ar kin ji?”
Nasreen ta girgiza kai tana tsananta kukanta, “Abba! Abba ka daina cewa wannan mutumin ubana ne, ba zan taba yin alfahari da shi ba. Ya wulakanta uwata, ya barta tana kwana a cikin garejin motoci, cikin kwata, cikin Kazanta. Ta kwana bata ci ba, ta tashi duniya suna yi mata kallon karuwa! Suna aibatata. Tana  cikin halin wahala, ga yunwa ga Kishin ruwa, ga ‘ya’ya biyu a cikinta, tana magana da Kyar, amma mutumin nan bai tausaya mata? Zai aiko a sassareta? Insha Allahu, Insha Allahu…” Takasa Karasawa saboda kukan da ya ci Karfinta.
Baba Mu’azzam kuka yake yi, ya rasa me ke masa dadi.. Ita kuwa Umma kusan suman tsayé ta-yi: Ta rasa meke yi mata dadi. Nadama ce ta shigéta. Ita dama Mairo tana can dakinta ta nade tana gudun fitowa ta sami dizgi daga Umma. Hafsat kuwa bude baki ta yi tana duban kowa da ke dakin. Naufal sai yanzu ya sami daman yin magana, “Ba ni da uba sai Deedina, shi kadai ne ubana, shi ne wanda ya ganmu a cikin halin matsi da Kazanta ya kusance mu a irin wannan lokacin. Da mahaifiyarmu za ta dawo duniya, babu wanda za ta ba ‘ya’yanta sai Deedinmu. Har in mutu ba zan taba kallonka a matsayin uba ba. Ban taba-jin wata alama a zuciyata da za ta nuna min Www.bankinhausanovels.com.ng kai ubana ne ba.” Haka aka tasa Baba Mu’azzam aka fice da shi ba tare da ya samu tausayawan ‘ya’yansa ba. Su Ashamaan gaba daya suka fice bayan sun bada umamin a kamo su Alhaji Kabir. Suna , fita Sultan ya kama Hafsat da wanié irin mahaukacin duka, babu ji babu gani, domin ya fi jin tsanarta fiye da kowa. Umma ta kasa ko daga kai, gaba daya ta muzanta, ta amince laifinta ne, ta kasa yi wa ‘yan uwanta musulmai uzuri, gani take yi duk wanda ya aro addini baya daya daga cikin jerin masu shiga Aljannah, ji take kamar ita ke da ikon sanya mutum a Aljannah ko kuma a  wuta, Gaba daya gidan babu dadi haka an rasa wanda zai Kwaci hafsat daga hannun Sultan.  Mairo ce ta yi Karfin halin fitowa ta Kwaceta da Kyar. Abba yana zaune ya nuna kamar abin bai dame shi ba, amma acan Kasar zuciyarsa kukan zuci yake yi, yau shi ne ‘yarsa ta cikinsa take dauke da cikin shege. Nasreen kuwa da ita da Naufal suka hada kai suka zauna shiru a waje, ba su cewa um bare um um. Umma tana son yi masu magana tana jin. kunya, ba ta san da wasu idanun za ta kalle su ba. Sultan shi ya kawo masu abinci ya zauna da su, ya tsoma hannun shi, sannan suma suka sanya hannayen su, suna ci fuskar nan babu fara’a kallo daya zaka yi masu baka buKatarn yin na biyu, zaka fahimci ba su jin dadin abinciza. Da daddare Nasreen tana zaune akan dadduma tana roKorwa mahaifiyarta Rahamar Ubangiji, ta ji an turo Kofa. Duba daya ta yi wa Umma ta kauda kanta. Tana jin zafin Umma fiye da kowa, sai dai kuma darajar Sultan ba za ta iya yi mata ko da kallon banza ba.
Umma ta Karaso ta zauna kusa da Nasreen
Sai kuma tasa kuka. Jikin Nasreen yana rawa ta rarrafo jikin Umma ta kwanta kawai tana ci gaba
da kuka. A karo na farko Umma ta rungumeta tana neman afuwanta. Ta kasa magana sai kuka da take yi, Umma tana yi mata nasiha sai daga kanta take yi alamun ta ji. Umma bata bar dakin ba, sai da ta tabbatar Nasreen ta daina kukan, sannan ta koma dakin Hafsat. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hafsat tana ganin Umma ta durKusa Kasa tana sharar hawaye. Ta ce, “Umma ki yafe min na ci mutuncinku, ban kyauta maki ba, Umma ki yafe min don Allah.” Umma ta shafa kanta kawai ta kasa magana, sai bubbuga bayanta take yi.“Na yarda da Kaddarata. Naga ishara akan Nasreen, na tsane su na wahalar da su, da ga Karshe na makantar da Nasreen, nasa aka kwashe su aka bar garin nan da su, saboda kawai bana son zama inuwa daya da mazinata. Kaicona! Da ban tashi ankarewa ba, sai da ya faru da ni. Allah na tuba. Hafsat gaya min yaushe kika yaudare ni k,’ka je aka yi maki ciki? Yaushe kika fara siyar da ;mutuncinki a kasuwa Hafsat?
Hafsat tana kuka ta gayawa mahaifiyarta yadda Salim ya yaudareta da sunan zuwa gaida mahaifiyars. yasa mata Kwaya a cikin lemu. Tana kuka tana cewa, “Wallahi Umma bana cikin hayyacina ki yarda da ni,” Sultan ya Karasa
shigowa yana duban Umma duba na mamaki. Ya ci alwashin idan ya kama wanda ya aikatawa Nasreen, wadannan abubuwan sai ya dauki mataki, sai dai yanzu ko da shi ne shugabarr masu daukar mataki wannan tafi Karfinsa.
Jiki a sanyaye yake duban Ummansa. Ya ce “Umma… Yanzu ke kika aikatawa Nasreen wadannan abubuwan? Wallahi Umma da a ce ba a bakinki na ji ba, ba zan taba yarda ba.”
Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.” Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya.
Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *