SAMU CHAPTER 6 THEND KARSHE

SAMU




CHAPTER 6 THEND KARSHE







A cikin daren abubuwa suka dame sam ya kasa runtsawa juyi kawai yake yi yana tuno abunda nace masa na bazan bishi kano ba,..

Ko da ya zo da safe ma Haka na turje,dama gashi idan ya zo gidan ma sai na ja masa rai sosai kafin na fito na same shi kuma magana daya nake yi bazan bishi kano ba, Har yanzu babu sauki.

Ni kaina na sha mamakin taurin zuciyar da nayi masa ina magananga nu wanda mafi akasari nasan bakara min ciwo suke masa ba., don yasan ya aikata min abunda ya kamata na guje sake zama da shi din..
Shima yaki sam ya amince da hakan,
Amma sai yace zaiyi magama da su mumy akan akara min sati guda a ransa yana ganin kafin nan ya shawo kaina still

nikam bam damu ba don ku daya gama fadan haka na kama hanya ta na koma daki na barsa anan

Hakan akayi kuwa da shike mumy na tafi daraja maganan sa ba tayi wani dogon musu ba aka kara mana sati guda…haka ya bani dama na dinga juya emotions din jabir da cewa bana kaunar sa rabuwa da shi kawai nake so…
a kwana kadan kawai sai da na sa ya tuno da kuncin da ya dan dana min musamman in yana raping dina a lokacin da nake da ciki..

Sosai na ke zagewa nayi masa kukan bazan taba koma gidan sa ba dana tabbata yana kashe masa zuciya yana sa shi jin nadaman abunda yayi min don kuwa hakuri ya fade shi yafi sau milliyon ma naki sam na dube shi da idon basira..

Sai ya soma blaming kansa da bai ma fada ma kowa damuwar sa irin wannan ai da ba haka abun ya ke ba tun farko..
gashi gani yake kawai am scared of him kuma na riga nayi loosing trust akan sa.

Kwana yayi yana tunanin yadda zai dawo da yarda da kuma so tsakani na da shi

A Washe gari ne zai zo dauka na anan gida kuma ba wanda ya san me muke ciki har an gama shirya min kaya na tass’mumy na har da min nasiha itama da dan guzirin ta..

Sai dai bata san kudirin mu da mumy salamatu ba gamim jabir yaki bada takardan kuma yaki fadan ma kowa abunda ake ciki ya sata ce babu inda zakije samha..talknis always cheap maza basu da tabbas yanzu da yake cikin ha ula’i ne yake wannan nadama sauyin yanayi kadan sai ya mance…

A fannin mumy kuma har Washe garin Ba wanda ya tanka mata har sai da karfe 11 na safe ya buga sai ga jabir nan ya taho

Sum sum ya nitsu afalo ya sha shadda brown mai shegen kyau,ban san me yake tunani ba,shi dai ya fito rass sai musu musu yake da fuska abun a tausaya wa

amma ko ajiki na,don tunda na zo na gaida shi na shiga daki na kulle kaina kamar yadda mumy salamatu ta gaya min ban sake lekowa ba…

Ita mumy salamatun tana falo da abba da mumy na suka gama zancen su ..har sukayi sallama da abba dama zaije Lagos wani muhimmin meeting, duk sun dauka ina chan ina kimtsawa ne abu kamar wasa na ci rabin awa a daki ina kwance da dana..

Mumy na ta soma kukuni ta aika mai aiki ta kirani yafi sau abun da yafi amma ba abunda nake cewa sai dai ni babu in da zanje..

Bata wani aminta ba,don ban taba nuna hakan ba, ranta ne kuma ya soma baci Karshe ma kawai sai ta aiko younger cousin sis dina wato khadija akan taje tace kar na bata musu lokaci da shasahncin banza maza na fito, anan ma nace taje tace ni ba bu inda zanje .

Story continues below


Zuciyan sa ne ke bugawa sosai, sabida shikam dama da fargaba ya taho yau din sai bai sha mamakin hakan da nayi ba, mumy tana mikewa zata zo dakin dakan ta shima ya biyo bayan ta,

Da fushi mumy ta buga kofar, tana masifan na bude cewar ta in ta shigo bazan ji dadi ba,

Dama chan bana kuka amma jin muryan ta ya sa na fashe da kuka ina cewa wallhy bazan koma da shi ba, ni bana son auren..

Mumy salamatu tana kime a falo inda suka kyale ta,

Sai da mumy ta soma kawo cewa idan ban bude kofar nan ba zata gaya min maganan da har na mutu bazan manta ba..

Da masifa mumy salamtu ta iso wajen,.tacen akan me?

Yarinya tace bazata bishi ba sai ace za a takura ta, ai sai ki tambaye ta meyasa ba dai ki tursasa sa ta..

Mumy ta juyo a hatsale tace ohhh salamatu hakan ma zaki ce?
Wato daure mara gindi zakiyi tana iskan cin data ga dama?

Samha…samha..mumy ta buga kofar, kansa a kasa sai bugun da zuciyan sa ya dada yi..

Nikuwa in banda kuka babu abunda nake yi..
Anan ina jin masifan da ke neman wanzuwa tsakanin mumy da mumy na ,.

Abun da ya dame sa sai ya soma bada hakuri ma dukan su hankalin sa a matukar tashe,

Yace ma mumy shi yasan meyasa nace hakan amma dan Allah suje palo zai gaya musu komai..

Nan hankalin mumy salamtu ya kwanta, aranta tace baka ga komai ba ma munafuki..

Nan suka dawo falo su ukun kowa na diri a zuciyan sa..

Zufa yake yana jin bugun zuciya ya rasa ta ina zai fara gaya ma mumy abubuwan da suka faru,
Haka dai ya danne zuciyan nasa ya soma da bata hakuri…

Duk dama ni ban wani boye ma mumy salamatu komai ba musamman issure kwanciyar mu da shi,

Shikam dai ya kasa fada amma sosai ya sake ya gaya ma mumy har sharrin dayayi min na cewa na sauya hali ina masa rashin da’a,

Ya kuma bada kansa laifin rashin kulawa da kuma rashin bani uzuri dayayi,. .
Har ya gama suna shiru suna kallon sa….ya dawo ya dan rusuna, rokon su yake har hawaye na bin fuskan sa a hankali..
Yana cewa mumy dan Allah kar ta raba shi dani,

Tunda suka soma maganan na bude kofar na labe ina jin ko zai sauya wani abu amma sai naga akasin haka…

Shiru mumy na tayi tana jimin abubuwan da yawa aranta gaba daya sai ta ji brain din ta ya dauke,

Mumy salamtu ko rufe ido tayi yana bada hakurin tana masa masifa mai dauke da nasiha, tace mai ai ko ba komai ni yar uwan sa ne kuma dukan mu dangin juna ne ,
“gaba dayan su da iyayen sa hankalin su a kwance suka bashi ni don sun yarda da shi amma sjine zaije ya basu kunya…?

shi dai hakuri yake bayar wa yana bakan ce akan bazai kara ba..har dace wa in ya kuma min wani abu mumy dakan ta ta yanke masa hukunci

sam bata taba jin meye matsala ta ba amma kullum idan jabir ya kawo magana sai tabi bayan shi,
Abubuwa da yawa sun zo mind dinta…
Sai kawai tace masa yaje zata neme shi..
Baiyi musu ba ya tarkata kansa ya koma gida

Anan magana ne mai zurfi ya wakana tsakanin mumy salamatu da mumy don sosai ta mata nasiha akan negligence din da take yi da ni,da kuma saurin condeming dina data keyi, tace,atlest komin bakin halin samha ki daure ki rika sauraran ta don gudun kuskure irin wannan.

Story continues below


Nima basu barni ba, sai da suka hadu suka sake min kafin muka dawo dai dai
anan mumy ke sanin duk shirin da su mumy salamatu suka riga sukayi min

Yau ma da zulumin da yafi na kowani rana ya kwana ,tunanin sa ko mumy zata kai maganan gaba wajen iyayen sa ko zata ce ma ya sake ni”
Tsoro ne ya mamaye zuciyan sa
Yasan muddin magana yaje gaban iyayen sa sunan sa sorry ne, don sukam sosai suke kauna ta kuma sun matukar yarda da ni sosai musamman mahaifiyar sa ummah..

Washe gari Da safe still ya taho aka sake zama
Mumy Duk dama tasan tana da laifi itama sai da tayi masa nasiha da nuna rashin jin dadin zaman namu da shi,Da kyar da lallami aka sassan ta komai a mutunce

Anan ne mumy salamatu ta zo dakan ta ta saisaita ni ta fito da ni a shirye
Suka dada haduwa suka mana fada Sannan muka kama hanyar kano tare da shi.

Tun a mota nake ganin zumudin sa, wani sabon salon soyyayar yake fitar wa kala kala kamar karamin yaro,don kuwa a kwana biyu shi kadai yasan wahalar da zuciyan sa tasha da na ce zan rabu da shi

” wani bin har ya bank tausayi yanzu Sosai nake so na dan sake da shi ko don na samu cimma buri na da kyau na zaman aure mai aminci tare da shi,da dan mu seif har ma da kishiya ta zuwairah.

Sai wajen karfe 5 saura muka iso gida sabida mun dan zaga ya sayo mana chops da suaran kayan cime cime..

Iya wannan lokacin kawai rawar kafar sa saida ya sani na fara tuna lokacin honey moon din mu..

Finally Da muka isa gidan A gajiye nake amma sam sai kaina ya daure da ganin yadda gida na ya dawo,

Shima ya saba da ganin haka so Har daki na yakai min luggages dina sannan yayi wankan sa ya dan zaga makwabta da seif…

Tun da muka shigo zuwairah bata leko waje ba don kofar dakin nata ma a kulle yake alaman tasan shi din ne ya shigo amma nata damu ba..

Ban wani tsaya hutu ba , na daura dammara na hau rage dattin dake gidan musamman ma kitchen

Sosai na bata lokaci na na goge nan tasss.
Ga kayan abinci jirgi ba ako tabawa kafin magrib ya rufa na samu na daura rice and stew mai dan karan dadi tare da kayan lambu ..sai nayi simple pimeapple and ginger juice

kafin abinci ya nuna na dan samu time agurguje na dan tattara falou, na goge dining table sai da na gama anan na jere abincin tsaf gaba daya na ke jin baya na sosai na gama gajiya..

Ko barin wajen banyi ba sai ga bude kofar ta, qamshin abinci ya fito da ita,

Batace uffan ba Sai da ta kare ma wajen kallo tana yatsine tabi ta tabe baki ta shige kitchen,

Nima ko na kula, ina shiga wanka na fito na same sa ya dawo da seif yana shirin komawa masallaci sallahr ishai

Gaba daya har kunya yake bani yada yake nuna farin cikin dawowa na

Ko ba komai yau yaga gidan sa kamar yadda ya saba.. 

Taje kitchen din tana mutsu mutsu ta kasa taba komai,
Dan kunya Haka ta juya ta dawo dakin ta, 

Sai chan 8 taji knock, naje ta fito muci abinci, 

Gaban ta ne ya fadi gashi tsaban yadda qamshin abincin yake ratsa ta har hadiyan yawo take kamar mayya sabuwar kamu,.
tayi min shiru dai bata amsa ba.. 

Shikam Yana kan wasa da seif ne amma yana lura dani nikuwa na ki barin waje sai faman knock nake..,.har sai da ya hatsala yace nifa yunwa nake ji ki taho kawai ki samin abinci..nace ok, a nitse na juyo kamar jira dama nake 

Na dawo na yi serving dinsa muna hira kadan kadan.. 

Rabon sa da ya zauna nan cin abinci tun kwana biyu da tafiya na gida … 

Story continues below


Minti 5 bamu cika ba sai ga ta ta fito, buguzum buguzun tana tauna chewing gum..
ta zo ba sallama babu gaisuwa ta nema makan ta wajen zama zata bude abinci ta deba rai a bace yace “ke?!!dakata zuwairah,
Wai shin ba mutane kika gani agidan nan ba? 

Ta dan hade rai ta harde hannun tana tsuka kasa kasa tace,aiho aini bangan su su waye anan din…ta murguda baki ta kau da kai 

A fusace ya daka mata tsawan da saida ya sa na dan firgita..ya mike tsaye 

Yace are you insane? Ina wasa dake ne… 

Bada ni yake ba amna bansan sanda Murya na ya sauya kalar kuka ba.. 

A hankali nace dan Allah kayi hakuri jabir pls kaci abincin tukuna… 

Fushi ne ya bayyana sosai kan fuskan sa yana masifa Haka kuma fir zuwairaha taki tace mai yayi hakuri bare ta kuma sauke kai ta gaishe sa da dawowa… 

Ranar gaba daya sai da ya bata mata rai amma ko ajikin ta.. 

Haka rayuwan mu ya kasan ce agidan ,
Sam na dena shiga harqar ta ko zata mutu tana kananun magana dani bana tankawa haka duk lokacin da muka ci karo bana fasa gaida ta ko da sannu ne ko salam babu ruwa da ko zata amsa ko bazata amsa ba.. 

Dadi na daya yanzu jabir, ya dawo dai dai har yana neman ya fi na da don a ranan ya ya soma rabar jiki na ,ni kaina na gane laifi na wajen rashin yin masa wasu abubuwan 

Duk sai na sa arai na zan cigaba da kokarin zame kunya da kyuwiya don na zame masa kasaitaciyar mace a dakin sa kamr yadda yake so. 

A kwana biyun Ni kaina sai da na soma sanin dadin aure, 
Gashi baya takura min wani bin ma har tsallaken kwana munayi apart from ranakun da zai kwana da zuwairah.. 

A fannin zuwairah kuma sosai abubuwa suka soma hatsala ta, dan kudin da take samu taro sisi daga hannun sa take bi kwaroro kwaroo tana siyan magani domin ta rika updating hq dinta yayi kasa… gani take yanzu ido na so ya juya da muciya hala nima kayan mallaka naje na siyo daga garin mu… 

A tunanin ta biyayya da saukar da kai da faranta ma jabir rai dana ke yi
Bakomai bane kawai na mallake sa nima… 

Da shike bana barin ta ta shiga damuwa ta, yasa take takure a gidan wani bin dagan gan zata chwakala kitchen din don nayi magana amma shiru kuma bana bacci sai na kimtsa bai dame ni ba ,nakan dauka ai kayan miji na ne.ita kuma halin ta ne so kowa halin sa ya ficce shi.

Haka nake yin hakuri da duk wani neman fitinan ta, Gashi ina ganin sakamakon abubuwa sam yanzu basu jiyuwa tsakanin ta da jabir wani bi har saina sa bako nayi masa nasiha akan ya sassauta mata.. 

Damuwa na da ita bata bada hakuri sannan bata rusuna ma kowa, 

Gashi Rashin manyan kudi masu kauri ya sa 
Bata samun ingantaccun maganin mata kamar da chan,in ta samu ne a hannun sa ta samu 5k don ko gidan maman gayu yanzu ba su kula ta in taje, 

Duniyan ta gaba daya ya cunkushe amma ta kasa saduda, 

Bayan wata uku…

Ranar da asuba da shike baya daki na na fito ina tattara falou kwasam sai naji kuka da hargowan zuwairha alaman dambe ake, gaba daya tsoro ya kama ni, 

Ji nayi tana zagin sa akan baiya mata adalci, ya ki bata kudi ta siya magani shikuma yana faman mata tsiwan cewa ba zai bata ko sisi ba infact ya ma soke maganan siyan maganin mata agidan sa 

Ya kuma gaya mata ya gaji da rashin tarbiyan ta da kazantar ta, ya bata kwana biyu cewa idan bata gyara zai kora ta gidan su, 

Sai dai ita bata shiru yana yi tana yi 
Sai da yakai har ya mata gorin bata da wani amfani agare sa in ba sex din ba, kuma ma yanzu baya bukatar ta ya gaji da kanzata,
he boldy told her that she stinks, kuma rufa mata asiri yayi ya airo ta, he’s deeply regrting marrying her in his life.

Story continues below


Maganan yayi mata zafi sosai har ya kai ga ta dauki hannun ta mare sa ta kuma masa gorin sai da ya gama cin dadin gindin na ta kafin ya zo yana so ya juya mata baya, 

Zuciya ya sa yayi mata likis sai da ta sume ta zube a kasa kamar mutacciya kuma ya cigaba da gaya mata ba dadi .. 

Sam sam banji dadin maganga nun da ya gaya matan ba, don ni kadai na san kukan da nayi a bakin kofar falo inda nake jin su.. 

Yana fitowa ya hadu dani anan na tsuguna ina kuka yasan naji komai me kuma bazan bi bayan sa ba. 

Kallo kawai ya bini da shi, ya shige room dinsa ya kulle kofa 

Haka kawai zuciya na ta bani na cire maganan kishiya na same zuwaira muyi maganan fahimta ko zata saurare ni ta sauya halayen ta ko da dan tsaftan nan ta rika yi ta ja mutuncin ta , sai dai ina shiga na same ta a kasa cikin jini tana wash wash a kasale ba ama jin muryan ta 

Tuni na ji na rude na ruga aguje na koma bakin kofar jabir sai dai ba abude take ba..
Iya magana nayi ma jabir ya bude kofa amma haka yaki fie yama share ni.

Haka Nayi ruwa nayi tsaki na kai zuwairah asibiti 

Tun Safe bai kuma kira na ba, kuma in na kira shi baiya dagawa 

Anan Asibiti na kwana tare da ita an sake mata wankin ciki sakamakon sake zubewan da yayi

Da shike babban asibiti ne,.da sassafe doc ya yi kirani a offishin sa.. 

Ya tambaye ni ko ni yar ‘uwan ta ne,? Nace masa ah a ni kishiyar ta ce..
Yace toh
Yana da bukatar ganin mijin ta da gaggawa.. 

Sosai hankali ya tashi ina tambayar likita ko lpya yace dole kawai na kira mijin ta, a haka na tashi na fice 

Nan na shiga na same ta sai Wash wash take tana juyi da cikin ta akan gado, 

Nace sannu zuwairah Allah ya baki lpya,.yaune rana na farko dana ga ta gyada min kai, ta amsa a hankali.. 

Tausayi tuni ya kama ni sai na ce mata zanje na kira jabir doc yana so ya gansa…nan ma ta gyada min kai 

Anan na dau niyyya na je gida,
Da shike saturday ne i was confident A zaune a daki na same sa yana shirin sa kaya ya fito daga wanka.. 

Na sauya fuska kalar tausayi da jimami na karaso ciki a ladabce na rusuna na gaishe sa… 

Gaba daya yadda na sauke kai na yamutse waje daya ya sa ya kalle ni baice komai ba.. 

Na kuma cewa kayi hakuri sweetj, amma meyasa baka daukar waya na zuwairah fa jikin ta ya tsanan ta.. 

Yayi dan guntun tsaki kasa kasa..sannan yace wai wayace miki ki fice agidan nan ne samha?
Da izinin waye kika kwana min awani waje.. 

Nayi shiru, kamar bana wajen sai na dada sa mada fuskan shagwaba ina masa bayanin komai a takaice.. 

Har ya gama shirin sa Ya mike zai fice da sauri na taso na dan sha gaban sa na saka masa kika mai dauke da kisisna da shagwaba nace, dan Allah kayi hakuri sweetj 
Anyi kuskure amma fa yar uwa ta ce, 
Hmm kar ka ga yadda take shan wahala jabir pls lets by gones, muje ka duba ta,
ka tuna fa duk laifin da zamu maka still hakkin mu na wuyan ka , 

Yana duba na irin shi to me zai ce min..nayi sauriin cewa
Plss jarumin maza ka yi hakuri ka zo muje kaga doc ma fa na son ganin ka… 

Ya kure ni da ido, sigar tsokana yace ni dai babu ruwa na da wannan maganan, 

Kije ki hada min breakfast ya karbe aeif dake bacci a hannu na ya juya ya koma ya zauna kan gado ya rungume sa yana dan shinshina sa .. 

Banso hakan ba ,cos ni naga yadda zuwairah ke fama da radadi,. 

Amma da shike nasan dole na bishi a sannu sai na yi sauri na shiga kitchen na hada simple fried yam da egg na hado masa shayi na kawo dakin nasa… 

By then seif ya tashi, sai surutun sa yake yi da sunan yana masa wasa.. 

Haka na ajiye nayi zaman diris muna ci hankali na duk ya koma kan asibiti shikam ko ajikin sa, 

Shiyasa wani bin haka kawai nakan ji mamakin zuciyan namiji wato idan abu ya fice musu aka sam basu sa sanyi ma ransu.. 

Daga nan dai na kimtsa mata dan abincin dana rage a warmers na sa shi agaba muka je asibitin …


Ko da na fita zuwa gida don na sami jabir, anan ne zuwairah ta samu dan bakin magana” cewa tayi a kira mata doc.yana zuwa kuwa anan ta yi masa tambayoyi akan abunda ke damun ta 

sam likitan ya ki cewa komai, amma haka tayi ta nace wa, a haka ma da kyar don ya so ace mijin na ta ya soma samu amma sai ta birkice masa dan dolen sa ya shiga mata bayani … 

Anan ta fahimci cewa fa ta samu wani babban matsala ne da mahaifar ta bazai taba rike ciki ba sakamakon wasu maganin da ta sha su a da chan marasa inganci wanda suka tara mata sinadarin da yayi sanadiyar gurba ta jijiyan da yake rike da mahaifan ta,
Gaba daya idan ciki ya shige ta bazai wuce 2 3 month ba zai kwabe…

Haka yaki fir ya gaya mata sauran results din ya bari aransa sai jabir ya iso, 

Ko da muka iso asibin Nikam ina daga waje a kayi musu bayani shi da ita 

Sannan doc ya gaya masa zai daura ni da shi da zuwairahn ma duka akan maganin infection wanda akasari aka fi samu jikin zuwairah, 

A cewar sa don maybe muna tsaftace namu wajen yasa baiya nuna wa sosai amma idan aka yi sake wata rana sai muga muma muna fama da shi kamar ita zuwairahn . 

anan ya rubuta kudin jinya da dan aikin da za’ayi mata da sauran su sannan ya bata shawaran ta hakura da shan duk wani magani in ba wanda za bata yanzu ba…. 

Zuwairah Tunda aka fara bayanan take kuka tana kukkuni,shikam jabir sosai abun ya taba zuciyar sa… 

Sai kawai ya yanke hukuncin cewa toh a cigaba da rike ta ana bata kula zuwa monday zai bada isashhen kudi a soma mata full treatment, 

Ita dai zuwairah kuka take har yanzu bata ce komai ba har suka fito kwata kwata ta share kowa ta hade rai bata dago ta dube mu ba,
Musamman da jabir ya zo yana maida min maganan doctor agaban ta..
Muna jimantawa muna dada bata karfin gwiwa

Acikin zuciya na tausayi ke dawainiya dani amma Sam bamu san cewa ita a ranta ba haka bane, 

tuni ta kaw cewa duk kisisi na da munafurci na ne Yasa aka shirya wayannan maganganu  akan ta 

Tunanin ta tunda ni na kwana da ita asibiti its obvious ni na shirya ma doc duk karyan nan daya fada musu don ya raba ta da mijin ta jabir, 

Baifi awa 3 mukayi mata ba, Haka jabir ya sa muka koma gida duk dama banso ba, anan ma na dan ja hanlakin sa da nasiha akan abubuwan da suka faru 

A tunani na hakan da yake mata ba zai kaimu ko ina ba dole mu hadu mu taimake kan mu… 

To alokacin da na kawo maganan Ni dai ya gwada min ya gamsu.. 

Don har naga canji a washe garin da muka koma asibitin da safe sai naga zuwairah ta nace zata dawo gida kawai tare damu…
akan tana mafarke mafarke anan asibiti.. Toh baiyi musu ba muka dawo din 

Haka taayi ta zaman kurmaye da mu 

On Monday ya dau kudi dubu 250 kamar yadda likita ya rubuta ya sa a mota tare da ita zasu je asan abun yi

Ni dai fatan sauki nayi mata na raka su har suka bar gidan, 

“Daga hanya ta ce masa ya taimaka ya siya mata pad kamar tana jin jini yana sauko mata,zata tafi da shi in yaso in sunje asibiti sai ta samu ta sauya a toilet,. 

Story continues below


Anan ma baiyi musu ba ya sauka ya barta a mota, 

Minti 5 mai kyau bata kara ba ta kwashe kudin gaba daya ta wuce tasha motar ma bai cika ba ta biya kudin sit aka cahle da ita maiduguri.. 

Ko da jabir ya dawo bai ganta ba sai ya dan saurara amma abu yaki ci yaki karewa har ya hankara ya fara neman ta.. 

Neman duniyan nan jabir yayi amma bai same ta ba, 

Ba shi ba har ni na da mu.. 

Ga wayar ta na dhiga amma bata dauka, 

Anan maiduguri ita kuma taje gidan su babu kowa anan ma gidan su karime hakan ne ance mata inna zulai na chan taraba karime ta samu sauki har an sake mata aure suna wajen bikin tun shekaran jiya.. 

Ta sha mamaki kam amma sai ta basar Kawai ta fanjama neman malam mai mallaka
Idon ta arufe
sai daii bata same san ba sabanin haka Yasa aka mata kwatancen wani waje na daban 

Anan ta je taga mata tatil irii iri suna layi akan tabarma a zauren gidan itama ta bi layi har Allah Allah take kuma azo kanta.. 

Duk dama munsan da qamshin cewa zuwairah da sannin ta tayi hakan bai hana hankalin mu duk ya tashi ba,
Musamman ma ni a daren Da kyar muka samu muka runtsa… 

Da safe bayan an idar da sallahn fajr sai ga kiran ta, 

Seif baida lpya nima yanzu nake idar da nawa Sallahr ko mikewa banyi ba ,saiga shi ya shigo daga masallaci agauggauce ya nayi min hannu alaman naji abunda zuwairah ke fadi don ya sa ta a handsfree 

Anan take  gaya masa dalilin ta na tafiya akan bata yarda da abun da doc ya fada ba, shima kar ya yarda da hakan ai kawai makirci na ne kawai,
kuma ya gaya min tafi karfi na, don zata ta amshi matsayin ta a gidan kamr yadda na sani… 

Abun sosai ya bata ma jabir rai ,bai taba tunanin dabbancin zuwairah yakai haka ba…Jabir yayi zuciya zosai ya haura mata da fada tana yi yana yi duk suka kidima ni da musu da sai’ns har yana bari yana kumfar baki,nikam na sha tsinuwa da zagi abakin ta,..abun babu dadin ji karshe sai da nayi masa kuka sannan ya nitsu ya saurare ni, acewar sa shi sam ya turje shi zai saki zuwairah that minutes ya huta maran sa. 

Abu yaki ci yaki cinyewa har akayi kwana biyu bata dawo ba 
Har aka ci sati guda, 

Gashi zata kira ko sau dari ne sai ya dauka sun yi ta yi..Anan ma sai da na hada da su umma mahaifiyar sa sannan Jabir ya hakura ya barta hakan nan 

Itama umman data ji bayan nasa akan abunda zuwaira tayi cike take tamm da zuwairah tana jira ta dawo 

Dangin sa kuwa ba wanda bai tofa albarka cin bakin sa ba..
Wasu har da masa gori akan  auro ta dayayi tun farko dama basu yaba ba,
Abubuwan sun faru da babu dadin ji.. 

Ranar juma’ah anan kan sauraron ta don yanzu kam kowa yasan tana maiduguri 

Ranar Jabir baya nan don tun safe ya fice yana chan wajen interior decors ana jere a sabon gidan mu da ya gina, 
Anan cikin haka aka sanar da shi baban zuwairah na neman sa.. 

Abun ya bashi mamaki amma,tunanin sa ko zuwairah ya dawo da ita a sasanta.. Bai yi niyyar zuwan ba amma sai ya daure ya je din 

anan baban zuwairah yake sanar da jabir jiya da daddare fa an kama zuwairah turmi da tabar ya da malam mai mallaka,
tare da sauran mata customers da ake lalata da su da sunan basu magani,acewar malamin idan ya kwana da mace ne kawai zai gane siffar yada zai tsara mata magani.. 

A halin da ake ciki sauran matan suna na  kulle a cell 

ita kuma zuwairah da malam suna nan a garkame anan za’a zantar da su gobe a kotun sharia, kotu zasu yanke musu hukunci bisa tsarin addini dama chan rashin hujja ya sa ake zuba masa idi amma jiya sai Allah ya cika masa mugun kaidin sa…. 

Jabir Yaji bakin ciki bana wasa ba, ba don komai ba sai dan tunowa da yayi zuwairah ta amsa sunan matar sa na sunnah… 

Haka dai ya daure Bai yi wani reaction ba ,amma sikinini ya je ya dauke kawun sa da kanin sa  sa salihu suka kama hanyar maiduguri a ranar ba jira

So nikam ma bansani ba sai da ya isa chan dare yake gaya min yayi nisa da mu amma zai dawo gobe. 

haka suka kawana a maiduguri washe gari
Har inda aka tsare zuwairah yaje ya sameta,..ta na hargowa tana surutan bakin ciki da borin kunya, bai kula ba ya bata sakin ta daddaya har uku…
Bai ma jira jin hukuncin da aka yanke musu ba
Ya juya kan mota suka dawo kano… 

Abakin salihu kowa yake jin labarin abun da ya faru.. na jimanta sosai sai na ji  gaba daya duniyar nan ba komai bane face miiraji ma yaudariya ga wanda ya bita da imanin sa.. 

Amma nayi addu’ar Allah ya sa hakan shine mafi alkhaiiri a gare ta damu baki daya..

Wasa wasa muka koma sabon gidan mu Shirgegen gidan sama ne mai hawa uku… anan muka baje sabon salon zamantakewar mu cikin tsaftataciyar soyayya da girmama juna.

Muna zaman mu cikin aminci da godiyan Allah.




_Alhamdullihi_ 😆 

  _kuskuren da yake ciki Allah ya yafe mana ya kuma bamu damar amfani da positive lesson dake ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *