ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 16 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

 ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 16 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

               Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya

A rude ya ce, “Umma wai me ke faruwa ne? Shin Ammi na ta warke ne? Wai me yake faruwa ne? Ni fa na rude naji tana kiran Hameed, me Hameed din ya zo ya yi? Ko an ganshi ne?” Abba gani, dama ba bata nayi ba”Gaba dayan su suka juyo suka kalli bakin Kofar shigowa inda suka jiyo muryar sa.
Hameed ne tsaye bakin Kofar yana mai Kokarin shigowa. “Kada ka sake ka Karaso nan gurin Ya Hameed, na tsane ka, ba zan taba yafe maka

ba, macuci, azzalumi, mara tausayi. Wallahi sai Allah Ya saka min abin da kayi min”.
Tana fadin haka ta fashe da kuka tayi sauri ta hangi wani kwalbar lemo ta dauka da sauri ta je ta doka masa a goshin sa, nan take jni ya wanke fusakar sa.
Kowa na gurin kasa motsi ya yayi, ana tsaye ana kallon ikon Allah. Nan da nan Mustapha ya Kara rudewa domin har yanzu bai fuskanci inda suka dosa ba. Hameed yana tsaye yana mamakin furucin Aziza nan take ya gane cewa tunaninta ya

dawo,Www.bankinhausanovels.com.ng murmushin farin ciki ya yi mai tare da takaici.
“Ammi meye haka kuma? Me yayan naki ya yi miki haka har kika ji masa wannan rauni haka?” Ya fada cikin tsawa. . Cikin kuka ta ce, “Abba bai kamata kayi mini tsawa ba don baka gane abin da Ya Hameed ya yi min ba”. Tana gama fadin haka sai ta fashe da kuka, Aisha tana kuka. “Abba ka bar Aziza:‘tayi min duk abinda ranta yake so matuKar idan tayi hakan zai sa ta huce ta yafe min abin da nayi mata. Abba ba ita ya kamata ka yiwa tsawa ba ni ya kamata ka yiwa tsawa, kamar yadda ta kira ni macuci, azzalumi hakan nake, kuma na yarda na amsa sunan da ta bani, domin babu irin’‘roko da kukan da bata yi ba akan kada na cutar da ita amma nayi burus da ita sai da na hakke mata. Abba ku yafe min, ni ne na cutar da rayuwar Aziza, na bata mata rayuwar ta, don haka ku yi min duk abin da za ku dauki fansa akan abin da nayi muku”. Zaman ‘yan bori Mustapha ya yi da ya gama fahimtar bayanin da Hameed yake masa, nan take wasu zafafan hawaye suka zubo a cikin idanunsa ya ji komai na cikin duniyar nan ya masa zafi, haka itama aisha sai yanzu ta gane me yake nufi._. .
Da sauri ta zo ta cakumi Hameed tana kuka tana cewa. “Hameed ka cuce mu,.ka ci amanar
yarda da Kaunar da muka nuna maka. Ashe
dama kaine ka yi mata wannan aika-aikar? To Allah Ya isa tsakani na da kai ba zan taba yafe maka ba, kaje insha Allah sai ka dandana Kuncin da yafi wanda ka jefa mu”Nan take ya fara kuka yana cewa don Allah ta yafe masa, haka ta ture shi taje ta zauna tana kuka. Haka yaje gurin Mustapha ya tsuguna gabansa yana kuka yana rokon ya yafe masa.
Cikin Kunar rai ya daga hannu ya wanke shi da mari, ji kake tasss! Idan baka tashi ka bar gurin nan ba zan yi Kasa-Kasa da kai naga uban da ya tsaya maka, mara mutuncin banza, munafukin wofi”. Ya fada cikin daga murya. Mikewa ya yi daga wurin da ya fadi domin ya yi mutuKar jin marin, nan ya sake dawowa gabansa yana kuka, ya ce. : Www.bankinhausanovels.com.ng
“Abba duk abin da zaka yi min kayi min matuKar zaka huce daga bacin ran da na saka, wallahi sharrin zuciya ne da rudin shaidan, duk su ne suka debe ni da aikata haka”.
Wani mari ya sake kai masa a karo na biyu nan ma ya Kara samun sa, a karo na ukun ne nayi sauri na saka hannu na tare, nace
Mustapha barshi haka tunda abin da zai faru ya riga da ya faru, kai kuma tashi ka taf? ‘abinka Allah Ya shirye ka, zalunci kuwa ka riga da kayi mana shi, kai namu ne babu yadda za muyi da kai, amma ba don haka ba ni da kaina zan sa a rufe ka a gwada maka hankali ka gane abin da ka yimana”. . Rarrafowa ya yi ya zo ya riqe ni yana . kuka yanacewa._Granny wallahi na tuba, ku yafe min, hakiKa na san abin da nayi ban kyauta ba, -Ammi kema ki yafe min”.
Sauri tayi ta dauke kallonta gare shi ta ce.
“Kada ka Kara kira na Ammi, ni ba Ammin ka bace Hameed, yanzu abin da zaka saka mana da shi kenan? Kaje abinka insha Allah sai Allah Ya yi mana sakayya da halin da ka jefa mu ciki, domin Allah baya bacci, Yana amsa addu’ar wanda aka zalunta_ cikin gaggawa”,
Cikin kuka yace, “Ammi ku yafe ni, nasan ban kyauta ba, amma ku yi min duk abin da zai fanshi bacin ran da na saka ku matuKar yin hakan zai sakuhuce”.
“Hameed ka tashi ka bace min daga nan domin ban son jin duriyar ka a gurin nan, domin kana Kara haifar ma da zuciya ta damuwa. Ka cuce mu Ka jefa mu cikin tashin  hankali, tsakanin mu da kai sai dai Allah Ya yi mana sakayya, amma maganar yafiya tsakanin mu babu, kaje can ka Karata, ka jira ganin sakayyar abin da kayi mana, domin Allah sai ya biwa ‘yar uwarka hakKin ta”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin kuka Aziza ta ce, “Ammi kada ki Kara kirana da cewar ni ‘yar uwarsa ce, idan da – ni din ‘yar uwarsa ce ba zai yi min haka ba. Bai tausaya min ba, bai kuma duba zumuncin mu ba sai da ya hakke min, to ya zan yi na yafe masa?” Nan kuka yaci Karfinta ta fado jikina tana yinsa, tana cewa. “Ya Hameed ba zan taba yafe maka ba”. Dukkanin mu kuka muka ci gaba da yi, aka rasa wane zai iya rarrashin wani a cikin mu.  Hameed ya matso gurina zai fara roKona
na daga masa hannu akan ya yi min shiru, ganin yanayi na yasa bai iya furta ko da kalma daya ba dole ya ja bakin sa ya yi shiru. —
Cikin fushi Mustapha muka ga ya damKi wuyan rigar sa ya ja shi sun yi waje ba tare da ya ce da shi uffan ba, haka suka yi waje tare, da har nayi tunanin naje na bisu na tambayi ina za su? Sai na dawo na tsaya, nan muka zauna muna ta jimami da nuna alhinin faruwar al’amarin, muna cikin wannan halin sai ga Maryam nan ta zo. Bayan mun sanar da ita abin da yake  faruwa hankalin ta ya yi mummunan tashi, itama kukan tayi mai isar ta domin abin ya daga mata hankali. Tun da ya yi (parking) motar sa a cikin (estate) din ya shiga kiran sunan duk wanda ya
zo bakin sa, haka ya zamo kamar Karamin mahaukaci.
Kai tsaye Kofar gidan Alh. Jafar ya nufa rike da rigar Hameed, shi kuma binsa yake bai ce da shi Kala ba, domin ba shi da abin da zai iya cewa da shi.
Alh. Hamza da Alh. Lukman su suka fara fitowa suka hangi Mustapha ya nufi gidan Alh. Jafar, sauri suka yi suka mara masa baya, suna hango shi da Hameed sai farin ciki ya kama su domin tunanin su ya gano Hameed daga batan da yayi. Haka suka nufo gurin cikin farin ciki tare da yi ma Allah godiya na bayyanar yaron su, domin dama kullum suna cikin zulumi.
Cikin daga murya ya shiga kiran Alh. Jafar babu Kakkautawa, a sukwane ya fito shi da Asiya. Yana ganin su ya hankada Hameed gabansu ya je taga-taga zai fadi da sauri mahaifin sa ya tare shi amma duk da hakan sai da ya fadi.
Dai-dai lokacin da su kuma suka Karaso, nan take suka yi turus cike da mamakin abin da
Suka ga yayan su yayi, take abin ya daure musu kai hade da mamaki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin daga murya yace”Jafar ka bani mamaki kai da azzalumin yaron ka, ashe ku dama maha’inta ne ban sani ba? To wallahi yau babu mai raba ni da ku sai kotu tun da kai da danka azzalumai ne marasa amana”. Kai Mustapha, nutsu kasan wane furuci kake yi da sanin wa kake jifa da wadannan kalaman, domin ba zan iya jure daukan su ba”.
“Dole ka jure su kuwa domin babu yadda zaka yi, ban san rashin imanin danka ya kai haka ba, haka kuma kai ma ban yi tunanin zaka yi min haka ba. To amma tunda Allah Ya bayyana mana gaskiya to ai shi kenan, dole gobe ku ga sammaci kai da danka a kotu, domin babu abin da zai sa na hakura tun da ku azzalumai ne”. Alh. Hamza ne ya matso kusa da shi, ya ce. “Subhanallahi! Yaya Mustapha menene ya yi zafi haka kake wannan furucin? Don Allah kayi hakuri ko ma meye ya faru a
tsakanin mu za mu iya maganta shi ba wai sai mun tozarta kanmu ba duniya ta jimu, domin wannan babban abin kunya ne a ce daya daga cikin mu ya maka dan uwansa a kotu saboda wani abu da ya faru tsakanin mu”.
“Hamza ka rufe min bakin ka a gurin nan, bari na gaya maka babu wanda ya isa ya hana ni aiwatar da abin da nayi niyya tun da abin ya shigo da munafurci da rashin imani. To bari na fada maka, ko kasan.cewa Hameed shi ne ya yiwa Ammi na fyade har ciki ya shiga wata uku?” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaba dayan su rudewa suka yi, Alh. Hamza da Lukman duk suka fito da idanun su waje, tsananin mamaki da tashin hankali ne ya bayyana a fuskar su. Nan take suka shiga raba idanu da kallon juna.
Nan take ya zayyane musu duk abin da ya faru, jikin su yayi sanyi, yana fada musu hawaye na zuba a fuskar shi. BOOK 1 KARSHE

HMMM Mu hadu a littafi na biyu Www.bankinhausanovels.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *