DR MUHSEEN CHAPTER 7 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 7 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

         📝………………Bayan wasu shekaru Allah ya Kara ba Ummeey ciki,Wanda ya Kara haddasa kiyayya tsakaninta da Hajiya Mariya domin karara take nuna batasan cikin dake jikin Ummeey.

Amma da yake Ummeey ma’abuciyar hakurice sai bata damuba,illa dagewa da tayi tana Kara neman tsari daga makircin Hajiya Mariya.

Lokacin da cikinta ya isa haihuwa ta haifo santaleliyar diyarta mai kama da Muhseen,ranar suna aka radamata Lailah.

Sosai Muhseen yake kaunar Lailah dukda lokacin Yana karatu a Sudan a shekarar shi ta farko kenan.

Tun Muhseen yana yaro ya riga daya fahimci Hajiya Mariya da mahaifiyarta Balaraba basu kaunar wannan family nasu,tundaga lokacin ya saka buri a ranshi na yanaso ya zama soja .

Haka ya dauki Karan tsana ya dorawa Ameerah dan tun farkon zuwanta gidan yake bala’in kaunar Muhseen,shiko gano hakan da yayi yasa yake Kara tsanarta Wanda kowa dake cikin wannan estate yasan da tsanar da yake yimata.

Ameerah tasha sanar da Hajiya Mariya ita dai tana kaunar Muhseen ta taimaka Mata dan ganin ta aure shi.

Haka Hajiya Mariya zata kontar Mata da hankali akan komai runtsi komai wahala saita mallaki Zuciyar Muhseen.Haka yasa Ameerah take jin kanta Yana Kara girma,Dan tasan inharta mallaki Muhseen to ta kerema kawayenta a komai,domin Muhseen miji ne na nunama sa’a.

   Tun bayan Muhseen ya kammala karatun shi na secondary School anan wata pravet dake cikin garin katsina.sai Alhaji Muhammad ya nema mai Admition a University of Sudan, Makaranta ce da take tafe da tsarin addinin Musulimci,sannan Kuma ga tsantsar ilimin tsamani.a bisa Alfarmar da Hajiya Aishatu ta nema na abata Muhseen ya zauna tare da su har zuwa lokacin da zai kammala digreen shi na farko.haka kuwa akayi abinka ga masu abu dandanan cikin lokaci kalilan aka kammala komai Muhseen ya daga Kasar Sudan inda zai fara karantar fannin theater,Amma a kasan zuciyar shi ra’ayin aikin soja ne a ranshi.

Haka duk matasan gidan suka dukufa a fannin  karatun addini dana zamani,domin Hausawa nacewa ilimi gishirin zaman duniya.

Muhseen hankalin shi konce a kasar Sudan karatu yake yi babu kama hannun yaro.Dukda yana fuskantar tsangwama daga bangaren Gimbiya Zulaihat Amma hakan baisa yayi wasa da damar sa ba.dan gimbiya Zulaihat akwai wulakanci ,shima sarki Abdulkareem zaman hakuri yake da ita,bayan ka kammala digreen sa inda dakyar su Hajiya Aishatu da sarki Abdulkareem suka bar Muhseen ya dawo kasar shi ta haihuwa.Domin ranar da zasu karasa karatunsu saida Yan Nigeria Suka je,kama daga Dadyn shi da Ummeey, Jabeer da Faruk da kanwar shi Lailah.Bayan sun je aka Sha hidimar yaye dalibai kafin Suka tarkato suka dawo gida Nageria.

    Bayan dawowar shi da wasu watanni results dinsu ya fito haka ya amso,sosai result yayi kyau.anan ya nunama Dadyn shi ra’ayin shi nasan zama sojan sama.da farko Abba ya nuna rashin amincewa,Amma ganin yadda Hajiya Kaka ta cije akan ya barshi yayi yasa ya hakura.

        Watanni tara Suka dauka a Kaduna suna gudanar da treaning,wani lokacin Muhseen sai yayi kamar zai gudo saboda tsabar wahalar da ake basu,Amma idan ya da burin shi sai yaji zai iya jure kowace irin wahala ce.

  Cikin ikon Allah bayan dawowar su Muhseen da wasu watanni,aka fito da list na wadanda Suka sami aikin soja.sunan Muhseen shi ne a farko.sosai yayi farinciki har bazai misaltu ba.

Farkon fara aikinshi Abuja aka kai,shi kafin daga baya a shekarar 2017 bayan an kammala gina bareak ta Daura aka dawo da wasu nan cikinsu kuwa harda Muhseen.

        *BACK TO STORY*

       Tunda Muhseen ya figi motar shi a guje yabi ta gaban su Faruk da yake rike da hannun Seeyerma Yana faman rarrashinta.ganin irin gudun da yake yi yasa hankalin Faruk ya Kara tashi Dan yasan an tabo soja,tunda yaga bai tanka ba yasan ranshi yayi mugun baci.faruk a zuciyar shi ya ce “tabbas akwai matsala dan idan har Ameerah tayi gigin zama da Muhseen to wataran Yana iya hallakata.suna shiga part din Hajiya Kaka ya zaunar da Seeyerma saman kujera Yana sharemata guntun hawayen dake saman fuskarta.

    Wayar shi ya ciro daga aljihunshi ya fara kokarin Kiran wayar Dr muhseen.jin ance a kashe take yasa yayi saurin duban inda Hajiya Kaka take zaune tana Jan casbaha.

Itama dubanshi tayi ta girgizamai Kai.

Shiru yayi Yana tunanin irin matsalar da take kunno kai a wannan ahali nasu.

Shiko Muhseen tunda ya haura da motar shi saman titin unguwar kwado yayi saurin kashe wayar shi.dan yasan tunda Faruk yaga fitar shi to ba makawa saiya Kira wayar shi.

Derect gidan su abokinshi ya nufa Lameer ya nufa.

Da sauri yake faman Danna horn Wanda ya saka mai gadin saurin bude gate din ba tare daya shirya ba.ganin Abokin Lameer ne yasa ya daga mai hannu,shiko gogan naka baisan ko Yana yiba ya danna hancin motar cikin farfajiyar gidan.koda ya bude da sauri ya nufi part din lameer saboda jin wani zazzafan zazzabi Yana neman rufeshi,cikin dauriya yake ya kamo lebenshi na kasa Yana taunashi da karfi dukdan ya samu sassauci,Amma ina.

Ko knowking bai tsaya yiba ya shiga.

    Baya falo dan haka ya wuce bedroom,ganin Yana kallo a system yasa ya fada bisa gadon Yana mayar da numfashi,Dan saboda bacin rai ya manta ashe ko murfin motar bai rufe ba.

       Ta kasan ido Lamerr ya kalleshi Yana jin wata dariya tana kamashi.dukda baisan damuwar abokin nashi ba,Amma Yana bukatar taimako.

Jinjina kanshi yayi Yana addu’ar Allah ya toni asirin masu hada munaficci a cikin wannan family.

Ruwan gora ya dauko masu sanyi ya mikamai.

      A hankali ya amsa Yana mikewa zaune.saida ya jingina da jikin gadon kafin ya bude murfin robar,tinda ya kafa Kai saida ya shanye tas kafin ya collar da emptyn goran Yana dafe kanshi jin yadda yake saramai kamar zai fita daga jikin shi.

      “Haba my Friend ka natsu mana,kaifa soja ne,duk soja kuwa ansanshi da juriya,kada fa kasa na hanaka auren Seeyerma”

Yana danne dariyar shi Dan yasan ya taboma kanshi masifa.

     Dakyar ya bude kwayar idonshi yana yima Lameer kallon kasan ido.

   “Mtsssssss banza Kaine Dan akuya dakaga mace sai kahau mazari kamar kaga nama,Ni kasan wannan kwailar yarinyar bazata iya daukata ba,Kai wallahi wacce ta fitama zan iya ballata ballantana ita,mtsssss”ya Kara Jan tsaki Yana kokwakarin konciya.

      Sosai Lameer ya saka dariya saida ya dara sosai jin maganar da Muhseen yayi, kafin ya ce “wallahi ni haryanzu banga dan ‘iska irinka ba,ehee Naga Kai rashin akuyancin ne yasa kake kasa iya control din kanka sai kayi ta faman taune lebe kaman wani tsohon maye,Ni wallahi duk wacce tsautsayi yasa ta aureka to kawai tasan ta zama sorry”.

      Cikin takaici da jin haushi Muhseen yakaima Lameer naushi a jikin hannun,Amma Lamerr yayi saurin kocewa Yana cigaba da dariya.

Da gudu ya biyo shi,ganin ya nufi falo yasa ya kyaleshi.

Dakin ya dawo ya sakama kofar key ya cire rigar jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando da singlet ya konta Yana tunanin tun ranar daya fara ganin Seeyerma da zuwa ranar data dawo estate dinsu da zama,baya da wasu shekaru da bazasu gaza biyar ba.

       Wata rana ne Muhseen ya zo hutu suna hira da Kaka Yana Kara bata labarin Sudan da gidan mai martaba sarki Abdulkareem da yadda Hajiya Aishatu take kula da shi.

Sosai ya mayar da hankalin shi ga Hajiya Kaka ya ce “Inaso na fadamaki wata magana,Amma Ina jin tsoro domin nidai a iya sanina Dady ya taba sanar da ni Baku da family a Sudan,shima aiki ne ya kaishi harya auro Ummeey”.

        Kaka cikin kula da jikan nata ta fahimci da gaske yake wannan maganar,Dan haka itama ta mayar da hankalinta gareshi kafin ta ce “maigidana ko wasu ka gani masu kama da wannan Family shiyasa kake wannan maganar”

    Saida ya kontar da kanshi bisa cinyar kakar tasu kafin ya lumshe idon shi tamkar mai son tuno da wani abu ya ce “Kaka idan har idona ba gizo yayiman ba to tabbas naga wata yarinya mai kama da Aunty Aliya sosai,kullum idan za’a kaini school sai naga yarinyar itama Driver ya kawota school dinsu saboda ba nisa a tsakaninmu da su,Amma idan na sanar da Aunty Aliya sai ta ce ba kowa kawai kamanni ne na Dan Adam,Barima kiga na nunamaki hoton dana saka aka  daukoman na yarinyar ba tare data sani ba”Yana kokarin binciko hoton daga cikin wayarshi.

            Mikamata wayar yayi Yana cewa “kinganta ko?wallahi ranar dana fara ganinta sai Naga kamar Lailah ce,Amma ta dan dara lailah hasken fata”

    Amsar wayar tayi tana dubawa,cikin razani da tsoro ta zabura tare da ture Muhseen daga saman cinyarta tayi saurin cewa…………cikin razani da tsoro ta zabura tare da ture Muhseen daga saman cinyarta tayi saurin cewa 

“Maigidana wannan ai jini na ce,tabbas duk inda wannan yarinyar ta fito ahalina ce”
Kara kallonta Muhseen yayi ganin yadda duk ta rude.
Hoton take kallo dan ganin yadda yarinyar take kama da fatimarta sak kamar an tsaga Kara.
       “Amma Kaka meyakai yan’uwan ki wata kasa”
  Mikamashi wayar tayi tana goge hawayen da suke kokarin zubowa daga saman fuskarta,dafa shi tayi kafin ta ce 
“Ka koramin mahaifin ka yanzu,inason ganin shi”.
       Da gaggawa ya latsa nomber Dadyn shi .
Jin ta kusan tsinkewa ba’ayi picking ba yasa ya cewa Hajiya Kaka “Kinga bai dauka Kiran ba,inaga aiki yake yi a office”
     Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ya Kara Kiran Dadyn nashi a karo na biyu,ganin kamar tsohuwar hankalin ta baya a jikinta.
      Yana jin yayi picking yayi saurin gaishe da shi Yana sanar da sakon Hajiya Kaka.
      Da gaggawa ya amsa da gashi nan tahowa Dan amsa Kiran gaggawa da mahaifiyar tashi tayi mai.
        Bayan zuwan shi ta sanar da shi abinda ya faru tare da nunamai hoton yarinyar.
    “Lallai wannan al’amarin da daure Kai yake,to amma koma meye mubi a hankali zamu gano bakin zaren,Amma Hajiya ni gani nake yi kamar kawai kamanni ne domin ance kowanne dan’adam a rayuwa akwai masu kama da shi a duniya gida bakwai”cewar Alhaji Muhammad.
      Cikin jimami Kaka tace “A a muhammadu inaji a jikina akwai abin farincikin da yake shirin riskarmu,Amma Ina ji a jikina wannan yarinyar jini na ce,Dan haka cikin satin nan a shirya mana tafiya zuwa kasar Sudan kafin nan a sanar da sarki Abdulkareem zuwan mu”
       Jinjina Kai Alhaji Muhammad yayi Yana cewa “to insha Allah za’ayi yadda kika ce,da mutum nawa za’a tafi?”
     “Ka shiryamana tafiyar mutum ukku,nida Maigida sai Yusufa,A sanar da shi saboda Kai Naga ayyuka sunyimaka yawa”
    Da haka ya amsa kafin ya fita.
   Bayan fitar shi Muhseen da yake zaune aka tattauna komai ya ce “to Kaka idan mukaje ba familyn mune ba hakan Yana nufin zamu dawo haka nan kenan?to nidai Koda bamu sansu ba Dan Allah ki rokamana Alfarmar su bamu ita ta zauna tare da mu,wallahi Ina kaunar yarinyar”.
      Jin abinda ya ce yasaka Kaka kallonshi tana murmushi,Dan tasan zuwan Muhseen duniya zai zamewa ahalinta akhairi.
      cikin week din Suka daga Kasar Sudan,kwanan su daya a gidan su sarki Abdulkareem a washe gari suka nufi school din su yarinyar.
     Cikin ikon Allah suna karasowa bakin gate din itama yarinyar drivern ta ya sauketa a bakin gate din.
     Hajiya Kaka tana bayan mota a zaune ta hango kyakkyawar yarinyar ta nufi cikin school din.jinjina Kai tayi tana jin wasu hawayen farinciki.
    Da sauri ta ce driver ya bi bayan motar daya kawo yarinyar.
     Haka sukayi ta bin motar ba tare da sun Bari ya gansu ba.
     Gani sukayi an wangale mai wani tangameman gate Wanda duk jikinshi glass ne,sosai suke kallon gidan ganin irin tsaruwar da yayi tundaga waje kenan.
      Bayan sunga shigewar motar Hajiya Kaka ta fito daga cikin motar,Suma Uncle Yusuf da Muhseen fitowa suka yi suna nufar bakin gate din.
  Daga ciki mai gadin gidan ya hangosu,yayi saurin tasowa.
Fitowa yayi Yana kallon su ganin kama suke yi da Yan kasar, Amma shigarsu ta nuna ba yan kasar ne ba.
      Cikin yaren larabci mai gadin ya tambaye su daga Ina suke?Kuma wa suke nema?.
       Muhseen ya bashi amsa kamar yadda ya bukata.
Balaraben baiyi mamaki ba jin yayi yarensu Dan kamaninin su ya nuna suna da alaka da masu gidan.sosai ya Kara kallon Muhseen ganin Yana kama da yarinyar masu gidan.
       Cikin gidan ya koma ya sanar da masu gidan cewar ga wasu sunzo daga Nageria suna bukatar a basu izinin shigowa.
      A tare suka shiga cikin gidan da mai gadin.
     Tun daga farfajiyar gidan zaka san an narka dukiya a wurin.kama daga parking lot, swimming pool,ga lambu mai girma da shukoki kayan marmari masu kyau.
A kalla motocin dake wurin parking sun Kai guda biyar kowacce ta amsa sunanta saboda kyau da tsada.
       A jikin kofar falon suka tsaya har saida door din tayi screening dinsu kafin ta bude da kanta.
     Cikin yaren larabci balaraben ya ce su shiga.
       Masha Allah shi ne abinda Uncle Yusuf ya ce saboda wani kanshi da sanyi daya ratsa jikinsu.kanshin turaren larabawa yake ta yawo a cikin  falon.
   Bisa manyan kujerun suka yima kansu masauki suna Kara kallon tsaruwar falon.suma sunsan suna da dukiya Amma wannan sun hauresu.
     Ta saman step din suka ji alamar motsin tahowa,kusan duk a tare suka kalli wurin.
Tunda suka taho Hajiya Kaka idonta Yana Kan mutanen ko kiftawa bata yi,dan gani take data yi kuskuren rufe idonta to zasu bacemata.
         Haka itama matar da suke kokarin saukowa hannunta na sarke cikin na mijinta,sai faman murmushi suke yi.
            Zumbur Hajiya Kaka tayi tana nunata da yatsa.cikin kakkarwa da in’ina  tace “Fatima ke….ce?tab. bas.. yau mafalki na ya zama gas…kiya,Alhamdlillah ala kullu halin”tana rungumota.
     Uncle Yusuf, Muhseen,da mai gidan Fatima tsaye sukayi suna kallon ikon Allah.domin abin ya daure masu Kai.
       Tabata ta rinkayi tana Kara nanata kalmar “tabbas wannan diyata ce,Fatima kin ganeni ko?Ni ce  Hajiya Kaka mahaifiyar ku,Kinga wannan yayanki ne Yusufa”tana nuna Uncle Yusuf da yayi sororo,shima suffar Fatima yake gani a gaban shi.
   Gani sukayi matar ta fashe da kuka tana Kara rungume Hajiya kaka.cikin yaren larabci ta ce “tabbatas kece mahaifyata,Allah abin godiya,Ashe da rabon zamu Kara ganawa Inada raina”
   Bayan sun dan lafa da kukan,kowa ya zauna sosai Hajiya Kaka bakinta yaki rufuwa saboda farincikin ganin wannan rana.
     Cikin girmamawa Mijin ta ya gaishe da su duk a cikin yaren turanci.
     Abinci da abin sha aka gabatar masu.harzuwa wannan lokacin Fatima tana like da Hajiya Kaka.
     Tunkafin su baro gidan suka sanar da sarki Abdulkareem abinda ya faru,shima sosai ya tayasu farinciki. 
     A haka suka rabu,bayan sun koma gidan sarki Abdulkareem suka yima Hajiya Aishatu bayanin abinda ya kawo su,da gano diyarta da tayi.
Amma abinda yafi daurema Hajiya Kaka Kai shi ne “Bayan an gane Fatima ta rasu aka kaita gidanta na gaskiya to meya faru a wannan lokacin?bata da Wanda zaya bata wannan amsar sai Fatima da ita ce abin ya faru a kanta.
Domin Saifudden ya fara rasuwa sanardin shan wani zobo da yayi Wanda an tabbatar daga part din Hajiya Mariya ya samo shi,domin Yana zuwa part dinta yayi hira harma yaci abinci.to a ranar baisha zobon a part dinta ba ya taho da shi part din Hajiya Kaka.
         Tun bayan ya sha bai Kara samun lafiya ba,har saida rai yayi halinshi.koda ya rasu Alhaji Abubakar yaso an gwada shi domin gano sanadin mutuwar,Amma Hajiya Kaka ta hana saboda gudun fitina.
     A wannan ranar cikin farinciki Hajiya Kaka tayi bacci,haka a bangaren Fatima Wanda saida mijinta yaga canji a ranar saboda irin kulawar daya samu.koda bayan Diyarta andaukota daga school ta sanar da ita bayyanar iyayenta na Nigeria itama taji dadi Dan tanaso watarana taje Nageria.
     Haka sarki Abdulkareem ya hada tawagarshi da su Hajiya Kaka suka dunguma zuwa  gidan su Fatima.
      sosai Jalaludden Mijin Fatima yayi mamakin ganin sarkin a gidan shi,Kuma abokin Baban shi.
    Bayan gaisuwa da aka karayi anan Fatima ta basu labarin abinda ya faru bayan an kaita makabarta.
Cikin zubar da Hawaye ta ce “Doguwar sumace nayi wacce ta hada da maganin gushewar numfashin da aka bani nasha Wanda yake dauke da tsawon awanni biyar kafin na farka,bayan farkawata na ji an daddaure ni da igiya ga wani daki mai duhu da aka saka ni,nasan nidai ba mutuwa nayi ba Amma saboda duhu bani iya ganin komai”tsagaitawa tayi saida ta goge hawayen da suke zubowa daga idonta kafin ta ci gaba da cewa “wata magana naji daga bayana wacce na tabbatar da cewa ba muryar mutum ba ce,Yana cewa “zan taimake ki Amma bisa sharadin zan kaiki wani gida to akwai wani saurayi a gidan ana Kiran shi da Abduljalal to shi nake so ki amince da auren sa daga lokacin daya nuna Yana sanki”
      ” A lokacin Ina matukar bukatar taimako Dan haka na amince,bayan yace na rufe idona daga nan ban Kara sanin a inda nake ba sai ganina nayi a gidan su Abduljalal “ta karashe maganar cikin kuka tare da nuna Abduljalal Wanda shi ne mijinta.
    Suna cikin wannan tattaunawar yarinyar ta shigo falon da gudu tana Kiran Abi na ka fito na dawo.ganin falon da tayi cike da mutane yasa tayi turus tana kallon su.
Cikin kulawa  Muhseen ya mikama yarinyar hannu alamar ta zo gurinshi.Aiko kamar ta sani ganin mutanen suna kama da Ummeeyn ta.
Da sauri taje tana gaishe da su cikin yaran larabci.
     Muhseen da sarki Abdulkareem kadai suka amsa saboda su kadai suka ji me ta ce.
    A takaice ranar da Seeyerma suka koma gidan sarki Abdulkareem dan sosai ta saka rigima akan saita bisu Nageria,Daman  tana ajin karshe a primary school.dan haka da amincewar iyayenta Suka taho da ita Nageria.
To wannan shi ne sanadin zuwan Seeyerma kasarmu Nageria.
     Cikin bacci Muhseen ya ji Lameer yana tayar da shi.cike da jin haushi ya tashi,A lokacin har sallar magriba ake Kira.alwala sukayi suka fice daga gidan a motar Muhseen dan zuwa masallaci……….¹⁵

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *