TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 6 BY MANSUR USMAN (SUFI)
Www.bankinhausanovels.com.ng
Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta hadu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan nasara Kasanta darajar ta ne da kimar ta, Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon fadanta yazamana cewa tana hada kai bugu da naushin hannu
da Kafa, .
Ai kuwa nan take labari yasha Bambam, domin a halin yanzu dakyar su yaslir ke iya mayar da martani . Idan ta daki gini ya tarwatse sai kaga duwatsun sun yiwa su lasmirat lugudan duka,_ . . . Sai da aka shafe tsawon dakika dari da doriya ana wannan fafatawa, . Ana cikin wannan yaki ne aljanar ta kaiwa sarauniya lasmirat da yaslir wawan naushi da nufin yi musu farat . daya, -Amma kafin hannun ta yakai gare su sai suka daka tsallea_ . sama tamkar an harbosu daga cikin. baka
suka bar kan ; dawakan su Sai gashi hannun ya sauka akan dawakan sun Www.bankinhausanovels.com.ng tarwatse – _° tamakar an talitse tumatir, daidai wannan lokaci ne yaslir.da lasmirat suka sauka akan aljanar bisa tsakiyar kanta su shiga kafta mata sara babu sassauci, ” Nan fa yazamana sun riki-ta aljanar yazamana cewa ta daina kaiwa dakaru hari —_ Sai dai KoKarin taga ta jefo su yaslir daga kan ta, ana cikin wannan hali ne aljanar ta samu nasarar damKo su yaslir ta -hannun ta ta matse su nan take suka sume sakamakon , ° makurewar,. ‘Ashe ta samu nasarar karya dan yatsan yaslir, lasmirat kuma ta samu gocewar Kashi, a hannun ta, Koda samun wannan gagarumar nasara sai aljanar ta bushe da shu’umar dariya. Tayi dariyar ta ishe ta sannan ta tsuke bakin ta . Saiita juya ta nufi kofar fita daga birnin tana mai kanta gami da yiwa kanta kirari, tana mai cewa ” Saini GAWURTACCIYA uwar hatsabibai, . GUGUWAR YAKI nake mai share MAYAKA, ANNOBA DARI nake duk wanda ya Kusan ceni. Zai’. bakun ci barzahu, Nine gagararriya uwar gagararru, So Haka ta cigaba da yiwa kanta kirarin tana lafiya a cikin birnin, , Duk sa’adda ta ajiye kafarta daya sai dai kaga Kasa tana ‘girgiza tamkar zata tsage abin da ke saman ta ya fada cikin ta . , ‘Koda sauran Www.bankinhausanovels.com.ng dakarun suka ga abin da yafaru sai suka ° dunga dame kwari da bakan’su suna Harbin aljanar–. Duk tsananin yawan kibban sai yazamana a banza domin ko gezau batayi ba , Sai dai ma kaga ta sanya -hannun ta daya tana karkade kibiyoyin kamar tana kade ganyayyakin bishiya, Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji aljanar ta kurma wawan ihu kuma ta fadi Kasa tim, Ta saki su sarauniya lasmirat suka fado Kasa babu alamun rai a tare dasu, Kuma akaga aljanar ta daga hannayen ta sama tana mai roKon gafara, . Al’amarin da yayi matukar bawa dakarun mamaki kenan, suka rugo izuwa wajen domin su ga abin da ke wakana, – . Su na isowa sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya, . Ai kuwa sai su kayi arba da wata kyakkyawar budurwa, Budurwur takasance dogowa mai matsakaicin kaurin jiki, cikin ta ashafe yake tamkar bata cin komai ba, ‘Kuma a tsuke yake daga Kasa, Kugunta mai fadi ne yayi tudu sosai, gashin kanta mai tsawo ne ya zuba har izuwa _ kan_kafadun ta bai ne sidik tamakar gilashi, a jikin ta – tana sanye da tufafi irin na mutanen birnin sun, Kanta daure da bakin rawani idanun ta kadai ake gani, . A sannanne dakarun suka fahimci cewa wannan bakuwar . budurwa ce ta ceci rayuwar su sarauniya lasmirat,Bakuwar budurwar ta nuna aljanar da dan yatsan ta na. hagu take aljanar ta Kame, tamakar gunki, komai na jikin ta ya daina motsi, an . Faruwar hakan keda wuya sai: budurwur ta taka da Kafafuwan ta izuwa inda su yaslir ke kwance, Kawai sai ta bude bakin ta ta karanto wadansu kalamai da ita kadai tasan me take fada,
Tana gama rufe bakin ta sai aka ga sarauniya lasmirat da saurayi yaslir sun mike tsaye zumbur tamakar babu wani abudayasamesu. ° . ‘ Kafin wani daga cikin su yace uffan, budurwar ta sake. nuna.aljanar.a karo na biyu da dan yatsan ta,take ruhin_ . aljanar ya dawo jikin ta, komai nata yana yin motsi, Budurwur ta budi baki cikin wata irin zazzakar murya tamkar ana busa sarewa tace” yake wannan ALZALUMA kiyi sani cewa na yarda zan barki Lafiya kici gaba da , © rayuwa amma. bisa sharadin cewa za ki dai na zaluntar ~ . al‘umma,
. Cikin ladabi da kan-Kan da kai aljanar tace Muryar ta na rawa saboda tsoro” Na amince ya shugabata na daukar miki alkawarin cewa bazan kara cutar da wata halitta har abada, Koda jin wannan batu sai budurwur.tayi wa aljanar nuni datatafi, : Cikin Www.bankinhausanovels.com.ng hanzari aljanar ta mike tsaye ta bude manyan fuka. fukan ta tashi zuwa sararin samaniya tana mai keta .gajimare cikin tsananin gudu keta Sa’a ta bace, Nan fa gaba daya jama’ar dake ‘wajen suka cika da matukar mamaki maral musaltuwa, _ _Abu na farko da ya basu mamaki shi ne yadda ta ceto rayuwar su sarauniya lasmirat kuma suka warke sumull, Abin da yafi basu mamaki kuma ya daure musu kai shi ne yadda bakuwar budurwar take sarrafa aljanar tamakar tana juya waina (masa) a tanda,
* A bangaren sarauniya lasmirat kuwa, mamaki ne ya cika zuciyar ta ta kasa cewa uffan, Yaslir kuwa yafi kowa mamaki domin ko a mafarki bai taba ganin ya mace mai baiwar sarrafa irin wadannan aljanu ba; Kawai sai ya Kurawa budurwur idanu yana nazarin ta, duk da kasancewar fuskar budurwur na rufe da rawani amma idanun ta kadai yaslir ya kalla ya fahimci cewa ta nunka sarauniya lasmirat a kyawyn sura, Lasmirat da yaslir suka taka da kafafuwan su izuwa inda _ budurwur take tsaye, suka risina da kawunan su kasa domin girmama wa agare ta, Sannan lasmirat ta ta dube ta cikin murmushi mai taushi tace”yake wannan basadaukiya mace mai kamar maza ; shin mene ne labarin ki? Menene. kuma dalilin da ya sanya kika ceci rayuwar mu.ni da jama’‘ar birni na?. Koda .jin wadannan’ tambayoyi sai budurwur tayi shiru . tana mai nazari, _ Daga can ‘sai ta dago da kanta ta dubi yaslir, lasmirat-tace cikin tattausar murya ‘* Da farko dai suna na Sunaila na fito daga cikin wata nahiya da ake yiwa lakabi da Haurul-zamras, Abin da ya baro dani daga birnin mu shi ne domin na sadu da wadansu irin mutane da ake yiwa lakabi da musulmi, Babban burina shi ne na sadu da su’kuma na karbi : Addinin su domin na samu nasarar daukar fansa ; akan azzalumin sarki da-ya rusa mini farin cikin _ rayuwa ta, -‘Wannan nasara da kuka ga na samu na sarrafa wannan aljana ba tsafi ba ne kawai ina neman taimakon Ubangijin ma’‘abota addanin Musulunci ne, WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
– Sa’adda jaruma Suraila tazo nan a bayanin ta sai mamaki ta turnuke su yaslir, . Sunaila ta dora da cewa” Na shigo wannan birni
Naki ne na dan wani lokaci ne domin na bincika ko zan dace na samu irin. wadannan mutane ma’‘abota addinin Musulunci.
‘ Koda jin wannan batu Daga bakin Sunaila sai lasmirat ta ce”Kada ki samu damuwa yake Sunaila zan baki masauki har’zuwa lokacin da za ki sadu da
– mutane ma’abota addanin Musulunci, domin ba za
~ mu iya biyan ki taimakon da kika yi mini ba, Koda jin hakan sai sunaila ta cika da matukar farin ciki tace” Godiya nake ya shugabata,
Da jin haka sai lasmirat ta matsa daf da ita ta yadda -suna iya jin numfashin juna ta dafa kafadun ta tace da ita” yake Sunaila daga yau bana so ki kirani da
-Shugabar ki face abokiyar ki ko. Aminiya, ” -Sa’adda Sunaila ta ji ‘hakan sai ta gyada kai cike da _farin ciki, _ , . Cikin hanzari sarauniya lasmirat da yaslir suka juya suka nufi gidan sarauta,jaruma Sunaila na biye da su, _Ana cikin tafiyar ne lasmirat ta lura cewa yaslir yana satar kallon jaruma Sunaila ta wutsiyar idanu, Nan take taji kishi ya turnuke ta, domin ta fahimci cewa yaslir yana yiwa jaruma Sunaila kallon SO ne,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG