Wani irin kakkauran yawu yarima yaseer ya hadiye a daidai lkcn da yaci karo da kirjinta Wanda ya Dan hauro izuwa Saman rigar dake jikinta farare Kal har sunfi sauran sassan jikin nata ma haske, da alama bra din data saka ne yyi mata kadan shiyasa suka hauro sama.
Kansa yaji ya Sara tunanin sa na dauko Masa Wani hoto acan kasan kwakwalwar sa me kama da kwatankwacin yyi mu’amala da irin Wannan abin saidai Sam ya kasa tunawa domin ya manta.
Duk yadda zai iya tunowa ya kasa saima jin kansa da yyi yana Masa nauyi alamar ciwo zaiyi Hakan yasa shi kawar da tunanin Yana janye idanun sa dakyar akan kirjin nata yyinda nasa kirjin ke bugawa har yanzu.
Cije kasan lips dinsa yyi yana daukar hijab din ya mike a hankali ya isa gaban kogin dake gabansu, Ruwa ya nado a ciki Yana tangadi domin shima jirin yakeji sama2 Yana zuwa wajenta ya dagota a hankali Yana dorawa bisa cinyar sa dakyar sannan ya matse ruwan akan Inda yaga jinin Yana fita.
Dan kwalin ta da yake kansa data bashi dazu ya warware domin d din daurawa yyi shima sannan ya dawo dashi daidai saitin goshinta ya daure ciwon a nutse domin jinin ya tsaya.
Yana gamawa ya dora jikakken hijab din a saitin wuyanta take bilqees ta sake Jan wata ajiyar zuciyar tana bude ido a hankali.
Ganinta dodar bisa cinyar sa yasa ta zabura da sauri tana kokarin tashi. Rikota yyi da sauri idonsa na lumshewa yace,
“ki nutsu pls”
Janye hannun ta tayi batare data kulashi ba ganin haka shima ya saketa kawai Yana dafe kansa.
Bilqees ta janyo hijab dinta da sauri zata saka sai taga Duk ya jike. Dagowa tayi fuskar ta a hade Tace,
“meyasa ka jika min hijab? Dama Bance kada ka ciremin ba?”
Dagowa yyi a hankali Yana zuba mata ido, beyi mgn ba kawai ya gyara zamansa a tsanake yana Dan kishingida idonsa na Kara rufewa gaba1.
Tsaki tayi tana Hararar sa, tace , “Mgn nake maka fa?”
Ganin ya share ta yasa ta tashi daga wajen tana matsawa can gefe ta kama buga hijab din tana dagashi can sama Dan ya bushe da wuri.
Juyowa tayi sai taga kamar Yana bcci. Mmki ne ya kama ta, sannan ta kalli dajin da suke ba motsin mutum ko daya take tsoro ya shigeta tayi sauri dawowa kusa dashi tana jijjiga shi tace,
“Kai….tashi mu tafi Nan ba wajen zama bane.”
Gani tayi be motsa ba, ta Kara kamo hannun shi tana jijjigawa tace,
“Wlh idan baka tashi ba Allah zanyi tafiya ta.”
Ta furta Hakan cike da takaici tana mikewa tace,
“dama can a daji na ganka Dan haka haduwar daji rabuwar daji.”
Tana idawa ta juya da sauri zata tafi. Har lkcn yarima yaseer be farka ba da alama ma besan a duniyar da yake ba tamkar Wanda ya Suma.
Bilqees kuwa Duk tsoro ya kama ta tana ganin gara ta hakura da zuwa gidan yaya Atika kawai ta wuce gida kafin dare yyi mata.
Saida tayi nisa da tafiyar ta juyo har lkcn Yana kwance kamar yadda ta barshi, kwafa tayi tana shirin juyawa taji an damko hannunta ta baya.
A razane ta juya tana kallon gefen nata sai kawai taga wasu maza biyu irin barayin dajin Nan tsaye a kanta Suna dariya sukace,
STORY CONTINUES BELOW
“Kan uban can yau ga tsuntsu daga sama gasasshe.”
Ihu Bilqees tasa a razane tana salati hade da kiran sunan yarima yaseer cewa take,
“bakon gari Dan Allah kazo ka ceceni….”
Juyawa sukayi Nan suka hango yarima yaseer a kwance. Dariya sukayi mata Suna nufar Inda yarima yaseer din ke kwance.
Fisgewa tayi iyakar karfin ta tana isa gaban yarima yaseer ta fada kansa tana jijjiga shi iyakar karfin ta a mugun tsorace tace,
“ka tashi…muna cikin matsala.”
“Kai baro kamo min waccar yarinyar.”
Dayan ya furta Hakan yana gyara tazugen wando.
A gigice bilqees ta sake dakume yarima yaseer hawayen ta na zuba akan fuskar sa domin ta Rasa mafitar da zatayi yanzu Wanda aka umarta ya taho Yana washe baki yace,
“ilu gani take fa Nan din ta tsira.”
Yana Ida mgnr ya kawo hannu zai taba ta bilqees ta sake tsallara karar data Kara karade dajin gaba1.
Yarima yaseer da damshin hawayen ta ya fara tashin sa daga dogon suman da yyi ya mike a firgice sakamakon karar data tsalla yanzu.
Ganin mutum biyu maza yyi a gabansa gasunan murtika- murtika majiya karfi, sai kuma bilqees data sandare Masa akan fa!adan kirjin sa yanzu.
Kallon-kallo ne ya afku Tsakanin barayin dajin babban cikin wato ilu ya kalle shi kallo na raini sannan ya watsar kafin yace,
“Kai malam tun muna shaida juna ka sakar Mana yarinyar Nan ka kama gabanka idan ba haka ba Wlh harda Kai zamu tubewa wando.”
Gwalo ido yarima yaseer yyi da mugun mmki. Yyinda baro yace,
“ai oga shidin ma ba haka Nan zamu barshi ba, yyinda kke shagalin ka da yarinyar ni Kuma zanyi nawa shagalin da Wannan mutumin Dan kur’ani kana ganin San Nan da alama zaiyi Mai yaseen.”
Dariya suka sa gaba1 dayansu. Ilu yace,
“shiyasa nake yinka baro domin kanada dabara Dan haka muje na karbi yarinyar Kai Kuma ka sabule Masa wando.”
Izuwa yanzu fuskar yarima yaseer ta hade sosai babu alamar murmushi bare dariya a tattare dashi Yana a yadda yake bilqees na kansa hannayen sa Suna dafe a kasa ya zuba masu ido kawai Yana ganin ikon Allah.
Da isarsu suka Karasa wajen nasu a daidai lkcn da ilu zai sa hannu akan bilqees a Wannan lkcn yareema yaseer ya damke Masa hannu ko Karasa tabata beyi ba ji kke bas ya balla Masa shi take ya sandara Kara,
Karar data fargar da bilqees ta mike a razane yareema yaseer ya dawo da ita kansa kamar yadda take dazun Yana girgiza mata Kai fuskar sa a hade.
Kasa Musa Masa tayi sai kallon ilu take a tsorace lkcn daya ja Baya Yana cije baki. Baro yace,
“Kutmelesi? Oga badai Wannan shafalfal dinne ya gwada maka karfin damtse ba?”
Banza yyi dashi kafin ya sake dawowa be daddara ba zai kamo bilqees yarima yaseer ya Karasa balla Masa dayan hannun karar azaba ya sake saki take ya matsa da sauri baro yace,
“Wlh mu bar Nan nifa nafi tunanin rauhanai ne.”
Baro ya furta Hakan yana juyawa zai gudu ilu ya bishi a Baya hannun sa rungume da juna Yana Jan numfashin azaba.
Sauke ajiyar zuciya bilqees tayi a daidai lkcn data daina hango inuwar su ta dawo da kallon ta kan yarima yaseer da shima mmkin karfin sa ya kamata.
Gani tayi itan yake kallo Hakan yasa idanuwan su ya sarke da juna..Dan yake tayi kirjinta na bugawa tayi azamar sauka daga kansa ya rike mata hannu, zaro ido tayi tana dan hade fuska Tace,
STORY CONTINUES BELOW
“me Kuma zanyi maka?”
Yarima yaseer ya yatsina fuska Yana kawar da Kai yace, “su waye mutanen Nan?”
Bilqees tace,
“Toh sakeni Mana saina ji dadi fada maka waye su.”
Tabe baki yyi yana sakin nata ta sauka lumshe ido yyi yana cije lips a hankali bilqees ta kawar da Kai da sauri Wani Abu na mata yawo a kirji.
“Yes ina jinki.”
Yarima yaseer ya furta Hakan har yanzu be bude ido ba. Bilqees tace,
“inata tashin ka dazun kayi banza dani shiyasa nayi tafiyata Nima.”
Ta furta Hakan tana turo baki. Gani tayi ya bude ido da sauri Yana zuba mata su yace,
“Pls maimaita banji me kikace ba.”
Wara ido tayi da mmki sai taga ya gyada mata Kai alamar cewar lalle baiji ba. Bata kawo komai a ranta ba ta sake maimaita Abinda tace tana Kara turo baki Harya Fi na da din.
“Hmm…!”
Yarima yaseer ya saki ajiyar zuciya yana tsareta da ido sai kallon bakin yake yana Dan murmushi.
Bilqees tace,
“wai har yanzu baka ji bane? Kodai ka samu lalurar Rashin ji ne yanzun?”
Yarima yaseer ya sakar mata murmushi yana mikewa tsaye ya miko mata hannun sa yace,
“Taso mu tafi”
Ba musu ta mike Dan dama ta kagu Subar wajen. Yarima yaseer yace,
“Inane hanyar garin da Zaki je?” Bilqees tace,
“na fasa zuwa gida zan koma.”
Yarima yaseer ya gyada Kai batare da yyi mgn ba Nan suka kama hanyar komawa gidan bilqees na nuna masu hanya har suka koma asalin dajin kauyen su.
Tun a hanya bilqees ke tufka da warwara har yanzu ta Rasa a wanne matsayi zata nuna yareema yaseer a kauyen su…
Duk yadda taso ta samu mafita kasawa tayi Dan haka kawai tasa a ranta gwara ta barshi a dajin kawai kamar yadda ta ganshi anan tun farko.
Sun danyi tafiya me nisa babu meyin mgn a cikinsu har suka Kai Inda bilqees ta fara haduwa da yareema yaseer ja tayi ta tsaya ya juyo da hankalin sa kanta Yana jiran abinda zatace sai ta danyi murmushi tace,
“mun
iso Inda kke zama ni zan tafi ka tsaya anan.”
Zuba mata ido yyi beyi mgn ba, bilqees tace,
“ko baka ji me nace ba?”
Girgiza Kai yyi a hankali Yana harde hannayen sa ya Kawar da kansa Wani side din.
Numfashi bilqees ta sauke kafin tace, “Sai anjima.”
Juyowa yyi a hankali Yana kallon ta yanayin fuskar sa na canjawa. bilqees ta juya zuciyar ta babu dadi ta wuce a wajen ta barshi.
Har tayi nisa be daina kallonta ba bilqees ta juyo a hankali sai taga har yanzu itan yake kallo be dauke idonsa a kanta ba, kasa daurewa tayi ta dawo gareshi gaba1 tausayin sa takeji ace mutum ba Dabba ba a daji ai babu dadi.
“Ko zaka bini ne?”
Tayi tmbyr batare data shirya Hakan ba. Daga Kai yyi da sauri sai taga ya saki ransa alamar yaji dadi, Wani mugun tausayin nasa ne ya sake kamata tayi kasa da kanta tana tunanin a matsayin da zata nuna shi, sai kuma ta tuna taimakon d yyi mata a wajen barayin dajin Nan Dan haka tace,
STORY CONTINUES BELOW
“shikenan muje.”
Ransa a sake ya biyo Bayanta Suna tafe tamkar Wanda suka dade da sanin juna.
A lkcn har yamma tayi Kuma dole ta wajen dandalin su zasu ratsa.
Hakan yasa tun daga nesa aka zubawa bilqees ido Ana kallo kowa mmki dauke akan fuskar sa. Bilqees dauke kai tayi bata kula da irin kallon da ‘yan kauyen ke mata da Wannan bakon ba tayi hanyar gidansu dashi.
“Dakata…dakata…Uban waye Kai?”
Mlm Musa ya furta Hakan lkcn daya fito daga gida, ya hango bilqees tare da Wannan mutumin zasu shiga gidan.
Kallon sa yareema yaseer yyi sai kuma ya dauke kai bece komai ba. Bilqees da tun dazu kirjinta ke bugawa tace,
“dama..dama ba!a…”
Ba!a yace,
“Wani shegen kika sake kawowa Kuma?”
Girgiza Kai tayi tana janye yarima yaseer daga gefensa yace,
“toh waye shi da zaizo Kai tsaye ya shige min gida?”
Bilqees tace,
“dama a soro zan barshi ya tsaya sai nayi maka sallama dashi.”
Mlm musa yace,
“meye hadina dashi dahar zai neme ni?”
Bilqees tace,
“Dan Allah kayi hakuri nayi maka bayani.”
Juyar da keya mlm Musa yyi yace,
“inajin Ki.”
Juyawa bilqees tayi sai taga dayawan ‘yan kauyen su duk anyi curko-curko a wajen Ana jiran abinda zatace.
Bilqees tayi kasa da kanta tace,
“ba!a shidin ya ceceni ne”
“kamar ya ceto? Ban gane ba”
Mlm Musa ya furta Hakan yana jiran Karin bayani. Bilqees tace,
“a hanyata na zuwa gidan yaya Atika wasu mutane suka so sace ni harma sunso suyimin mummunan Ilah Allah ya turo Wannan bawan ALLAH ya Cece ni ba!ah.”
Ba!ah yaja tsaki Yana gyara zaman hular sa yace,
“Toh munji ya ceceki, sai kuma akayi yaya? Ko biyanshi za’ai? Kinsan dai ko kashe ki akayi ba ruwana Dan ban aike ki ba dama.”
Ranta ne ya baci irin cin zarafin da ba!a ke mata a gaban koma waye ke Bata mata rai gashi kamar Wanda akaga sabon halitta sai Kara taruwa ake.
“Ba!a besan waye shi bafa, ya Rasa tunanin sa”
Bilqees ta furta Hakan hawaye na shirin zubo mata. Da mmki kowa yake Kara kallon su.
“Shashancin banza shashancin wofi, ni Zaki maida Dan iska? Kiga mutum zabgege kamar Wannan kice besan waye shi ba? Dodo ne shi? Ko Aljani???”
Mlm Musa ya furta a fusace yana ganin rainin hankali karara bilqees ke shirin yi Masa. Kowa na wajen karyata mgnr yyi, yyinda wasu ke Al’ajabin Abinda bilqees tace game da Wannan bakon da Sam beyi si!a da mutanen kaf kauyen su ba.
“Mlm Musa…haba mlm Musa, lpy kke Wannan fadan a kofar gidan ka haka?”
Kwafa mlm Musa yyi kafin yace,
“Allah gafarta malam Dan Allah ka tayani duban wancan mutumin…”
ya nuna yareema yaseer da a yanzu ya matsa can nesa dasu Yana yatsina fuska domin hayaniyar mlm Musa ta fara damunsa yace,
STORY CONTINUES BELOW
“wai shine besan kansa ba”
Alaramma Idi yace,
“Ban fahimci abinda kkeso kace ba mlm Musa.”
Mlm Musa ya nuna bilqees da kanta ke kasa yace,
“Nima shirmen da yarinyar Nan ta kawo min kenan Dan mgnr Bata fahimta bace.”
Alaramma Idi yace,
“Bilqees ko zaki iya min bayani a nutse ta yadda zan fahimta?”
Bilqees ta goge guntun hawayen takaicin daya gangaro mata a kumatu kafin ta Kara sanar dashi yadda ta fadawa mahaifin ta, Sanna ta Dora da fadin,
“Tun a lkcn na tmbyi waye shi? Daga Ina yake? Kuma Ina zaije? Sai ya nuna sam-sam besan waye shi ba, ciki harda sunan shi kuwa, shiyasa na yanke shawarar tahowa dashi Nan asa cikiya a gari ko Allah zaisa a samu Wani bayanin daya dangance shi ko dangin sa.”
Alaramma yace,
“tabbas kinyi tunani mekyau bilqees, kamata yyi asa cikiyar sa hadda makotan kauyen mu ko Allah zaisa a dace.”
Bilqees ta girgiza kai cike da gamsuwa. Tabe baki mlm Musa yyi yace,
“Tohm duk naji Abinda kuka tattauna, Amma a Ina zai zauna? Dan bazan aje gardi a gidana ba.”
Bilqees tace,
“Dan Allah ba!a ka bari yyi kwana biyu a soron Nan tare da su yaya sabi’u kafin ya dawo hankalin sa ko kuma a samu Wanda ya sanshi saiya tafi.”
Tsalle Mlm Musa yyi ya dire yace,
“Wannan ne Kuma Sam bazan lamunta ba, ai Abinda yasa na yiwa tufkar hanci kenan tun wuri haka kawai na aje mutum da ban sani ba a gidana? Nasan waye shi? Da kikace ya ceceki na sani Duk karyace shima a cikin barayin yake? Haka kawai cikin dare yyiwa ‘yan uwansa alama suzo suyimin sata ko su yanka ni? Billahillazi bazan yarda ba kinji na rantse atoh.”
Kasa cewa komai bilqees tayi domin a yanzu kam ta Rasa mafita.
Alaramma Idi yace,
“Akwai dakin Almajirai na dake karatu jiya Wani Almajiri na ya koma gida Dan haka za’a samu waje su goma ne a ciki idan ba damuwa saiki kawo shi ya kwana biyu kafin wancan din ya dawo.
Girgiza Kai bilqees tayi hankali ta na tashi ga bikin zuwa babu zanin daurawa…yadda dakin Almajirai yake da wari na tashin hankali da kazanta take hangowa Wannan bakon da har yanzu bata San sunan shi ba, Toh Amma ya ta iya? Ina lefin Wanda ya nemi ya taimaka maka a daidai lkcn da kke bukatar Hakan? Matukar Bata amince da tayin Alaramma ba toh Bata San Kuma Ina zata Kai yareema yaseer ba.
Haka dai tayi yaken dole tana Kara gyada Kai tace,
“shikenan mlm na gode sosai Allah ya Kara Arziki.”
“Ameen bilqees muje Kuga wajen koh?”
Bilqees ta girgiza kai tana komawa Inda yareema yaseer ya harde hannayen sa Yana kallon su daga nesa tamkar tv.
Tsaki mlm Musa yaja Yana kallon mutanen da suka zagaye kofar gidan sa yace,
“toh ai saiku tafi ko? Sa’idinawa.”
Sum-sum kowa na wajen ya fara darewa Ana gulmar Abinda ya wakana a wajen da haka hirar mutanen kauyen ta canja salo zuwa labarin zuwanta da bako cikin kauyen su, kowa dai da Abinda zai fada.
Kallon shi tayi a tsanake tace, “muje.”
Beyi Musu ba domin dama ya gaji sai yatsina fuska yake tun dazu Dan haka ba gardama ya fara bin bayanta a nutse.
Sun danyi tafiya me nisa acan gaban layinsu gidan Alaramma yake Suna zuwa lkcn Ana kiran magrib Alaramma yace,
“Toh bilqees ki jiramu Anan bari muyi sallah sai na nuna muku dakin.”
Bilqees ta gyada Kai tace,
“bari na Karasa gidan naka Nima nayi.”
Alaramma yace,
“Toh ba damuwa.”
Kallon yarima yaseer yyi yace,
“muje ayi sallah ko?”
Ko kallon sa beyi ba bare yasa ran zai saurare shi. Bilqees tace,
“kuje yanzu Zaku dawo Ina Nan”
ta nuna Masa inda take zaune. Kamar bazai bishi ba saida ta sake nanatawa sannan ya yarda ya bishi Yana waiwayen ta tamkar wacce zata gudu ta barshi.
Murmushi tayi Masa sai ya danyi murmushin shima Yana sakin ransa har suka wuce masallaci tare da Alaramma dake daga wajen Ana iya hango masallacin.
Ajiyar bilqees ta saki tana mikewa a hankali tayi hanyar gidan mlm domin yin tata sallar,
A hanyar ta na shiga gidan daga gefen kofar gida taga window din Almajiran mlm a bude, matsawa tayi domin ta leka,
Tana cusa kanta wajen ta dawo baya a gigice tana toshe hanci saboda Wani irin mugun wari da tsami daya bugi hancin ta lkci guda.
Hankalin sa sosai ya maida kan bilqees da suke tafiya a yanzu Kai kace Wani bodyguard dinta ne yadda yake kulawa da gaba d bayanta ko kuma Wani dogari. Ganin yadda yake gaba Yana baya bilqees ta juyo a tsanake tana Kare Masa kallo tace,
“ka nutsu gefe daya Dan Allah.”
Yatsina fuska yyi yana Bata rai yace,
“banason Wani Abu ya taba ki ne”
Ya furta Hakan d kulawa. Wara ido bilqees tayi kafin tace, “sai kace wata sarauniya me tafe da dogari?”
Ji yyi kansa yyi Wani irin sarawa d hanzari ya dafe kan yana er Kara auccch.., d sauri bilqees takai hannu tana rike shi ya kwace hannun sa yana cije lips dakyar, bilqees tace,
“meya sameka? Kanka ke ciwo ne?”
Duk ta furta Hakan a rude. Kokarin saita kansa yyi cikin ransa Yana mmkin kalaman d bilqees ta furta ya sashi Wannan sarawar kan ko kuwa Wani Abu ne daban?
“Kayi mgn Mana.”
Bilqees ta furta Hakan d damuwa. Yake yyi mata Yana gyara tsayuwar sa yace,
“ba komi.”
Sauke ajiyar zuciya bilqees tayi kafin tace, “Toh muje.”
Sun danyi taku kadan kafin suka iske inna dake jiransu tun dazu. Suna karasawa inna habi ta dubesu gaba1. Kafin ta dubi bilqees tace,
“ku jirani Anan kofar gida bari naje na fito.”
Gyada Kai bilqees tayi inna ta shige gidan. Ita kuma bilqees ta nunawa yareema yaseer dakalin gabansu su zauna. Zama sukayi har lkcn yareema yaseer be daina cije lips ba sunan sarauniya da dogari yyi masa kama da Abinda ya taba sani can Baya, Amma Kuma ya manta. Idan yyi kokarin tunowa da meye Hakan ke nufi? Sai yaji kansa na sarawa, haka dai babu yadda ya iya yyi shiru yana kawar da tunanin a ransa Domin samun saukin sa. Inna habi ce ta fito tare da Wani namiji.
Bilqees na ganin su ta mike da sauri tana gaishe shi tace, “barka da dare kawu.”
Kawu isa yayan inna habi yace,
“bilqees kwana biyu baki leko mu ba.”
Murmushi bilqees tayi tana dukar d kanta batace komai ba. Zama sukayi Suma inna habi ta dubi kawu isa tace,
“Wannan ne yaron yaya, idan da hali Dan Allah a taimaka Masa dukda dai bansan asalin yadda suka hadu d bilqees din ba.”
Gyada Kai kawu isa yyi yace,
“Ah..Toh ai wanna babu matsala habiba, ke bilqees taya kuka hadu da Wannan yaron? Domin musan ta Inda zamu taimaka Masa.”
Bilqees tayi shiru tana tunanin kawu isa yace,
“ki saki ranki bilqees yadda kikayi niyyar taimako muma haka mukeso mu taimaka Masa ko Allah zaisa a gano asalin sa.”
Gyada Kai bilqees tayi kafin daga bisani ta fara sanar dasu asalin yadda ta hadu da yareema yaseer. Daga inna har kawu isa babu Wanda beyi mmkin jin Wannan lamarin ba. Inna habi tace,
STORY CONTINUES BELOW
“Amma meyasa tun farko baki sanar dani Hakan ba bilqees? Baki San boyemin Hakan d kikayi ya jawo Mana cin mutuncin da mahaifin ki keyi Mana ba? Ai da ace tun farko kin sanar dani d tuntuni an Samo mafita bilqees, Amma sai kiyi shiru????”
“Kiyi hakuri inna.”
Bilqees ta furta Hakan a hankali tana dukar da kai. Yareema yaseer daya juya masu baya ya juyo d sauri yana kallon bilqees jin yanayin muryar ta ya canja kamar me shirin kuka ya koma kallon sa kan inna habi d keyin fadan sai kuma ya Kawar dakai d sauri sbd yadda yaga tayi Masa kwarjini saiya kasa yin kudirin d yyi niyya akan kamo hannun bilqees din su tafi.
“Shikenan habiba yanzu ba batun fada za’ayi ba, batun mafita ake nema.”
Inna habi taja numfashi kafin tace,
“kana ganin akwai damar ya zauna a dakin naka na kofar gida?”
Kawu isa yace,
“Wannan ba matsala ya zauna dama ba kowa a ciki.”
“Alhamdulillah”
Inna habi ta furta ranta a Sake tace,
“toh saimu sa cikiyar shi a kewayen kauyikan mu ko Allah zaisa aga Wanda ya sanshi ko?”
Kawu isa yace,
“Nima Abinda nake tunani kenan Kuma Insha ALLAH zamuyi iyakar kokarin mu n ganin an Samo waye shi tunda baya cikin tunanin sa.”
Sosai bilqees taji dadin tattaunawar su akan yareema yaseer, Hakan yasa tace,
“Mlm Idi ma yace zai tayamu Addu’a d Kuma mgnin Karya sammu domin yace Wannan juyawar tunanin baya wuce Asiri ko sammu.”
“Ba shakka tabbas biri yyi kama da mutum”
Cewar inna ta furta da Al’ajabi, tana ci gaba d fadin,
“Abinda yake ta yawo a Kaina kenan ace mutum kamar shi ya kasa sanin waye shi? Dole akwai wata a kasa.”
Bilqees ta girgiza kai, yyinda kawu isa yace,
“Duk tsanani duk wuya Bi’izinillahi ta’ala zai warke Harya tuna asalin sa.”
Inna habi tace,
“tohm Allah ya datar damu.” “Ameen Yah hayyu yaa qayyum.”
Suka furta Hakan a tare. Dakin kawu Isa ya nuna masu gashi nan fes sai taburmar Kaba a ciki sai daga can gefe akwai gadon bunu irin Wanda ake cikashi da yayin Nan, da pillow na bunu shima Wanda aka cika da yayi aka kulle Dan aji dadin kwanciya.
Bilqees ta juyo gefen yareema yaseer daya harde hannu da murmushi kan fuskar ta tace,
“ga Inda Zaka dinga kwana Annur gurin yyi kyau ko? Ba wari ba kazanta komai fes.”
Ta Karasa mgnr cike dajin dadi. Ganin yadda Duk ta saki ranta akan wajen ya sashi daurewa Amma badan yaso ba ya gyada mata Kai Yana murmushin yake alamar yyi, bilqees ta washe baki domin dama tsoron ta kada ya sake musanta wajen dan haka tace,
“shiga ciki bari nazo.”
Tana gama fadin haka ta koma wajen su inna da suke shawara da kawu isa, da murnar ta tace,
“Zai zauna a wajen kawu.”
“Toh madallah”
kawu Isa ya furta Hakan yace,
“ki Shiga gidan idan larai ta gama sallar kice ta baki tuwo na bakon d nace a kwasa Masa.”
Bilqees tace, “Toh.”
Juyawa tayi da sauri yyinda su Kuma suka bita da ido. Shiga dakin yyi yana karewa yanayin wajen kallo. Ginin kasa ne na tubali, saman dakin rufin tumba ne irin Wanda ake Dora itace a mannne da kasa hade da yayi sai kofar window ‘yar karama. Kamar dai tun farko gadon na gefe sai taburmar Kaba katuwa da aka malale dakin da ita.
STORY CONTINUES BELOW
Zama yyi yanajin zuciyar sa ta aminta da wajen kawai ya kishingida akan pillow din yayin da akayi. Mikewa yyi d sauri jin tsinke ya soke shi a damtsen hannun sa, yatsina fuska yyi yana janye rigar hannun sa a daidai lkcn bilqees ta shigo da kwano a hannun ta,
Ajewa tayi da sauri ganin yanata faman cire Abu ya kasa. Zama tayi a gabansa tana riko damtsen nasa tace,
“Lpy? Meya faru? Ko cinnaka ne ya cije ka?”
Rintse ido yyi be iya yi mata mgn ba bilqees ta haska wajen da aci bal-bal din data shigo da ita. Irin fitilar Nan da akeyi da gwangwanin Madara a sa mata lagwani a ciki, cikinsa Kuma kalanzir. Wara ido yyi yana matsawa gefe hade da kwabe fuska kamar zaiyi kuka ga sokewar tsinke ga zafi d hayakin fitilar aci bal-bal duk abin ya isheshi.
Bilqees Bata kula d Hakan ba tasa hannu a hankali ta zare tsinken daya soke Masa damtse tana dagowa sama ta kalleshi sai kuma tasa dariya.
Mmki ne ya isheshi, Hakan ya sashi zuba mata ido beyi mgn ba. Bilqees tace,
“Akan Dan wanna Abu kke shirin yin kuka? Gsky duk yadda akai a zahirin ka rago ne.”
Harara ya balla mata Yana Kawar d Kai. Bilqees ta shanye dariyar ganin yaji haushi, tace,
“oh..na manta kaifa jarumi ne sbd kayi fada da manyan barayin daji.”
Juyowa yyi a Hankali Yana kallon yadda take ta boye dariyar da take Masa ya cije lips a hankali Yana kokarin kwanciya Dan duk ya gaji.
Bilqees tayi saurin dakatar dashi tana kwaso abincin data shigo dashi tuwo ne na dawa da miyar kuka Wanda yasha man shanu sai kamshi yake ta dire Masa a gabansa tana budewa tace,
“Ya kamata yaudai Kaci Wani Abu me nauyi a cikin ka.” Gwalo ido yyi yana kawar da Kai bilqees tace,
“baka ci?”
Yatsina fuska yyi yana janyewa gefe alamar bayaso. Yaushe ma zai iya cin Wannan abun a cikinsa? Ga Abu Nan sai kace Dutse da wata Miya tamkar daurayen gantsa kuka wai yaci tabdin. Bata rai bilqees tayi tana rufe kwanon tace,
“Ttunda baza Kaci ba shikenan na tafi.”
Ta furta Hakan tana kokarin tashi Duk zuciyar ta babu dadi. Ganin yadda ranta ya baci ya sashi matsowa d sauri yana gyara zaman sa a gaban abincin yace,
“zanci.”
Ya furta Hakan kasa2 badan yaso ba. Juyowa tayi a tsanake, yadda taga ya furta a takure saiya Bata tausayi. Kuma izuwa yanzu har mmkin gudun bacin ranta d yakeyi take. Ikon Allah, zama tayi ta bude Masa kwanon ta tura a gabansa tana sakin ranta yadda zaici din tace,
“Toh gashi nan, Kawo na zuba maka ruwan.”
Ta daga kofin ruwan data zo dashi tana tura Masa wata roba Inda zai wanke hannun sa. Mika hannun yyi kamar baya so ita kuma tahau tsiyaya Masa a nutse yyinda ta bangaren sa Kuma ya zuba mata ido Yana karewa fuskar ta kallo.
“Yauwa yanzu sai Kaci ko?”
Ta Ida zancen tana dagowa taga ya kafeta da ido. Wara idon nata tayi tace,
“kana jina kuwa?”
Firgigit…ya motsa Yana gyada Kai yace, “Eh.”
Bilqees ta Kawar da Kai tana mikewa tace,
“Inna tana jirana a waje, Kac
i abincin Saida safe zamu hadu kaji? Kada ka tafi ko Ina kaji? Zan dawo da safe Insha ALLAH, duk abinda kke bukata kawu Isa zaiyi kafin na dawo kaji?”
Yanayin fuskar sa ce ta canja gaba1. Bilqees ta dauke kai domin ta fahimci baya son tafiyar tata, yoh Banda Abinsa baligi dashi so yake ta kwana dashi? A haka tabar wajen Bata waiwaiye shi bama bare ya Bata tausayi.
STORY CONTINUES BELOW
Kamar yyi kuka haka yareema yaseer ya kwabe fuska Yana Bata rai, hararar tuwon gabansa yyi tamkar shi yyi lefin haka ya ture gefe beci tuwon ba Yana shirin komawa ya kwanta wata zuciyar ta tuna Masa bilqees, dukda bata wajen sai yaga bazai iya mata Hakan ba tunda ya Tabbatar mata da zaici din. Tashi yyi a tsanake ya zubawa tuwon ido Yana mmkin Wanne irin abinci ne wannan? Shifa zuciyar sa tafi aminta da kayan fruits din d bilqees ke bashi domin yafi jin Hakan a ransa kamar d can ya saba da ci saidai bazai iya tuna yanayin ba.
Gutsuro tuwon yyi yasa a baki a hankali ya fara taunawa dakyar tamkar ya samu mgni. Ba karamin kokari yyi ba Yana zare ido haka ya hadiye tuwon kamar dole. Haka ya sake daurewa ya gutsuro Wani, Ana ukun kuwa kasawa yyi, ji yyi cikinsa ya kulle waje daya, ba shiri ya janye kwanukan gefe Yana yatsina fuska a haka kawu isa ya shigo da sallama.
Dagowa yyi da Dan sakin fuska ya Amsa Masa sallamar. Kawu Isa ya zauna kusa dashi da murmushi yace,
“harka koshi ne?”
Gyada Kai yareema yaseer yyi batare daya furta komai ba. Kawu isa ya dubi gurbin daya gutsira bana kirki bane, yace,
“Annur ai bakaci na kirki ba”
Dan murmushi yareema yaseer yyi kafin yace,
“Na koshi kawu.”
Ya furta Hakan kamar yadda yaji bilqees ta ambata. Kawu isa ya girgiza Kai yace,
“Tohm Madallah”
kafin yaci gaba da fadin,
“Mun gama mgn da mahaifiyar bilqees zamu je mu baza lbrin ka ko’ina cikin Wannan kauye namu da kewaye ko Allah zaisa a samu Wani Wanda ya sanka ko Wanda ya San lbrin ka.”
Yareema yaseer ya Kawar da Kai beyi mgn ba. Haka kawu Isa ya gama bayanin sa kafin yyi Masa sallama bayan ya sanar dashi akwai ban daki a gefen Inda dakin yake idan yanada bukatar zagawa. Amsa Masa yyi da Toh sannan shima ya tafi.
Zuciyar sa babu dadi ya lumshe ido bayan ya kwanta, besan meyasa ba amma baya Wani murna da Wannan binciken da suke Masa wai asalin sa? To dama mutane sunada Wani asali ne? Ai yadda ya ganshi haka kawa, Gani yake kowa ma haka kawai yake ba Wani asali ko lbrn sa ko dangin sa d suke ta faman furtawa tun bayan daya shigo kauyen Nan. Mtwss yaja tsaki Yana Kara gyara kwanciyar sa a takure a haka bcci ya dauke shi.
Tunda suka koma gidan Kuma sai habaici ke tashi daga inna Zabba da mlm Musa. Inna Zabba tace,
“Gsky kinji kunya habiba ace harda ke za’a aje zabgegen saurayi a kauyen Nan? Mutumin da ko asalin sa baku sani ba? Sbd tsabar neman Suna ne ko gindin zama?”
Banza inna habi tayi mata Bata Amsa Mata ba tayi wucewar ta daki tana janyo hannun bilqees din.
Matan makotan su da suke zaune a tsakar gida anata gulmar goyon bayan da inna habi ta bawa ‘yarta wata daga ciki anace da ita rakiya tace,
“ke kuwa zabba’u Ana neman da namiji ba’a samu ba sunga tsuntsu daga sama zasu makale Masa.”
Zabba’u tasa dariya tace ba shakka na gaba sai tace ita ta haife shi. Dariya sauran suka saka Suna ci gaba da gulmar su inna habi na jiyo su Amma Bata tanka masu ba. Ko wanne irin cin mutunci zasuyi mata Mlm Musa ne ya jawo mata ta barsu da Allah kawai. Bilqees duk ta damu da yadda ake yadawa mahaifiyar ta mgn, ba Abinda ta tofa nata Albarkacin bakin ba inna habi bazata bari ba, haka sai ta karaci takaicin ta ta kwanta bcci hade da tunanin yareema yaseer data baro a gidan kawu Isa. Bambambam….., Daga waje suka dinga jiyo Ana girgiza kofar gidan tamkar za’a ballata ta, mlm Musa daya gama shan kokon safe ya mike a fusace yana nufar wajen yace uban uban waye me shirin ballemin kofar gida?? Lauwali daya dawo daga daji ba shiri ya ware murya sosai yace lauwali ne. Shanye jarabar sa Mlm Musa yyi ba shiri ya fara washe bakin dole bayan ya zare sakatar gidan yace auhoo Ashe kaine. Fuska a daure lauwali yace eh nine. Mlm Musa yasha jinin jikinsa Hakan ya sashi fara zuba ba shiri yace Nake fada maka Wlh ba yadda banyi ba yarinyar Nan ta yage bakon Nan daga jikinmu Amma tayi min kunnen uwar shegu, Dan iya shege ma mahaifiyar ta ce ta Samar Masa mafaka a gidan Dan uwanta. Lauwali yace meyasa tun wuri baka kirani na saita masa hanya ba?? Ko ka manta bilqees yanzu a matsayin matatat take? Taya za’ai kayi irin Wannan sakacin harta nemi taimakawa Wani shirgegen Kato can wanda ba’a San asalin sa ba? Mlm Musa yace billahillazi lauwali ba irin kokarin da banyi maka ba, ai na fada maka tun farko karshe ma Korar su nayi ita d bakon….kace me?? Lauwali ya furta da karfi Yana zare Masa ido. Mlm Musa yace Ina nufin ta mayar dashi Inda ta ganshi ai ita bilqees a gida ta kwana. Toh ai inace harda ita ka kora da anyi hawan bori a kofar gidan Nan yaseen. Mlm Musa ya girgiza Kai da sauri yace idan kanaso ma saina Kira maka ita. Da dai yafi. Lauwali ya furta hakan yana gyara tsayuwar sa. Da sauri Mlm Musa ya juya cikin gidan Yana rarakawa bilqees Kira. Bilqees data samu bcci ya dauke ta d safe ta mike a firgice tana juye2 Mlm Musa ya bankade labulen dakin su yace kinaji Ina zabga maki Kira bazaki taso ba? Mikewa tayi d sauri ganin yana shirin afkowa dakin ta janyo hijab dinta ta saka tana fadin yi hakuri banji bane. Dogin tsaki yaja Yana ha baya yace jeki wajen ja’irin yaron Nan Yana kofar gida. Ko be ambaci suna ba ta fahimci da lauwali yake. Hakan yasa ta Bata rai sosai tana daure fuska ta sanya silifas dinta ta fito.
Baalkiii…lbrn da nakeji a gari gsky ne? Lauwali ya furta Hakan yana tsareta da ido. Banza tayi dashi tana kawar da Kai, lauwali ya dawo ta gefen da take ta matsa d sauri yace hankali na ya tashi Baalkiii kinsan yadda nake sonki kuwa? Taya Zaki min haka? Meyasa Zaki biyewa bakon da ko kadan baki San asalin sa ba? Idan Mugu ne fa?? Harara ta banko Masa tana sake kauda Kai a ranta tana fadin wai Mugu, Toh idan akwai Wanda yafi cancanta da a kirashi da Mugu Toh ya biyo bayan Kai….., Baalkii dake nake mgn fah? Kinsan a kanki billahillazi Ina iya kashe shi. Juyowa tayi a razane lauwali ya gyada Kai alamar Tabbatar wa kafin yace toh meye Dan na sheke shi? Da sauri bilqees tace kada ka fara tunanin haka lauwali. Da mmki ya dubeta yace sbd ya fini a wajen ki? Girgiza Kai bilqees tayi d sauri ganin yana hade fuska ta sassauta nata fushin Dan taga alamar dgske sai ya iya neman yareema yaseer da fada Kuma fada dashi ba kyau. Dan haka tace baka fahimce ni bane lauwali, lauwali yace toh inajin ki, ki fahimtar Dani. Bilqees ta sauke ajiyar zuciya kafin tace taimaka Masa zanyi fah? Bako ne Wanda besan asalin waye shi ba ya manta tunanin sa. Tabe baki lauwali yyi yace toh sai me? Kinga nifa wlh bazan yadda da Wannan kusancin naku ba Baalkiii, haka kawai naje yamin illah. Bilqees ta daure fuska kafin tace shikenan idan ka tabashi saidai a kawo gawata gidan ka. Gwalo ido lauwali yyi yana rike haba yace Baalkiii? Akan shi bakon? Gyada Masa Kai tayi alamar Tabbatar wa, shikenan, naji zan kyale ki Amma Wlh ya kiyayeni kada ya shige miki da yawa idan ba so yake nayi gunduwa-gunduwa dashi ba. Wara ido bilqees tayi a tsorace lauwali yace Dan fa kece, da Wlh saidai ki nemi bakon Nan ki Rasa tun dare zansa a dauke min shi aje can a cillar dashi Wani wajen yaje ya karata. Kasa cewa komai tayi domin lauwali wanna ba karami aiki bane a wajen sa tsaf saiya aikata. Kuma da nace sai Nan da wata daya ayi bikin mu Wlh na fasa Nan da kwana uku za’a daura iyakar hakurin da zanyi kenan na dinga ganin ki da Wannan bakon…zaro ido bilqees tayi a firgice jin kalaman lauwali, lauwali yace kwaraii gwarama kiji da kyau Kuma kisan yadda zakiyi dashi Dan ba binki zaiyi ba atoh. Dan naji lbri yadda kasan bindi haka yake binki duk Inda kikeji Toh ki sanar Masa billahillazi kunyar sa ta kiyayi shiga gonata. Lauwali? Bilqees ta furta Hakan hankalin ta a tashe, lauwali yace kinada abin fada ne? Bilqees tace yanzu bazaka tayani tausaya Masa ba? Shifa yadda kasan jariri haka yake besan a wacce duniya yake ba. Toh Kuma sai me? Ubansa ne ni dazan damu dashi? Toh ko uwar mu daya ub
an mu daya dashi naga Yana kokarin shishige maki Wlh sare Masa Kai zanyi…ya furta Hakan yana zare takobin bayan sa. Ja Baya tayi a mugun tsorace lauwali ya kwashe da dariyar mugunta yace kwantar da hankali ai kekam ko kuda ya nemi takura Masa fille Masa Kai zan domin babu Dan shegiyar daya isa tabaki matukar Lauwali Yana Nan. Wannan takobin jinin masu shiga gonata take sha. Kasa mgn bilqees tayi domin tsantaar gksyr sa yake fada Hakan yasa ta juya Baya tana dafe kirji can ta hango yareema yaseer a bayan wata bishiya ya harde hannayen sa idonsa a kanta fuskar sa a daure tamau. Gwalo ido tayi kirjinta na bugawa tana fatan ace kada lauwali ya ganshi ta dawo da hankalin ta kan lauwali dake shafa takobin sa a hankali fadi yake Wlh jini take bukata Wannan ‘yar amanar. A kidime bilqees ta juya da nufin yiwa yareema yaseer alamar ya tafi Dan bataso su hadu abin bazaiyi kyau ba sai kuma taga ya fara takowa Inda suke gadan-gadan fuskar Nan ya sake daureta sosai tamkar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa.