TAWA TA SAMENI CHAPTER 13 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
nace Assalamu alaikum sai naji ance Wa’alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini? nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok! nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna Ify?nace Ify lau yace to kice da Maman Sagir ina gaisheta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin sona. Www.bankinhausanovels.com.ng Lokacin da zai tfy nan ko ince da zaya koma ina cikin
wannan tunani sai naji yace kin gama?dama na gama sai nace e yace to gashi na isa na dan rage tsawo yace wannan ya turo mani akwati naki ne sannan daya kuma zaki kaima Mimi nata nace to nagode Allah ya kara daukaka duk da bai amsa ba nasan yaji dadin
ZAMU TASHI
adduar,na dau akwatin nayi cikin gida Allah yasa ba kowa a tsakar gidan ni da mama muka bude muna ganin kaya nayi mamakin kayan domin suna da yawa bayan haka kuma zasuyi tsada english ne kala bakwai sai jakunkuna da takalma sai rigunan barci masu kyau sai wani zobe cikin akwatinsa mai kyallin gaske,na dauka ina dubawa zobe ne na Zinari mai nauyi akwai stone mai kalar ruwa gargar tamkar kankara in ka kura ma stone din ido zaka ga an rubuta A guda biyu daya kan daya nace la mama duba ki gani harda farkon
sunana tace kin gode sai dai fa in har irin na ‘yan uwanshi ne to ba zaki sa su ba na dan bata Www.bankinhausanovels.com.ng
rai sannan nace bama iri daya bane na tashi na soma
gwadawa duk wanda nasa sai su zauna min tamkar a
jikina aka kerasu,da yamma ina zaune a daki ni dai bani son zuwa aiken yayanmu domin na tsani ganin
Mimi nasan ma wulankanci zasu min Sagir ne yace yayanmu na kirana dama a shirye nake ina son inga ko ya manta ne in share in ya tambayeni daga baya sai nace na manta ne nima haka na tashi na tafi dakin mama na sanar da ita tace sai na dawo,su hudu na samu na gaishesu suka amsa dayan cikinsu yace Maska wannan ma sister ka ce?yace ban sani ba ya wani daka min tsawa yace shiga ciki ki dauko jaka adidas kizo ki wuce kin wani tsaya kina kallon mutane na shige dakin barcinshi da sauri ya juya gun abokanshi yana ce mishi dj bana son abonda kuke min baku san yaran nan da raini ba sai taga kamar sa’aninta ne mu wani yace to Nasir fa da zai auri Mami kanwarka?yayanmu yace ai yaga zai iya ne sannan nace mishi kar ya yarda ya kawo min karanta raina shi ga Www.bankinhausanovels.com.ng manyan babys a gari yazo Zai nace gun wadannan yaran,jikina yayi sanyi na sabi jaka na fito ya dubeni yace kikai mata saura ki dade na fito ba tare da ya bani kudin mashin ba, gidansu Amira na shiga bayan mun gaisa da mamansu tace min tana cikin dakinta na shiga tace daga ina haka?nace ina zani Zakice ta ce to sai ina?na zauna bakin gado na ajiye jakar a
kasa na dubeta na nace don Allah zaki raka ni?tace ina? nace malali gidansu Anty Mimi tace to jeki ki gaya ma mamanmu sai na shirya kafin ki dawo nace to amma fa kece zaki biya mana kudin mashin tace wane irin ni zan biya nace to bai bani kudin mashin ba gashi har yana cewa inyi sauri ni kuma ban fito da ko sisi ba na fito gun mamansu na sanar da ita tace sai mun dawo muka fito muka hau mashin sai malali
Yanda na zata hakan ce ta faru domin da Mamnsu wato Haj Laure ta ganmu haka ta hau zaginmu wai
mu juya da kayan ba’a so inshi ba zai kawo ba to ya bari,Anty Mimin itace ta hana tace mu kawo Amira tace ki barshi mana sai mu maida Anty Mimi tace ke bani son rashin kunya Amira tace ba rashin kunya bane ance ne mu juya dashi
na dubi Amira nace don Allah ki rufa mani asiri Amira ta jani zamu juya Anty mimi ta biyomu ta fisge jakar ta juya ni dariya ma abin ya bani,muna jiran mai mashin wani yazo da mota a gabanmu ya tsaya ya dube mu yace kuzo muje yanmata ina za’a kaiku?kafin nayi magana Amira tace unguwar rimi na dubi Amira nace kina hauka ne?tace zauna nan in ba zaki ba sai dai kiyi ta zama anan yace magana fa nakeyi nace ku shigo muje nima can na nufa,nace nidai ba zan shiga wannan motar ba Amira ta bude baya ta shige sannan tace ai kina da kudin mashin ko?nan na tuna bani da ko sisi nayi tsaki,saurayi mai mota yace yar kanwata shigo mana jan ajinki ya burgeni kuma na yaba,na dubi Amira ta wani kame tamkar motar kanin babanta nace bani naira dari tace nace maki bani da kudi ko?in zaki shiga ki shigo dole,dole na shiga motar nima bayan na shiga yace yi hakuri kanwata dan dawo nan mana na koma don Www.bankinhausanovels.com.ng
surutun ya soma isata yaja muka tafi,sannu a hankali
yake jan motar sunana ya tambaya nace mashi Amira,
Amira da take baya ashe taji tace yar iska sunanta Iman yace yauwa mai sona fada min gsky Amira ta cigaba da cewa xan kaika har gidansu yanda tace maka haka takeyi ma samari tace sunanta Amira kuma ta yi masu kwatancen gidanmu ina jinsu ban kuma magana ba sai su keta faman labarinsusmuna zuwa kofar gidanmu ya faka a daidai lokacin yayanmu yayo ma abokanshi rakiya kallon motar ya tsaya yi da sauri na bude na fito daga motar ido hudu mukayi da yayanmu nan da nan fuskarshi ta sauya yayi murtuk tamkar bai taba dariya ba koda dai dama ban taba ganin dariyar tashi ba,a hankali yake tahowa har inda muke nayi zaton zai mare ni ne sai naga ya wuce ya isa gun motar daidai kofar dreba ya
kwankasa gilashin motar,ina zaton Amira da bata fito ba ita ce tace masa yayanmu ne sai naga ya fito daga cikin motar da sauri sannan ya mikawa yayanmu hannu gami da sallama,yayanmu nokewa yayi yaki bashi hannu sai dai ya amsa sallamr a ciki ya dubeni yace menene dalilinki na shiga motarshi?nayi shiru shi kuma saurayin mai motar sai cewa yayi yallabai ai ina sonta ne kuma banzo da wasa ba,sai ya kara daure fuska sannan yace ita me tace maka?yace bamu yi magana ba tukunna,yayanmu yayi mishi wani kallon wulaknci sannan yace kar na kuma ganinka a gidan nan ka fahimceni? yarinyar nan krt zatayi ku ne masu hure ma yaran mutane kunne suki krt bani Www.bankinhausanovels.com.ng bukatar sake ganinka understand?so kama gabanka ya juyo ya kalleni wata uwar harara ya sakar mani ba zaki wuce a nan ba? Da gudu nayi cikin gida.
Tara daidai na dare na gama shirin kwanciya kamal ya shigo ya dubeni ke Iman yayanmu yace kikai mashi
tea,ban tsaya dogon turanci ba na fito falo dakin mama na shiga ko zan samu ta dafa ma Alhj bata cikin dakin na fito falo kan tebir naga plas din shayi na duba naga akwai a ciki yar butar shayi na dauka na zuba na dora kan tiranshi na hada da kofunan na fita sam na manta ban sanya hijabi ba rigar bacci ne a jikina mai hawa biyu sai hular hijabi nayi sallama da kyar ya amsa na dan dube shi fuskarshi a daure cikin tsoro na shiga zaune yake kan kujera mai zaman mutum biyu ya dora kafarshi suna kan teburin tsakar dakin irin dan karamin nan na rage tsahona na ce gashi ya zuba min harara na ajiye da sauri na zan fita sai naji yace ke zo nan na dago ya
dubeni yace zauna na zauna kan kafet cikin hankali ya sauke kafafuna daga kan tebur din ya zauna da kyau,Amina naji ya kira sunana a hankali yar
naji cikin jikina gashi ya iya fadar sunan a gajiye na dubeshi sannan na amsa yace na lura dake kina shaawar ganin bacin raina ko? (hhahhh su yaynmu anyi nisa) na girgiza kai alamar aa yace haka ne mana(a raina nace to me nayi maka?) Yaci gaba in ba haka ba so nawa zance miki bani son kina kula samari ko kema auren kike so?nace aah yace kar ki damu in ma auran kike so to sanar dani don akwai wani da yayi mani maganar yana sonki,gabana yayi mugun faduwa a raina nace ni kai nake so ya kara Www.bankinhausanovels.com.ng
tausasa murya yace in har kina so ya kara tausasa
murya yace in har kina so ki kwantar min da hankali to ki tsaya kiyi karatunki kar ki damu da su mami basu san matsalolin da ke cikin auran ba,kinga kema karamar yarinya ce baki san komai game da aure ba undaerstand me?na gyada kai alamar eh yace to yi min alkawari da bakinki cewa ba zaki kula kowanne da namiji ba ko bana garin ko bana kasar har sai na dawo na bada izini ba tare da wani tunani ba nace nayi alkawari ba zan kula kowa ba ko ba kanan yace promise nima nace promise yace good ya saki fuska tashi kije ki kwanta na mike sai da naje kofar fita na juyo shima ni yaje kallo ga mamakina sai naga ya min murmushi mai tsayawa a rai na saki labulen na tafi zuciyata na dauke da murmushin da yayi min,haka na kwanta ina juya maganganun da yayi min musamman in da yake cewa in har kina so ki
kwantar min da hankali to ki daina sauraron samari me yake nufi?wata zuciyar tace min abokinshi mana haka nayi ta juyi har barci ya daukeni Washegari da safe ina shirin tfy comp Jamila da Sagir
suka shigo da gudu suna rige rigen fada min kiran yaya Kabir na daka musu tsawa nace kai ba makaranta zaku je ba?suka ce ai mun fita sai yayanmu yace kizo nace yayanmu babba?suka ce a’a Kabir,na dan yi tsaki sannan nace kuce gani nan,sagir yace anty kizo muje yace in kika zo muje yace in kinzo zai bamu naira 100 nace ku bace min da gani a nan suka fita sai da na gama sannan nayi wa mama sallama sannan na fita,ina dauka ya tafi gun aikinshi sai na ganshi a kofar dakinshi sai faman duban agogo yake yi na isa gurin shi fuskata babu walwala nace ina kwana?bai amsa ba sai dubana yake yana Www.bankinhausanovels.com.ng murmushi yace da raina ya baci domin kin shanya
ni amma yanzu kin wanke min zuciyata na dubeshi nace kamar yaya?kinyi dressing irin nawa,na dubi kayan jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani kicin kicin nace a’’a yace to fita ki min bai saurari amsata ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu tafi nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata
magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi yasa na bude motar na fito shima yayanmu na
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG