SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 3 by Nura Muhammad

SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 3 by Nura Muhammad

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

batasan lokacin da hawaye yafara zuba a idanuntaba sannan taiwani siddabaru wata takobin wuta tabayyana ahannunta itama tafara sarar idanunsu wanda a daqiqa daya takan kashe wajan aljanu 20 sbd tsananin xafinnama. saida kowanne aljani yashiga taitayinsa domin ganin yadda take kashesu. shikuma aljani DURFAN tini anmai wata qatuwar sara acinya wanda yana kwance jini sekwarara yakeyi. cikin sa’a daya GIMBIYA SAFRAH takusan qarar dasu amma cikin rashin sa’a wani dakaren aljani yakaiwa GIMBIYA SAFRAH wata mahaukaciyar mangara dukda takauce amma seda yasameta kadan dalilin dayasa taiwata mahaukaciyar qara kenan domin tinsanda aka haifeta bata ta6ajin xafinduka irin naranarba.

 farat tafadi akan gwiwarta domin tagalabaita amma cikin qarfin hali ta ambaci wasu kalaman tsafi nantake wuta tabaiyana aljaninnan yaqone qurmus. al’amarin daya tadawa da sauran aljanun hankali kenan domin atarihi tsafi beta6a tasiri akan daya daga cikinsuba. haka gimbiya SAFRAH taita amfani dawutarnan tana qonasu. 

cikin mamaki data waiga taga wa’innan bakin aljanun da aka tawo dasu duksun mace. taga masu rai acikinsu ukune daga ita sai aljani DURFAN sai BOKA KIRYAN dakecan kwance asume. 

aljani DURFAN yakasa tashi daga baya sai KIRYAN yafarfado, gimbiyace taqarasa kansa cikin hanxari sannan tatasheshi tasamai magani arauninsa sannan yatashi yaje yasawa ALJANI DURFAn magani sannan suka farfado…  

Bayan kimanin dakika dari biyar da tamanin saisuka tashi domin tinkarar tsakiyar dajin inda aljanin MARKAHUL NAR yake.

ABANGAREN SARKI DAWWAM KUWA BAYAN SUNJE GARIN DA MANYAMANYAN TSUNTSAYENNAN SUKE.

Yayinda suna shiga fadar sarkin tsitsayen sai sarki Dawwam yazama tamkar Dan kano yashigo kaduna

Domin iyaka fadar takai girman garinsa gabadaya. Nandanan wannan badakaren tsuntsun yarikida Yakima karami sannan yafada gaban sarki yayi gaisuwa.

Bayan gaisuwa saiya fadawa sarki bukatarsa amma sarki yayi amincewa domin yasan shiga dajinnan Nada hadari sosai.

Alokacinne sai sarki Dawwam yamike yaje gaban sarki yatsaya. Koda sarkin tsuntsayen yakalli fuskar sarki Dawwam saiyayi matukar razana domin alokacinne yagane koshi waye.

Kafin sarki Dawwam yace komai tuni sarki yabada umarni cewa aje afuto da dakarunsa guda dubu abashi suzama bayinsa gabakidaya. Cikin tsananin mamaki tsutsayen suka cika umarnin sarkinsu.

Bakomaibane yasa sarkin tsuntsayen yatsorata face yataba ganin sarki Dawwam awani yaki dayataba kaiwa yayinda tsuntsayen sunkai kimanin dubu ishirin amma tin sarki Dawwam yana karamin matsafi a dakika dubu daya da Dari daya da goma shadaya 1111 tak yakarardasu. Shiyasa betsaya yimasa jayayyaba. 

Nandanan aka hada tsuntsye guda dubu sannan sarki yace musu daga yau har iyaka karshen rayuwarku kunzama bayin sarki Dawwam. Dukansu sukayi mubayi’a sannan suka karbi umarnin Dawwam sannan suka yunkura zasu tashi kaikace yakin duniya gaba daya zasu zagaye.

yanda tsuntsayen sukai sahusahu duk garin yayi duhu domin suntoshe sararin samaniya ko rana bata bullowaqasa sbd tsananin girmansu. saida sukai sa’a biyu basu gama wucewa daga garinba. acan bakin dajin da sauran aljanun sukaga tsuntsayennan suntunkarosu duk hankalinsu yatashi wasu faduwa suka farayi aqasa domin tsoro. saisuka sauko wanda saida qasargun taimatuqar girgixa domin nauyinsu. nanfa sai sarki DAWWAM yace kowani aljani daya yahau bayan tsuntsu daya domin taimakamai yayinda yaware tsuntsayen guda Dari biyar yace sujirashi abakin dajin.

nandanan kuwa hakan takasance. batareda bata lokaciba suka fada dajin. farko saisukaga wata qaramar macijiya nantake tsuntsudaya yayi farat yadageshi yakashe ashe suntono tsuliyar dodone. 

kawai sai ganin wata dantsareriyar macijiya sukayi tadawokai. girmanta yayi girman tsuntsu daya. nantake yakama wuyan tsuntsu daya yafyadashi akasa nantake yamutu. sarki DAWWAM yayi kururuwa yayi tsalle yafada kan macijin. kafin yakarasa macijin yadude bakinsa sarki DAWWAM yafada cikin bakinsa.

yayinda sarki dawwam yafada bakin macijiyarnan nantake tahadiyeshi. amma dayake sarki DAWWAM hatsabibine kawai saiji akai macijiyar tayi qara wadda dukkan.tsuntsayen saidai suka firgita wasu daga cikin aljanin harsuma suka farayi domin tsananin karar.

kawai saiganin sarki Dawwam akayi yadago domin yafasa cikinta. qarar da maciciyar tayi yasa duk dajim yafara girgiza. sauran macixan duk suka fara kunno kai. wasu macixanma girmansu yaninka na tsuntsaye guda biyu. Nanfa dajin yakauraye da axababben yaki wasu daga cikin macixanma wutace kefita daga cikin bakinsu. nanfa dajin ya turnuke da qarar da macixan keyi mekurumta da kunne. 

sarki dawwam yayi umarni dacewa dakarunsa surinqa watsaawa macixan wutar tsafi wanda hakanne takasance. 

 macizan sunkasance suna kaiwa tsuntsayen sara wadda cikin xafin nama tsuntsayen suke kaucewa amma dukda haka duk tsuntsun dasuka sama saiyaje kasa. al’amarin dayatayarwada sarki DAWWAM hankali kenan domin yasancewa inhar al’amarin yacigaba ahaka to lallai rayukansu xasu salwamta…

Sarki DAWWAM Nandanan Yahada Tsafinsa Waje Daya Sannan Ya Ambaci Wasu Dalasaman Tsafi. Nandanan Wata Gagarumar Guguwa Tahadu Sannan Tafara Yawo Da Macixan Tana Wurgi Dasu Awannan Halin Duk Yawancin Rayukan Macixan Suka Salwanta.  

Al’amarin Daya Farantawa Sauran Aljanun Da Tsuntsayen Rai Kenan Duk Suka Fara Dariya. Kwatsam Bashiri Sejin Dajin Sukai Yacanja Domin Wata Wuta Data Tashi Sama Hade Dawata Qara Wadda Duk Seda Tsuntsayen Harda Sarki Dawwam Suka Fadi Kasa. Kwatsam Seganin Wata Shirgegiyar Macijiya Sukayi Takunnokai Wadda Girmanta Yawuce Inmusalta Mukushi Domin Nikaina Dagudu Nakoma Canbaya Dan Kartayi Break Fast Dani Dan Naga Kamar Lokacin Tafarka HHh. 

Macijiyar Takasance Tanada Kawuna Uku. Nafarko Feshin Wuta Yakeyi Ta Annoba. Nabiyu Wato Matsakiya Wata Qara Yake Fitarwa Me Kurumta Dadukkan Mesauraro. Na’uku Kuwa feshin Wani Dafi Yakeyi Wanda Duk Inda Yaxuba Sedai Kaga Qasar Gurin Natafasa…

Macijiyarnan tayi matuqar tayarwada aljanunnan hankali, domin a rabim dakika tayi amfani da kawunanta uku nantake tamurkushe tsuntsaye guda shida. ganin haka shikansa SARKI DAWWAM seda hankalinsa yatashi amma benunaba saboda dakakkiyar zuciyarsa irinta sadaukai. 

macijiyarnan taqarayin wata kururuwa wadda nantake wasu daga cikin aljanun suka fadi sumammu. nanfa taikan tsuntsayennan tana musu kisan wulaqanci domin saita qonasu sannan tawatsamusu dafi wanda nantake sedai kaga tsuntsu kamar dafaffe babbakakke. (hummm aranarne naga tsuntsu asama gasashshe).

 adakika sittin duktakusan qarar da tsuntsayen. (hmmm nikuwa inacan daga baya na makale abayan wata bishiya bakina abude ido nakallo baki na kalla). duk aljanun datsuntsayen suka dena farmakar macijiyi suka koma kare kansu kadai domin koni nasan bayadda zasuyi da macijiyaranan.

 Cikin tsananin fishi sarki dawwam yayikan macijiyarnan. itakuwa takawo masa wata sara amma cikin xafin nama irin shu’uman aljanu yakauce sannan yahaye bayanta.

 saidayayi gudun tsawon dakika20 sannan yakarasa kanta, wata takobice ta bayyana ahannunsa wadda yakai mata sara atsakiyar kanta. cikin mamaki yaji takobin tayi tsalle domin jiyayi kamar yasara dutse. itakuwa sai kawo masa mummunar wawura takeyi yana kaucewa cikin zafin nama. yayi kusan sa’a biyu yana fafatawa da ita amma ba wanda yayi nasara akan wani. 

Wani abu daya kara lura dashi shine ko alamar gajiya batayiba domin ganin xafin namanta qaruwa yakeyi. be ankaraba seji yayi tafyadoshi qasa da bindinta amma yana xuwa qasa yadawo kamar anharba kibiya. takobinsa yabuga mata a ido sanadiyyar dayasa tafeso wuta amma sannan yaqara sokawa dayan idon wuqar. nanfa duk tabi tahaukace domin tsananin zafin dataji.

kai sara takeyi tako ina amma yana kauce mata. cikin dabara yacigaba lahantata yafasa idan kandake feshin wutar.

 da sarki DAWWAM yagane lagon wannan macijiya aikuwa saiya bada himma wajan fasa dukkan idanunta. 

Cikin lokaci qalilan duk yatada hankalinta sannan yasamu dama duk yamakantar da ita. dukda haka bata kyaleshiba domin duk inda taji motsi setaka sara da dukkan kawunan. ahakanma takashe tsuntsaye kusan 20 sannan tafadi matatta. sarki dawwam yabada umarni cewa xasu shiga daji nagaba amma bisa mamaki saiyaji ba’a amsaba. daya waiwaya saiyaga sadaukan aljanunsa wa’inda basu mutuba basu wuce guda50 sekuma tsuntsayem daba’a rasaba kamr dari. 

alokacin shima duk agalabaice yake domin dayagansu haka duk sai yarasa qarfin gwiwar shiga dajin. 

Tadole yanke hukuncin cewa zasu tsaya suhuta na yan awanni sannan sucigaba da tafiya. duk aljanun sunyi farin ciki dajin wannan xance domin kowanne daga cikinsu jikinsa yayi la’asar. hakanan suka yada zango domin hutawa. al’amarin dabasu saniba shine bawanda yasan abunda kecikin dajin daxasu fiskanta hattashi sarki DAWWAM din. kawaidai sunsan zasuyi yakin dabasu ta6ayin irinsaba.

ACAN.BANGAREN SAFRAH DA BOKA KIRYAN HADIDA DA ALJANIDURFAN KUWA.

 Daduk Raunukansu Suka Warke Sesuka Dugunxuma Cikkin Tsakiyar Dajin Domin  Su Je Su Bude Aljani MARKAHUL~NAR.

 daxuwansu tsakiyar dajin sesuka gamu dawata bishiya gajeriya wadda ajiki akwai wani kejin tsuntsuwa na lu’ulu’u. acikin kejin kuwa akwai wata farar tsuntsuwa gwanin bansha’awa. gimbiya SAFRAH ce taqarasa tana shirin ta6a kejin domin tsuntduwar tayi matukar bats sha’awa.

 cikin hanxari boka KIRYAN yayi wani tsafi yajanyota baya sannan yadurkusa cikin biyayya yace ‘yake shugabata kisani wannan ba tsuntsu bane face sadauki MARKAHUL NAR’. kisani daxarar kinta6a wannan kejin to mutuwa tatabbata agaremu domin MARKAHUL NAR zefito harya halakamu domin wajan budeshi akwai ka’idojin daxamubi dan karya raunata harya halakamu domin fishinsa tamkar gobarace daga ruwa.

kingato abinda yafi shine mubi komai atsari da ka’ida mutsiratar da rayukan mu harmu samu nasarar cikar burinmu.

cikin sanyi jiki GIMBIYA SAFRAH tace Waiwaye Wannan MARKAHUL~NAR Dinnanne daxakaxo kaitawani yimai kirari agabana?” 

BOKA KIRYAN yayi murmushi sannan yace kisani wannan ba aljani bane irina ko irinki domin mu muna cikin jinsin JINNUL SHU’UM NE. shikuma MARKAHUL~NAR yanacikin jinsin JINNUL NARII ne. kisani aljani MARKAHUL~NAR ba irin sifar dabeyi domin inyayi sifar irin aljanunmu to duk duniya ba aljanin dazai gane cewa shibadaga jinsinmu yakeba.¹² 08108488607

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *