TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 4 BY MANSUR USMAN (SUFI)
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar lasmirat take ta zube Kasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace “me kike da buKata ya shugaba ta? Lasmirat ta dube ta tace”’ yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so wannan bako dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya . . bukata kiyi sani cewa yana da matukar muhimmanci agareni . . Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace ” , angama ya shugabata bin umarnin ki ai shi ne ibada ta, – ‘Tana gama fadin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta ‘. Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya Amma koda ya waiga ya hada idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani mayataccen kallo mai dauke da alamar tambaya.
ZAMU TASHI
~ Cikin hanzari sarauniya lasmirat ta juya tada linzamin ‘dokin ta ta nufi bangaren da turakar ta take, – _ Lokacin data isa sai ta shiga izuwa kewaye ta tsala wanka _ Sannan ta shiga tsaba ado tana mai fuskantar wani madubi Tana cikin wannan hali ne sai ta jiyo-motsin tafiya a bayan — ta . . : Koda ta waiga sai tayi arba da shi ba wani bane face — wazirin ta mai suna ukashat, – Waziri ukashat yakasance dattijo mai yawan ‘shekaru .amma duk da hakan babu gajiya a tare da jikin sa, . Yana da kaurin jiki, dogo ne tsaka-tsaki,yana da tarin gemu da Kasumba fararen sol, . _ Fuskar sa tana da kwarjini Ukashat yakasance dan uwa a wajen mahaifin lasmirat wato sarki kazmal kuma babban aminin sa, bisa wannan — – ; dalili ne yasanya duk abinda lasmirat zata zartar sai ta ‘ nemi
Www.bankinhausanovels.com.ng shawarar waziri ukashat, sO . Bisa al’ada duk sa’adda waziri ukashat zai gana da. sarauniya lasmirat yana sanya ayi masa iso,kuma zai shigo – ne fuskar sa cike da annuri ; Amma a wannan karon sai ga fuskar sa a murtuke babu annuri tamkar an aiko masa da sakon mutuwa, Kawai sai ya zaune a bisa wata kujera dake fuskantar lasmirat ya dude ta cikin tsananin fushi yace” yake lasmirat shin menene yasanaya za ki Www.bankinhausanovels.com.ng karrama wanda ya wulakanta ki a gaban talakawa?.
Tabbas hakan zubar da darajar wannan masarauta ta mu . ne da muka gada tun iyaye da kakanni, Shin yanzu da wane irin idanu zamu kalli sauran sarakuna abokan gabar mu? _ . . Wai shin ma bakya-tunanin cewa wannan saurayi daya . daga cikin abokan gaba ne yayi badda kama domin ya yaudare ki? Koda. jin wannan tambaya daga bakin waziri ukashat sai – Sarauniya lasmirat ta dube sa a nutse tace”yakai waziri kayi sani cewa ko kadan bana taba da nasanin karrama wannan saurayi kuma jiki na ya_bani cewa tabbas_ bazai cutar da Ni ba, hakika zai zamo mai amfani a gare ni,- Ukashat ya katse ta ta hanyar daga mata hannu yace ” __ HakiKa ke yarinya ce, tabbatas Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai iya gani ba, Ban yi mamakin maganar ki domin na fahimci cewa . tsananin kauna da soyayyar wannan saurayi ce ta _ makantar da idanuwan ki, ta ‘sanya har kika manta da burin zuri’armu na kare martabar wannan masarauta, Koda wannan batu daga bakin ukashat sai sarauniya — lasmirat ta fusata ainun ta daka mai tsawa ta dube sa tace” yakai ukashat kayi sani cewa ni nake da ikon bayar .da umarni a wannan masarauta don haka abin da naga ya dace shi zan aiwatar, Www.bankinhausanovels.com. Tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta fice daga cikin turkar ta bar waziri ukashat a zaune Cikin alamun tsantsar damuwa waziri ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da takaici.
Da shigar saurayi yaslir izuwa cikin turakar, sai ya tarar turakar takasan ce Kasaitacciya da aka Kawata ta da . nau’ikan kayan Kawa da alatun jin dadin rayuwar – duniya, Gaba daya turakar.shimfide take da wani koren kilishi mai taushin gaske,Bayan yaslir ya fito daga kewayen wanka wani wanzami
yayi masa gyaran fuska da saje, sai wata.kuyanga ta kawo masa wadansu fararen tufafi masu taushi ya sanya a jikin Sa,Nan take tsakanin kyawun sa. ya fito fili Karara, kawai sai ‘ ya nufi teburin da aka tanadar masa abinci da abin sha ya ~
shiga kimtsa cikin sa, Bayan ya kammala ne da yake a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai, Sai ya kunna fitulun dake turakar ta kaure da haske, oo Sannnan ya zauna a bisa‘kan gadon sa kuma ya zurfafa’ izuwa kogin tunani, .. Www.bankinhausanovels.com.ng Yana cikin haka ne sai yaji an turo kofar shigowa turakar
Ai kuwa kofar na budewa sai ya yi arba da ita ba’wata ba -ce face sarauniya lasmirat ta cafa ado wani irin daddadan Kamshi na tashi daga jikin ta. ~ Cikin Wata irin tafiya mai daukar hankalin duk wani da namiji,ta nufi wata Kasaitacciyar kujera dake fuskantar yaslir ta zauna a kan ta, Cikin annurin fuska ta dubi yaslir tace’yakai yaslir kafin mu kai ga tattaunawa abinda ya taramu anan Yana da kyau ka sanar dani labarin rayuwar ka, Koda jin wannan tambaya sai idanun yaslir su ka ciki da kwalla ya dubi lasmirat yace” ya sarauniyar kyawu shin ina dalilin son kiji labarin rayuwa ta? . Lasmirat ta numfasa tace”Domin sanin labarin ka ya na da matukar muhimmanci a gareni, – ° Yaslir ya yi gyaran murya a karo na:biyu sannan yafara dacewa Kimanin shekaru arba’in baya anyi wani Kauye da ake kira da suna Darul-Na’am,_ – . Gari ne mai dauke da arzikin noma, kiwo, Sarkin dake a mulkin kauyen yakasance adali mai tausayin talakawa, . Ana kiransa da suna Abu-salimat, Abu-salimat yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa maza a filin daga, Yana da ya guda daya kyakkyawa tagaban kwatance ana kiran ta’suna salimat ta gaji mahaifin ta a kyawawanh halayen mahaifin ta. ‘ Kauyen Darul-Na’am na karkashin mulkin wata babbar , masarauta da wani kasaitaccen sarki ke mulki mai suna_ Husnalu ibn kailub, Sarki Husnalu yakasance GWARZON MATSAFI, kuma mashahurin mayaki, dadin dadawa kuma_ yakasance AZZALUMI nagaban kwatance, ; Www.bankinhausanovels.com.ng Kwace,kashe rayukan al’umma,tare da farauce dukiyoyin su ba a bakin komai yake a wajen sa ba, A rayuwar sarki Husnalu babu abin da yake tsananin kauna fiye da dansa guda daya mai suna Hatmal, Yarima Hatmal yakasance dan lele a wajen sarki Husnalu baya son Bacin ransa ko kadan, Bisa al’adar Sarki Husnalu duk bayan shekara daya sarakunan dake Karkashin ikon sa kan biya sa haraji na dukiya da adadin ta yakai dinare dubu dari tara, gami-da kayan amfanin gona da dabbobinni’‘ima Tsakani na da gimbiya salimat akwai soyayya mai karfi, — – kasancewar mahaifina shi ne wazirin mahaifin ta,tun muna yara Kanana muke kaunar juna. ‘ Wata rana daga cikin ranakun da sarakunan ke kaiwa . sarki Husnalu haraji, kamar yadda aka saba duk shekara, + Sai yazamana cewa a wannan shekara anyi tafiyar tare da nida masoyayi ta gimbiya salimat, .Bayan dukkanin sarakunan sun kammala hallara a fada, Bayan shiru da ya mamaye fadar na dan wani lokaci sai aka hango sarki Husnalu da Www.bankinhausanovels.com.ng yarima Hatmal sun shigo fadar, suna sanye cikin suturu iri daya hatta takalmin dake — ’ kafar su iri daya ne, | . . Koda jama’a suka hango sarki sai suka mike tsaye domin : girmama a gare su, Kai tsaye sarki Husnalu da yarima Hatmal suka huce izuwa inda karagar mulki take suka zauna a tare, Sannan sauran jama’a suka zauna, batare da bata lokaci ba sarakunan suka dunga tashi daga wajen zaman su suna guwa gaban na Husnalu suna kwasar gaisuwa sannan su gabatar da harajin su da jama’ar da suka yi musu rakiya Sarki na farko da ya gabatar da harajin da ana kiransa da suna zulaibu, yana mulkin wani dan Karamin gari mai_ suna madinatul-shaswal, _ WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG A gaba daya sarakunan .da suka: hallara a fadar babu , wanda yakai zulaibu yawan shekaru da kuma dadewa
akan karagar mulki, Sai da sarakuna biyar suka gabatar da harajin sannan aka iso kan sarki Abu-salimat, – Abu-salimat ya mike tsaye ni da gimbiya salimat muka_mara masa baya, dakaru na biye da mu dauke da akwatin dinare gami da kayan amfanin gona, har mu ka isa inda karagar mulKi take, muka zube Kasa muka kwashi gaisuwa_ ‘* muna masu sunkuyar da kawunan mu. .. Kawai sai wadansu ‘dakaru daban a fadar suka karbi wadannan akwatin dinare suka lissafa kuma suka bincike kayan gonar suka tabbatar da ingancin su sannan suka dauke suka fice daga fadar, . Ana cikin wannan hali ne.na dan saci kallon yarima . Hatmal ai kuwa sai na ga ya Kurawa gimbiya salimat idanu yana mai yi mata wani irin kallo daya sanya hantar cikina_ . ya kada, Ku ma tsoro ya kamani.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE