SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 19

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 19

Gaba daya suna zaune a parlor wayar Nazeefa ce tai ringing, Mikewa tayi ta shiga d’aki, Kafin ta shiga call din ya tsinke Zurawa Fuskar wayar ido tayi tana tinanin kota kirane wata zuciya Tace nop don’t call him Kidan ja class mana+ Kusan 10mins Mansur be kiraba, Yar karamar tsaki taja ta kwanta, Har bacci yadan Fara fisgarta taji wayarta yai Kara, dubawa tai taga *My LOVE* “Picking din call din tayi tace Assalamu Alaikum, Dayan bangaren ya amsa da waalaikumus Salam gimbiyar Mata Tai murmushi Tace uhm ya kake ya kokari kuma? Yace Alhamdulillah inanan inata missing dinki Rufe ido tayi kamar yana kallonta tace Nima haka Yace wow really Tace” Yes dear Sannnan tace m sorry naga Sakon waya nagode sosai. Allah yabar zumunci yai smiling yace karki damu it’s my duty to make you happy! Tai yarrr da ido kaman yana kallonta Tace yeah hakane dear nan sukasha hirarsu ta mosoya sosai, Haka suka rabu cikin mararin juna Suna gama wayar, Mansur ya kalle hotanta dake screen din wayarshi yai ma screen din kiss sannan yace I love you myLady Ita kuma Nazeefa sa wayar tai a chest dinta, tana smiling Tadau minta kusan 5 a dakin sannan ta fito fuskarta cike da walwala, Kusa Da Faeez taje tace zo kaji wata magana! Yace OK Dear 6s sannan suka fito harabar gidan! Mubeen kamar ya kwalla ihu dan haushi aranshi yana inama ni nasama chance dinnan Fitowa sukai harabar gidan Tace please inasone ka dinga koyamun waya kasan ban iya ba Ya kalle wayar yace wayasai miki? Tai murmushi tace guy dinnan, yace wow phone din ya hadu shi manyan yara suke rikewa yanxu, tace KO? Yace yes Sannan ta kalleshi tace” please kayi hakuri da abun da ya faru badason raina bane! Sannan duk ta bashi Labarin halin da ta shiga bayan tabar gidan, Sannan tace do you knw yaya Mubeen kuwa ya batamun rayuwa! Zare ido yayi yace I don’t get you nan ta bashi labarin musassabin barinta gidan! Kuka faeez ya farayi ahankali tace haba bro meye haka? Dan naga fa Kai jininane sai yasa na sanar dakai, ni na yafemai kuma ba laifinshi shi Kadai bane harda nawa! Kara bata hakuri sosai yayi yace taita istigfari, kuma inshaa Allah ba Wanda zaiji labarin nan, tace tom nagode, nan ya Fara koya mata har yai saving number shi a cikin wayarta! Koda dare yayi su umma da hajiya asma’u hira sukai sosai, Malan nalado da Baban mubeen suma hira sukai na yan uwantaka sosai Faeeza kuma da Nazeefa daki daya suka kwana, amma ba Wanda yacewa kowa Komai, Dan kowa harkar gabanshi yakeyi, Sau tari faeeza nason yiwa Nazeefa magana amma taita d’aurewa! Tana hada rai batason wata magana ma ya hadata da kowa! Ba ruwanta kawai Har safiya abun ya ishe Faeeza, bayan sunyi break fast ta ce Please Nazeefa inason mui magana dake Kunnanta sanye yake da earphone bata jiba, Faeeza tabata tayi tace Nazeefa! A fusace ta waigo ta cire earphone din dake kunnata, ta zura mata ido Faeeza ce Tace please inaso muyi magana! Tace OK inajinki Nan itama ta bata hakuri sosai harda kwalla, Nazeefa aranta Tace meye duniyar ma? Kawai ta sakko Tace OK bakomai, Allah ya yafe mana gaba daya, amma kam kinyi kuskure a rayuwa, shi duniyar nan da kike ganinta bakomai bane fa, I see no reason da mace Yar uwarka zata dinga treating dinka bad! Saboda wata rana! Faeeza tace hakane I did a mistake kiyi hakuri, Nazeefa Tace alright bakomai ya wuce, Sannan ta sake jiki da ita sosai kusan komai ayan kwanakin tare sukeyi, Kowa ya sake jikinshi a gidan but banda Mubeen, Gaba daya bejin dadi yanaso yazo ya bata hakuri amma ya kasa! Ko kowa na falo ana hira to shi kadai yana daki, duk yabi ya chanza Ya slzama ainihin Silent guy, Duniya kenan!! **** Bangaren Mansur Turaki kuwa son Nazeefa sai ruruwa yakeyi a zuciyarshi, dan tacemai zasuje chan kauyan Su tare da iyayanta ji yake da yanada dama ba inda zataje Dan 24 suna online suna chat KO waya, ba abun da yake rabasu sai bacci dan KO a baccin nema to suna mafarkin junansu, Ana gobe Nazeefa zasu tafi kauyensu dan suje su tattaro wasu abubuwa da sukeso, Sannan su bayar da gidan chan ga mabukata, da kuma Su sanar da makwabta da yan uwan arzikin sun bar garin Nazeefa ta roka alfarma Tace zataje ta gaisar da kawarta Ameerah (her frnd ) Su umma sukace to amma karta Dade! Tace toh Nazeefa tasa kayan alfarma, Kallo daya zakai mata kasan Ta hadu ta koina, Ta fito gidan da yake ba nisa Takawa tai a kafa KO ina ta shiga kallonta kawai akeyi, Tun daga nesa yaran gidan Su Ameerah kawarta suke ga wata angayu Chan! Su ummansu sunata dariya, Ameerah ta fito Tace baridai naga an gayun nan da ake cewa Tana fitowa sukai ido hudu da Nazeefa, tsayawa tai tana kallonta Tace ikon Allah kamar Nazeefa! Nazeefa ta kyalkyale da daria tace ba kama bace itace! Rungume juna sukai suka shiga gidan Nazeefa ce tai dariya tace Ameerah ba kama bace nice! Rungume juna sukai suka shiga gidan+ Iyayan Ameerah Rik’e baki sukai sukace Nazeefa aure kikai ne ba labari, Smiling tayi ta tsugunna ta gaisheshu tace a’a Mama, Ameerah Tace mu shiga ciki mana Tace toh Daki suka shiga ta kawo Mata ruwa tasha, Ameerah kam binta da kallo tayi kamar bata taba ganintaba, tace ikon Allah kinga yanda kika koma kuwa? Kamar bakebe meye sirrin? Nazeefa tai smiling tace it’s a long story amma bari kiji, Nan ta gyara zama ta kwashe labarin komai tun barinta gidan aiki har izuwa yanzu da take bata labari Ameerah Tace ke Dan Allah cikin Ihu! Nazeefa Tace Wallahi dear, Ameerah fita tai ta kira mamanta da kishiyar mamanta take basu lbarin Nazeefa taga iyayanta Alhamdulillah sukace mun miki murna, Ashe ke yar gata ce! Ikon Allah kenan ashe gidan yan mahaifinki kikai Aiki, Allahu Akbar Nazeefa Tace sosai, kam, Sukace sannu yar nan, Gaskiyane duk Wanda yai hakuri tabbas yana tare da nasara! Sannan suka fice a dakin suna mamakin Lamarin nan Bayan fitarsu sukaci gaba da hiransu na kawaye, dama zancen yan Mata be wuce na samari Lol Ameerah tace ansamun rana fa kafin azumin nan za’ai bikina “Nazeefa ta riko Hannunta Tace ke Dan Allah tace da gaske nake, Nazeefa tai murna sosai Tace” wazaki aura? Tace wani doctor ne Allah ya hadani dashi, Allah ya dauramun sonshi sosai! Nazeefa tace Wow Allah yabarku tare, Ameerah Tace Ameeen! Sunsha hira sosai, Zasu fito kenan wayar Ameerah yai ringing! Tana dubawa taga My Doctor, da murmushinta tai picking yace hello my princess Tace hea Likita na ya kke, yace I’m fine yace ganinan a kofar gida Tace OK ganinan zuwa da wata Frnd Dina Ku gaisa yace OK! Yana kashe wayar ahankali yace Allah yasa ta fiki kyau na kwaceta! Yana jingine a jikin kofar motar suka fito! Tun lolacin da ameerah tace ga kawarta nan ta zatazo su gaisa taji gabanta na fadi Fitowar da zasui kenan Taga Dr Bashir abokin Mubeen! Kutamah tace aranta Tana karemai kallo Shi sam daya kalleta sau daya ya rasa gane ina yasanta, but yasan confirm yasan face dinnan Murmushi ya Fara mata, Ameerah Tace sannu da zuwa ga Frnd Dina nan Ku gaisa! Washe baki ya farayi yace sannu baiwar Allah, Kallon fuskar Nazeefa da zasui suka ganta a tsuke ta hada rai, Dakamai tsawa tayi Tace Malan Dakata! Macuci Kawai Kana nufin baka ganeni ba? Dr Bashir jin kirjinshi yayi ya Fara bugu da karfi, muryanshi na rawa yace banganekiba Wani murmushi tayi tace tabbas bazaka ganeniba, nice nan Nazeefan Mubeen a da kenan amma fa! Zare ido yayi Yace Nazeefa innalillahi……. Tace wato ka lallabo ka yaudararmun kawa kamar yanda mugun Abokinka ya yaudareni KO? To karyanku ta kare! Ameerah dake tsaye tana jinsu Tace meye haka kenan dama kunsan junane? Nazeefa Tace eh nasanshi through Mugun Brother na mubeen, Sannan ta kalle Dr Bashir Tace halinka yaja maka, seda ka gala lalata yaran mutane sannan zaka lallabo wajen saliha? Ai baka isaba, good wifes are for good husbands, indai Ina nunfashi bazan taba bari ta aureba koda kuwa tana sonka! Tana magana tana hawaye tace ba abun da zance maku sedai ince Allah ya Kara shiryaku Dr Bashir ya tsugunna yana Mata magiya dan Allah tayi hakuri wallahi yanzu ya tuba, Tace tuban mazuru ba, kana daya daga cikin wanda ya ziga mubeen ya yaudarene sannan ta fashe da kuka Ameerah Tace kawata kidena kuka! Ta kalle Dr Bashir Tace kasani inasonka Amma bazan boye maka ba nafison kawata fiye dakai saboda Ashe dakaine aka hada baki a ka cutar da ita? Gashinan kunfara gani tun yanzu ai sukai Mai tatas Sannan suka shiga gidan madadin Nazeefa ta tafi gida Sororo yayi a waje ya rasa mekemai Dadi, Ashe munfunci zuwa take ta dawo kanka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ya fada, Dandan me karfin haline da kuka zaiyi Sosai, Shiga motor yayi yace dole na nema mubeen duk inda yake Koda suka shiga gida iyayansu suka gansu wani iri, tambayarsu sukai meya faru? Nazeefa cikin sheshekin kuka wani hikima yazo Mata Tace mayaudarine, munyi alkawarin aure na nemeshi na rasa Ashe Wajen Ameerah ya dawo Maman Ameerah Tace Ahab, ni dama tun farko ban aminta dashi ba, yarinyar nan ta kafe, Ai yanzu kinji da kunnanki ko? Itama tanta a bace Tace mama naji, Allah ya Kara mana tsari da irinsu, Zan kirashi yazo ya kwashe kayansa na sa Rana! Sukace gwanda Su Nazeefa shigewa daki sukai, sunata wa junansu jajee Sundau kusan awa daya suna ta hira, Nazeefa ta bata labarin Dr bashir sosai, tace kiyi hakuri fa na katse soyayyar dake tsakaninku, though bansan irin soyayyar da kike mai ba, nidai a ganina baki dace dashi ba gaskiya+ Ameerah ce ta nunfasa Tace hmm nayi mamaki fa, maza sai Allah gaskiya, Allah ya bamu nagari kawai, Nazeefa Tace Ameeen sys nan ta bude Mata WhatsApp group din da take, da yake an turo addu’oi sosai ta sama taji ta rubuta, Sannan Tace ta daure ta dinga yin sallah raka’a biyu fatiha da qulhuwallahu, a kowani raka’a bayan tayi sallama sai ta koma tai sabuwar sujjada ta karanta _La ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz-zalimeen._ Sau 41 sannan ki roka abunda kikeso, insha Allah, Allah zai karba, kuma ki yawaita istigfari da hailala da salatin manzon Allah S.A.W zakiga chanji a lamaranki Ameerah Tace amma Nagode sosai, Allah yabarmu tare Tace Ameeen ni Zan tafi, har baking hanya ta rokota sannan ta karasa gida cike da Tinani **** Bangaren Dr Bashir kuwa, tun da yabar Wajen Ameerah kwata kwata ya kasa natsuwa, Gabanshi se dukan Tara tara yakeyi, gashi sunyi uwar watsi da mubeen yanxu ta yaya ma zaije ya sameshi, Wata zuciyar Tace gwandama ka je ka sameshi kaji kan labari, cos yaga Nazeefa ta chanzamai sosai so yanason jin ba’asi ya hakan ta faru *** Mubeen na kan sallah yana karatun qur’ani Feeza ta shugo Tace yaya Ana sallama dakai a waje! Yace alright kije kice ganinan zuwa, feeza sanye da hijab take ta fito, ta sanar da Dr bashir, kallonta yayi yace anya ba wani Abu a kasa wai yau faeeza ce dasa hijab lalle kuwa, da yarinya sai rashin kunya dasa kaya matsatsu girgiza kai yayi Dr Bashir na tsaye a jikin motarshi Mubeen ya fito, Kallo cikin ido sukai wai juna! Mubeen yai ajiyar zuciya sukadai gaisa, Suna tsaye saiga Nazeefa ta sauka a daidaita sahu taba me napep 500 yana Hajiya ga chanjinki tace katafi dashi kawai Sake Baki Dr bashir yayi, Nazeefa ce tazo ta wuce ta gabansu ta gansu Su biyu, Wani tsaki taja ta balla musu harara Tace Allah ya shirya kawai, tai shigewarta gidan Tana shiga Dr Bsshir yace how comes ta dawo gidan bangane ba ne, still tana aiki a gidan ne ko ka aure ta ne? Wani kallo mubeen yamai seda hanjin cikin Dr bashir ya kad’a, Mubeen ya furta ka cucece, Dr bashir yace kodai ka cuceni, yanzu daga gidan Ameerah kawar Nazeefa nake, tana ganina ta zazzageni, Wai ni ba mutumin kirki bane, kaga abunda kaiwa Nazeefa nima ya shafeni KO? Mubeen sa hannu a aljihu yayi yana karewa Bashir kallo, yanzu wallahi badan giwa tayi lafiya ba daka sani ayau dinnan, ai dama mugun abu zuwa yake ya dawo, duk abunda kasa naiwa Nazeefa shike dawo maka, Inda kasan yanda Nazeefa ta dawo gidan nan Seka yi mamaki, tabbas na yarda, duk abunda mutun yai mekyau zai gani inma mara kyau ne zaigani Bashir yace ni duk bangane me kke nufi ba ka fito a mutun kaimun bayani Nan Mubeen Yace tun da za’a auramun Haleema, Nazeefa Taji labari tabar gidan ai ka sani! To from then dai ta hadu da that guy dinnan (MANSUR TURAKI) har yakaita gidan Su sukazo nan gidan, intakaice maka dai Nazeefa she’s my cousin, babanta da babana Uwarsu daya ubansu daya, Dr Bashir zare ido yayi yace” did I heard you well kuwa? Mubeen yace yanda kaji haka maganar yake, mune fa har prison aka kaimu, yadai boyemai dad dinshi yaiwa Baban Nazeefa asiri saboda gori da tonan asiri Ko nan gaba! Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Dr bashir yace lalle Allah baya zalunci, Mubeen ya kara da cewa tabbas kuwa, Ashe dad dinta me kudin gaske ne, intakaice maka dai duk kudin babana, Mahaifinta ya fishi kudi, shuru Dr bashir yayi ya kasa cewa komai Nan sukaci hirarsu nidai nai gaba abuna nabi Nazeefa dan jin ya ta dawo gida! Nazeefa na dawowa gida Taga ummanta da Hajiya asmau suna kitchen suna dafa abinci, ajiye jakarta kawai tayi ta shiga kitchen din itama ta tayasu, Faeeza kuma da yake bata iyaba tana zaune a kujera tana game a waya Tana ganin Nazeefa ta shiga kitchen itama ta bita tana ganin yanda sukeyi har suka gama Sunci abinci sun koshi sosai dare tayi kowa ya shiga daki danyin bacci Nazeefa kuwa waya sukai sosai da Mansur se kusan 11 tai bacci, while Faeexa itama sunata ta chats da fri3nds dinta a group, Har zasu kwanta Nazeefa Tace inaso inyi miki magana though bansan KO zakiji dadinta ba, kinga duk sanda Mamanki Tana dafa abinci kidinga zuwa kina tayata, if possible ma kije kiyi kawai1 Faeeza Tace hakane zandingayi kinsan amma ban iya girki ba har yanxu, Nazeefa tace OK KO dinga kallon tashar girke girke, kuma Zan bada number dinki ai adding a group Tace OK Nagode *NOTE* Please iyayanmu ba gata bane wai kace bazaka dinga ba Yaro girkiba, kodan kunada kudi kace zaka nemo Yar aiki no, Yayankunr Ku kuka haifa ai da dadi ace danka ya Iya girki sosai, sannan yaran kuma koda bazasu baka ba on your own kadinga dafawa, Kana kwabawa, *practice makes perfect* wata rana zaki Iya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *