SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba ɗaya kansa ya kulle yarasa meke damunsa,  wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaɗai zai iya fayyace masa halin da yake ciki,  tabbas shi koda son Zahrah Abid ɗin yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani,  saurin laluɓar wayarsa ƙirar  Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa ƙira, bugu biyu Abid ya ɗaga ƙiran cikin muryan kasala yace “Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata”+

“mcheeww aikin ka kenan cin ƴaƴan mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai” Zaid yafaɗi haka cike da zaƙuwa.

Miƙa Abid dake kwance shame shame a gado yayi haɗe da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin ƴaƴan mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a ƙarƙashin Zaid yake, domin kuwa Iskancin Zaid me lasisi ne.

Cike da ƙuluwa Zaid yace ” Nifa bana ƙira ka kamin iskanci bane, da zaka tsaya kanamin dariya”

“Yi haƙuri mana nawan, maganartaka ce tabani dariya, zuwa anjima mu haɗu a Millinion Park ina fata de bawata matsala bace ta afku?”

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe da duban agogon Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.  “Shikenan to muhaɗu ƙarfe 5 na yamma banakumason kamin african time, 5 nacika idan bakazoba, bazan tsaya ɓata time ɗina wajen jiranka ba” yayi maganar cikin yanayi da yake nuna cewa ba wasa yake ba..

“Okay” kawai Abid yace haɗe da aje wayartasa yajawo babe ɗin dake kusa dashi, suka ci gaba da watsewarsu ko kunyar Allah dayake ganinsu basayi, Allah karabamu da ƙeƙashewar zuciya Ameen.

Zaid yana aje wayartasa yasanya hanu yashafi cikinsa, sai alokacin yake tuna rabonsa da yasanya abinci acikin cikinsa tun jiya da yammaci,  amma saboda tsabar yashiga tension ko yunwarma bayaji,  murmushi yayi tunowa da yayi da yanda yaji muryan Abid, dagajin yanda yaji yanayin muryartasa yatabbatar masa cewa holewa da mace Abid ɗin keyi, “hmmm Abid ba dama wajen iya latsa mace” yafaɗi haka a fili, shikamma rabonsa daya kusanci wata mace harya manta,  shi yanzu ko mace ma yagani bata wani burgesa, yanzu idan zaiyi sex to badakowacce mace yakeso yayi ba, face Zahrah ita kaɗai yakejin cewa zai iya sauƙewa damuwarsa yanzu, itakuma kaɗaice zata iya basa gamsuwa ɗari bisa ɗari.  Miƙewa yayi yanufi wajen fridge ɗin dake ɗakin nasa, fresh milk ya ɗauka haɗe da tsiyayawa a cikin glass cup, zama yayi yasoma sipping fresh milk ɗin a hankali,  gaba ɗaya hankali da tunaninsa sunaga Zahrah, ko yanzu wani hali take ciki? Allah masani…

***

Sake narke masa murya tayi cikin shagwaɓa tace “Nide bance bana sonka ba, aikaima kasan inasonka, kawai de nakasa sakewa da kai ne har yau!” taƙare maganar tana me rausayar dakanta gefe tamkar yana ganinta..

Dr.Sadeeq dake zaune cikin luntsumemiyar kujeransa na office ya lumshe idanunsa haɗe da gyara zaman wayar akan kunnensa,  sosai shagwaɓan Zahrah ke sauƙar mai da kasala acikin jikinsa, yayinda idan yaji muryarta yake samun nutsuwa a cikin zuciya da ruhinsa…

STORY CONTINUES BELOW

“To meyasa bakya iya sakewa dani ne My Princess, kinkuwa san irin sonda nake miki?  inasonki Zahrah fiye da tunaninki,  amma bazaki gane hakan ba, sai idan nasameki a matsayin matata, na tabbata nan da 3 weeks kinzamo mallakina daganan kuma zaki gaskata soyayyata a gareki!” yafaɗi maganar tasa cikin  yanayi na shauƙi..

Saurin kulle idanunta  tayi haɗe da sanya hanu tarufe fuskarta, saikace wanda take aga banshi,  sosai maganarsa yasa taji kunya,, ta lura haka Dr.Sadeeq ɗin yake watarana baruwansa kansa tsaye yake faɗar maganar da zaisanya taji kunya.

“My Princess kinyi shiru” Dr.Sadeeq  yafaɗi haka a kasalance.

Numfashi Zahrah ta fesar haɗe da sake yin ƙasa da muryarta cikin shagwaɓan daya zamemata sabo tace “Munyi magana da Baffa, yace ku kawo kayan lefen duk sanda kuka shirya kawai”

Daɗi ne yakama Dr.Sadeeq harsaida yakasa ɓoye murnarsa idan kuwa hakane to tabbas acikin satin nan zai sanar da ƴan uwansa saisu shirya rananda zasu kawo kayan, shida zasuce yauma to tabbas da zaiso hakan.

“Naji daɗin maganarki My princess saboda haka kincancanci nabaki kyauta ta musamman, idan banzo da dare ba gobe zanzo insha Allah”

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗi da cewa “Nagode amma kariƙe kyautarka bayanzuba”

“Meyasa?” yatambayeta cikin yanayi na ɓata fuska.

“Saboda hidiman da kakeyi yayi yawa, dan Allah kabari haka kaji!” taƙare maganar cikin yanayin shagwaɓa. 

“Inde akan kine Zahrah bazan taɓa gajiyawa ba, zanyi wani aiki yanzu zanƙiraki anjima kinji princess ɗina!” yafaɗi haka cike da lallashi…..

Haka sukayi sallama cike da kulawa ga junansu, yanzu kam tagama aminta da Dr.Sadeeq insha Allah kuma idan ta auresa zata basa farinciki me ɗorewa, iyaka iyawarta…..

Sosai Zaid yashaƙa da irin yanda Abid yasanyasa agaba yaketa yi masa dariya,,   tsuka Zaid yaja me tsayi haɗe da kawar da kansa gefe jiyake tamkar ya tashi ya rufe Abid da duka, idan banda iskanci taya zai sanyasa gaba yayi ta masa dariya bayan yagama jin matsalarsa…

Wani mugun kallo Zaid yajefawa Abid me ɗauke da tarin ma’anoni da yawa, ganin haka yasanya Abid saurin gimtse dariyarsa haɗe da kama hanun Zaid ɗin…

“Yi haƙuri Abokina, maganar ce tabani dariya”

Tsuka Zaid yakuma ja batare da yace komai ba…..

“Nafuskanci inda matsalanka ta dosa Zaid amma kuma nasan abune me wahala ka yarda da abun dazan faɗa ma”

“Bazaka gane yanda nakeji agame da’ita ba ne Abid, dakasan yanda nakeji a zuciyata da ka tausaya kasanar dani maganin matsala ta, kodai shine so ɗin da kake cewa?” Zaid  yatambayi Abid cike da damuwa…

“Ƙwarai kuwa Zaid wan nan shine SO, sai de naka SO’n ya banbanta da sauran soyayya’n, kai naka soyayya’r me tsanani kakeyi, wanda tariga da tajima acikin jikin ka batare da ka sani ba, ina da yaƙinin cewa tun farko Son Zahrah kake bawai sha’awarta ba kamar yanda ka ɗauka!” Abid yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa…

Nannauyar ajiyar zuciya Zaid ya sauƙe haɗe da sanya duka hannayensa ya dafe kansa wanda yake ɗan sara masa a hankali..   Tabbas yanzu kam ko yaso ko yaƙi dolensa ya yarda da maganan da Abid yafaɗa masa, domin kuwa idan har ba soyayya ba menene ke damunsa dayake sawa yakejin zafi a zuciyarsa? idan ba soyayya ba menene yake sanya tunaninsa hargitsewa da zaran yatuno Zahrah? idan ba soyayya ba menene yake sanya sa rasa sukuni da nutsuwarsa aduk sanda yatunanota kokuma yaganta? lallai kuwa soyayya baimasa adalci ba da bai sanar dashi kansa ba tun sanda yafarasa batare da yasani ba..  

Idanunsa da sukayi jajur dasu ya ɗaga haɗe da maida kallonsa ga Abid  “Inasonta Abid inasonta sosai!”

Waro idanu Abid yayi yana me kallon Zaid  idan da ba Zaid ɗin ne da gaske a gabansa ba, to tabbas da sai yace badaga bakin Zaid wa ƴan nan kalaman suka fitoba, yau Zaid da kansa yake cewa yakamu da son wata? lallai kuwa rayuwa tana shirin juyawa abokin nasa baya.1

STORY CONTINUES BELOW

Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan ɗan ƙaramin table ɗin dake aje gabansu.

Kallonsa Abid yayi cike da mamakin ganin yanda lokaci ɗaya yanayin Zaid ɗin ya sauya.

“Inakuma zaka?”   Abid yatambaya..

“Zanje gidansu Zahrah Abid, idanuna sun matsamin zuciyata har bugawa take Abid, ita kawai nakeson gani,  idan har zata amince inaso ayau base gobeba koda ƙarfe ɗaya ne  na dare  a ɗaura mana aure da’ita” yanakai wa nan a zancensa yayi tafiyarsa.. Hangame baki Abid yayi yana kallonsa harya ɓacewa ganin idanunsa.   Anyakuwa Zaid yana cikin hankalinsa? Kodai asiri yarinyar talakawan nan tayi masa ne?  Abid yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin,  bayan yasan baida amsa bai kuma da me basa amasar…

Zahrah dake zaune tana gudanar da assigment ɗinta, wani yaro yashigo cikin gidan nasu haɗe da kwaɗa sallama..  Amsa masa Zahrah tayi batare da taɗago kanta takalli yaron ba..

“Wai ana ƙiran Zahrah a waje” yaron yafaɗa yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi ƙiranta..

Sai alokacin Zahrah taɗago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaɗi, to waye kenan yake sallama da’ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da’ita ta ɗauka haɗe da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq,  dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji ƙiran nasa ba, kenan shine yazo yaƙira wayarta bata ɗauka ba shiasa yaturo yaro.   “Jekace inazuwa” ta  bawa yaron amsa a taƙaice..

Miƙewa tayi haɗe da tattara takardunta tayi ɗaki.  Mayafi taɗauka   ta yafa akan kayan dake jikinta…

Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman  motar yana me kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa..

Kanta a ƙasa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta.  Tsayawa tayi cak bayan ta haɗe wani  miyau dayazo me ɗaci ya maƙale mata a maƙoshinta. 

Murmushi yasakarmata haɗe da soma takowa zuwa gareta..

Lokaci ɗaya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haɗe da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa….

“Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah,  inaso ki saurare…..” kasa ƙare maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiɗa masa akan  kyakkyawar fuskarsa…

Cikin ƙuna da kuma zafin zuciya     haɗi da raɗaɗi Zahrah ta haɗa yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaɗa ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..

“Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka,  wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naƙara ganin fuskar  ka to zanyi maka abun da baka taɓa tunani ba!” cikin matsanancin ɓacin rai taƙare maganar tana me raɓan gefensa zata wuce,  Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi ƙasa a guiwa ba yasake shan gabanta.

“Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daɗima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!” yaƙare maganar cikin rawan murya…

Kuka ne ya ƙwacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa…..

“Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaɓi cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na ɗau soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaɓi ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin ƙunci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid,  Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaƙara haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!” cikin matsanancin kuka taƙare maganar tana me durƙushewa ƙasa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa ƙafafunta…

Idanun Zaid ne suka kaɗa suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono.   gaba ɗaya jikinsane yasoma ɓari, shi ɗin ma durƙusawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaƙira sunanta,, saurin ɗaga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..

“Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani,  zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai ɗaukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taɓa yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !”  a fusace ta faɗa cikin gida haɗe da banko ƙofar gidan nasu. 

Tashi yayi daga durƙuson da yake haɗe da bin bayanta da kallo, gaba ɗaya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi,  zafi yakeji azuciyarsa irin sosai ɗin nan.

Zahrah kuwa zamewa tayi jikin ƙofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raɗaɗi dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata?   ganinsa yasake tasomata da mikin daya ƙi warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta,  maiyasa Zaid yazame mata bala’i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai…

Zaid kuwa daƙyar ya iya jan ƙafafunsa yanufi motarsa,  kasa tuƙa motar tasa yayi, gaba ɗaya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taɓa iya tuƙa mota yana a irin wan nan halin ba,, da ƙyar ya’iya laluɓa wayarsa yaƙira driver’nsa… Mintuna kaɗan drivern Zaid yazo ya wuce dashi….

Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haɗe da miƙewa daga jikin ƙofar tashige cikin gida, direct ɗakinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauƙewa, lokaci ɗaya zazzaɓi yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluɓi jikinta….

Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai,  wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi,  da ƙyar ya’iya jan ƙafansa yashiga ɗaki,  kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faɗa ɗin nan,  wlhy a gurinshi da ta faɗi wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan ƙuncinsa..     Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,,  wasu ƙwayoyin magani yaɗauko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba’a sai dasu a bayyane sai de a ɓoye, kuma suna mugun sa bacci sosai…   Saida ya ɓalli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haɗiye magungunan,  yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai ɗaga masa hankali,  kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake ƙwato numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwace masa da ƙyar.  wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci ɗaya kuma komai najikinsa ya sake…1

Zahrah kuwa zazzaɓine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci ɗaya jikinta yasoma ɓari ta fara rawan ɗari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin ƙuncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haɗu da Zaid ƙuncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?…..Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don  Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun…

“Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!” Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.

“Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!” Labisat tafaɗi haka cikin shagwaɓa. 

Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon…

Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan,  jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya😂)

Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,,   bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa…

“Brother! Brother!”  ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin ɗakin ko baya ciki ba..

Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta…

“Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door ɗinsa amma bai amsa ba”

“Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba,  miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba” Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..

Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..

Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..

“Zaid!” taƙira sunansa cikin kakkausar murya… Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..

Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma’abocin yawan bacci ba’a bisa ƙa’ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi,  “Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?” tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin,  “Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu’umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi”…

STORY CONTINUES BELOW

A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..

Idanu Mom tasake warowa waje, tabbas idan de idanunta de de suka gane mata to kuwa Zaid baya numfashi, domin  babu wata alamar  da take nuna akwai nunfashi a tattare dashi saboda ko cikin sa baya motsawa, alama ta baya shaƙan numfashi kenan..

Hanunta takai setin hancinsa ko da zataji ɗumin numfashin sa.

Salati Mom tasa haɗe da dafe ƙirjinta, sakamakon wani irin bugawa da taji zuciyarta tayi.

“Zaid!Zaid!” Mom tashiga ƙiran sunansa cikin tashin hankali haɗe da soma jijjigasa.

Hawayene suka shiga bin ƙuncin Mom bashiri ta fita daga ɗakin, direct ɓangaren Alhaji Ma’aruf ta nufa saboda yana gida baikai ga fita office ba..

“Alhaji! Alhaji! katemaka wlhy Zaid baya numfashi zo muje ka gani, katemakeni kada na rasa ɗana mafi soyuwa a gareni!!” gaba ɗaya cikin tashin hankali Mom keyimawa Dad bayani..

Mamaki haɗi da al’ajabi ne yakama Alhaji Ma’aruf amma de yanzu balokacin tambaya bane gwamma yabita yaga meke faruwa da Zaid ɗin….

Shima sosai ya tsorita kuma hankalinsa yatashi daganin Zaid yashe a gado baya numfashi sai kace gawa…

Da ƙyar Abba ya’iya sungumarsa yasanyasa a mota, abunka da ƙaƙƙarfa kuma ma’abocin yin gym shiasa jikinsa yake ko ina a murɗe, san nan kuma me ƙaramin ƙarfi bazai iya ɗaga sa ba, Dad ɗin ma saida temakon Mom ya iya ɗagasa… Daga Mom har Labisat hankalinsu amatuƙar tashe yake haka suka shiga mota suka rankaya zuwa asibiti…

Direct Emergency  aka kai Zaid cikin gaggawa likitoti suka shiga basa temakon gaggawa…

Jigum jigum haka Abba da Mom sukayi a wani ɗan corridor dake kusa da ɗakin da aka kai Zaid, iya ƙololuwar tashin hankali sun shigesa, kuka kawai Mom da Labisat keyi, kasa koda rarrashinsu Alhaji Ma’aruf yayi domin shima da akwai hali da kukan ze sanya ko da zaiji sassauci a cikin zuciyarsa…

Likitotin nan sunci baƙar wahala kafun da taimakon Allah suka samu suka daidai ta numfashin Zaid. Haka suka fito suna sharce gumi….   Kallon Alhaji Ma’aruf ɗaya daga cikin Doctors ɗin yayi haɗe da cewa “Ranka ya daɗe muje office”    ƙoƙarin binsu Mom tasomayi Alhaji Ma’aruf yaɗaga mata hanu alamar tajirasu….

Handkerchief likitan nan yaɗauka ya ƙare share gumin dake tsatstsafawo akan goshin sa..

Ganin haka yasa Abba cike da tashin hankali yace “Yade Dr.Bilal meke faruwa ne, dan Allah kada kafaɗamin wani mummunan labari!”

Jinjina kai Dr.Bilal yayi haɗe da kallon Dad.  “Kwakwantar da hankalinka Alhaji zuwa yanzu komai ya daidaita munshawo kan matsalan”

Nannauyar ajiyar zuciya Dad yasauƙe haɗe dayin hamdala acikin ransa…

Sake gyara zama Dr.Bilal yayi haɗi da cewa “Sai de kuma agaskia bazan ɓoye maka ba Alhaji ɗan ka yana cikin matsala wanda yake gab da rasa rayuwarsa matuƙar baikiyayewa kansa shan ƙwayoyi masu mugun haɗari ba, baya ga haka kuma idan har ya cigaba dashan giya  nan da ƴan kwanaki tofa sai de kuma abun da Allah yayi!”

Yanzukam Dad ne yashare gumi ba Dr.Bilal ba, domin kuwa a iya tsawon rayuwarsa baitaɓa sanin Zaid nashan wasu ƙwayoyi masu bugarwa ba,  yade san da ya nashan giya amma kuma atunaninsa yajima da dena shan giyan.

“Bangama fahimtarka ba likita, naji kace ƙwayoyi na bugarwa, kana nufin shiɗin ne yakeshan ƙwayoyin bugarwa?” Dad yatambayi Dr.Bilal cike da son sanin ƙarin haske akan batun..

“Wato a iya bincikenmu mungano cewa akwai wata ƙwaya me haɗarin gaske da yakesha lokaci zuwa lokaci, wanda kuma haɗarin ƙwayar yana da matuƙar yawa,  bazanyi mamakin a ina yasamu ƙwayan ba, saboda nasan shiɗin isashshene, saboda ƙwayar ba ako ina ake samunta ba, a ƙa’ida ma anhana shigo da ƙwayar nan gida Nigeria, kawai de rayuwar yanzune  da ta zama sai a hankali, zai iya yuwuwa kuma ba anan yake sayan ƙwayan ba daga can waje yake shigowa da abarsa, sai de kuma wan nan duk bashine damuwar ba, idan har ya cigaba da shan wan nan ƙwaya to ina me tabbatar maka da cewa zai iya rasa ransa ako da yaushe, duk da kuwa dama munsan mutuwa tana kan kowa yanzu ko anjima, amma tabbas kiyayewan shine yafi, san nan kuma giya tayi masa mummunan illa saboda tasamu mafaka acikin cikinsa, wataƙila yamai da ita ruwan shansa ne, amma kuma duk hakan ba wani babban matsala bane idan har ze kiyaye to da taimakon Allah komai zezo masa cikin sauƙi!”

STORY CONTINUES BELOW

Salati Alhaji Ma’aruf yayi a bayyane haɗe da sanya hanu yazame hular dake kansa,  ashe bayan giya hadda wata tsinanniyar ƙwaya me haɗari Zaid yake sha? anya kuwa Zaid yanada cikakken hankali? shin wani irin haline haka da Zaid? amma babban abun tambayar shine laifin waye acikinsu, laifinsune su iyayensa kokuwa laifinsa ne shi kansa Zaid ɗin?

“Haƙiƙa dukansu suna da laifi, amatsayinsu na iyaye basu wani tsaya sunbawa Zaid kyakkyawar kulawa ba, kuɗi kawai suka sake masa haɗe da turasa makaranta har wata uwa duniya, amma duk da haka bekamata ace yakasance haka ba, idan su basa lura da al’amuransa shi ɗin mahaukaci ne da be san dede ba?   tabbas yasan shiyake da alhakin kulawa da tarbiyan Zaid tunda shine yaɗaukosa daga wajen Mahaifiyarsa yadawo dashi  America kusa dashi,  tunda suke America bai taɓa tsayawa da kyau yakula da wani irin rayuwa Zaid ɗin keyi ba, shide kawai yabuɗe masa bakin aljihu yana ganin hakan shine gata,  ƙwarai mafiyawancin iyaye ayanzu sunfi bada kulawarsune ga Ƴaƴa mata, yayinda ƴaƴansu maza kuwa ko oho, duk wata kyakkyawar tarbiya Ƴaƴa mata ake ƙoƙarin koyawa, yayinda Ƴaƴa maza kuwa suka zama hoto, aganin iyaye komiye ɗa namiji yayi adone bakamar ƴa mace ba, tabbas hakane duk abun da ɗa namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi ɗa namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba,  shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faɗan damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ƴaƴansu maza saboda ba mata ne kaɗai suke buƙatan kulawa ba harsuma maza suna buƙata……

Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaɗa me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi.    “Zaid yana buƙatar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa”

Jiki ba ƙwari haka Dad yafito daga office ɗin  yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..

“Yaya de Alhaji me likitan yacema?” Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali ɗanta yake ciki..

“Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauƙi zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buƙatar hutu ne, to dole zamu barsa yaɗan huta” Dad yaƙare maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..

Hamdala Mom tayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya

Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace “Meyasanya naga fuskarka ɗauke da tashin hankali me tsanani Alhaji?”

Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faɗa mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan ƙwayoyi, sede abun da bata sani ba shine haɗarin da ƙwayoyin suke ɗauke dashi….

********

Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaɓi sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta ƙoshi a daren jiya..

Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da’ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu….

********

“Kuka bazai taɓa yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raɗaɗi a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba,   aure zakiyi  yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin ƙunci!” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau ɗin da sukayi amakaranta bata gane kan ƙawarta ta ba…

Hannayen Husnah duka Zahrah takama haɗe da kallonta.  Cikin murya me rauni tasoma cewa…..

“Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa,  koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa  akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni?  Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta,  mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani  kyautar budurcinta,   mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu,  san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin  ga wani daban,   rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure  su samu matansu  da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta,  haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa  budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure’nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,,   wan nan ranan nake gujewa kaina  Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!” gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba’a taɓa mantawa da’ita,,  rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba’asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa…..

STORY CONTINUES BELOW

Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,,   

“Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauƙi insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko”

Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa……

***********

Jigum haka su Dad  dake tsaye  agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buɗe idanunsa ba, gashi kuma  4 hours likita yace musu zaiyi….

Babban yatsar ƙafansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buɗewa a hankali,, da sauri Dad ɗinsa yaƙaraso jikin gadon yanayi masa sannu…

Ƙoƙarin tashi zaune yasomayi da sauri Dad ɗinsa yamaidasa ya kwanta “Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaɗan wastsake tukunna kafun kasoma yunƙurin tashi”

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe dabin ledar ruwan da aka ɗaura masa da kallo.

Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid ɗin yabuɗe ido tace da Labisat tayi mata ƙiran Doctor…

Ƴan gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haɗe dayi masa wasu ƴan tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid ɗin saboda haka shirun da Zaid ɗin   yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,,  kallon Dad Dr.Bilal yayi haɗe da cewa

“Ko yanzu idan kuna buƙatar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faɗa”

Kai Dad yajinjina haɗe da cewa “Shikenan Doctor insha Allah za’a kiyaye, muje sai nakarɓi takardan sallaman ko”    Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiƙe tsaye, kafaɗun Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗan nata suka nufi hanyar fita daga ɗakin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai ƙara 1 hour a cikin asibitin ba…

Yana riƙe da kafaɗan Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat  mota ɗaya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita… Direct  gida suka nufa

Idanunsa gaba ɗaya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.

Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin ɗan uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaƙuwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa  saboda tana matuƙar son ɗan uwan nata bandashi batada wani ɗan uwa dasuke uwa ɗaya uba ɗaya shikaɗaine yayanta kuma garkuwanta……

Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har ɓangarensa,,  zama yayi akan kujera haɗe da jawo wani ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon yaɗaura ƙafafunsa akai..

“Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!”  cike da ɗar ɗar Labisar tafaɗi maganar saboda tasansa sarai ba’a iyarmasa yanzu saiya saceka..

“Friedrice” yafaɗa a taƙaice batare kuma daya buɗe kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..

Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice ɗin dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..

Mintuna kaɗan tadawo hanunta ɗauke da ƙaton tire hadda plate ɗin  yankakkun kayan marmari akan tire ɗin,, adede gabansa ta ajiye tire ɗin haɗe da ɗaukan plate ta buɗe kulan da friedrice ɗin ke ciki ta zuba masa.

“Yaya gashinan na kawo” tafaɗa tana me tura masa plate ɗin friedrice ɗin gabansa.

Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miƙewa sumu sumu tafice daga falon nasa…

STORY CONTINUES BELOW

Jawo plate ɗin yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaɗan kaɗan duk da kuwa bawai buƙatar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci…   Lomansa huɗu ya aje spoon ɗin dake hanunsa haɗe da jawo plate ɗin yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha,  sai alokacin yasoma jin daɗin bakinsa, amma da kwata kwata bayajin ɗanɗanon komai,, fruits ɗinma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake ƙauna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau ɗin koda kuwa idan yaje zata ɗauki wuƙa ne taluma masa a cikinsa…..

Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu,  kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaɗan kaɗan tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daɗin jikinta..

Inna ce zaune daga gefenta tana ta ƙoƙari wajen ganin ta seta tashan radion ta..

Wani yarone yayi sallama yace wai ana ƙiran Zahrah,,   “Jekace tanazuwa” Inna tahanzarta faɗa, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haɗe da cewa “Kace bazata zo ba”

Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah “Bazakijeba fa kikace?”

“Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili” tayi maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.

Harara Inna ta watsa mata haɗe dayin tsuka baƙin ciki kawai Zahrah’n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke ƙiran nata da alkhairi yazo…

“Wai Bazata zoba” yaron nan yafaɗawa wanda ya aikosa.

Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya…

“Wayene yacema bazata zo ba?” Zaid yatambayi yaron.

“Ita da kanta” yaron yabasa amsa domin kuwa shiɗin ɗan maƙotansu ne saboda haka yasan Zahrah’n.

Kai Zaid yajinjina haɗe da cije laɓɓansa,,  Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata ƙasƙantacciyar unguwa kuma ƙofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid ɗin da har gobe ƴan mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?”   ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace “Kaje kace injini nace tayi haƙuri tafito”   bamusu yaron yakoma yakuma faɗi saƙon da akabasa umarnin yafaɗa..

Tsuka Zahrah taja haɗe da tashi tsaye  “Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba” tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta ɗaki..

Abunda Zahrah tafaɗa shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid,   kuɗi Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron  dafari yaron yatsorita yaƙi amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna…

Motarsa yabuɗe yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taɓa iya runtsawaba matuƙar baiga Zahrah ba,  yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi..      Jan motarsa yayi yakoma ƙarƙashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaƙudurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah….

Bayan awa ɗaya

Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riƙe a hanunta se kuma wani littafi.     Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haɗe da sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi,   jiyakeyi tamkar yaje ya ɗauƙota can caɗak yatafi da ita… Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa  da sauri yabuɗe murfin motarsa daniyar ƙarasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba,  haushine yasanyashi buga tayar motarsa da ƙafarsa,      haka yakoma yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu cike da ƙuncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta…

*********

Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za’a kawo lefenta,,   yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za’abawa baƙi.  Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,,   kallon Zahrah Husnah tayi haɗe da sakin murmushi.

“Ƙawata nifa yau daɗi nakeji jinake tamkar ma nice za’a kawowa lefen”   dariya Zahrah tayi haɗe dacewa “To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinƙi”

“Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci” Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa,   “Allah yashiryeki Husnah” Zahrah tafaɗa tana dariya..  Haka de sukaci gaba da ƴan hirarrakinsu irin na ƙawaye……….

Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a ƙofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haɗe da soma ƙarewa wajen gidansu Zahrah kallo,   motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah..  Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari’a Inna da tawagarta suka tarɓi mutanen haɗe da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi…

“Sannunku da zuwa lale marhaba” Wata mata maƙociyar su Zahrah tafaɗa ga matan da suka kawo lefen.  Amma kuma daƙyar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..

Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuɗe,,  su Inna ne suka fara ɗagawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,,  Aunty Raliya ce ma tayi ƙarfin halin cewa  “Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa’a,  Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri’a”  dagajin yanda tayi maganar kaɗai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daɗin rai,,,  da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,,  kuɗi Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir ɗin ƴan dubu dubu har na dubu ɗari ta ɗaura akan wani akwati haɗe da kallon ƴan uwanta tace  “Muje ko”   dukansu miƙewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maƙotansu suka kwashi kayan tarban baƙin da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi’a ɗaya daga cikin maƙotan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuɗin da suka aje tabawa ƴarta Badi’a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,,  dawowa da kuɗin Badi’a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita ƙurar motarsu kawai tagani,,, “To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan ƙaya” Maman Badi’a tafaɗi haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,,    washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace “Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buɗe kanti” ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buɗe akwatunan,, kowanni akwati shaƙe yake da kaya nagani na faɗa,, take Inna tasoma rangaɗa guɗa hadda rawan murna…….Hayaniya haɗi da guɗan da su Inna keyi  shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a ɗakin Zahrah sunyi muƙus,,,,+

“Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aɗaki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama” Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take,,,  murmushi kawai Zahrah tayi mata haɗe da binta da kallo hartafice daga cikin ɗakin…

Hamdala Husnah tayi haɗe da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen ƙawartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi ƙoƙari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaɗai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai….

Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haɗi da shaddodi dakuma  dangin su materials,,     ɓangaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaɓo masu kyau da tsada,,  haka ɓangaren sarƙokima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarƙoƙi da ɗan kunnayenta babu wani mai sauƙin kuɗi acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma ɓanagaren jaka da  takalma ma yayi ƙoƙari sosai, domin kuwa  kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi ƙoƙari sosai  wajen fidda naira yasai kayan shafa ƴan yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace…

“Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi,  ai wan nan kayan ko ɗiyar babban attijiri sai haka” Maman Badi’a tafaɗi haka bayan taƙarewa wani haɗaɗɗen leshi dake riƙe a hanunta kallo wanda a ƙalla kuɗinsa zai kai 50k,,,

“Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi’a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!” Inna tafaɗi haka cikin murna…

Wata dake zaune kusa da Inna tace “wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu ƴaƴan mazajen aure masu ƙashin arziki” 

Duka matan suka haɗa baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce  zataƙi ace ƴarta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan….

Sai kusan magriba matan dasuka karɓi lefen Zahrah suka  soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin ɗin daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maƙiyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun…..1

Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi,  sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taɓa zaton zai ɓarnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taƙudura aranta cewa zata faɗa masa   kayan sunyi yawa……

STORY CONTINUES BELOW

Gidansu Doctor…

“Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan,  kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuɗin yashine, kallo ɗaya zakai musu kafuskanci cewa suɗin faƙara’une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani ɗa namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!” Auntie Raliya ce ke faɗan haka cikin ɓacin rai…..

Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin ɗacin rai tace  “Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har ƙarana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naƙi amincewa da aurensa,  ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiɓowa kansa shiya sani”

Ƙwafa Auntie Raliya tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiƙewa a waje san nan kuma ƴar talakawa futuk…

Auntie Raliya tana fita falo ƙawayenta da ta gaiyato suka kai lefe  tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin  Sadeeq  yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma ƙuduri aniyar lalata zancen auren abune me sauƙi kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen ƙanin nata……..

1

Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba  cike da shagwaɓa tace “Dagaske nake faɗa maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko ɗazu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya” taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daɗi sosai…

Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti ɗaya.

“Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne” yafaɗi haka yana me kafeta da idanunsa..

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaɗan sosa mata rai,  wato idan ma ta manta to yatuna mata…

Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya ɗan sauya lokaci ɗaya yakuma san maganarsa ce batai mata daɗi ba, dama kuma yafaɗi hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a’a….

“Bansan wani irin daɗi da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar  taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daɗi idan har Allah ya gwadamin wannan rana!” yafaɗi haka cikin shauƙi, dason kawar da wancen zancen nasu..

Cike da mamaki Zahrah taɗan saci kallonsa haɗi da cewa “Wace rana ce wan nan?”

“Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za’akawomin ke ɗakina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko ƙyafta ido”

Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta  tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faɗi abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai…

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuƙar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaɗan zaisha fama da’ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.

STORY CONTINUES BELOW

Kallon agogon dake ɗaure a hanunsa na dama yayi.

“8:30pm” yafaɗa a bayyane  kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata ɗago kanta ba.

“Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi” yafaɗi haka adai dai lokacin da yake ƙoƙarin  ɗaura sit belt ajikinsa..

Sai alokacin taɗago kanta amma bata yadda ta kallesa ba,, “Sai da safe” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin fita daga cikin motar domin dama taƙosa yace mata zaitafi saboda tagaji da zaman motan gashi tana da assigment kuma gobe zasuyi submit ɗinshi, san nan kuma tana buƙatar kasancewa ita kaɗai domin tattaunawa da zuciyarta a game da sabon al’amarin dayake shirin kunnu mata kai….

Kansa yajinjina haɗe da cewa “Dama so kike natafi ko?”

Murmushi tayi masa kana taɗan  girgiza kan ta alamar a’a, cikin murya me sanyi tace “Bahaka bane kawai de nafara jin bacci ne”

Kansa yakuma jinjinawa cike da gamsuwa  haɗe da juyawa baya yaɗauƙo wata farar leda dake aje kan kujeran gidan baya na motar.

“Idan Allah yakaimu da safe zanƙiraki ina fata zakiyi bacci me daɗi” yafaɗi maganar yana me miƙomata ledan dake riƙe a hanunsa…

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da marairaice manya manyan idanunta da suke sauƙar masa da kasala aduk sanda ya kallesu,,   “Gaskiya ni dai a’a nagaji da wayon da kakemin, kuma tun ba yauba na faɗa ma hidiman dakakemin yana yawa!”

Lumshe idanunsa yayi  haɗi da buɗesu alokaci guda, idan yanaganin irin wan nan shagwaɓan nata to tabbas zata iya zautar dashi lokaci ɗaya, yafice a hayyacinsa, domin shi shagwaɓan mace nasanyawa yaji feeling ajikinsa sosai,, cikin murya me sanyi yace “Kiyi haƙuri  ki ƙarɓa kinji princess ɗina, kinga ba kyu maida hanun kyauta baya!”

Sake turo baki tayi haɗe da kwaɓe fuska,    abun mamaki sai taga shima ya marairaice mata fuska kamar wani ƙaramin yaro,,  “Please!” yafaɗa cikin muryarsa da tayi ƙasa sosai..

Dole babu yanda ta’iya haka tasanya hanu takarɓi ledan haɗe dayi masa saida safe tafice daga cikin motar,,,  yanaganin shigewarta cikin gida yasaki murmushi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa,  key yayi mawa motar haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu.    Yana tuƙi amma shikaɗai yaketa zuba murmushi, aduk sanda yake tare da Zahrah yakansamun kansa cikin farinciki da nishaɗi, tabbas yanayimawa Zahrah so me tsanani…..

Zahrah kuwa tana shiga cikin gida direct wajen da Inna ke zaune tanufa,  ƙoƙarin zama tasomayi haɗi dayimawa Inna sannu da gida.

Washe da baki Inna ta amsa mata bayan ta kafe Zahrah da’ido, Allah Allah take taga menene acikin ledan da  Zahrah ta shigo dashi..

Dariyane ya ƙwace mawa Zahrah sakamakon ganin yanda Inna ta tsareta da’idanu tamkar wata mayya.

“Dariyan uban me kike? banson shashanci wallahi” Inna tafaɗi haka ga Zahrah a hasale, ganin bata da shirin buɗe ledan…

Hannayenta tasanya ta toshe bakinta haɗe dasoma ƙoƙarin shanye dariyar ta.

Ledan da tashigo dashi ta buɗe tasoma dubawa gasassun kajine manya guda biyu sai kuma sauran kayan ciye ciye kamar su snacks dakuma chocolate,,

Ledan da kajin ke ciki ta ciro ta miƙamawa Inna ae kuwa hanun Inna har rawa yake lokacin da tazo karɓan ledan tsabar kwaɗayi.

Fari’ar Inna ne yasake yawaita sakamakon ganin kaji da tayi, babu wani ɓata lokaci ta yago cinyar kaza ɗaya takai bakinta,, tsabar daɗin kazar saiga Inna tana lumshe idanu haɗi da jijjiga kai.

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da ɗaukan sauran kayan tawuce ɗakinta yayinda tabar Inna tayi pieces  tana cin kaza hadda rausayar da kai gefe alamar daɗinta takeji….

STORY CONTINUES BELOW

Jigum tayi haɗe da sake takurewa  waje ɗaya akan ƴar katifartata,,,  tabbas Dr.Sadeeq yacancanci ta sadaukar masa da duka soyayyarta ko dan saboda halaccin da yayi mata a rayuwa, bazatace batasan menene so ba, itacema zata ba da labari akan so, domin ta ɗanɗana zafinsa me matuƙar ɗaci da dafi,,   idan tace Dr.Sadeeq baya burgeta tayi ƙarya, haka kuma idan tace Dr.Sadeeq baida abubuwan burgewa ajikinsa da zasu sa mace tasosa nan ma tayi ƙarya? tabbas Dr.Sadeeq baida wani makusa daga halayya ɗabi’a harma da surarsa yacika cikakken namiji, amma babban abun dake damunta shine batajin tsananin soyayyarsa acikin zuciyarta, bawai tana ƙinsa bane, kawai de zafin soyayyar tasa ne bataji a jiki da zuciyarta, ba kamar yanda taji na Zaid ba,, ada batajin soyayyar Dr.Sadeeq acikin zuciyarta amma ayanzu tayi ƙoƙari wajen ganin takoyawa zuciyarta sonsa,  takuma yarda cewa zata iya zaman aure dashi domin baida wani makusa  atattare dashi wanda zaisa a ƙisa, murmushine yasuɓuce mata sakamakon tunowa da tayi da irin kallon dayakeyi mata ɗazu, tabbas ya iya nuna soyayyarsa a fili, abu ɗaya ne ajikinsa wanda yake ɗaukar hankalinta,  shine ƙwayar idanunsa, duk da cewa shi ɗin namiji ne amma yanada idanu masu kyau wanda zasu sanya maka nutsuwa aduk sanda ka kallesu, hakan yasa ako da yaushe takeson kallon cikin idanunsa amma bata iyawa saboda kunya….. Tunanin Zaid ne yakutso kansa cikin zuciyarta harsai da taji faɗuwar gaba,,    “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” shine abun da tashiga nanatawa acikin zuciyarta,, wannan wani irin bala’i ne? tunda Zaid yashigo cikin rayuwarta shikenan kuma komai nata ya ruguje, lallai itakam taɗaukeshi amatsayin annoba wanda gani da jinsa babu alkhairi …..1

Yau Kwanansa ɗaya da wuni ɗaya cur baisanya ko wani irin abinci abakinsa ba, sai ruwan giya dayake ta kwankwaɗa ba dare ba rana,, damuwa ce tayi masa mugun yawa abubuwa gaba ɗaya sun caɓemasa,    kallo ɗaya zakai masa kafuskanci cewa yanacikin halin damuwa, domin kuwa lokaci ɗaya ya zabge rama ta bayyana kanta ajikinsa, yayinda manya manyan idanunsa suka sake fitowa waje,,    wani irin zafi zuciyarsa keyi masa, baisan da yaushene kuma ta yaya yakamu da soyayyar Zahrah me tsanani haka ba,     tunjiya yarasa nutsuwarsa a sakamon labari dayaji daga bakin wanda yasanya  yana kulamasa da shiga da ficen   Zahrah,  inda yasanar masa cewa ankawowa Zahrah kayan lefe, iya ƙololuwar tashin hankali Zaid yashiga dajin wannan magana, sam be shirya wa rasa Zahrah ba saboda rasata dai dai yake da rasa rayuwarsa gaba ɗaya, akuma yanda yakejin matsanancin sonta a cikin zuciyarsa zai iya sadaukar da komai nasa gareta, ko da kuwa ransa ne…

Yanzuma zaune yake yatusa wani ƙaton hoton zanen fuskarta daya zana a daren jiya a gaba yana kallo, saboda tsabar kyawun da zanen yayi idan kagani bazamakace zane bane…

Idanunsa dake kan idanunta na cikin zanen ne suka kaɗa sukai jajur dasu.  Saiyanzu yakejin tsanar kansa dakuma tsanar wannan banzan halin nasa, sai yanzu yake tsananin danasanin abun daya aikatawa Zahrah, haƙiƙa yasan cewa ya zalunci Zahrah ya cutar da’ita ya lalata mata rayuwa, kuma hakan da yayi mata shiya nisan ta masa ita, wani irin tsana ne Zahrah tayi masa haka? shin tasan irin zafi dakuma raɗaɗin dayakeji akanta kuwa? yadaina cin abinci tasanadiyar ta, wannan yasa  ulcer tayi masa mummunan kamu, gakuma soyayyarta da ta sanya masa ciwo a zuciya,, ta wani ɓangare kuma yana fama da wani  matsanancin ciwon kai wanda dashi yake kwana yake kuma tashi, cikinsa kuwa tamkar anhura masa wuta haka yakeji aciki,, hanu yasanya yashafi zanen fuskartata, tabbas idan baisamu Zahrah ba bazai taɓa iya cigaba da rayuwa ba,,, abun da Zaid baisani ba shine tuni  ruwan hawaye sun cika idanunsa gangarowa kan fuskarsane kawai da basuyi ba,  zumbur haka yamiƙe tsaye haɗe da zura silifas ɗinsa ko wayoyinsa bai tsaya ɗauka ba, haka yafice daga cikin ɗakin nasa….

Yana fita compound ɗin gidan nasu driver’n sa yaƙaraso garesa da sauri,,,, “Oga fita zamuyi ne?” driver’n yatambaya cike da girmamawa,,  kai kawai Zaid ya ɗaga masa alamar “eh”    jikin driver’n na rawa yace “Oga da wacce motar zamu fita?”

Cike da ƙosawa Zaid yace “Kowacce”

Driver yayi mamaki sosai dajin maganar Zaid domin yasan idan dai har fita Zaid ɗin zaiyi to sai yazaɓi motar dayakeso amma kuma sai gashi yau yace kowacce..   Wata haɗaɗɗiyar baƙar benz driver’n yatuƙo daga cikin parking space zuwa inda Zaid ke tsaye ya harɗe hannayensa acikin  aljihun wandon track suit ɗin dake jikinsa..

Zaid nashiga cikin motar driver yabawa motar wuta yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan…..

Baffa ne zaune akan dakalin ƙofar gidan yana me latsa ƴar ƙaramar wayarsa, zaman da yayi Zahrah yake jira ta dawo daga aiken da yayi mata,, daf dashi motar tayi parking, hakan yasa Baffa  ya kafe motar da’ido don ganin wanene zai fito daga ciki…

A hankali Zaid yabuɗe murfin motar yafito, kallonsa Baffa yashigayi daga sama har ƙasa saboda sarai yagane shine  ɗan iskan me kuɗin da yamawa Zahrah fyaɗe,  saida Baffa yagama ƙaremasa kallo kafun yakawar da kansa gefe…

Da sallama Zaid yaƙarasa wajen Baffa,, ciki ciki Baffa ya amsa masa sallaman,    durƙusawa Zaid yayi haɗe dayin ƙasa da kansa cikin murya me sanyi yace “Kagafarceni Baffa, nasan ban kyautaba amma dan Allah kada ka hanani auren Zahrah, wallahi a yanda nakeji idan bansamu Zahrah ba mutuwa zanyi!”

Baki Baffa yasake yana kallon Zaid,  namiji har namiji amma wai yana cewa idan bai auri Zahrah ba mutuwa zaiyi kuji iskanci fa,,

Sake ɗago kansa Zaid yayi haɗe da watsawa Baffa jajayen idanunsa,   “Wlh Baffa yanzu da gaske nake aurenta zanyi, kada kace zaka hanani ita dan Allah, wallahi Zahrah tana da matuƙar mahimmanci acikin rayuwata!”

Yanzukam kallon tsab Baffa yashiga yi masa saida yaɗauki kusan minti biyu yana kallon Zaid ɗin kafun yaɗan nisa haɗe da cewa “Bantaɓa tunanin kana da idanun da zaka dawo ka kallemuba, amma sai gashi kadawo kana kallona har kuma kana roƙona dana baka auren Zahrah, idan da kanasonta tunfarko mai yasa baka aureta ba kalalata mata rayuwa? ni bazance maka komai ba saide ince munbarka da Allah saboda bamu da yanda zamuyi dakai, amma kuma kasani bazan baka auren Zahrah ba harsai da amincewarta, idan har tace ta amince zata aureka shikenan nime iya baka aurenta ne” Baffa yana kaiwa nan a zancensa yatashi yayi shigewarsa cikin gida.. Da ƙyar Zaid ya’iya tashi ya  zauna akan dakalin da Baffa yatashi hannayensa duka biyu yasanya ya dafe kansa dake yi masa nauyi kamar ze faɗo ƙasa…..

Da ɗan sauri take tafiya tana latsa wayanta burinta kawai shine taganta acikin gida, duk sanyin da akeyi yau yagama ratsata, saboda haka take Allah Allah ta’isa gida.. sam bata lura da akwai mutum a ƙofar gidan nasu ba dan hankalinta gaba ɗaya nakan wayartata…

“Zahrah!” taji anƙira sunanta da murya wacce bazata taɓa mantawa da’ita ba a iya tsawon rayuwarta…

Ja tayi  ta tsaya haɗe da maida kallonta inda taji sautin muryar tafito,, tabbas kuwa  ba gizo kunenta keyi mata ba shiɗinne dai, kallonta yashigayi da idanunsa wanda suka zama jajaye, itama tsayawa tayi tana kallonsa, a wannan karon kam babu alamar wasa kokuma tsoronsa akan fuskarta,, kallonsa takeyi ido cikin ido…

“Dan Allah Zahrah ki saurareni, wallahi inasonki inamiki so me tsanani, inamiki soyayyar da babu wani wanda zaiyi miki shi a duniyar nan, meyasa bazakisoni ba Zahrah? Inasonki, Inasonki, Inasonki da duka zuciyata, dan Allah kiyarda muyi aure Zahrah!” cikin rauni yaƙare maganartasa saikace ba jarumin namiji ba…

Kallonsa Zahrah tashigayi tundaga ƙasan sa harzuwa samansa, wani irin murmushi tayi masa wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa,,,      “Bantaɓa tunanin zaka iyayin wannan jarumtar ba,  ƙwarai kayi ƙoƙari dahar ka iya tunkarana da wannan maganar, sai de kuma tun awancan lokacin na faɗamaka kafita a rayuwata, idan duka mazan duniya zasu ƙare na gwammace na mutu babu aure dana aureka,  ka kalleni da kyau bancancanci zama matar mazinaci kuma ɗangiya ba,  niba irin matan nan bane da yacancan ci fasiƙai irinka su samuba,  natsaneka Zaid tsana me tsanani, wlhy danaga ranar da zan zamo matarka gwamma acemin naga ranar mutuwa ta,  katafi kawai Zaid kaje nabarka da Allah, kuma inaso kasani cewa yau ɗin nan za’a tsaidamin ranar aurena da wanda zuciyata ta aminta dashi, wanda yake kamili me tsoron Allah,  shi ba kamar kai bane ɗan giya!” tanakaiwa nan azancenta tajuya daniyar shigewa cikin gida…

Dasauri Zaid ya kamo hanunta haɗe da jawota  da ƙarfi tafaɗa cikin jikinsa, dai dau lokacin ne kuma motar Dr.Sadeeq taƙaraso wajen….Saurin turesa tayi haɗe da hankaɗasa gefe da iya ƙarfinta ta ƙwace jikinta daga nasa, wani irin mugun kallo tashiga yimasa haɗe da tofar da yawu aƙasa, da ace wulaƙanta ɗan adam abune me kyau to tabbas da akan fuskarsa zata tofa wan nan yawun ko hakan zai sanya ya gamsu da irin tsantsar tsanar da takeyi masa.

“Banafatan na sake haɗa jikina da wan nan ƙazamemmen jikin naka mai ɗauke da tarin najasa!” cike da tsananin ƙyamata Zahrah ta faɗi haka ga Zaid haɗe da juyawa tanufi hanyar shiga gida..+

“Koda kuwa na daina aikata zina nakuma daina shan giya?” Zaid yafaɗi haka cikin dakakkiyar muryarsa…

Cak ta tsayawa daga tafiyan dakeyi, sosai maganar tasa ta daki zuciyarta..

A hankali yashiga takowa zuwa inda take saida yazo gaf da’ita kafun ya tsaya……. ” I promise to leave all my bad habit if you wish to marry me, I love you Zahrah, trust me for the sake of God, i will not hurt you!” gaba ɗaya muryarsa tayi rauni dagajin muryartasa kasan cewa yana cikin matsanancin damuwa…1

Idanunta da suka kawo ruwa ta ɗago ta watsa masa su,,,,, Shi ɗin ma kallon ta yakeyi da idanunsa wanda suka zama tamkar an watsa musu garin barkono,, sun ɗauki tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafun da ga bisani Zahrah tajuya ta shige cikin gida, ko sake waiwayosa batayi ba yayinda yashiga ƙiran sunanta amma bata amsa masa ba harta shige cikin gida, because tagaji da wannan ɗan iskan yaudaran nasa, yanzukam bazata iya ɗauka ba….

Iskan dake cikin bakinsa ya fesar haɗe da meda duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin sanyin jiki haka yakoma cikin motarsa driver yayimawa motar key suka ɗauki hanyar fita unguwar batare da sun kula da Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa ba…

Haƙoransa ya sanya ya danne laɓɓansa na ƙasa komai daya faru akan idanunsa ya wakana sai de baijiyo magan ganun da suka shiga tsakaninsu ba,, wani irin ɗaci yaji maƙoshinsa nayi, iya matuƙa ɓacin rai yashigesa, bakomaine yafi komai ƙona masa ransa ba kamar yanda yaga Zaid yajawo Zahrah jikinsa, hakanan yaji wani irin mugun kishi ya turnuƙe masa zuciya,, babban abun dayafi ɗaga masa hankali shine yanayin daya hango fuskar Zahrah, tabbas yafuskanci wani ɓoyayyen abu daga gareta,,, key yayi mawa motarsa cikin ƙunan rai yayi reverse haɗe da barin ƙofar gidan nasu batare da ya aika ayi masa ƙiranta ba..

Zahrah na shiga cikin ɗakinta ta durƙusa a ƙasa haɗe da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya kaicon zuciyarta da ta so mata namiji irin Zaid, ashe da gaske shiɗin mazinaci ne tunda gashi da bakinsa yafaɗa, kuka tashiga yi tamkar wacce aka sanarmawa da ranar mutuwarta, yayinda wani abu yataso ya tokare mata ƙirji wanda batasan komenene shi ba kamar yanda batasan kukan me takeyi ba…

Driver yana parking motar Zaid yace yafita ya bashi waje, aikuwa babu musu driver’n yafita daga cikin motar….. Kansa ya kafa ajikin kujera haɗe da fidda wani irin zazzafan numfashi ta bakinsa, zuwa yanzu kam bazai iya jurewa ba, sam bazai iya jure raɗaɗi dakuma azaban soyayyar Zahrah dake damunsa ba, tabbas da ace zai iya to da yayi iya ka ƙoƙarinsa wajen ganin ya yakice soyayyarta acikin zuciyarsa amma hakan bazai yiwuba domin kuwa duk kowani kwanan duniya soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarsa, zuwa yanzu soyayyar Zahrah babu inda bata ratsa acikin jikinsa ba,,,, a ƙalla yakai kusan 30 minute acikin motar yana saƙawa da kuncewa, da ƙyar ya’iya fitowa daga cikin motar kai tsaye yanufi babban parlour’nsa dake cikin guest house ɗin nasa, domin kuwa daga gidan su Zahrah guest house ɗinsa suka yiyo….

STORY CONTINUES BELOW

Yana shiga cikin falon ya faɗa kan doguwar kujera haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, kansa ne ke saramasa yayinda juwa ke ɗibansa, lallai yazame masa dole yasamawa kansa mafita, yazama dole yafarka daga wannan mafarkin daya keyi tabbas al’amuransa a yanzu suna masa kama da al’amara,, tabbas yana buƙatar samun relief daga damuwar dayake ciki, amma sai dai babu amfanin shangiya a yanzu domin kuwa koda yashama bata basa wani relief ɗin da ya kamata, miƙewa yayi yashiga cikin ɗakinsa, kai tsaye wani ɗan drower yanufa haɗe da buɗewa, hanu yasanya ya ɗauko wata wayarsa ƙirar techno phantom 9 wanda dama yana ajewane saboda rana irin haka, kasancewar baifito da wayoyinsa ba duk yabarsu a gida,, yana kunna wayar ya laluɓo wata lamba haɗe da turawa lambar text message, yana ganin alamar saƙon ya isa inda yakeson yaje yayi switch off ɗin wayar haɗe da maidata inda ya ɗaukota kwanciya yayi akan makeken gadonsa wanda yasha shumfuɗa ta alfarma, cusa kansa yayi cikin pillow haɗe da soma fitar da numfarfashi akai akai….

A hankali taturo ƙofar ɗakin wanda kafun ma tashigo tuni ƙamshinta yarigata shigowa, sanye take da jan wando pencil wanda yayi matuƙar bayyana kyakkyawar surar jikinta yayinda rigarta yakasance baƙa me kyau, rigan irin masu faɗin wuyan nan ne hakan ne yasanya manya manyan breast ɗinta bayyana kansu tasaman rigar,, takalmine me uban tsini a ƙafarta yayinda ta tufke dogon gashin kanta da jan ribbon kalan wandonta,, kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa wayayyar macece ƴar duma, shigarta kaɗai ya isa yabayyana maka ainihin ko wacece ita, saboda bashigane da mata masu mutumci sukeyi su fita ba kamar yanda ita tayi, domin kuwa ko ɗan kwali babu akanta, wani irin murmushine kwance akan fuskarta dake nuna alamar cewa tana cikin farinciki,, lumshe idanunta tayi haɗe da buɗesu alokaci guda, kallon surarsa kaɗai ya isa sanya mata nutsuwa, tajima tana tsumayi da kuma fatan Allah ya sake ɗaurata akansa, harta cire rai saikuma gashi yau shi da kansa ya gayyatota, lallai zata iya cewa a rana irin ta yau tafi kowa sa’a..

Duk da yaji ƙamshin turarenta acikin hancinsa hakan baisanya yaɗago kansa ba,,

Cikin taku irin na matan da suka goge wajen iya ɗaukar hankalin ɗa namiji tashiga takowa har zuwa inda yake kwance ya yinda juyawa ƙofa baya…

Hanunta tasanya a bayan wuyansa haɗe da soma shafawa a hankali,, cikin wata murya me sanyi dajan hankali tace “Man!”

Shiru yayi bai amsa mata ba, duk da kuwa cewa yanajinta,,, ganin bai amsa taba yasanya tayi murmushi haɗe da cire takalman dake ƙafarta ta hawo kan gadon,, bakinta ta sanya adai dai saitin tsakiyar bayansa tashiga tsotsa haɗe da shafa bayan wuyansa a hankali,,,, wani irin zubawa Zaid yaji tsikar jikinsa tayi, adai dai sanda take ƙoƙarin nuna masa wani sabon salo…. “Meenal!” yaƙira sunanta da wata irin murya wacce ta riga da ta cushe..

Murmushi Meenal tayi haɗe da mirginowa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, lumshe idanunta tayi alokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa, wallahi tana matuƙar son Zaid komai nasa me kyaune daga ciki har waje, ba abunda yake ɗaukar hankalinta akan fuskarsa kamar wannan kyakkyawan sajen nasa dayake shan gyara da mayuka masu kyaun gaske..

“Nayi kewarka Man, ashe de kaima kayi kewata? katafi ka barni da tunanin daɗin da kajiyar dani, wanda har rana me kamar ta yau babu wani ɗa namiji da yajiyar dani kwatan kwacin wannan” Meenal taƙare maganar cikin yanayi na shagwaɓa haɗe da sake matsowa tashige cikin jikinsa,, ɗan guntun murmushi yasakar mata haɗe da soma ƙarewa fuskarta kallo, Meenal kyakkyawar yarinyace wanda kyawun nata kuma yazama na ɗan maciji, domin kuwa Meenal tantiriyar ƴar iska ce kuma cikakkiyar mazinaciya wanda idan ta kafamawa namiji ƙahon zuƙa duk nuƙu nuƙunsa sai ta jefasa cikin raminta, sai dai idan kuma shiɗin ya kasance gwaska na gasken gasken, tofa nan ne zasu dai dai ta, kamar dai Zaid da ta buga ta rawa yaƙi faɗowa raminta, domin kuwa shi ɗin ma ɗan iskane me lasisi san nan kuma gwaska ne me zaman kansa, wannan yasa Meenal takasa turasa a cikin raminta..

Hanu Meenal tasanya akan faffaɗan ƙirjinsa tashiga shafawa haɗe da cusa kanta acikin wuyansa cike da ƙwarewa take manna masa kiss,, tamkar wata mayya haka take sake shigewa cikin jikinsa..

STORY CONTINUES BELOW

Lumshe idanunsa yayi haɗe da cusa hanunsa cikin sumar kanta,, take yasoma sauƙe ajiyar zuciya akai akai domin kuwa gani yake tamkar Zahrah ce kwance haka a jikinsa,, idanu Meenal ta kafesa dashi cike da mamakin irin sauyawan da yayi, nafarko ta hango tarin damuwa acikin idanunsa yayinda na biyu kuma ta hango wani abu mai ɗaure kai acikin idanunsa,,, “Man!” taƙira sunansa cikin wata irin murya, idanunsa kawai ya jefa acikin nata idanun batare da yace da’ita komai ba,, dama haka takeso burinta shine yaɗaga kyawawan idanunsa ya kalleta,, take ta sauya salon nata kallon ta marairaice idanunta,, fuskarta ta matso daf da tashi fuskar lokaci ɗaya tasoma ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya, kamar koda yaushe ƙin aminta da hakan yayi da sauri ya kawar da kansa gefe, saboda hakan baya daga cikin tsarinsa haɗa miyau da matan bariki, domin babu abu mafi saurin sanya shaƙuwa kamar haɗakar yawun baki, sosai kiss yake sanya shaƙuwa a tsakanin masu yinsa, domin haɗuwar yawun bakuna biyu wani sinadari ne na musamman,,,, bata damu ba domin dama tasansa bayawa mace kiss batakuma san dalilinsa na hakan ba, wan nan kuma ita duk ba damuwarta bane matuƙar zai kusanceta to zatafi kowa farinciki,,,,, hanunta ta sanya akan mararsa tashiga shafawa a hankali haɗe da ɗaura bakinta akan nipples ɗinsa, jawota yasakeyi jikinsa bayan ya cire mata ƴar ƙaramar rigar jikinta, kansa ya cusa acikin ƙirjinta yana me shaƙar ƙamshin turarenta, haɗe da sanya hannayensa a bayanta yasoma shafawa a hankali,, take Meenal tasoma sauƙe numfashi akai akai dama ƙiris take jira saboda akunne take ƙwarai… Lokaci ɗaya Meenal tarikice wasu irin salo take gwadawa Zaid masu sanya mutum ya fita a hayyacinsa, yayinda shima yagama ruɗata da nasa salon har saida yakusa sanyata shiɗewa,, amma kuma wani abun mamakin shine yanayin hakan ne cikin wani irin yanayi wanda baisan dame zai ƙira sunan yanayin ba, kwata kwata baijin wani abu mai suna sha’awa a jikinsa duk dakuwa irin romancing ɗinsa da Meenal keyi, lumshe idanunsa yayi haɗe da jawota yadawo da ita ƙasansa aniyarsa shine ya kusanceta amma kuma sai yaji zuciyarsa tashiga bugawa da sauri sauri yayinda Zahrah tashigo cikin ransa ta tsaya cak, take idanunsa suka haskomasa irin kallon tsanan da tayi masa ɗazu, nan danan yaji komai yafice masa arai, da sauri ya ture Meenal gefe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa da yayi masa nauyi, da wani irin kallo Meenal da takai ƙololuwa wajen sha’awa ta bisa, meye haka yakeyi? badai halin nasa na wulaƙanci zai gwada mata ba? idan kuwa hakane Zaid yacuceta, saida yagama jefata acikin masifaffiyar sha’awarsa san nan yajuya mata baya, hanu tasanya ta rungumosa ta baya haɗe da soma goga masa breast ɗinta akan bayansa “Meke damunka Man? kada kabari damuwa ya hanaka jin daɗin rayuwa please” tafaɗi haka cikin narkakkiyar murya, hanunsa yasanya ya zameta daga jikinsa wani irin haushinta ma yake ji, miƙewa yayi direct ya wuce toilet ɗinsa ko waiwayota baiyi ba, baki sake haka Meenal tabisa da kallo harya shige cikin toilet ɗin,, kuka ta fashe dashi haɗe da matse cinyoyinta, tsakani da Allah take kuka domin kuwa iyaka cuta a wajenta shine abun da Zaid yayi mata…

Zaid kuwa yanashiga bathroom ya zame wandon dake jikinsa haɗe da nufar inda babban bathtub ɗin wankansa yake, ruwa ne me kyau da tsabta acikin bathtub ɗin, amma duk da haka saida ya zubar yakuma taran wani ruwan, turaren wankansa me daɗin ƙamshi ya sanya a cikin ruwan haɗe da shiga cikin ruwan ya kwanta a hankali,, lumshe idanunsa yayi haɗi da jingina kansa, zafi yakeji adai dai saitin zuciyarsa, tabbas yanaji ajikinsa cewa akwai abun da zai faru dashi bayan wanda yake faruwa dashi yanzu, “wace irin soyayya ce haka yake yiwa Zahrah me zafi?” tambayar da kullum sai yayimawa kansa kenan, lallai yau yasake tabbatar mawa kansa cewa yazama mutum me rauni, A she dama akwai wata rana da zai iya kasancewa haka? yaƙira Meenal ne don taɗebemasa kewa yakuma samu ya rage tarin sha’awar dake damunsa, domin kuwa har wani ciwo yakeji mararsa nayi masa, amma kuma sai gashi ya kasayin komai da Meenal, ashe ba Meenal ɗin bace muradinsa Zahrah ce, haƙiƙa yasake yardarwa kansa cewa abunda kake so shi yake wahalceka sannan kuma yasake tabbatar mawa kansa cewa ƘAUNA guda ɗayane tal aduniya, SO ne kawai yake da yawa, amma ƙauna ƙaunace,, kafun yaƙira Meenal yayi tunanin cewa idan tazo zata gusar masa da damuwarsa, sai kuma bayan tazo yaga ashe bazata iya ba, ashe yin sex da shan giya basune maganin damuwarsa ba, Zahrah har lau itace maganin damuwar sa,, anya kuwa zai warke daga damuwar nan tasa?

STORY CONTINUES BELOW

Yajima acikin bathroom kafun yayi wanka yafito jikinsa sanye da farar rigar wanka,, kallonsa ya maida kan gado inda yabar Meenal don ganin wani hali ta ke ciki domin kuwa sarai yaji kukanta lokacin dayake cikin bathroom,, dariyane taso ƙwacemai sakamakon ganin Meenal da yayi takure a can ƙarshen gado tana bacci, yayinda ta cusa hanunta na hagu a ƙasanta, sarai yasan Meenal jarabebbiya ce yanzu haka fingering tayi don samawa kanta relief, abun da yafi tsana kenan wato mutum yayi amfani da kansa don biyan buƙatarsa, amma kuma wannan halin Meenal ne,, kai kawai ya girgiza haɗe da nufan gaban dressing mirror ɗinsa, vaseline yashafa ajikinsa kasancewar garin ana ɗan yanayi na sanyi, saida ya feshe jikinsa da body spray kafun yasanya kayansa riga da wando na jeans masu kauri, sosai kayan sukai masa kyau, kuɗaɗe yaciro a cikin drower ɗinsa ya ajiye a kusa da Meenal daketa sharan bacci, kana yayi ficewarsa daga ɗakin, direct bai zarce ko inaba sai compound ɗin gidan, yanzu kam shida kansa yakeson yayi tuƙi, don hakane ma yazaɓi BMW blue colour amatsayin wacce zai fita da ita….

Dr.Sadeeq

Duk yanda Dr.Sadeeq yaso samawa kansa nutsuwa hakan yagagara domin kuwa sam zuciyarsa bata amince da zuwa wajen Zahrah da Zaid keyi ba, duk da yau yafara ganinsa aƙofar gidan su Zahrah’n amma jikinsa ya basa cewa ba yaune zuwansa na farko ba, amma bakomai zaiyi maganin abunne zai nisanta Zahrah da Zaid nisantawa me tsanani kuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa…

Washe Gari.

Dasassafe Zahrah ta shirya tayi tafiyarta makaranta sai dai a ranta tana mamakin rashin ƙiranta da Dr.Sadeeq yayi, rabonta dashi tunjiya da yamma sunkuma rabu dashi akan cewa zai ƙirata sai gashi kuma har zuwa yanzu bai ƙirata ba, uzuri tayi masa akan cewa ko aikine yayi masa yawa domin tasan hakanan Dr.Sadeeq bazaiƙi ƙiranta ba…

Tana tafiya ba jimawa motar Dr.Sadeeq ta tsaya a ƙofar gidan nasu, fitowa yayi daga cikin motar yasha adonsa cikin blue ɗin shadda sosai kuma yayi kyau,, yaro ya aika cikin gidan yace yace ana sallama,, bajimawa yaron daya aika yadawo ya shaida masa ance me gidan yana fitowa…. Washe da baki Baffa yaƙaraso wajen Dr.Sadeeq dake tsaye ” Maraba da Likita, dama kaine ai da kashigo ciki amma ka tsaya a waje sai kace wani baƙo”

Murmushi Dr.Sadeeq yayi cike da girmamawa ya sunne kansa ƙasa haɗe da durƙusawa ya gaishe da Baffa,, fuska cike da fari’a Baffa ya amsa gaisuwan,,,

“Aikuwa kayi rashin sa’a domin kuwa mutumiyar taka bata jima da fita a gidan ba, tatafi makaranta ko karyawa bata tsaya tayi ba, amma ina ga zaifi kyau mushiga daga ciki ko”

“A’a Baffa nan ɗin ma yayi, dama wajenka nazo ae”

“To to masha Allah, saimu zauna ae ko abisa dakalin nan” Baffa yaƙare maganar yana meyi mawa Dr.Sadeeq nuni da dakalin ƙofar gidan.

Duk yanda Baffa yaso Dr.Sadeeq ya hau kan dakalin su zauna ƙiyawa yayi, domin kuwa Baffa surikinsa ne baidace ace sun zauna gaf da juna ba kodan saboda kara da matuntawa,,

“Shikenan to tunda dae kaƙi zama, inajinka Allah yasa dai lafiya?”

Kansa yaɗan sosa haɗe da sakin murmushi “Lafiya ƙalau Baffa dama akan maganan aure nane da Zahrah…” sai kuma yayi shiru ya kasa ƙarasa maganar dake cikin bakinsa, gani yake tamkar idan yafaɗi maganar kai tsaye Baffa zaice masa yayi gaggawa ko kuma yace yayi rashin kunya…

“Ka kwantar da hankalinka Likita kafaɗi duk wani abu dake ranka” Baffa yafaɗi haka ga doctor ɗin..

“Am dama…dama inaso ne kabani izini nasake turo magabatana dan sukawo sadaki san nan kuma a tsaida ranar aure”

“Alhmdlh to ai wannan abun farinciki ne Likita, wannan ae bawani abun damuwa bane, nabaka dama ka turosu aduk sanda kakeso, sai de kuma zakaɗanyi haƙuri, saboda zansa lokacin da ɗan tsayi saboda kasan ba a yin aure kai tsaye haka dole sai anɗanyi mawa yarinya sayayya, ina fata hakan bazai sosa ranka ba?”

Murmushin jin daɗi Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa “Naji daɗi sosai Baffa, amma kuma maganar sayayya basai kun wahalar da kanku ba, domin zuwa yanzu gidan da zamu zauna baya buƙatan komai, saboda haka don Allah kada kusa kanku a wahala”

Murmushi Baffa yayi haɗe da cewa “Ƙwarai mungode da wannan ƙoƙarin naka, amma sai de nace kayi haƙuri, duk da cewa mahaifin Zahrah baya raye ni ƙaninsa ina raye kuma niɗin ma ubane a wajenta, zan yi amfani da ɗan abun da nake dasu wajen ganin namata kayan ɗaki iya dede ƙarfina, kamarde yanda kowani uba keyiwa ƴarsa, wannan shine kaɗai gatan da zamu iyayi mata a yanzu” Baffa yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..

Ajiyar Zuciya Dr.Sadeeq ya sauƙe, haƙiƙa shi Zahrah kawai yakeso bawai wani abu na daban ba, kuma shi baiso akawota da komai, domin musamman ya ware mata ɓangarenta, kuma tuni yabawa wani abokinsa me saida furnitures a Dubai order akan akawomasa setin kujeru dakuma gado harma da duk wani abu wanda yasan zai ƙawata ɗaki,, amma tunda yaga Baffa yadage akan cewa shima zaiyi iya nasa ƙoƙarin shikenan zai ware wani ɗaki na da ban idan yaso sai a sanya kayan da Baffan yayi mata acan,,, cike da mutuntawa Baffa da Dr.Sadeeq sukayi sallama….

Baffa na shiga gida ya kalli Inna dake zaune,, “Salame inajin fa tafiyana yola yagabato idan banje jibi ba to zanje gata insha Allah”

Fuska ɗauke da mamaki Inna ke kallonsa, “Yola kuma Malam?”

“Ƙwarai kuwa, kinga fitana ɗin nan to yaron nan ne Sadeeq yazo min da maganar cewa inbasa dama yaturo magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuɗin nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan ɗaki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa ƴarsu dan baiyiwuwa ace mu miƙata haka”

Ajiyar zuciya Inna tasauƙe haɗe da gyara zama ” Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma”

Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da’ake biya mata ba, don haka baiƙara cewa da’ita komai ba yawuce ɗakinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da’ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baƙin ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiƙara jari da kuɗin, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan ɗaki,, haka taita ƙananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata……

Da yamma Dr.Sadeeq yaƙira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq ɗin amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,

Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar ɗin tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa’n da dare a ƙarɓi baƙin dashi……

Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaƙiƙin amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haɗe dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miƙa sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu ɗari (100,000) bawani ɓata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata ɗaya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna……

.Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!” Inna tafaɗi haka aƙufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin ɗakin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuƙar ɓace yake da’ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi… Tattara books ɗin dake gabanta tayi haɗe da miƙewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin ɗakin…..+

Da sallama ɗauke a bakinta takutsa kanta cikin ɗakin Baffan nata,, zama tayi akan tabarman dake shimfuɗe a tsakiyan ɗaki, haɗe dayi mawa Baffa barka da gida,, fuska ɗauke da fari’a Baffa ya amsa mata..

Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa “Bakomai yasa nayi ƙirankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danƙamiki haƙƙin ki a hanunki, yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki, nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danƙamin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu ɗari ne cus nakine halak malak” Baffa yaƙare maganar yana me miƙa ma Zahrah maƙudan kuɗin dake hanunsa….

Gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi laƙwas gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.

“Ki karɓa mana Zahrah” Baffa yafaɗi haka ganin da yayi ko ɗago kanta takasa yi.

Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi tace “Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riƙe a wajenka, saboda ko kabani babu abun da zanyi dasu!” taƙare maganar cikin ladabi.

“A’a Zahrah ki karɓi abunki haƙƙin kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karɓi abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba” maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.

Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karɓi sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karɓa..

“Yauwa kinga idan kika riƙe abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata ɗaya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya ƙoƙarin da zamuyi wajen sayan ƴan kayayyakin ɗaki”

Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki, haka nan taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi ɗakinta…

Zama tayi akan katifarta haɗe da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,, shikenan yanzu saura mata wata ɗaya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faɗan wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,, idanunta ta buɗe haɗe da maida kallonta ga kuɗaɗen dake riƙe a hanunta,, tsurawa kuɗin idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuɗin,, hawayene suka kuma ɓalle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani ƙwarai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk ɗaya suke, amma kuma shine ya cire maƙudan kuɗaɗensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu ƙara farashinta babu kaso tara, saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,, hanu tasanya ta share hawayenta, haƙiƙa bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta, amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taƙi aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa…. Cikin wata jakarta tasanya kuɗin sadakin nata, haɗe da dawowa ta kwanta akan katifarta, bazama ta iya ƙarisa assigment ɗin nata ba domin kuwa gaba ɗaya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da’ita,, da ƙyar ta iya jawo wayarta taƙira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daɗine ya kama Husnah sosai take ta hau farinciki haɗe da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata ɗaya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya…

STORY CONTINUES BELOW

*****

“Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuƙar bai fasa auren da zaiyi da waccar ƴar ƙasƙantattun mutanen ba, ni bazan iya haɗa iri da jinsin matsiyata ba!” Abunda Hajiya Habiba take faɗa kenan cikin ɓacin rai.

Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caɓa caɓa da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa ” Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taɓa iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naƙori ita yarinyar”

Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baƙin ciki taja tsuka haɗe da watsawa Saleema’n harara “Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buƙata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni” fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu….

****

Baffa na zaune a wajen sana’arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi.. Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma’aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba..

Bayan sun gaisane Alhaji Ma’aruf ya nisa haɗe da cewa “Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba”

Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe haɗe da tattaro duka nutsuwarsa yadubi Alhaji Ma’aruf…

“Bazan taɓa ɓoyemaka ba Alhaji, kamardai yanda nafaɗa maka afarko yanzu ma hakane, domin maganan da nakeyi maka yanzu ma jiya aka kawo sadakin yarinyar, saboda haka sedai nace kawai kuyi haƙuri”

Kai Alhaji Ma’aruf yashiga jinjinawa, zuwa yanzu dolensa zaibawa Zaid haƙuri akan cewa yayi haƙuri yacire yarinyar aransa, domin kuwa idan ba wani ikon Allah ba to babu alamun cewa Zaid zaisamu auren yarinyarnan Zahrah..

Haka Baffa da Alhaji Ma’aruf suka rabu, bayan Alhajin yayi mawa Baffa alkhairi maiyawa, amma sam wannan karon Baffa yaƙi karɓa yace bai buƙata, duk yanda Alhaji Ma’aruf yaso Baffa ya amshi kuɗin hakan bai samu ba,, haka Alhaji Ma’aruf yayimawa Baffa sallama shida tawagar body guard ɗinsa suka bar wajen, sam Alhaji Ma’aruf baiji daɗin hakan ba, yaso ace ɗansa yasamu abunda yakeso…..

Cike da tsananin damuwa Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid dake zaune a ƙasa yayi shiru, gaba ɗaya ya sanja, komai nasa yazama sanyi sanyi, ga alamomin damuwa da suka bayyana kansu a jikinsa, baisan wani irin masifaffen soyayya ɗannasa ya kamu dashi ba, baimasan taya ya Zaid zai ɗauki maganar da zai faɗa masa ba, amma dai yazama dole yafaɗa masa gaskiya amatsayinsa na mahaifinsa.

“Zaid!”

Alhaji Ma’aruf yaƙira sunan Zaid murya a tausashe.

“Na’am Dad” Zaid ya amsa murya ƙasa ƙasa.

“Inaso kabani hankali da nutsuwarka, dan Allah Zaid ka kwantar da hankalinka, nasani kuma kaima kasani nema cikin nema haramunne, kacire wannan yarinya acikin zuciyarka domin kuwa yau naje nasamu shi Baffan nata, yakuma shaidamin cewa a halin yanzu har ya karɓi sadakinta, saboda haka zaifi kyau kacireta a zuciyarka, kanemi wata nasan babu wata mace da zata ƙika”

Tamkar wanda Dad ɗin ya watsa masa ruwan zafi haka yaji sauƙar maganganun mahaifinsa acikin kunnuwansa, da sauri yaɗago jajayen idanunsa ya watsawa mahaifin nasa su,, bakinsa na rawa yace “Ankarɓi sadakinta kuma Dad?”

“ƙwarai kuwa Zaid abunda Baffan nata yafaɗamin kenan, shiyasa nace ka cireta a ranka”

Kai Zaid yashiga girgizawa,,,,, “Bazai taɓa yiwuwaba Dad, wlhy wani bazai taɓa auran Zahrah ba matuƙar ina numfashi acikin duniyar nan, inasonta fa Dad meyasa bazaku gane hakan ba? bazan iya cigaba da rayuwaba idan har babu Zahrah a gareni, nasan laifinane Dad, amma duk da haka bai dace a hanani Zahrah ba, saboda inasonta inamata wani irin so me tsanani please Dad niko yanzu dan Allah a ɗaura mana aure idan yaso daga baya ni na amince zan shawo kanta, nasanma tana sona har yanzu, kuma nasan daga baya zata yafemin abunda nayi mata!”

Cike da tsananin mamaki Dad ke kallon Zaid wanda gaba ɗaya ya ruɗe alokaci ɗaya, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikinsa ba ? Dad yatambayi kansa cike da tsananin mamaki, domin kuwa sam Zaid ba haka yake ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu amma kuma wani babban abun mamaki shine yauga Zaid nan yana faɗin wai bazai iya rayuwa ba idan babu wata,,

“Zaid!” Dad yakuma ƙiran sunansa cike da tausayawa domin shikam baitaɓa ganin soyayya irin wannan ba…

Zaid bai iya amsawa mahaifinnasa ba, saide idanunsa daya ɗago ya kalli Dad ɗinnasa dasu.

“Zaid ka kwantar da hankalinka, ba ita kaɗai bace mace a duniyar nan akwai mata da yawa, kana da ƴancin da zaka zaɓi duk irin macen da kake so” Dad yafaɗi haka ga Zaid cikin lallami…

“Idan ni inada ƴanci ita kuma dana cuta fa? nacutar da ita Dad cuta mafi muni, na zalunceta, banda wata hanya dazanbi na goge laifina a wajenta, sai ta hanayar aurenta, dan Allah Dad kayi wani abu, bazan iya jure rashin Zahrah ba!” yanzu kam har ƙwalla suncika idanun Zaid batare daya sani ba. (hmm so mugun wasa)

Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sa kai yafice daga cikin falon Dad ɗin nasa, da kallo kawai Dad yabisa dashi harya fice, baisan me yake shirin faruwa da ɗan nasa ba amma ae so ba hauka bane…..1

Zaid yana fita daga ɓangaren Mahaifinsa direct part ɗinsa yanufa, idanunsa gaba ɗaya sun rufe yayinda kansa ke matuƙar sara masa, sam bazai iyaba, bazaitaɓa iya jure rashin Zahrah ba, lallai yazama dole yakuma yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa,, tabbas yazama dole ya kusanto Zahrah zuwa garesa koda kuwa hakan zai jawo faruwar abubuwa masu tarin yawa…key ɗin motarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe babu wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah…..

Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaɗan yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta ƙaita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba Zaid yayi yo kansa….

Tuƙi yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riƙe a ɗayan hanunsa yana sha, jinkansa yake gaba ɗaya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi, idanuwansa Zahrah kawai suke hango masa, batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta ɗagu sama haɗe da faɗowa ƙasa sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *