TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 5 BY MANSUR USMAN (SUFI)
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
hallara a fadar babu , wanda yakai zulaibu yawan shekaru da kuma dadewa
akan karagar mulki, Sai da sarakuna biyar suka gabatar da harajin sannan aka iso kan sarki Abu-salimat, – Abu-salimat ya mike tsaye ni da gimbiya salimat muka_mara masa baya, dakaru na biye da mu dauke da akwatin dinare gami da kayan amfanin gona, har mu ka isa inda karagar mulKi take, muka zube Kasa muka kwashi gaisuwa_ ‘* muna masu sunkuyar da kawunan mu. .. Kawai sai wadansu ‘dakaru daban a fadar suka karbi wadannan akwatin dinare suka lissafa kuma suka bincike kayan gonar suka tabbatar da ingancin su sannan suka dauke suka fice daga fadar, . Ana cikin wannan hali ne.na dan saci kallon yarima . Hatmal ai kuwa sai na ga ya Kurawa gimbiya salimat idanu yana mai yi mata wani irin kallo daya sanya hantar cikina_ . ya kada, Ku ma tsoro ya kamani.
ZAMU TASHI
Domin kallon da naga Yarima Hatmal na yi mata kallo ne – ma nuna kamuwa da soyayya. . __ Jikina a sanyaye na mayar da kai na kasa, sannan sarki Husnalu ya Umarce mu da mu fice daga fadar, Cikin hanzar sarki sarki Abu-salimat ya mike tsaye muka rufa masa baya muka fice daga fadar Fitowar mu keda wuya sai muka fara shirye-shiryen komawa izuwa Kauyen Darul-Na‘am_Bayan‘an. kammala ne muka hau bisa dawakan mu muka fice daga kasar Baitul-sharhal muka nufi
hanyar da zata_sadamu da Kauyen Darul-Na’am, — – A wannan lokaci sarki Abu-salimat ne akan gaba tare da ’ wani hadimin sa mai suna Haimar suna hirarrakin su cikin nishadi, Ni da salimat muna hira irin ta masoya, ana cikin Www.bankinhausanovels.com.ng wannan – hali ne gimbiya salimat ta dube ni tace” ya masoyi na kuma – _ hasken rayuwa ta shin nayi maka watatambaya mana Cikin annurin fuska nace fadi tambayar ki ya abar kauna’ – Salimat tayi ajiyar zuciya ta ce ” shin a halin yanzu yaya ° matsayin soyayya ta yake a zuciyar ka? . – . Koda jin wannan tambaya sai na tuntsire da dariya na . dubi lasmirat nace ” shin kina kina tantama ne akan matsayinki araina kokuwa,A,a kawai ina so naji matsayi na ne
Salimat ta fada fuskar ta cike da annuri,. – Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi nayi a karo na biyu nace” Ai matsayin ki a waje na tamkar hanta da jini ne domin babu abin da zai raba tsakanin mu face mutuwa, a Salimat tayi murmushin jin dadi tace Ni kuwa ka zame mini tamkar numfashi a rayuwa ta, Nan take mu duka biyun muka fashe da dariyar farin ciki – Ana cikin wannan hali ne muka jiyo alamun takun sawaye a bayan mu, Cikin firgici muka ja linzamin dawakan ma muka tsaya koda muka wai ga sai muka yi arba da wadansu ZARATAN DAKARU masu matukar yawa Shirye cikin gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini daban tsoro, “Har mun yunkura zamu zare takubban mu sai sarki Abu
salimat yayi mana nunida mu dakata. Bisa lura da yayi cewa ba wasu bane-dakarun face na sarki Husnalu . Sannu a hankali dakarun suka iso har. izuwa inda muke suka yiwa dawakan su Turkiya, .
Sarki Abu-salimat ya dubi wani garjejen kato mai kirar ‘ samudawan farko wanda da alama shine shugaban dakarun yace dasshi” yakai muraizu shin wane saKo kuke tafe dashi izuwa gare mu ina fatan dai bamu sabawa mai ‘ girma Husnalu ba,
Sadauki muraizu ya bushe da dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aika masa da sakon mutuwa, – . Cikin Wata irin kakkausar murya yace” ya kai AbuSalimat. kayi sani cewa bakomai ne ke tafe da mu ba sai domin ka bamu yar ka salimat mu Kaita izuwa ga sarki saboda dan sa Yarima Hatmal ya kamu da soyayyar ta kuma yana so ne ya aure ta Cikin matukar kaduwa Www.bankinhausanovels.com.ng Abu-salimat ya dubi muraizu a lokacin da idanun sa suka zazzaro yace” shin wace irin. maganar hanza kake yi yakai muraizu anya kuwa a cikin. ~ hankalin ka kake kuwa? Muraizu ya bushe da dariyar mugunta har ya kusa fadowa daga kan dokin sa daga bisani ya hade rai yace”Tabbas garau nake nasan Abin da nake fada ina cikin hayyacina, A halin yanzu ba neman shawarar ka muke yi ba face zartar da umarnin mai girma Husnalu, a Koda jin wannan batu daga bakin muraizu sai na fusata. ainun na daka masa tsawa cikin matukar fushi na dube__ nace ” karyar ka tasha karya yakai wannan. la‘ananne kuma BAKIN AZZALUMI kayi sani.cewa karyarka tasha karya baza mu taba lamunta da wannan magana taka ba, Kafin na gama rufe bakina sadauki muraizu ya fusata ainun ya zaro kibbau guda biyar a gadon bayan sa ya ya sakawa a cikin bakan sa yaja ya dame cikin wani irin zafin nama ya harba kibban Kafin daya daga cikin mu yayi wani yunkuri kibiyoyin -guda biyar sun sauka a kan wadansu jama’ar mu mutum biyar sun fadi kasa matattu _ a ‘ Mutum biyar din sun kasance dattijawa kuma manyan yan majalisar sarki da muke matukar alfahari.dasu a cikin Kauyen Darul-Na’am Koda sarki Abu-salimat yayi arba da gawarwakin yan majalisar tasa sai hawayen takaici da bakin ciki suka zubo masa, -a ‘Lokacin da saurayi yaslir yazo daidai-nan a labarin sa sai hawaye suka zubo daga idanun sa, . Al’amarin da ya sanya sarauniya lasmirat ta kamu da matukar tausayin sa kenan. -Har.ta budi baki da nufin tace wani abu sai kawai suka ga__ sararin samaniya yayi dubu dundim Cikin matukar firgici lasmirat-da saurayi yaslir suka mike tsaye zumbur suka ruga izuwa wajen‘turakar, suna fita suka ci karo da Sarkin yaKi, °Sarkin yaki ya dubesu cikin tashin hankali yace ” ya shugabata muna cikin gudanar da ayyukan mu na tsaron kofa kawai sai mu kayi arba da wata gibgegiyar halitta mai matukar muni daban tsoro tana ta hallaka mutane, Ya shugabata na rantse da karfin mulkin ki babu wata halitta da zata tsira da ga sharrin halittar,
Kafin Sarkin yaki -yagama rufe bakin sa sarauniya lasmirat ta tari numfashin sa tace” A yi maza aje a busa Kahon yaki, Batare da lasmirat ta jira Sarkin yaki ya furta wani abu ba ta shige gaba yaslir._ya mara mata baya yana mai dogare da . sandar Sa A can cikin gari kuwa halittar ta wanzu tana ta hallakamutane jama‘a suna ta guje-guje da ifice-ifice domin tsira. ‘ darayukansu, , Duk inda halittar ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin ° . . Jama’a birjik kwance a Kasa cikin jini, ~ A wasu lokutan ma sai kaga halittar ta sanya hannun ta ta yaye rufin daki ta dauko mutum ya na ihu ta sanya a bakin ta ta laKume tayi loma daya dashi, . “Ana cikin wannan hali ne sai aka hango sarauniya lasmirat . da saurayi sun rugo wajen a bisa dawakai cikin gagarumar ~ shigar yaKi suka tsaya cak, — . Kawai sai’lasmirat ta Www.bankinhausanovels.com.ng dakawa halittar tsawa, Koda halittar taji an dakama tsawa sai ta tsaya cak a waje ~ guda Kurawa su lasmirat idanu tana mai nazarin su, ‘Ita dai wannan halitta takasance,shirgegiyar aljani mai _ matukar tsawo,muni,gami da ban tsoro, . Dan Babu wata halitta da zata yi arba da wannan aljanar face’ firgici, Saboda matukar munin ta Duk irin dakewar zuciya irin ta lasmirat da saurayi yaslir Sai da tsoro ya darsu a zukatan su, Dakarun dake bayan su kuwa sai jikin su yakama kyarma yana tsuma tamkar ace kyat su cika wandon su da iska Saboda tsananin tsoro,Sai da aka shafe tsawon dakika talatin a cikin wannan hali ; ana kallon kallo . Daga can sai aljanar ta bushe da dariyar wanda ta haddasa . girgizar kasa, Nan fa bishiyoyi suka dunga karairayewa suna zube Kasa, ‘gida je su ka dunga rushewa suna hallaka, Kasa tana ‘ ” – tsagewa dawakai da mahayan su suna_rufta wa cikin ta, . Tuni mazaje,mata, tsofaffi gami da yara ya cika dodon . kunne, Sa,adda sarauniya lasmirat taga yadda jama’ar ta ke hallaka sai ta cika da tsananin bakin ciki maral musaltuwa, Cikin fushi ta sake dakawa aljanar tsawa-a karo na biyu ; tana mai cewa “yake wannan shu’umar aljana yau dubunki ta cika idan har kin isa ki fito muyi fito-na fito na rantse da ° _ karagar mulki na saina ga bayan Ki, Koda jin wannan batu sai aljanar ta tsuke bakinta komai ya samu dai dai tuwa bishiyoyi suka daina Www.bankinhausanovels.com.ng karyewa duwatsu suka daina fashewa kasa ta dai na tsagewa, Aljanar ta bude.bakin ta wanda yafi kama da kofar . gari cikin murya mai ban-tsoro tamkar saukar aradu tace”yake wannan sarauniya kiyi sani cewa bakomai ne ya kawo ni wannan birni naki ba sai domin na kashe mutanen birnin ki kuma na mallake ki saboda wata muhimmiyar bukata ta, Kafin aljanar ta gama rufe bakin ta saurayi yaslir ya tari numfashin ta yana mai -daka mata tsawa cikin fushi yace”yake rafkananniyar .aljana kuma yar tsakuwa a cikin jerin JARUMAN DUNIYA, kiyi sani cewa karyar ki tasha . karya ina mai tabbatar miki dacewa bazaki tsira daga sharrin mu ba, ‘ _ Sai ki shirya ka maza nan bisa kanki, _ Yana gama fadin hakan ya sakarwa dokin sa linzami yana . . mai gyara rikon sandar sa cikin hanzari lasmirat ta mara masa baya tana mai daga takobin ta sama, – . . – Sauran dakaru mutum dubu arba’in sukayi koyi dasu Ana haduwa aka kacame da azababban yaki mai matukar tayar da hankali Domin kafin a hadu sai da aljanar ta sanya hannu ta ta _debi dakaru mutum hamsin har da dawakan su ta watsa a ; . . bakin ta ta taunesu tayikalacidasu,. . -Sannan ta afkawa su lasmirat.‘Lokacin da aka WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG “kacame da azababban yafi tsakanin __ Shu’umar aljana da su sarauniya lasmirat, . , Sai lasmirat da yaslir suka wanzu suna kaiwa aljanar sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA _Duk sa’adda makaman su suka sauka a jikin aljanar . *‘ §ai kaji-sun bada kara Kal Kal !! Tamakar karfe suka . Sara . In banda lasmirat da yaslir suna cikin kariyar tsafi da tuni sun hallaka, “Idan aljanar ta kaiwa yaslir da lasmirat hari da . hannayen ta, idan suka goce duk abin da-hannun ta ya Sauka akai sai dai kaga ya tarwatse,idan kuwa a Kasa ne sai ya haddasa wani rami mai zurfin gaske, Take dakaru da dawakan su zasu afka cikin sa suna ihu da kururuwar neman taimako, Nan fa waje ya cika da ihun mazaje mata da yara da matasa, – ; Karafniyar Karafa ta cika dodon kunne, JINI DA KASA suka cakudu, Kura ta turnuKe sararin samaniya, Lokacin da aka shafe dakika dari biyu da sittin ana wannan bakin gumurzu,-
Sai ya zama na cewa aljanar ta samu nasarar hallaka * dakaru Fiye da dubu shida, -Amma bata samu nasarar koda lakutar jikin-su lasmirat ba sai ta cika da matukar mamaki kuma ta fusata ainun,
Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta hadu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan nasara Kasanta darajar ta ne da kimar ta, Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon fadanta yazamana cewa tana hada kai bugu da naushin hannu
da Kafa, .
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG