ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Haana Umma ta kira ni, to yanzu ya za ayi? Ko mu Karasa bakin (gate) ko ya zo mu yake jira? Don kin san ba shi da wayar mu bare ya kira ya ce mana mu zo ya dawo”.
“Gaskiya ne kuma, mu Karasa kada na fara yin wani laifin da ba nawa ba ya ce na shanya shi, don ni na kasa gane kalar sa wallahi”.
Haka suka Karaso suna zuwa ba su ga kowa a gurin ba-sai iya motar sa kawai da wani mutum a tsaye kamar mai gadin motar, Haana ce tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
” – “Zahra ga dai “‘motarsa can*muje ma tambayi wancan mutumin ko ina ya shiga”. “.“ Kashe motar ‘suka yi suka nufo’ “shi, sallama suka yi masa ya amsa nan suka tambaye – shi ina mai motar don Allah? Nan ya basu amsa ~ da cewa.
“Dama ni ya bari ya fade min za kuzo karber moter ku, da fatan dai kune?” Cikin sauri Haana ta ce, “Eh mune to ina moter?”
“Yauwa, yace dama idan kunzo sai ku danyi hakuri dan fito naje na kirawo shi, don wani Uziri zai tsayayi”., Murmushi tayi tace, “Babu laifi malam, idan ba zaka dade ba zan jira ka”. ” , “Ba zan dade ba, bani minti biyar yanzu _ -zaki gannu”.Dai dai-da lokacin da wayar Zahra ta fara Kara, tana dagawa ta ga sunan Umman su ne. Haana ga Umma tana kira”. ” “Kije kawai naga alama ta matsu da zuwan naki, ma yi waya idan na isa gida”. “Babu komai dai ko Kawata?” _ Murmushi tayi ta ce, “Babu komai Zahra na, ki daga wayarta kar ta katse sai muyi waya”. Haka ta daga wayar tana tafiya tana mata _ magana har ta shiga mota tana daga mata hannu suna musayar murmushi, haka ta ja ta fice. Shima. dan jiran moter Malam M.J ya shiga Www.bankinhausanovels.com.ng
“motar ya yi. ficewar sa, ta tsaya tana jiran dawowar sa. . Shiru-shiru Haana tana jira, gashi ta kashe sama da mintinan da ya ce, har ya kai kusan “ minti na ashirin. Nan take ta soma jin ranta ya baci, sai tayi kamar za tafi sai wata zuciyar ta ce ki tsaya ki gani tunda ki ka ga hakan wani abu ne Kila ya tsayar da shi. Haka Haana ta ci gaba da tsaiwar jira, duk ~ wanda ya shigo ko zai fita sai ya ganta, ranta ya yi mugun baci, haka duk wanda ya zo wucewa zai tsaya ya tambaye ta ko lafiya? Sai ta ce motar ta ce ta samu matsala, yanzu za a dawo mata‘da ita. SO, Ranta ya. gama baci, sai kawai ta bude jakarta da niyyar kiran su Zahra ta gaya musu – ‘cewa ga abinda ya faru, tana jiransa har yanzu bai zo ba. Wayam ta nemi wayar ta bata gani ba, nan take tayi wani uban tsaki don ta tuna ta – manta wayarta a cikin motar Zahra kan sit din da ta zauna. . A Kalla sai da ta shafe kusan. awa guda, ranta ya yi mugun baci da jiran Malam M.J, babban abin da yasa ta dade haka saboda ta rasa yadda zata yi da tuni ta kira direban su ya zo ya dauke ta, to babu wayar kuma bata rike (number) dinsa ba bare ta ara ta kira. _ Haka ta yanke shawarar ta fita ta dauki Adai-daita sahu ya kaita gida, tana fara tafiya sai ta hango mutumin nan ya nufo ta cikin’sauri. Ranta bace ta amsa sallamar da ya yi mata, sannan ta daure fuska tana jiran taji me. kuma zai ce da ita?”Wai ya ce kiyi hauri za ki iya tafiya, gyaran ne ba a yi ba, wai gobe kwa hadu shi ya wuce gida sauri yake” Kallon raini tayi masa don ji tayi kamar ta samu abin duka ta doka masa, domin ta gane shima Www.bankinhausanovels.com.ng dan rainin hankali ne don ta ga daga inda ya taso, wato sa shi yayi ya fada haka. . . Tsaki ta sakar masa domin abin ya yi matuKar bata mata rai, nan take tayi tafiyar ta Tana zuwa bakin (gate) tayi sa’a ta samu ~ Dan Sahu ta haye, nan ta juyo ta hangi mutumin nan yana mata dariya, don magana -suke yi da wani. Hmm! (plan) din’ Malam M.J kenan akaina? Ya yi kuma ya ci nasara, amma ya shirya nima sai nayi masa wulaKanci, sai dai ko me zai min yayi cikin makarantar nan. Ya bata min lokaci son ransa safe da rana, muje zuwa, sai ka gane ko ni wace domin babu mutumin da ya isa ya wulaKanta ni”. Da wannan tunanin suka ja suka tafi. Tana shigowa cikin estate dinsu ta fara > tunanin ya zata yi da batun motar data fita da ita? Nan take dabara ta fado mata, sai tayi Har bakin (gate) dinsu ya kaita, ta zaro. dari biyar ta bashi, zai bata caji ta ce yaje.kawai. Farin ciki ya kama shi, ya tafi yana mata godiya. Tana shiga falon Granny ta fara gani zaune a falo tana kallon tauraron dan Adam tashar Saudi, da saurinta taje ta fada kan cinyarta kamar yadda ta saba kullum. Tureta ta shiga Kofarin yi, ta ce, “Kai Raihana, ban san lokacin da za ki bar min wannan Kafar tawa ta huta ba, ke kenan kullum sai kin daneta, ke kiyi Kannen ki ma suyi”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya tayi ta ce, “Kai Granny, kin san babu abin da nake so idan na gaji kamar wannan cinyar taki mai dadin kwanciya”.”Ai kuwa kina daf da Karasa ta matukar ba za ki bari ina hutawa ba”. Cikin sauri ta dagata, ta ce, “To na daga ki don bana so na Karasa ta”.Dariya suka yi gaba daya, Granny ta ce.. “Raihanatu, sai naga kamar lokacin da kika fada za ki dawo ba shi ki ka dawo ba, ko wani abu ne ya tsayar da ke?” . Nan da nan damuwa ta bayyana a fuskarta, domin da ita ta shigo ganin Granny a falo da tayi ta soma manta damuwarta, domin tana matuKar — Kaunar kakarta, duk lokacin da take cikin damuwa da ta ganta sai ta nemi damuwar ta rasa. ‘”Granny matsala na samu amma bari naje na shirya daga nan na cika cikina”. Tana miKewa sai ga Amminta tayi mata barka da gida sannan ta wuce abinta, ta dawo ta ga duk Kannenta sun kewaye Granny suna ta hira. Ranta ya yi mata dadi don ko da yaushe dai-dai wannan irin lokacin sukan saka su nishadi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kannenta da suka ganta sai suka shiga murna suka yi mata sannu da zuwa. Abincin da ta dauko zata ci duk suka saka mata hannu suna ci tare kamar basu ci ba, don haka Allah Ya yi su da son junansu, duk abin da daya yayi dan uwansa sai ya yi tsabar shaKuwar da suka yi da Sun gama da komai suna hira sai ga mai gadinsu ya yi sallama ya shigo, ya ce. .Wai ga wayar Haana Zahra ce ta aiko direban gidan su ya kawo”.
Da murna ta karba. ‘ Ammi ta ce, “Au,wayar taki a can makaranta ki ka yar?” Eh a motar na bari da mukataho”.Ke ina motar taki? Ba da ita kika je ba?”
Nan take ta ce, “A’ah, mun fita ne wata dubiya daga makarnata, shi ne na manta ta a — ciki”.
– “(Okay) babu laifi”. – Sai bayan sallar magariba ne suka samu _suka kebe ita da Granny, sannan ta kwashe duk abin da ya faru ta fada mata, don ba zata iya boye mata komai ba, don matuKar ta fadawa Ammi fada zata yi mata sosai, domin ita bata. ragawa kowa a cikin gidan matuKar mutum ya yi. ba dai-dai ba. Ga mamakinta sai ta ga Granny ta rufe ta da fada sosai kan abin da tayi bata yi dai-dai ba, sauKinta daya. da Allah Yasa malaminsu ta ‘barwa motar. Fada tayi mata sosai akan cewa dole gobe idan taje makaranta taje har (office) dinsa ta bashi haKurin rashin kunyar da tayi masa, idan ba haka ba kuma da kanta zata kira mahaifinta daga tafiyar da ya yi ta fada masa abin da ta © yiwa malamin ta.
Tsorata tayi, taji dama bata fada ma Granny abin da ya faru da ita ba, domin ta san duk abin da ta ce zata yi to zata iya, ita kuwa da akai Kararta gurin Abbanta gara ta je ta bashi hakuri ko da zai wulaKanta ta, don ko kadan bata son saka Abbanta cikin damuwa kamar yadda shima bai so ya ganta cikin damuwa. Cikin sanyin jiki ta fito daga dakin — Granny, don ta ga yau hirar tasu ba zata yi armashi ba. ° Www.bankinhausanovels.com.ng
Dakirta ta dawo ta dauki wayarta ta kira Zahra ta fada mata duk yadda abin ya faru bayan sun ; rabu. Dariya tayi mata sosai hade da cewa, “Amma Malam’M.J ya burge ni, gaba ba zaki sake yiwa wani haka ba, don da ina da yanda zanyi da na yi masa kyautar abin da ya yi miki dazun”. Nan ta kawo ta wuya, ta ce, “To muguwa, ki jira kiga yadda zamu yi da shi, wallahi sai na . bashi mamaki, ba dai ni ya yiwa haka ba? Lokaci _ guda duk ya yi nasara akaina, na fadawa.Granny ta goyi bayansa haka kema”.To ai gaskiya ne, kowa yasan abin da kika yi ba ki kyauta ba, kama wannan danyen kan da kika fara irin su Malam M.J sune dai-dai dake”,”Ke kada ki cika min ciki da wani Malam M.J ki Kara sani tsanarsa kan wacce nayi masa, sai anjima”.Tana gama faidin haka ta kashe wayar, bata jira ta ji amsar da zata bata ba.
Bayan ta dan huce ne sannan ta janyo (i pad) dinta kamar yadda suka saba a kowacce
rana ita da yayanta a can Kasar da yake karatu, nan take ya bayyana cikin (screen) yana fara’a. Bayan sun gaisa ne ya ce, “Little”. , – Sunan da yake kiranta kenan lokuta da dama, wata rana kuma yace da ita Haana kamar yadda kowa ke kiranta. _Yanayin ‘kalar shagwaba tayi masa kamar yana gabanta, ta ce. . “Ya Abba, Granny ne da Zahra suka saka ni damuwa”. “Subhanallahi Garin yaya hakan ya faru? To gaskiya ba su kyauta min ba, musamman . Granny da na bata amanar ki akan cewa kada ta sa ki damuwa, kuma kada ta bari wani ya saki . damuwa, sai gashi da kanta ta saki ta kuma bar wata itama tasaki”,Ganin yadda ta ga shima ya shiga damuwar nan da nan taji ranta bai so ba, domin haka Ya Abbanta yake matuKar tana da damuwa idan ya tashi nunawa sai nashi yafinata. … Nan da nan ta ce, “(Relax) Ya Abba, bari _ na fada maka me ya faru”. Do Tiryan-tiryan ta gaya masa duk abin da ya faru da ita a makaranta har kawo lokacin da suke maganar duk ta gaya masa.Abin mamaki tana gama fada masa sai ‘kawai ta ga ya kwashe da dariya, sakin baki tayi “tana kallon sa. “Ya Abba me kuma ya baka dariya a ’ ciki?” Da Kyar ya tsayar da dariyar, ya ce, “Little wannan Malamin naku dan duniya ne, lallai yasan kan tsiya, na tabbata ya yi hakan ne don ya rama abin da kika yi masa” “Nima haka na yi zato, amma wallahi sai na rama abin da yayi min ta wata hanyar, yadda zai gane nima ramawa nayi”Girgiza kai yayi, ya ce, “A’a Little ban yarda ba, malamin ki ne kuma wanki ko babanki, — _ ba zan so naji ance kin yiwa-na gaba dake rashin kunya ba”.. Tab Wallahi ni.dai wannan bai isa ya haife ni ba, za fa kuyi kusan (age mate) shekaru dayada shi”..”To naji, duk da haka babu rashin kirki Www.bankinhausanovels.com.ng
tsakanin ku tunda malamin ki ne, domin idan har
ya dana miki sai kin ta samun matsala akan (course) dinsa, gwara ko me zai miki ki kau da kai kada ki yarda wata matsala ta shiga tsakanin ku, domin ja da (lecturer) ga dalibi ba abu me mai sauki ba, don na san yadda suke, (just) dai ~ kawai kikiyaye”, ‘
Sum jima suna hira da shi daga baya ya koma shima kamar yana bin bayan sa, nan take a daren taji ta tsani Malam M.J, domin babu wani da ya goyi bayan tayi masa rashin mutuncin da ya yi mata.
Da gari ya waye ta shirya tafiya makaranta — kafin ta tafi sai da Granny ta kirata tayi mata nasiha akan taje ta nemi Malam M.J ta bashi hakurin abinda tayi masa, kuma ko me zai yi mata kada ta daga ido ta dubeshi da niyyar rashin kunya, domin ta san ba halinta bane hakan. .
Tabbas ta dauki’ nasihar da Granny tayi mata domin ta wargaje mata dukkan shirin da tayi na daka Malam M.J matuKar ya zo mata da wata fuska ta rashin mutunci, nan tayi mata alKawarin insha Allahu babu abin da zai faru sai alheri. Www.bankinhausanovels.com.ng
‘ Murmushi tayi nan take ta shiga saka mata albarka kamar yadda ta saba yi mata a ko da yaushe.
Tana fitowa ta nemi Mal. Hamza (driver) ta ce ya kaita makaranta, domin tun jiya ta fada masa don bata son tafiya da wata motar Mal. M.J ya kawo mata waccan. Yana ajje ta ya juya ya koma gida abinsa. Kai tsaye (class) ta nufa, nan ta tarar da su Zahra suma sun zo, tana shiga‘sai ga (lecturer) – dinsu ya zo Dr. David, nan suka shiga (lecture) ’ dinsu. _ Sai bayan da suka gama ne ta samu damar ” sanar da su yadda komai ya faru da ita, dama ta fara gaya ma Zahra zata bata mata rai ta kashe wayar abinta. Su Salma dariya suka yi sosai domin sun san abin da yayi mata ya yi ne don ya Kona mata rai, yadda suka nuna abin bai dame su ba sai suka bata haushi. ku abin ma baku dairya ya yi, cikin ku babu wanda zai taya ni jin haushi ko?” Salma tayi dariya ta ce, “Haba Barrister, ai duk ku biyun mukewa dariya. Shi Malam M.J a
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG