SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 1 by Nura Muhammad
Www.bankinhausanovels.com.ng
Azamanin Da Kusan Shekara1000 Dasuka Shude
Anyi Wani Babba Kuma Shahararren Gari Mesun “DARUL-SHU’UM. Darul Shu’um Yashahara Tafannin Mayaqa, Dakaru, Manya Manyan Gine Gine Da Shahararrun Matsafa.
Sarkin Dake Mulki Agarin Wani Axxalumin aljanine, Babban Matsafi, Sadauki Kuma GagaraBadau Afannin Yaqi Me Suna “DAWWAM,
Sarkin Yanada Wani Shaharren Boka Me Suna “Boka Balbalin Bala’i” Sbd tsananin san duniya irin na sarki DAWWAM yatara dukiyarda shikansa besan adadintaba.
Sarki Dawwam Yanada Wata Kyakkyawa Kuma Jarumar Yarinya Mesuna “SAFRAH”
Gimbiya SAFRAH batabar komaiba awajan ubanta tafannin jarumta da tsafi, abu dayane yabambantata dashi shine ita batasan zalumci shikuwa yakasance azzalumi nagaban kwatance.
wannan dalilinne yasa sarki DAWWAM bayasan ganin SAFRAH kokadan akusa dashi.
Sarki DAWWAM Yanada wani buri wanda cikar burinnan tamkar yakin duniya ne.
bakomai bane burinsa face ya mulka dukkan aljanu da bil’adaman duniya suxama suna mulki aqarqashin mulkin zaluncinsa. sakamakon hakane bokansansa yacemasa dolene saiya kashe yarsa domin indan da’ita burinsa baxai ta6a cikaba.
nanfa hankalin saki DAWWAM yatashi matuqa domin duk abinda ya mallaka natsafi itama tanadashi ko fiyeda shima. hakama afannin jarumta.
boka “balbalin bala’i” yagayamai cewa baxai ta6a samun nasarar kashetaba saiya mallaki takobin mutuwa wandakecan kulle acikin ‘darul ahbab” dajin wannan xancen sarki DAWWAM yayi matuqar raxana, idonsa suka xaxxaro waje gashin jikinsa suka tattashi tsaye cak domin shiga birnin ‘baitul ahbab’ tamkar yasewa kansa tikitin mutuwane.
domin atariyi bawanda yata6a shiga yafito garin daransa se dancan garin. bokansa yace masa zeshiga halwar tsafi nakwana arba’in dan nneman mafita tayadda zasu samu damar tinkarar DARUL’ABAB.
sarki DAWWAM Besamu sukuniba wanda mutanen garin sun huta nakwanakinnan. GIMBIYA SAFRAH seda tafara tantamar cewa akwai abinda kedamun babanta domin taga hartsawon kwana40 beyi wani xaluncin dayasababa. tadau alwashin seta nemo menene sirrin. sakamakon hakane tatafi can gefen garin wajan wani qaton dutse inda ta ambaci wasu kalmomin tsafinta. nantake kogon yabude setashiga.