SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 6 BY Xayyeesherthul-humaerath

SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 6 BY Xayyeesherthul-humaerath

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta farka , Hamdallah Mammaah ta fara. Cikin farinciki ta fita.

Maryam ta rike Nafeesa, “Sannu Habibbty kin tashi?”

Kan gadon ta fara bincikawa ta nemo glass dinta tare da kafawa a idonta ta gyara zaman.

Da Murmushi Nafeesa ta kalleta , “Na tashi Habibbty yaushe kikazo?”

Maryam ta ce, “Tun Safe kinata barcinki abunki.”

Waige,waige ta fara, “Umm Habibbty ina wayata naji ana kirana,ki dubamin ita.”

Maryam ta tashi tana, “Oh keda kike barci ina zakiji wani kiri ni kaina banji Ba bara na duba jakar nan taki.”

Cikin sa’a kuwa ta Ciro wayar tare da mik’a mata, “To Madam ga shi wayar ma da akashe take, ko ta ina ki ka ji kiran mu ba mu ji ba oho.”

Murmushi kawai tayi tare da kunna wayar kamar yadda taji aranta cewa Jameel na nemanta hakan ya sa ba inda ta fara lekawa sai Group din Marubuta, Message ko na farko d ya fara zuwa mata shine wan da sahibinta ya yi tagging dinta.

Tsayawa kallon message din tayi kawai tana sakar murmushi ba tare da ta Ankara ba.

Shigowar Mammah da Abhi ne ya katse ta daga duniyar ta shige acikin kankanin lokaci.

Abhi ya karaso gareta tare da dafa mata kai, “Ammienah ya jikin dai, barcin nan na lafiyane kuwa?”

Kallon agogon wayarta ta fara yi sannan ta dago ta kallesa, “Lah Abhi Yaushe ka dawo yau date 30 fa.”

Cikin fara’a yake fadin, “Eh mana nazo kinata sharban barcinki nace ko takwararaki ce tazo kuke hira taki karewa kun manta damu.”

“Abhina ke nan, ai da naga Kaka ko ba zan dawo ba yasin sai dai inyo maku byebye.” Cewar Nafeesa tana kokarin latsa wayarta

Abhi Yayi Murmushi, “Wato dai ba za a ajiye wayar nan ba ko? To maza a ajiye ayi wanka ai  sallah sannan aci abinci.”

Shagabewa ta yi, “Umm Abhi nemana ake bara ince masu ina zuwa tam.”

Shafa kanta yayi yana, “Yawwa Yar Albarka Ammiena,bara mu barki da Maryam ta tayaki kintsawa Muna falo in kin gama kya fito ki karbi tsarabarki.”

Girgiza kai tare da murmushi kawai Nafeesa tai.

Mammah,Abhi tare da Sabeer suka fita, sai Nafeesa da Maryam.

Reply tayowa Jameel da , “Tab Yasin ni ba gauruwace ba,Dan dai bana da lafiyane Amman da yanzu nayi jajjagen miyar Kuka da kai.”

Message din na Isa Yayo murmushi , “ni ko zan jira har ki samu sauki domin inga yadda ake jajjage da mutane.”

Dariya Nafeesa tai wadda sai da ta fito fili ta ce, “Bara inyi wanka in dawo yau zanyi caskale da wani agidannan.”

Da fadin hakan ta rufe data Amman har yanzu murmushi ya kasa gushewa daga fuskarta hakwarannan kamar mai tallan makilin.

Mamaki ya sa Maryam yin shiru tare da tafiya dogon tunani,domin tun da take bata taba ganin  Nafeesa Cikin farinciki kamar na yau ba,duk da kasancewar kullum cikin murmushi take Amman bata cika washele baki da sunan tana dariya ba.

Nafeesa ce ta dakawa Maryam duka abaya, “Dilla ni kin tafi wani tunani rikeni in tashi jikina ba kwari.”

Cikin Ranzana Maryam tayi tsaki, “To ai ke dince naga kinata wani kyalkyala dariya tamkar sabuwar kamu wai miye Sirrinne?”

Dafa Maryam Nafeesa tai tare da kokarin tashi, “Sirrin na da tsawo Dana baki labari.”

Maryam ta riketa ta karasa tasowa tana, “Ina binki fa bashin wani sirrin ga wani ma na yau ni gaskiya na zaku inji sirrukannan Dan kwanakinnan salon ya chanja gabadaya.”

A kofar toilet din ta tsaya, “In Lokacin ki San Sirrin yayi zan sanar da ke batare da kin ankaraba Amman ba yanzu ba.” Ta sake mata murmushi akarshen maganar tare d shigewa cikin bandakin.

Wanka tayo tare da dauro alwala sannan ta fito tayi sallah, gabadaya yau yanayin Nafeesa ya chanja ba Magana illa murmushi da ke bayyana afuskarta.

Cikin Shigarta ta Farar doguwar Riga tare da mayafinta ta fito hannu rike Dana Habibbtynta.

“Oyoyo Ammien Dady,kullum kara girma da kyau Babyna ke yi.” Cewar Abhi.

Rufe fuska da hannu Nafeesa tayi tare da shagwabewa , “Uhum Abhina ni ka daina.”

Abhi ya ce, “To, to na dain a Ammien Abhi Zo in baki abinci da kaina nasan Mammah ba wani kulamin da ke take ba.”karasa maganar yayi tare da bude hannunsa alamar tazo.

Sabeer ya sa kuka, “Mammah kin gama Abhi ni baya ban abinci abaki Amman zai baiwa Aunty ko?”

Mammah ta ce, “Rabu da su Sabeer dina Dadinta ma kowa ya san kai ne Auta ita kuwa gardiyace.”

Dariya Sabeer yayi yana kallon Nafeesa tare da yi mata gwalo.

Nafeesa ta kalli Abhi , “Abhi ka gan su ko?”

“Sharesu ke kadai zan ba tsaraba da Maryam,Amman Sabeer kam da Mammahsa sai kallo.” Fadin Abhi.

Gwalo ita ma tai wa Sabeer kamar yadda yayi mata.

Gabadaya dariya suka sa afalon.

Abhi ya fara bawa Nafeesa Abinci,kamar magani take karba cikin shagwaba harda guntun kuka, can ta tuna da tacewa Sahabinta tana zuwa.

Azabure ta mike batare da ta ce komai ba ta shige dakinta aguje.

Tsayawa kallonta kawai sukai sai gashi ta dawo hannu dauke da waya.

Abhi ya ce, “Oh wannan waya dai, to zo ki karasa abincin ko?”

Cikin shagwaba take fadin, “Um umm ni na koshi Abhi inna kara amai zan yi fa.”

Murmushi  yayi, “Allah dai ya shiryamin Ammienna.”

Itama Murmushin ta yo masa tare da bude wayarta ta shiga WhatsApp .

Kamar Yadda take tsammani Reply Din sa ta fara gani.

“Hhhhh Lallai yau ba samu gamona ni za ayi caskale dani,ni da nake da mutane yau za ayi Dani,Oh shiyasa nakejita jin tsammi maza kam aje ayi wanka.” Cewar Nafseen.

Nafeesa ta gyara zama tare da fadin, “Hhh To ai dai gani nadawo ba kai ne zakayi Fada da jarumar mata ba? Muzuba mu gani,kuma ysin ni bani tsami sai dai wani.” Ta kare maganar tare da murguda baki tamkar yana wajen.

Cikin sa’a kuwa yana Online ya maido mata, “Yo za mu gani dai Amman da kwai yan adawata agidannan sosai gwara muje PC kin ga ko kin kayar dani ni daya zanji kunya batare da wani yaji ba.”

“Hhhhh To Ashe dai ana tsoro, Wanda ya Riga zuwa Pcn ma shine Jarumi.” Reply din Nafeesa.

Jameel….

Jameel ne yafara yi mata magana ta private , “Assalam Alaikum, tun yanzu gashi na fara cin nasara.”

Bata Rai Nafeesa tai cike da yanayin shagwaba tamkar yana ganinta ta yo masa reply, “Umm umm Yasin ta katanga ka diro ni ko ta kofa na Shigo nice dai Jarumar.”

Dariya yanayin maganarta ta tabashi domin yanayin shagwaba karara ya bayyana.

Murmushi Ya yi , “To! To!! Yanzu fadamin tsakanin ni da ke waye Jarumin?

Da sauri Nafeesa na wangale baki ta ce, ” Nice.”

“Iye Cuwacuwa kenan kin yi sonkai Amman shi ke nan ba komai aje zuwa.” Cewar Nafseen.

Nafeesa ta ce, “Umm ni kam.

Nafseen yace “Umm ke kam me”? Tace “a’a bance komai ba” yace “faɗi gaskiya zan siya miki sweet” nan take tace “haba kamar wata yarinya” yasa Alamun dariya “to da wace in ba yarinya ba”? Jin yace hakan kawai sai ta sa Alamun tafiya kamar dai taji haushin kiran ta da yarinya da yayi, nan take ya shiga lallaɓa ta har yana cewa “haba jaruma ya kike haka ne kamar ba jaruma ba”! Ai kuwa nan da nan ta saki wani murmushi a zahiri saboda kiran ta da jarumar da yayi ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi  nan take tace “umm umm to ka yarda cewa ni jaruma ce yanzu”? Yace “ai ya zama dole na yarda tunda naga kin nuna jarumtar” cikin mgnr sa sai ya haɗa da alamun gwalo a nan sai ta ƙara cewa “umm wato wayo zaka min shine ka kira ni da jaruma saboda  ka lallaba ni ko”? Yace haba dai wane mutum, ai da gaske ke jarumar ce” tace “to shikenan kaci sa’a da yau idan na tayar da rikici sai ka zo da ƙafar ka ka bani haƙuri zan haƙura” yayi murmushi zuciyar sa cike da mamaki ya fara zancen zuci yana cewa “shin wannan yarinyar me take nufi da cewa sai naje da ƙafa ta na bata haƙuri” nan zancen zuci ya fito fili yace “koda yake meye ma zan tsaya wani zancen zuci muje zuwa dai koma menene  zamu gani idan muna raye”

Ganin shiru bai yo reply ba yasa Nafeesa fadin, “Ko dai kaji tsorone,Hhhh Gaskiya ni Jarumar gaskiyace.”

Tana tura masa karaf Abhi ya kwace wayar batare da taga reply din Sa ba.

“Haba Ammie na tun tuni kina kan waya kamar wata mai aikin office? ga Maryam kin barta gaho ko? To na kwace wayar nan ba zan maido miki yanzu ba.” Cewar Abhi.

Nafeesa ta zaro Ido kan Maganarsa ta karshe cewa ba zai dawo mata da wayarba,,nan take ta tuno Nafseen, lokaci guda kanta ya fara Sarawa ta fara gani bibbiyu, zata…..

🤔🤔 *SHIN NI KADAI NA FAHIMCE CEWA A LAMARIN NAFEESA SURUKANNA NA DA YAWA,NA DAYA BA SUMA TAKE BA,KUMA BA BARCI TAKE BA🤔SHIN ME TAKE??*

Zata fadi Maryam ne ta riketa  Abhi ko yana amsan wayan tafiyarsa yayi bai ma tsaya ba, Maryam ne ta daga ta suka shiga daki  sai kuka Maryam dinma take ta kan yi, aiko abin data sani shi ne ya faru Nafeesa faduwa tayi tamkar wata matacciya gefen Idonta sai hawaye ke fita ga shi bata numfashi,Maryam ko tasa niyyan bazata fada ma su Mammah ba sabida Ita a ganin ta yaushe suka Fita a damuwa kan Nafeesa kuma su kuma komawa  gaskiya gara suyi farin ciki suma, ta dauka alkawarin bazata fada ma kowa ba in sha Allah har sai Allah yayi farkawan Nafeesa.

Maryam Wayan ta,ta dauka ta kira Umminta ta mata bayani sosai kuma ta fahimta itama  anan  ta ce mata zata kwana da Nafeesa Ummi ta amince Mata ta ce, ” Zan fada ma Abban ki kinji.” Maryam ta ce, “thank you Ummi na shiyasa nake kara sonki.”

Ummmi dariya tayi ta ce, ” yadda Kike a Zuciyata haka Nafeesa take kinga ko ba banbanci ko?” Maryam ta ce, ” hakane kan Ummi “, Ummi ta ce to sai anjima ki kula da ita sosae kinji Maryam tace in sha Allah ummi.” sallama sukayi ummi tadan  wayan aranta  ta ce, ” bansan mesa Allah ya daura min  son Nafeesa da tausayin ta ba ya Allah ka yaye ma wannan yarinyan ka cika mata burinta in dai shine mafi alkairi.”

Tana cikin wannan tunanin Abba yadawo ya tadda  ta ya ce, “Lafiya kuwa Ina ta magana shiru?” Ta ce , “hmm Wlh ban san ka dawo ba.”

” haba uwar gida tunanin me Kike hakane Ina Maryam naji gidan shiru anan Ummi ke ba shi labarin abin da ke faruwa shima shiru ya yi ya ce, ” wlh kin ga duk abin da zanwa Maryam Zanyi ma Nafisa,Allah zai cika mata burinta kuma zai yaye  Mata.” da Ameen ummi ta amsa suka wuce ciki .

Abangaren Maryam kuwa  bayan ta ajiye wayan fitowa tayi falo  Mammah ke tambayarta ina Nafeesa Maryam me hanaki  tafiya har yanzu?

 yanzuma fitowa nayi nace Maki yakamata ki koma Gida dare ya yi.”

Maryam ta ce, “Mammah Zan kwana a tare da Nafeesa  harna Kira Ummi na fada mata kinga bata da lafiya kuma Abhi yadawo yakamata a samu Mai zama kusa da ita shine na ce zan kwana a tare da Ita.” Mamma  bata San Erin dadin da taji ba koba komai Nafeesa tayi dace da kawa ta gari bata San da bakin da zata godema Maryam ba. 

“Ngode sosai da Erin abin da Kike ma Nafeesa a lokacin da mutane da yawa suke  kallon matsalanta kaman ba gaske ba amma ke kin tsaya akan Al,amarinta Maryam nagode sosai, Allah saka miki da alkairi .”tana yi tana zubda kwalla Maryam itama kukan ta Fara “Mammah Dan Allah ki daina Fadin haka ki daina kuka.” hannu  ta sa  tana goge hawayen dake zuba  a Idon Mammah, 

“Mammah plzz you have to and rest, stop crying kinga Abhi yadawo zan kula da Nafeesa kar ya ga kina cikin damuwa.”

Mammah ta ce, “to Maryam thanks so much god bless you let me letf but before I have to see Her.” Maryam ta ce, “Ok Mamma amma bacci take a Haka suka shi ga dakin tare Mamma taje ta zauna a gefen Nfeesa addu’ah  sosai ta Mata kan ta fita  a dakin .

Maryam ta kara gyara. Mata kwanciya  tana, ” Nafeesa Allah baki lafiya in sha Allah burinki zai cika,kuma komai ma zai wuce.”

.

Abangaren napseen kuwa, replied yayi da look at that baby girl nifa bana tsoro sai dai aji tsorona Dan kiji .”  ya tura tare da emoji na gwalo amma shiru bega  reply nata  ba kuma ga hiran  nasu yana sashi  nishadi  shirun daya ji  ne yasa ya Kara tura “yeeee itane Ashe taji tsoron ma.. still shiru yace “aa lafiya kuwa ina ga she have a lot to do Bari nima na sauka .”nan ya sauka.

Abhi ko yana amsan wayan ya kashe shi baki daya yaje ya ajiye sai da dare yayi  yadawo daga mosque shida sabeer yake cewa , “Ammyna lafiya kuwa bata fito ba ga lokacin dinner ma yayi.” anan mamma ke gada masa ai bacci take ta yi ma Maryam ma zata kwana da ita nan da nan hankalin Abhi ya tashi meya faru da ita mamma ta ce. “aa ba komai kasan dai yau bata jin dadi ana bukatan ta huta ai karka damu ba komai.”

 amma  Abhi dai hankalinsa bai  kwanta ba ya ce , “to bari na dubo ta amma nan suka wuce dakin Nsfeesa suka ganta tamkar ba rai  a jikinta amma tana numfashi Abhi ya ce, ” Maryam Allah miki albarka .” da “Ameen” ta amsa Abhi ya ce, “to kin ga tana bukatan Hutu amma ta biye  ma waya kinga ma gara Dana amsa .”Maryam kirjintane ya buga taji wani hawaye na bin face nata  aranta  tace “Allah sarki Ahi besan rashin wayan shine ya jepata a wannan yanayin ba amma in sha Allah zanyi kokarin ganin abhi yadawo Mata da wayan amma dole saita hakura da kanta  dole zan bata hakuri ta danne duk abin da zataji tayi ma Abhi biyayya .” 

 Fita su kayi Mamma ta ce, “Maryam ta fito suyi dinner haks nan ta fito amma duk hnklnta bayi  jikin ta .

Nafseen kuwa ta bude data tare da zumudin ganin Erin amsan da samu wajen Nafeesa amma me sai yaji  shiru Kawai ji  yayi ransa ya baci  ma ko group din be shiga ba ya rupe datan sai kuma ya fara tunani shi kadai “to meye ma bashi na damuwa har haka yayi kokarin cire  tunanin ta aransa amma hakan be samu ba Sabida Nfeesa Yarinya ce shagwababbiya Edan yana tuna Erin yadda take masa shagwaba sai yayi murmushi kuma sai yakara cewa meke damu na ne Haka to mema  zaisa na damu haka, Abu daya yake tunawa salon yarinya yana matukar birgesa gata yarinya Amman in tai wani abun babbama ba zai ba, duk abunnan bai taba ganin hotonta ba kuma bai taba tambaya ba Amman yana sawa aransa cewa kyakkyawace ajin farko kamar yadda halinta da kalamanta suke.

 Maryam bayan tadawo addu,a ta karama ma Nafeesa ta kwanta aiko can cikin dare wajen 2:00 taji nafeesa na “Abhhi Dan Allah kayi hakuri kabani wayana na san Nafseeen ya min reply.” Nan take ta fashe da kuka , Maryam ta riketa.

 “Abhi ka taimaka min kaji Dan Allah Wallahi rabani da wayannan kaman Ana min baraxana da rayuwats ne  Abhi plxxx .”

Maryam ta ce, “haba Nafeesa ki dawo hankalinki mana Wai yau ke ce  Kika tashi ba addu’,ah a bakinki keda Kike yima wasu fada  akan addu’ah amma ace yau kene  kika  tashi ba ita?”

nan Nafeesa ta Fara share hawaye ta ce, ” Astagfiirullah addu’a ta fara jerowa tana hawaye tana tuna abin da ya Faru Wai da gaske Abhi ya amshi wayana gaskiya bazan iya jure hakan ba.

 tana wannan tunanin Maryam tace , “Mata babe oya a tashi a yi sallah ko nan ta Mike tayi alwala ta rama dukkan  sallanta ta dear tana edarwa tasa kuka tace, ” Maryam meya hanani tafiya kuma Wai da gaske ne Abhi ya kwace min wayana Maryam Idan ya baki ki bani ne Dan Allah kar kimin wasa kinsan yadda nakejikuwa?”

 Maryam da hawaye suka cika mata Edo ta ce, ‘ nafeesa ki kwanta ki huta zamuyi maganagobe kinji.”

 kuka Nafeesa takara sautinsa “plss Maryam kibani amsa Dan Allah.” Maryam ta ce ,”promise zan fada Miki gobe amma yanzu ki samu ki huta da kyar Maryam ta lallaba nafeesa ta hakura akan sae gobe.

Wa she gari

Ana kiran asuba Nafesa ta Fara tashin Maryam Sabida ita bacci ko na second daya be dauke ta ba hasalima hangowa take Erin amsan da Nafseen ya tura Mata gobe Maryam na bata wayan shi zata fara dubawa nan suka yi alwala sukayi sallah Nafeesa ta ce , “to ban wayan  Habibbty.”

Maryam ta ce, “baby girl ki saurari abin da zan fada Miki .”

Nafeesa ta ce , ,”to ban wayan sai muyi maganar.”

 Nafeesa Maryam ta fada cikin raunanniyar murya Mai dauke da damuwa nan da nan Nafeesa ta ba da attention dinta wa Maryam Sabida  tasan  abind a zata pada Mata yanada mahimmanci.

“inajinki baby girl da farin cikin ki Dana su Abhi wanne kika fi so ?”

Cewar Maryam.

Nafeesa ta ce, ” Na su Sabida suma koda yaushe suna hana Kansu farin ciki domin suga nasamu.”

 Maryam ta ce to, ” yanzu suma suna bukatan taemakonki da kuma kulawanki .”

Nafeesa ta ce , “akan me kenan ?”

Maryam ta matso kusa da Nafeesa tana , “Babe dole zaki yi hakuri da amsan wayan ki wajen Abhi Sabida farin cikin sa domin yana kallon kaman wayan na hanaki  samun Hutu dole ki yadda da abin da yayi kiyi hakura ki danne damuwanki a gabansu dukda nas an da ciwo kan amma kiyi hakan Saboda su nasan edan kinyi haka Abhi zaiji dadi kin bi magna din sa yadda Kike nuna so a wayan ki nuna hakan tamkar be dameki ba Edan har Anga hakurinki wayan zai dawo wajenki soon.”

Tunda Maryam ke mgnan nafesa kafeta tayi da ido ko kiftasu batayi ga farin cikin ta gaban iyayenta wanne zata bi?

Nafeesa ta…

******

Nafeesa Ta Fara Kuka, “Habibbty Ban san ya zanyi da raina ba wallahi,kin fi kowa sanin muradin raina, Amman ba yadda zanyi farincikin Abhi da Mammah ya zarce nawa koda kuwa karshen rayuwatane zan ba su farinciki,na hakura da wayar in sha Allah na hakura.”

Ta rike hannun Maryam gam tana, “Zasuyi Farinciki ko Habibbty? Indai za suyi ya fi nawa mahimmanci na hakura kinji.”

Tsabar Tausayin Nafeesa ya gama mamaye zuciyar Maryam bata San lokacin da itama ta bige da kukan ba, sautin kukansu kadai ke tashi adakin, Nafeesa ta fara sharewa Maryam Hawayen tana, “Habibbty ki daina kuka kinji,bana so ina saku damuwa, In sha Allah zan jure dukkan radadin da zanji Dan ganin na faranta maku ki daina kukan kinji Nima na daina, Amman fa…..

Kawai sai ta kara fashewa da kuka ta kasa karasa maganar da za ta yi.

Maryam ta ja dogon numfashi kan ta ce, ” Yawwa Habibbty Kinga mu yi shiru kar Mammah ta gane ko.”

Nafeesa ta kakalo wani murmushi Wanda da ka gani zaka fahimci cewa na karfin haline.

Maryam ta ce, “Yawwa wai meya farune Ranar Kinje Skul Amman ban ganki ba.”

Nafeesa ta tsaya Chan kuma sai ta ce, “Ranar! Hmm Mutansir ne.” Sai kuma tayi shiru.

Maryam ta zaro ido tare da fadin, “Mutansir me? Me ya miki? Fadamin Habibbty.”

Abubuwan ne suka fara dawo mata cikin wani yanayi kamar mafarki,kan ta ne ya fara juyawa ta fara kallon Dakin Uku Uku.

Tallefa kanta tayi  da hannunta na dama tana, “Maryam ba zan Iya ba ki bar maganar nan kai na zai fice ni ban san meya faru ba.”

Tana gama fadin hakan ta kwanta awajen kamar yadda ta saba ba barci tayi ba kuma ba suma tai ba.

“Innalillahi-wa’inna-ilaihir-raji’un.” Abun da Maryam ke Iya furtawa kenan yayinda hawaye ke saukowa daga idanunta.

Riketa Kawai tai tamkar wata jaririya tana kallonta gabadaya ta ma rasa me za ta yi,ba abun ta kira Mammah ba hankalinsu ya tashi.

Kuka take bilhakki da gaskiya tausayin Nafeesa ya gama mamaye zuciyar Maryam ,ji take inda tanada dama da ta dawo da radadin da Maryam ke ji cikin jikinta.

Chan kuma ta tuna da maganar Nafeesa,  “Habibbty ba abun da ya gagari ubangiji aduk lokacin da wani Abu ya samemu addu’ah ce Kawai mafita koda ace da maganin abun ta addu’ah na kan gaba domin itace babban magani ga dukkan mumini.”

Tana gama tunano maganar Nafeesa ta share hawayen da ke fuskarta kan ta fara jerowa Nafeesa addu’o’i daga bisani ta dauko gorar ruwa ta fara tofa addu’o’in ciki.

Bayan ta kammala Addu’o’in dago Fuskar Nafeesa tai tare da shafa mata ruwan afuska,Sanan ta bude mata Baki kadan ruwan ya samu damar shiga.

Bayan ta gama shafa mata tagumi tai kawai tare da zubawa Aminiyarta ta ido,acikin zuciyarta tana rokon Allah da ya tada Nafeesa ayanzu batare da kowa ya fahimci halin da suke ciki ba.

Kamar wasa Nafeesa ta kusa yin Rabin awa kwance ba motsi ba alamar motsi sai numfashi.

Maryam ta rasa abun yi gabadaya zuciyarta ta jagule kwatsam ta hango inda littafan Nafeesa yake,da hanzarinta ta karasa wajen aiko ta ci Karo da Al-Qur’ani kamar yadda ta aiyya na aranta.

Dauka tayi yayinda tashinta kwatsam ta bige wani littafi takarda mai dauke da zanece ta Fada kasa, batare da ta waiwaba da ta lura takardane  ne kawai sai ta nufi inda Nafeesa take.

Dai,dai lokacin  da wannan takarda ta fada kasa,Nafeesa ji tai tamkar allura akayo mata, a hankali take fadin, “Kin Yar min da shi,ki daga min shi,nace ki daga shi.”

Tsayawa Maryam tayi cak kasancewar tana jin magana Amman ta rasa ta inda maganar ke fitowa.

Nafeesa ta kara da”Habibbty nace ki daga min shi,ki daga min shi.”

Cikin dimuwa Maryam ta kalli Nafeesa tare da waigawa kallon inda Nafeesa ke nuni da hannu,wannan takardarce dai data bige batare da saninta ba.

Da sauri ta karasa tare da dagawa zanene ta gani irin Wanda Nafeesa ta sabayi akullum tana fadin cewa Nafseen dinta ne.

Mik’o mata hannu Nafeesa ke yi alamar ta bata zanen.

Karasawa gareta tayi tare da mika mata, kamar wasa Nafeesa na karban zanen ta dawo normal tashi tayi ta zauna tare da jero addu’o’i.

Bayan ta kammala ta shafa hamma ta fara” Habibbty wallahi yunwa nakeji muyi wanka na San Mammah ta kammala Abinci yanzu.”

Maryam da ke cikin tsananin mamaki ta ma rasa bakin magana murmushi tayi tare da girgizawa Nafeesa kai kawai.

Ta shi tayi tayi wankanta tsaf Kai kace ba ita ba,Abu dayane kawai da ya tsaya mata rashin waya ga shi ta tsinci kanta da tsananin son ganin sakon da Nafseen zai yo mata,amman in ta tuna da maganar Maryam sai tai kokarin kawar da damuwarta.

Bayan ta fito daga wankan zama tai bakin gado dauke da zanen sahibin nata ahannu sai kallo kawai take tana ta sakin murmushi,Allah ne  kadai ya San me take aiyyanawa cikin ranta.

Fitowar Maryam daga wankane ya katse mata tunani, “Habibbty abani kaya in Sa,kin San dai ba zan maida na jikina ba.” Cewar Maryam.

Dagowa tai ta karewa Maryam kallo cikeda shagwaba take maganar, “Haba Habibbty wannan ai wulakancine kayanma sai na baki? Yaushe ki ka zama haka,ni fa bana so Allah na Fada miki ban so.”

Murmushi Maryam ta yi, “To al-shagwabatu bara in dau abuna.”

“Eh din naji.” Ta kare maganar cikin murguda baki.

Maryam ko ba abun da take ban da dariya.

**Bayan Maryam ta shirya tsaf riko hannun Aminiyarta tai tare da fadin, “Oya bebe Muje aci abinci tun tuni kike kukan yunwa Amman tunda kika dau Zane kin manta da komai.”

Sai da ta ajiye takardar zanen tamkar kwai Dan tattali kan ta ce, “Habibbty Zanennan tamkar rayuwata yake, na kan kasa ganin komai aduk lokacin da ba glass a idona Amman ban da wannan zanen kullum cikin shege yake ga idanuna,ina son zanen nan fiye da tunaninki,kinga ko ba ma yunwa ba zan Iya daina jin komai,mantawa da komai aduk sanda nake tare da shi.”

Maryam ta kara janyota tare da fadin, “Kinga nifa yunwa nake ji muje kawai.”

PSuna fita kuwa suka Tarar da Abhi Da Sabeer zaune Mammah na zuba ma su abinci.

Murmushi Abhi ya yi, “Ma sha Allah,Ammie na ta fito, kinga karfan wayannsn jiya fa har kiba kika kara aiko ban baki ita yanzu kam.”

Daga Nafeesa har Maryam wani Ras sukaji acikin ransu,cikin sauri Maryam ta radawa Nafeesa magana akunne aiko ta sake murmushi tare da fadin, “Ina kwana Abhi,Ina kwana Mammah,Ina Kwana Little Bro.”

Daga Abhi har Mammah amsawa sukai cike da fara’ah.

Sabeer ya ce, “Ina kwana Anty.”

Maryam ma gaishesu tai suka amsa kamar yadda sukaiwa Nafeesa.

Mammah ta zubawa kowa na shi Nafeesa ta ce ,”‘Ni bana ci na Abhi na zance.” Cikin shagwaba.

Abhi ya ce, “Sorry Ammiena zo muci waya isa hanaki cin abinci da Abhin ki.”

Kusa da shi ta koma ta zauna sannan ya fara bata abaki tana ci,ban da shagwaba ba abun da Nafeesa ke zubawa Abhinta kowa kawai sai dariya domin inda sabo an saba Da ganin halin Nafeesa in tana tare da Abhi.

Suna gama cin abinci Abhi ya ce, “Oya Ammiiena ta rufe Ido,ita zan fara yiwa kyauta agidannan.”

Cikin Sauri kuwa ta rufe.

Kwalin waya ya Ciro awata Leda kirar INFINIX Sabuwa gal, Murmushi Yayi Oya bude.

Tana budewa me za ta gani,sai waya, bata san lokacin da sake wani irin ihu ba cen kuma sai ta ce, “Alhamdu Lillah, Na gode Abhi na.”

Ta rungumesa.

Ba karamin Dadi Maryam taji ba aranta domin ta san matsalar Aminiyarta ta kau kenan.

Sabeer ya ce, “Abhi to ni fa?”

Murmushi Abhi ya yi, “Sabeer kai kam agogo ne na siyama domin ba ka kai rike waya ba Amman in ka kai nama alkawari.”

Karban agogon yayi yana Murna tare da godiya ga mahaifin nasa.

Maryam kuwa miko mata wata sarka Abhi ya yi cikin fara’a yake fadin, “Na san dai duk kinfi karfin wannan Amman karamar kyautace na miki daso Allah yayi albarka.”

Murmushi Maryam tai ta durkusa har kasa ta karba , “Na gode Abhi Allah kara budi.”

Abhi ya amsa da “Ameen, kallonsa ya koma ga Nafeesa.”yawwa Ammina Bana so hankalinki kullum yana kasancewa kan waya ki tuna cewa yanzu kika fara karatu indai kina son muna shiru to ban da shiririta,kuma ki kulama da lafiyar idonki,ga dayar wayar nan ki kwashe abubuwan ciki.”

Nafeesa ta ce, “In sha Allah Abhi na gode.”

Mammah ta bata rai , “ka gama da kowa wai ni ba za azo kaina bane?”

Duka falon suka fashe da dariya.

Abhi ya ce, “Sorry madam naki ai na mussamanne.”

Daga nan suka bige da hira ita kuwa Nafeesa tuni ta dauki tsohuwar wayarta tare da shiga whatsApp.

Kamar yadda ta saba sakonsa take fara dubawa.

Tana Shiga………..

Dai,dai da lokacin da ya sauka online .

Murmushi ne ya fara bayyana afuskarta, tamkar tana gabansa take jin kan ta alokacin.

Kara gyara zama tai tare da karin sakar wani murmushin mai banbanci da na farkon domin wannan na mussamanne, shagwabe fuska tai tare da yo masa repy mai nunin ga yanayin da take ciki, wato emojin Shagwaba ta fara sawa kan ta ce, “Umm Uncle Allah ni fa jarumace,kuma in ka cigaba da mun dariya kuka zan yi, mu yi baram-baram ba ma ruwana da kai,sai ka ce min SORRY Anty Nafeesa.” 

tana gama turawa ta kalli online status dinsa minti hudu kenan da saukansa,bataji dadi ba sam har cikin ranta, wani irin yanayi ta tsinci kanta da bata san dalilin hakan ba, rufe datar wayarta tayi kawai tare da daukan Al-Qur’ani ta fara karatu, sai da ta karance Surutul TAUBA tas kan daga karshe tayo addu’o’i nan take taji wani irin sanyi na ratsa mata zuciya tare da shaukin so na mussamman, Murmushi ne ya bayyana afuskarta da ka kanga zaka fahimci cewa tana cikin wani yanayi na mussamman wanda za a iya alkantashi da shaukin SO!

Ajiye Qur’anin ta yi tare da daukan jerin littafan Masoyin nata da ta saba karantawa a kullum batare da ta gajiya ba.

Falo ta fito ta tattarar da Mammah,Sabeer da Maryam sun kunna wani hausa film.

Har zata zauna sai ta tashi tare da gyatsine fuska tana fadin, “wannan kallon naku ma ba bari na nai karatun zai ba gwamda na fita fasej hankali kwance.”

ta kare maganar tare da gyara glass dinta.

Ba wanda ya kulata, kamar ance ta jiyo kawai sai taga an rubuta STORY AND SCREENPLAY BY JAMEEL NAFSEEN.

Gabadaya suna gani kallonsu ya koma ga Nafeesa suka bar ta T.V

Wayancewa tayi cikin salon shagwaba tare da tebe baki, “Umm nama fasa fitan,anan zan yi karatun kuma kar kowa ya dameni.”

Mammah ta kalli Maryam kan ta ce, “Maryam Anya MARUBUCIN NAN zai yi kyau kuwa? chanja mana wani kawai.”

Maryam ta tashi zata chanja Nafeesa tai sauri tare da tare gaban TVn “Ayyah Mammah zai yi kyau wallahi ku tsaya mu kalla nima kallon zan yi shine ya rubuta fa.” ta rufe fuskarta batare da ta kara fadin komai ba.

Mammah ta dalla mata harara , “Shi wa? Ammien Abhi ki kiyayeni fa tam.”

 Nafeesa ta tabune baki, “Umm Mammah ni yau kallo na ke son yi ko abarni ko in fadawa Abhi ya zane mana ke.”

Mammah ta sake baki, “Iyeee? Lallai Mamana, Allah shiryamun ke, na san zaki iya hada bom din da yafi hakama asha kallo lafiya.”

Gwalo ta ma Mammah tana, “Hhhh Ashe ana jin tsorona ma.”

Murmushi Mammah kawai tai azuciyarta tana kara jin son yartata matukar gaske,mussaman inta dubi halin da Nafeesa ke ciki ta fannin Ido tana matukar tausayin ‘yartata, abu daya ke kwamtar mata da hankali yadda Nafeesa ke cire damuwoyi aranta, ta nuna kamar komai bai faru.

“Laaah Mammah ba an Hana Anty kallo ba saboda idonta?”cewar Sabeer.

Nafeesa ce ta kallesa cikin sauri, “To daman ni ina kallonne dan dai yau zan yi shine ake bakin ciki.”karasa maganar tai tamkar zatayi kuka.

Da sauri Mammah ta katseta , “Miye na kukan? ki rufamun asiri dan Allah muyi kallo na yau dai daya, ni ai ina son ganinki cikin walwala Mamana kinji, oya SMILE.”

Tasowa tai daga inda take tana gyara glass dinta ba inda ta nufa sai wajen Mammah kifa kanta tai akan cinyarta tare da dasa idonta ga talabijin din domin yin kallo.

Mammah ta ce, “Allah Mamana mijinki ya shiga uku da son jiki, ni kam anya zakina aiki ma kuwa?”

Nafeesa ta ce, “Umm bayan tare za mu je kina yi mana ko kin mantane?”

Duka Mammah ta daka mata abaya , “Mara kunya kawai.”

Dariya Nafeesa tasa, “Umm daman so nake ki bar ni nai kallona.”

kallo suka farayi abin Mamaki yau ga Nafeesa gaban Tv na kallo har bata so wani yayi magana akatse mata, ban da murmushi ba abun da ke bayyana afuskarta da ka ganta zaka fahimci cewa tana cikin yanayi mai dadi, mussaman in ta ga ALI NUHU wanda yafito da sunan jaruminta NAFSEEN aciki.

Suna cikin kallo dif nefa suka dauke huta,gwalalo ido Nafeesa tai tare da karewa falon kallo shin da gaske daukewan sukai ko kuma ya?.

ta shi tai ajikin Mammah ta zauna tare da yin tagumi tamkar wadda akayiwa rashi,hawayene kawai ya fara bayyana daga fuskarta.

Mammah tsabar Mamaki ta ma rasa bakin magana,Sabeer kawai kallon Antyn nasa yake, Maryam ce ta tashi tare da karasawa ga aminiyarta ta.

Cire mata hannun tai daga tagumi tana, “Habibbty miye haka? miye na kukan kuma?”

Shiru Nafeesa bata da niyar yin magana.

Maryam ta cigaba d magana tare da share mata hawayen, “Haba Habibbty kan kallo wai kike kukan nan? to kalli Mammah kiga itama kukan take.”

Gabantane yafadi ras jin cewa Mahaifiyarta na zubda kwalla 

Can kuma tintsirewa da dariya tai ta tashi tana tsalle, “Yau dai naga kukan Mammahna, daman ban taba gani ba ysn.”

Da taga abun dai da gaskene Mammah kuka take tsayawa tai shiru kan ta durkusa gaban Mammah,hawaye ta fara share mata, “Mammah na, Allah wasa nake ki daina kuka kinji in kika cigaba nima zan yi,am sorry Mammah.” ta kare maganar cikin shagwaba tare da riƙè kunnuwanta da hannu.

Mammah ta kawar da kanta daya barin, Nafeesa ta riƙè hannun mahaifiyarta ta tana,”Smile Lovelyn Abhi, ni ba ruwana inya dawo ya ga kina kuka dariya zai yi yasin,kuma ma yace shi baya son mata mai kuka kinga kenan za akaro mana Anty ko?” ta wangale baki alamar murna zance ko mamaki ma.

Harara Mammah ta fara bin Nafeesa da shi kan ta   tashi tana, “Ki rabani da maganar Wata Anty in ba so kike inyi jajjagenku daga ke har Abhin ba.”

Nafeesa ta bita tare da rungumar bayanta, “Mammahna tafi ta kowa, Am so sorry please, ban san zaki shiga damuwa bane kin san da ba zan yi hakan ba, Ki yafemun kinji,kada Allah ya yi fushi dani sanadina kin zubda hawaye, Ki yafemun sannan kiyi murmushi kinji.”cikin salon shagwaba take maganar

Mammah ta juyo da Nafeesa gabanta tare da kallon fuskar ‘yarta ta cikin salon so da kauna.

“In sha Allah,Allah ba zai yi fushi dake ba tamkar yadda nima ba zan yi fushi da diyar kirki ba,ina son ki Mamana,Allah raya mun ku cikin aminci,ba na so kina damuwa da kananun abubuwa kinji,Abhinki ba kowa bane sannan Mammanki ma ba kowa bace,duk da na san kin sa hakan aranki amman a kullum ina kara yi miki tunine domin ban da burin da ya wuce rayuwarki ta inganta, na san wa ki ke so,na san burinki amman ba abunda muka isa yi,mun barwa Allah zabi,ba zan hanaki bin muradin ranki ba,amman ina so ki sani ki kara sani mutuncin ki na ‘Ya mace ya fi komai mahimmanci arayuwarki,ki rike kan ki,ki san darajar kan ki ako ina ako da yaushe kuma,ki lura ,a yanzu kam ke ba yarinya bace kinji ko Mamana.” Cewar Mammah tana shafa kan diyarta ta.

Murmushi Nafeesa tayi , “Maddallah da samun uwa ta gari,ina alfahari da ke Mammana,ina sonki,so mara misaltuwa,Allah sa inga tsufanki.”

Mammah tayi gaba tana, “Allah shiryamun ke ni ma din ba abari ba a tsokanar,Maryam kawar nan taki tana bukatar ganin likita.”

har cikin ran Maryam tsarin gidansu Nafeesa na matukar birgeta, ba su da kudi amman sunada wadatar zuci ga rayuwa cikin farinciki gwanin sha’awa maganar Mammahne ya katse mata tunani, ta sake murmushi tana fadin, “Mammah ai inaga Asibiti za mu kai Habibbty aduba mana ita.”

Nafeesa ta tebe baki, “Yasin ras nake, na ma fi ku lafiya ehee.”

Maryam ta ce, “kyaji da shi nikam ki rakani, muje in tafi gida.”

Nafeesa ta ce, “Tab ai sai dare.”

Har Mammah zata shiga daki ta juyo tana, “Aa fa kul ta tafi gida yanzu, kina gani anbarta ta kwana tun jiya yau kuma ta kai dare,maza rike hanun Sabeer ya rakaki ku rakata.”

Nafeesa ta shagwabe fuska tana kokarin kuka, Mammah ta kara da, “Laa kar ki, kuskura Gobe ai da kwai makaranta kwa hadu acen amman yanzu kam Maryam na da bukatar komawa gida.”

Ba ason ran Nafeesa ba haka ita da Sabeer suka raka Maryam ta hau nafe.

Tana komawa gida sallah tayi tana idarwa kuwa da zumudinta ta dauki wayarta tare da kunna data…

Messages ne suka fara shigo mata, zuba ido kawai ta fara yi tare da jiran sakon abincin ruhinta, da mamaki har sun gama shigowa amman ba ta ga nashi ba, sannan ko nuna alamar yana online ko ya zo online din ma babu.

Wata ajiyar zuciya Nafeesa ta sauke, ta dafa hannu a bangaren kanta, tsintar kanta da karanto INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN ta yi. 

Nan take ta ji wani sanyi a ranta.

“Allah kenan!”

Abun da ta iya furtawa kenan, sannan ta kara riƙe wayar hannunta gam, group din marubuta ta leƙa, ai ko ban da zuba ba abun da marubutan ke yi kamar ‘ya’yan kanya, hira cikin nishadi da barkwanci suke, wani sa’ilin su juya wa’azi ko wani bangaren na daban a cikin wannan group, kai duk tsegumin da kuke tunani to ya fi karfin hakan.

Murmushi ta sake a zahiri tare da fara bin hirar cikin group din, aranta tana sa ran  cewa za ta iya gamo ko cin karo da hirar masoyin nata amman kash, har ta kai ga karshe ko alamar gilmawarsa ba ta gani ba.

Sallama ta yi cikin group din, cikin sa’a kuwa a amsa mata wajen mutane biyar a lokaci guda.

Cikin hirar da suke kawai ta tsinduma inda aka sa daya daga cikin marubutan a gaba da tsokana, SAIFULLAHI MUHAMMAD LAWAN duk da kasancewar yana da baki amman taron dangin da aka yo masa ya sanya shi yin tsit, ita kuwa Nafeesa abun nema ya samu tuni ta shige masa fadan tare da ba kowa amsa daidai da shi.

Dariya ya fara yana mai jin dadin ya samu ‘yar team, tun dai ana gabzawa har da karshe fadan ya juye izuwa barkwanci da hira mai cike da nishadi da walwala, har ta rufe datarta kasancewar dare kuma gobe tana da skul, a zahirance bata da wata damuwa amman cikin zuciyarta damuwa ce fal domin tana da muradin jin lafiyar sahibinta, sai da ta yo alwala tare da sallah raka’ah biyu kan ta kwanta cike da yin addu’o’i kamar yadda ta saba kullum.

A bangaren NAFSEEN kuwa, gabadaya aiki ya yi masa yawa ba shi da lokacin wani abu ban da aikin da ke gabansa, a duk lokacin da aiki ya masa yawa irin haka bai samun damar hawa social media  bare ya yi chatting sai tsakar dare yayin da komai ya lafa masa, mussaman in bai gaji da yawa ba.

Yau ma kamar kullum, karfe sha-biyun dare daidai ya kunna datar wayarsa domim duba sakonni yadda ya saba.

Abun mamaki da bai karewa dangane da Nafeesa Cikin barcinta hakan ya zo mata, abun da ke faruwa azahiri.

Daukan wayarta tai kamar yadda shi ma ya yi, messages din da yake tsammani gun abokan aikinsa ya fara dubawa tare da yi masu reply kan ya dawo kan ‘yan uwa da abokan arziki.

Idon Nafeesa na kan Numbersa mussaman da ta ga yana yi mata typing gyara zama tai ji take tamkar ta kwato ta ji abun da yake rubutawa alokacin, ban da murmushi ba abun da ke bayyana a fuskarta.

“Iyee Antynwa?  See dis rigima girl, an ki ace Antyn.” Reply din NAFSEEN.

Cike da yanayi irin nata na shagwaba ta ce, “Ni ko? To ma ka daina kulani, kuma ba ruwana da kai, Uncle mai kan gwangwanni kawai.” 

Dariya maganarta ta ta ba shi har cikin ransa ya ce, “Sorry, dawo Momy Nafeesa ma ba Anty Nafeesa ba, shikenan ina mun shirya?”

“Yeess mu kulla tunda da mun kunce ne ma.” Nafeesa ta yi masa reply cike da dariya tana mai jin dadi.

Ya ce, “Ok, to amman waye mai kan gwangwannin? Momy Nafeesa ce ko? dan ni dai na san Uncle ba ya da                     kan gwangwani.”

“Umm… Umm… Ni dai yasin ba ni ba sai dai Uncle, shi ne mai katon kai irin na gwangwani.”

Murmushi ya saki, har a zuciyarshi yana jin dadin yanda suke chat da yarinyar nan, ga barkwanci kamar ‘yar mahauta, ga uwa-uba shegiyar shagwaba. Ya sake murmishi a karo na biyu kan ya tura mata da, “Byee Momy mai kan gwangwani aiki zan yi yanzu, kuma kin ga dare yayi sha biyu daidai, a yi barci kar Mama ta miki fada ko ki kasa ta shi sallah.”

Ba ta so hakan ba ko kadan domin ji take zata iya kwana sannan ta yini in dai suna hira ne ba tare da ta taba gajiyawa ba, amman a yanzu ba yadda ta iya ko dan farincikinsa yadda ya bukata dole ta sauka.

“Nyt Bye, bye Uncle mai kan bera, kuma yasin ni ba na makara ni ke tashin limamin unguwarmu ma.” ta rubuta ta tura masa, ji take rabuwa da shi tamkar rabuwa da numfashinta.

Batare da ta bare ta ga sakon da zai turo ba ta kulle data tare da gyara kwanciya, ta so kam ta ga amsarsa amma gudun kar ya fahimci tsananin kaunar da take a gare shi ya sa ta sauka, tana jin wani sashe na zuciyarta yana mata radar ta sake kunna datar amma ta basar saboda tsaro.

Duk hirar da Nafeesa tai kar ku ji mamaki in na ce maku a cikin barcinta ne batare da ta farka ba har yanzu, to shin da wa Nafseen ya yi chatting? Nafseen ce ko kuwa? 

Al’amura boyayyu  suna da yawa wanda muna bukatar saninsu…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *