UMM ADIYYAH CHAPTER 35 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 35 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

fitar matar can Fariha daga ofis dinsa, ne saboda ta yarda da shi har cikin ranta, da ya ce mata ya tuba, ta yarda da shi, da ya ce ita yake so, ta yarda da shi da ya ce ya yanke duk wata mu’amalar banza da Kadangarun bariki. Nade Kafafunsa ya yi, bayansa na manne da bayan kujerar, ba tare da ya sake
hannunta da ke Kirjinsa ba, ya ce “… Yes! Turarenta ne a jiki na, kamfaninsu yana cikin daya daga cikin wadanda abin nan ya shafa na (Data Breach), ita take bibiyar yadda abubuwa suke a bangarensu, tun aurenmu ban sake kulata ba, ba hanyar da
bata bi ba don ta samu Kofa, saKwanni, waya, (Social Media), ta kai ga sai da na kira kai tsaye na ce ta daina nemana. Ba na son mu rasa kasuwancinsu, haka nan ba na son na rasa kaina, don haka da
ta nemi zuwa don maganar Business, ban hana a bari ta shigo ba, illa iyaka na ba ta
damar ta gama abinda za ta yi, ta fita, niyyata ma na mayar da al’amuranta wurin Femi.

ZAMU TASHI 

Na amince kuskurena ne da farko da na bari muka fada hanyar da ba daidai da itaba, duk da na san ba aurenta zan yi ba, asali ma ba ita ba ce a raina. Ga shi lokacin da na samu natsuwa na ke son rabuwa da ita, tana kawo min matsaloli a rayuwata”
Shiru ya dan yi sannan ya numfasa, “She came on to me, na tureta, inda na fada mata ta kama kanta, ta daina wannan rayuwar, na kuma fada mata gaskiya duk wanda za ta yi irin wannan mu’amalar da shi, ta sani ba aurenta zai yi ba, ta je ta natsu ta samu mai sonta tsakani da Allah ta yi aurenta. I know, ban kyauta miki ba, ban kyauta mata ba, ban kuma

Www.bankinhausanovels.com.ng kyautawa kaina ba tun farko. Amma kuskure ne, da na riga na tafka a baya. Kuma ba na fata na sake
kwatantawa, I held on to my promise. Ba zan taba saba alKawari ba. Musamman alkawarin da na yi miki Twinkle. Don Allah ki yi hakuri. Ba ni na taba ta ba ranar.” Ya Karasa maganarsa, cikin rauni, dago idanunta tana hawaye ne ta ga abinda ba ta
taba tsammani ba. Kwalla ne a cike taf! A idanun Yaya Zaid. Hada idanunsu ke da wuya, daya ya gangaro kan kuncinsa. Hannu ta sa ta toshe kukan da ya taso mata.

************

“Ina iyaka KoKarina don ganin na zama mutum mafi kyaun halaye, na canja, kuma zan Kara canzawa, zan zamo mutumin da ki ke so na zama har sai kin yarda da ni, amma don Allah ba na so ki Kara kira min kalmar rabuwa, yana min ciwo a nan.” Ya murza Www.bankinhausanovels.com.ng hannunta da ke saman Kirjinsa a gurbin zuciyarsa.
“Ba na so ka canza Yaya Zaid, ba abinda za ka zama na ke so ba, ba kuma abinda da ka ke na ke so ba, ko kuma abinda na yi tunanin da ka ke, kai na ke so a yadda ka ke a yanzunka. Ai So shi ne idan idanunmu basa ganin laifin dan-uwanmu, za ta iya kasancewa na ga laifin Karara idan na so. Amma ba na son ganin laifin, Kauna kuma ita ce na amince da kai a yadda ka ke na taimaka maka mu gyara tare, Kaunarka na keyi mai zurfi Yayana ba na buKatar Kari ko ragi a yadda ka ke. Sai dai idan za ka Kara da ni a zuciyarka.” Ta Karasa fada kanta a sunne cikin Kirjinsa.
Dariya yayi mai dan sauti ya sa yatsarsa ya can dago fuskarta tana kallon cikin nasa
idanun, duk da haka idanunsa sun mata nauyi, don haka ta dan lumshe nata ganin. Gashin idanunta ya yi wa kuncinta shimfida. Mashaa Allah, you’re beautiful Adiiyyah, ciki da waje.” Ya rada mata Kasa-Kasa
cikin muryarsa mai zurfi, yadda kunnuwanta ne kadai za su ji. Wasu sambatu ya shiga mata, tana cikin riKonsa, wanda gaba daya ya Karasa kashe mata jiki.
Wani bal-bal ta ji Kirjinta na yi kamar zuciyarta za ta faso ta fito daga bangon Kirjinta. Shiru ya gitta mai zurfi a tsakaninsu, kafin ya gyara muryarsa ya ce. Wai ni ba, ta ina wannan kunyar ta samo asali ne? Da dai ce min ake H…” Da sauri ta sa hannu ta toshe masa bakin sa, hade da girgiza masa kanta, idanunta ko sun ciko da ruwan kuka, amma ba masu zuba bane, na tsantsar dadin da take ji ne a wannan lokacin. Yaya Zaid, don Allah ka daina.” Ta fada a shagwabe. Wallahi yarinyar nan ki na da niyyar Karasani ne tun da Kuruciyata.” Na ga ta kaina, daina fadar haka, ba abinda zai sameka Inshaa-Allah. Yanzu dai taimaka ma kanmu mu je mu ci abinci, mu kwanta har dayan dare ya yi fa, kar mu makara.” Ta Karasa tana dan kallon agogon da ke manne a bangon falon. Wa? Ina za mu wai? Ai gobe da mai zuwa da inda za aje duka sai dai su yi hakuri, ni kam ina gida wurin Twinkle dina.” Dariya ta yi ta ce, “Neman dai rigima ka ke yi, ka san a gobe ne za mu kammala batun kwangilar (Farraza Groups), sannan ga bakinka da ka ce ba su tafi ba dazu da muka yi Www.bankinhausanovels.com.ng waya, ba yadda za ayi, kuma ba ka wurin. Sannan bayan abinda ya faru kwanaki, neman riKe kwastomas muke yi ba korarsu ba.” “Femi na nan zai wakilceni, ke ma kuma Musa da Mr. Akim suna nan ba za a ga gibinmu ba a wurin.” Kallo ta Kura masa, ta san yadda wannan kwangilar take da muhimmanci a wurinsa sosai, domin yadda sunan kamfaninsu zai samu daukaka bayan sun yi wannan aikin, ga shi ya shafe kusan wata guda akan aikin. Sannan ka ga na manta ban fada masu batun Main swi…” Sauran maganar ce ta tsaya a hanya sanadiyyar toshe mata su da Zaid ya yi, lokacin da ya manne labbanta da nasa tausasa. Sumbatarta yake yi kamar ba gobe. Farko cikin ruwan sanyi, kafin ya katse mata duk wani motsi, ba abinda take ji a kunnuwanta face
bugun zuciyarta da yadda numfashinta ke fita.
Sun dau tsawon lokaci a haka, kafin ya saketa, “Yanzu za ki fada min waye Sarkin nacin aiki a cikin ni da ke?” Kanta ta saddar Kasa tana murmushi, kafin ta dago ta ce, “Wannan kam kowa ya sani ba sai na facda ba, kai dai kawai za ka…” Katseta ya yi lokacin da ya daga ta sama cak! “Yaya Zaid, ka saukeni, za ka kada mu.” I don’t care, muddin ki na tare da ni. Yanzu ki yi shiru ki ji batutuwan da na tanada
don na fada miki, kuma sai kin fanshe muguntar da ku ka min ke da Anty. By the way, you suit yellow. (Kin karbi launin Yalo).” Murmushi ta yi, lokacin da ta ga idanunsa sun Kara duhu, yau kam ba ta tantamar
irin son da Yaya Zaid yake mata. “Ka na nufin ‘Yellow Suits me’ (Yalo ya karbeni) dai ko?”
“A’a ke fa tauraruwa ce, sai dai ki haska abu, ba a haska ki ba.” Ya fada lokacin da suka shiga dakin sa.
“Amma tauraro ma ai a jikin rana aka ce yake samo haskensa.” “Then, ki ba ni dama na ba ki haskena a Www.bankinhausanovels.com.ng daren nan, da ma sauran dararrakin rayuwarmu.”
Hannu ta sa ta sagale wuyansa zuwa gareta. “Ni taka ce har abada, Noorie.” “Hmm… Ina son hakan.”

******

Gaba daya sun yi tsuru-tsuru, cikinsu babu wanda za ka duba ka ga alamar natsuwa ko kwanciyar hankali a tare da shi, ba komai ya janyo hakan ba, illa abin da ya faru a safiyar ranar da ta shude. Kai tsaye Fayemi ya shigo da Mr. Femi cikin ofishin nasu, suka ce duka su biyo su. Ba su fadi inda za a kai su ba, ba su fadi me ya faru ba, a zatonsu taron gaggawa
aka shirya, amma Mr. Femi da kansa ya zo kiransu? Dole akwai alamar tambaya.
Sun yi minti goma a zazzaune a ofishin Stella, wato falon karban baki na ofishin Zaid. Yayin da Mr. Femi ya nutse cikin ofishin abokin huldar ta sa. Fayemi yana binsu daidaya da kallo, ya san ba wanda ya isa ya tambaye shi abinda yake faruwa, sun dai san shi ne shugaban bangaren kula da ma’‘aikata da ma daukarsu da duk wata hulda ta ma’aikatan (AZ IT). Kasancewarsa (Personnel Manager). Bayan abinda ya fi kama da dogin awanni biyu ne aka masu iso cikin ofishin, daya bayan daya suke shiga suna fitowa, kowa ya shiga ya fito, sai aga yana hada gumi, yana zare idanu. Gaba dayansu sai da suka gama shiga, sannan Zaid ya ce duka su koma cikin ofishinsa.
“Sorry for the inconvenience, kamar yadda ku ka sani gaba dayanku abubuwa sun yita faffaruwa cikin watannin da suka shige, abubuwa wanda suka janyo mana manyan asarori, amma Alhamdulillahi, an shawo kan matsalar, domin kamar yadda na fada maku duka a ciki, an samu wanda ya aikata wannan laifin.”
Shiru ya yi yana kallonsu, daya bayan daya. Adiyya ta sauke tagumin da ke fuskarta, ta dubi WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG Mai-gidanta kuma shugaban kamfaninsu. “An bi komai, an samu an turo Virus ne ta Imel daga komfutar Umm Adiiyya…” Ya nuna masu ita, gaba ki dayansu idanunsu ya yiwo waje, amma sun kasa hada idanu
da Adiyya domin ba su isa su tuhumi matar Oga a gaban Oga ba, amma zuKatansu
cike fal! Da wasi-wasi. Ayo ne ya ce, “Sir, anya ba kuskure kuwa?” Mr. Akim ya ce, “Amma ga-rin yaya?”
Teburin gefensa, ya kalla Stella ta yi wuf! ta mika masa abinda yake nema. Dagawa ya yi ya ce, “Kun gane wannan na waye?”
Komfutar (Laptop) ce a hannunsa. Gaba daya kallonsu ya koma kan Umm Adiyya wacce ta sadda kanta Kasa. Hasan ya ce “What!” Duka wurin ya karade da Kus-Kus. Zaid na kallonsu gaba daya.
“Don haka, bayan mun samu duka shaidun da suka dace, (AZ IT) ta sallami Umm Adiyya Zubair daga aiki, daga matsayin ma’aikaciyarta. Kamawa daga yanzu. Za a ci tararta, kuma wannan bayan hukuma ta yi zama an kiyasance barnar da ta janyowa
kamfani. Stella, karbi katin shaidar aikinta da sauran ababen da suke na kamfani.”” Ba wanda ya yi Kwakkwarar numfashi a cikinsu gaba daya, ciki kuwa har da Mr. Femi, bai taba zaton abinda Zaid zai yi ba kenan, a lokacin da ya kawo shawarar su WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
kira taron gaggawa, ya samu mai laifi, da ya san matarsa ce da laifin, da ya bada shawarar an warware a cikin lumana cikin sirri, idan ya so ya bada uzurin cewa, rashin lafiya ya matsa mata, ba za ta dawo aiki ba, amma hakan da ya yi sam, sai bai masa dadi ba, don haka jan Zaid gefe ya yi. Engr. Wane irin abu ka aikata haka? Lafiyarka kuwa?”
“Na gane waye mai laifin na gaske.” Zaid ya
fada cikin murmushin nasara, wanda ya Kara Kawata fuskarsa. “Me ka ke nufi? Ka na nufin ba Madam…” “Eh.” “To me ya sa?” “Za ka gani, da kansa zai fada ramin da ya tonawa kansa. Ka ba shi zuwa gobe…
No, he won’t last that long. Nan da awa biyu za ka ga koma waye ne.” Don haka Mr. Femi kam sai ya koma ya nade hannu yana zubawa sarautar Allah
idanu.

*************

Dago kansa ya yi daga kan abinda yake yi a kan teburinsa, yayi murmushi mai fadi, ya kalli agogonsa, Karfe biyu da minti talatin da takwas. “Ba laifi, wannan yana da hanzari, no wonder, ya iya WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG shammatan dukanmu cikin KanKanin lokaci.” “You’re two minutes early, I’ve been expecting you. Sit, Mr. Akim. (Ka shigo da gaggawa, kai na ke jira. Zauna Mr. Akim)

*******

BABI NA SHIRIN DA SHIDA

“Ni kuma Yallabai?” Zaid ya dan leKa saman kafadarsa zuwa bakin Kofa, alamar neman wani mai
shigowa, “Ina da tabbacin kai kadai ka shigo cikin ofishin ko? Ka san ina da kyamarar tsaro a nan, ba kowa a falon waje.” Ya fada yana nuna dan Talabijin din komfuta da ke fuskantarsa, Kirar kamfanin (Apple). Waya ya daga, “Stella, kar wani ya dame mu.” Mr. Akim ya gyara zama, sannan ya muskuta cikin kujerar da yake. Zaid ya kafe shi da idanu hade da harde hannayensa cikin juna a saman teburin nasa. “Ina saurarenka, me ya shigo da kai?” Har yanzu idanunsa masu tsirga jiki da sa mutum ya shiga taitayinsa suna kan Mr. Akim. “Uhm, Yallabai dama na zo ne batun matsalar nan, ni ina ga hukuncin da aka yi wa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *