ABU-MALEEK CHAPTER 2 BY Nimcyluv
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Jikin King Tunde Muhammad Jalal ya tsananta, babban tashin hankalin yadda yake ta kiran sunan Queen Roomana”
Dam dam dammm zuciyar Mai Babban ɗaki ta bada sauti,
Cikin tashin hankali da kuma tsoro haɗi da zullumin daya gama ratsa zuciyar mai Babban ɗaki,
Ta sanya tafin hannunta tare da dafe gishintuta shiga sharfe zufar da yake karyo mata,
Baya tayi kaɗan tare da fesar da numfashi haɗi da kallon,
Hadima Zubaida cikin jarumta tace.
“Kije ki kira Oumuu-Ayman ta sameni a tirakar King Tunde,
Sannan ki kiramin OTUN (Galadima), shima ya sameni a tirakar King Tunde”
Cikin ladami da girmamawa Hadima Zubaida ta sunkuya har ƙasa tace.
“Faɗe taki cikawa tawa,Mai Babban ɗaki”
Kai kawai Mai Babban ɗaki ta jinjina,
Shekarunta sun ja, amma komai na rashin tsoran Allah da kuma son zuciya ƙara bayyana yake,
A cikin Alaafin (Masarauta).
Hadima Zubaida na shirin fita Mai Babban ɗaki tai saurin faɗin.
“A tsananta tsaro a shashin, ki tabbatar babu wanda ya san da maganar ciwon na King Tunde,
Hatta matarsa kada ki faɗa mata, sannan ko sirikan gidan nan kada suji wannan labarin mai tarwatsa zuciya,
Ki sani fitar wannan al’amarin yana nufin rushewar Wannan Masarauta wacce ta kafu shekara da shekaru,
Ki kiyaye da wannan Hadima Zubaida, duk abinda yaje ya dawo kiyi kuka da kanki”
Ƙara sunkuyar da kai Hadima Zubaida tayi cikin son bawa Mai Babban ɗaki girmanta na mahaifiyar King Tunde tace.
“Ubangijin Al’arshi yana kallon komai,
Kuma yana ji yana gani, idan har maganar ta fita dukkan hukunci daya dace aimin ni Hadima Zubaida na aminci”
Tana faɗin hakan ya juya da sauri domin zuwa sashin Oumuu-Ayman.
Ajjiyar zuciya a karo na barkatai Mai Babban ɗaki ta ƙara saukewa,
Zuwa yanzu abubuwa sun fara mata yawa,
Tana son samun mataimaki Tabbas,
Amma yaushe? Ta ina? Wace zata zama hasken da zai yaye duhun dake cikin Alaafin?
Shine abinda har yanzu bata sani ba,
Yadda shekarunta suka ja hakama Oumuu-Ayman ba komai zata iya ba,
Jigon gidan biyu ne, gashi an wayi gari babu Queen Roomana,
Ɗaya ɓangaren wanda ya kasance haske da kuma tauraron gida ƙaddarar sa kaɗai da ishesa,
Ƙaddarar kuma da ita ce sanadiyyar faruwar dukkan wani mugun tuggu dake cikin Alaafin,
Miƙewa tsaye tayi tana runtse ƙafarta wacce take mata,
Tsananin zafi da kuma zugi domin kwana biyu,
Ciwon ƙafar ya dawo mata sabo fill har bata iya taka ƙafafuwan ta,
Tana dogara sandar zallar azurfa ta mai sheƙi ta nufi Parlo idan Kuyanginta suke jiranta.
A can tirakar King Tunde kowa Oumuu-Ayman ce zaune a gefe guda, sai Otun da kuma Hadima Zubaida.
Gaba ɗaya Babban shashin wanda ya kasance shine sashin Oba watu sarki ya cika da masu tsaro ko alamun fara’a babu a fuskarsu bare ka tabbatar cewa idan kazo zasu barka ka shiga,
Mai Babban ɗaki ce ta ƙarasa shiga ciki yayinda kuma,
Kuyangunta suka tsaya can nesa da Babbar ƙofar shiga tirakar ta King Tunde,
Tana shiga Oumuu-Ayman ta Miƙe tsaye sabida nuna girmamawa,
Cikin sabon tashin Hankalin daya samesu bayan wanda suke ciki,
Mai Babban ɗaki taja Jikinta can gefe kusa da King Tunde tana faɗin.
“Kiloshèle?” (Meke faruwa)
Cikin jan wahala da kuma tsananin a zabar da King ya keji a cikin zuciyarsa ya sanya tafin hannunsa,
Dake ɗigar da gumi yace.
“A nemu Queen Roomana duk inda take,
Kada a bari a rasata, Tabbas jikina yana bani akwai wani abu,
Ban san mene shi ba, ban kuma san yaushe ya faru ba,
Amma Queen Roomana itace hasken Alaafin”
Ɗauke kai Oumuu-Ayman tayi sabida hawayen daya sakko daga cikin idanunta,
Babu abinda yake tayar mata da hankali irin rashin Queen Roomana,
Babban abin fargabar har kawo yazo babu wanda ya faɗawa,
Jalaluldeen sabida tsoran abinda zai yi,
Tana tsananin son Jalaluldeen so mai yawa musamman idan ta duban mummunar ƙaddarar data hau kansa,
Gyara zama Mai Babban ɗaki tayi tace.
“Babu abinda zai faru da Queen Roomana, ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ko babu Queen Roomana akwai hasken da zai zo cikin Alaafin yay fatali da duhun da yake cikinta,
Tabbas nayi imani da hakan lokaci kawai muke jira”
Ta ƙare maganar tana tasbihi a ranta,
King Tunde kallon mahaifiyar tasa yay yace.
“Wanne haske ne wannan wanda ya wuce na Queen Roomana?,
Bana jin akwai wani haske da zai yi iya yaye wannan duhun dake cikin Alaafin”
Murmushi Mai Babban ɗaki tayi tace.
“Da kasan zaka samu Queen Roomana? Ko kuma kasan zaka samu MALEEK yaro mai fikira da hikimar gaske, to mafarki na bazai taɓa gayan ƙarya ba,
Sai dai bansan lokacin da mafarkin zai zama gaskiya ba”
A can waje kam wata mai matukar kama da Hadima Zubaida ce ta nufi cikin sashin Kinga Tunde,
Yayinda gaba ɗaya kayan jikinta irin na Hadima Zubaida ne babu wani bambanci,
Hannunta ɗauke da ƙwayar zumar da aka haɗawa King Tunde ta nufi wajan,
Sanin cewa kowa yasan ita ɗin itace Babbar Hadima kuma Amintacciyar King Tunde yasa babu wani shamaki aka buɗe mata tafkekiyar Kofar glass ɗin ta shiga ciki tana mai sakin tattausan murmushi.
Tana shiga ta samu ta silale ta shige cikin wata ƙatuwar akwati wacce duk yadda kakai da fahimta baza ka taɓa fahimtar abinda yake faruwa ba,
Ƙara ƙasa kunne tayi sabida jin Oumuu-Ayman tana faɗin.
“Maleek yana raye, sam bai mutu ba, kawai rayuwarsa tana cikin hatsari,
Kuma shine kaɗai ƙarfin guiwar mu, shine last hope ɗin mu,
Shine zai sanya mu tuni ƙaryar da take ɓoye shekara da shekaru”
Oumuu-Ayman ta ƙare maganar tana sakin tattausan murmushi domin ita kaɗai tasan abinda yake zuciyarta,
King Tunde ya ja numfashi yana ƙara kallon Oumuu-Ayman da kuma Hadima Zubaida wacce take tsaye gefe guda yace.
“Bikin (ODUN EGUN) saura sati biyu,
Bana jin cewa zakai wannan lokacin ina raye,
Amma a tabbatar cewa ko na mutu sai a gudanar da wannan bikin, domin shine zai tabbatar wa da al’ummar Kanzaf Alaafin tana cikin ƙoshin lafiya,
Ban yarda a binne gawata ba har sai an gabatar da wannan bikin al’adar”
Cikin sabon tashin hankali Oumuu-Ayman tace.
“Meke faruwa dakai ne King Tunde? Ka sanya zuciyoyinmu cikin zullumi, ka sanya zuƙatan mu cikin juyayi”
Murmushin baƙin ciki king Tunde yay kafin yace.
“An samin goba cikin abincin sha na, ina jin zafi da raɗaɗin ta, jikina kamar ana hura min wuta haka na keji, babu mai magance min wannan cikin sai Aremo JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL”
Shiru sukai sabida tashin hankali gaba ɗayansu zufa ke karyo masu,
Fake Hadima Zubaida dake cikin akwati wacce tai pretending kamar itace Hadima Zubaida ta gaskiya,
Tai saurin fitowa tana rufe bakinta domin,
Dukkan abinda ya dace ta samu labari akai yanzu taji komai,
Da sauri ta juya ta fita fuskarta cike da farin ciki da kuma daɗin samun nasarar da tayi.
Washe gari
Tsaron cikin Alaafin ya tsananta matuƙa, haka kawo lokacin babu wanda yake da labarin abinda yake faruwa,
Kowa ya tambaya Meke faruwa ana bashi bayanin cewa sabida bikin ODUN EGUN da Za’ai shiyasa aka fara shiri tun yanzu!
Sabida bikine da ake yinsa duk shekara wanda ake gayyatar,
Manyan sarakuna da kuma manyan mutane,
Biki ne dake nuna wa jama’ar Kanzaf cewa ƙwarai da gaske Oba (sarki) da jama’ar cikin Alaafin suna lafiya,
Rashin yin bikin kuma yana nuni da cewa akwai wani,
Gagarumin abu dake faruwa a cikin Alaafin wanda hakan zai iya tada hankalin jama’ar Kanzaf.
Wannan dalili yasa gaba ɗaya Hankalin Mai Babban ɗaki da kuma Otun da Oumuu-Ayman ya tashi matuƙa,
Domin sunyi imani cewa mutum ɗaya ne zai iya zama ya gudanar da wannan bikin al’adar ba tare da an samu wata matsala ba,
Amma su gansu basu da tabbacin cewa zai amsa kiran king Tunde ɗin ko kowa?
Rabonsa da cikin Alaafin (Masarauta) yanzu kimanin shekaru wajan 20 kenan,
Yaya ya koma? Ya yake yanzu no one’s know!
Gaba ɗaya suna zaune a saman babban danning table wanda a ƙalla yake da kujeru wajan 20 ciff, wanda sukaiwa table ɗin ƙawanya,
Bisa al’adar mutanan cikin gidan ne duk ranar juma’a tare suke zama yin breakfast, lunch, and dinner!
Yanzu ma suna zaune Mai Babban ɗaki ce a babban kujera, gefenta kuma Queen Ayoola ce, daga ɗaya gefen kuma Oumuu-Ayman ce.
Sai kuma sirikan gidan wanda suke cikin kaɗai ci da kuma kewar mijinsu,
BOLA, sai kuma KUBRAAH, sai kuma Aremos (prince’s) Adams, Shakiru, Sharefddeen, Femi, kana Salimerh.
A hankali kowa keyin breakfast ɗinsa baka jin ƙarar komai saita Spoons knives and forks!
Boola ta ɗan ja Ajjiyar zuciya tana ta juya Arish ɗin dake plate ɗinta ta gagara cin komai,
A tsanake Mai Babban ɗaki tace.
“Kiloshèle Boola?”
Marai-raice fuska tayi a hankali kuma hawaye ya sakko daga cikin idaniyyarta zuwa kan farar ƙyakkyawar fuskarta tace.
“Allah ya ƙara maki lafiya da kuma yawan rai, abubuwa sun fara min yawa, babu miji babban tashin hankali yadda ake nemi Mami aka rasa!
Yanzu da wanne kalar baki za muyi wa Jalaluldeen bayani? Wanne hali Mami ke ciki tana ina ta mutu ko tana raye babu wanda ya sani”
Runtse idanunsa sosai Adams yay yana jin zcyarsa na tafasa ainun, wane zata rainawa hankali,
Bayan a jiya ya gama fahimtar komai cewa Jalaluldeen ya sanya aka sace Queen Roomana (Mami) sabida cimma buƙatarsa,
A hankali jikinsa ya ɗan shiga rawa kana a zafafe kuma ya hankaɗe plate ɗin gabansa yana mai jin yadda zuciyarsa ta cika da tsanar Jalaluldeen.
Mai Babban ɗaki bayan Adams tabi da kallo tana mai son karantar yanayinsa amma ta kasa.
Cikin tarin mamaki na sauyin yanayin Adams da juya dubanta ga Boola tace.
“Kuyi addu’a, in sha Allah! Babu abinda zai faru da yardar Ubangiji tana cikin kariyar Allah, ita ɗin haske ce koda an rasa ta Tabbas Ubangiji zai kawo mana madadinta wacce zata kula da komai na cikin Alaafin Tabbas”
A tare Queen Ayoola da Aremo Shakiru suka kalli Mai Babban ɗaki cikin son kawar da abinda yake ransu a tare abin kamar haɗin baki suka furta.
“In sha Allah!”
Sharefddeen kam abincinsa kawai yake ci yana mai tunanin abubuwa da dama.
Rarraba idanu Kubraah ta fara kafin cikin nutsuwarta haɗi da kamewa tace.
“Ina Maleek ne?”
Dam zuciyoyinsu suka buga a tare musamman Oumuu-Ayman, wacce tuni zufa ya gama wanke ta kanta a ƙasa,
Hannunta mai ɗauke da spoon ya shiga rawa sabida tsananin ta’ajjujin tambayar ta Kubraah domin sam ba tayi tunanin hakan ba a kuma dai-dai wannan lokacin..
Cikin rashin sanin amsar kuma daza su bawa Kubraah ne yasa a sukwane Oumuu-Ayman ta ɗaga hannunta daga cikin plate ɗin tare da miƙewa tsaye,
A hankali cikin nuna cewa tana da cikakken hankali da kuma tarin nutsuwa ta nufi shahinta,
Ganin haka yasa Mai Babban ɗaki gyaran murya a hankali tace.
“Ki Sanarwa Hadima Zubaida cewa ina nemanta yanzu da gaggawa”
Mai Babban ɗaki ta faɗa tana kallon hanyar da Oumuu-Ayman tabi.
Da “to” Oumuu-Ayman ta amsa tana mai yin gaba abinta,
Kubraah ganin babu wanda ya amsa ta yasa taja bakinta tai shiru,
Shakiru wani kasalallan Murmushi ya saki yana mai jan gemunsa da hannunta,
A ransa yake faɗin.
“A juri zuwa rafi da tulo..”
Wajan 11:30 Mai Babban ɗaki na zaune saman ladduma idar da walaha ɗinta kenan Hadima Zubaida tayi sallama bayan ta nemi isu wajan Hadimar Mai Babban ɗaki wato Hadima Akin.
Zubewa tayi gaban Mai Babban ɗaki tana mata kirari kamar yadda ta sama,
A taushashe cikin son ƙara jan kunan Hadima Zubaida tace.
“Zubaida ina mai ƙara jan kunanki game da wannan sabon al’amarin, mu huɗu muka san da wannan maganar, ni Oumuu-Ayman sai King Tunde da kuma Otun (Galadima),
Idan maganar rashin lafiyar king Tunde ta fita da kuma ɗaya maganar wacce tafi komai muhimmanci a gare mu ta rashin mutuwar MALEEK ta fita, Tabbas kada kiyi tunanin zan goyi bayan ki,
Dukkan abinda ya faru ki kuka da kanki”
Cikin gamsuwa da maganar Mai Babban ɗaki Hadima Zubaida ta jinjina kanta tace.
“Raina fansa ne ga Alaafin, dukkan abinda zai cutar da jama’ar cikinta kuma ina yaƙi dashi, na aminci da dukkan hukuncin da Za’ai min idan har wannan Maganar ta fita”
Murmushi jin dadi Mai Babban ɗaki ta saki domin ta aminta da Hadima Zubaida sosai fiye da jikokinta.
“Ke nemu min Amintacciyar kuyangar Jalaluldeen yanzu”
Da makaki Hadima Zubaida tace.
“Ai Jalaluldeen bashi da wata Amintacciyar kuyanga, rabonsa da Nigeria yanzu kimanin shekaru ashirin kenan ciff”
Da sauri kuma Mai Babban ɗaki tace.
“Ai haka ne, daman na kiraki domin naja kunanki ne”
Murmushi Hadima Zubaida tayi sabida rikitar tsufan Mai Babban ɗaki, danma tana jajir cewa,
Cikin ƙasa da kai tace.
“Ai kin faɗan”
Kallonta tayi sai kuma tace.
“Au toh! Toh! Shikenan, kawo min zuba yanzu da madarar shanu mai zafi, ki haɗa da Algaragis”
Miƙewa Hadima Zubaida tayi ta nufi babban kitchen ɗin Mai Babban ɗaki ta a shirin shiga ciki Mai Babban ɗaki tace.
“Ki haɗo min da Algaragis”
Hadima Zubaida tai Murmushi tace.
“Ai kin faɗa min”
Jinjina kai tayi tace.
“Toh! Toh! Shikenan”
Haɗo mata komai tayi kana ta kawo mata wajanta tare da Miƙewa tace.
“Na barki lafiya Mai Babban ɗaki Allah ya ƙara lafiya”
Jinjina kai kawai Mai Babban ɗaki tayi ba tare da tace komai ba,
A hankali kuma ta sanya hannunta mai cikakkiyar lafiyar ta cire Inibi guda ɗaya mai sanyin gaske tai Bisimillah tare da sanyawa a bakinta.
A can ƙofar sashin Mai Babban ɗaki kowa cikin nutsuwa Hadima Zubaida take tafiya harta isa sashinta domin hutawa,
Kai tsaye gaban babban mirror’n dake maƙale a jikin bangon parlon ta kalla.
A hankali kuma ta fara ɓaɓɓaka dariya har hayaƙi na fita daga cikin bakinta,
Tana gama dariyar ne kuma ta tsuke fuska tare da sanya hannunta ta cire fake fuskar data maƙala irin ta Hadima Zubaida,
Nan take