UMM ADIYYAH CHAPTER 38 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 38 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

, a taKaice kin amince mijinki bai da kirki kenan? Ki fada min da mace mai gudun mijinta da miji mai tarairayar matarsa, waye marar kirki?” 

“Ho! Ya-Salaam da na san haka za ka matsa min da gori Allah da ban Ki tafiyar nan ba, idan ya so kowa ya ce Shugaban (AZ IT) ya faye son kai.” 

“Ba na fada miki ba, ni kam ai da zan dauki nauyin abina, amma haka kawai ina ji, ina gani aka min rinto, gani nan an bar ni da kame-kame kawai.” 

Zabura ta yi daga kan gadonta ta zauna, “Kame-kamen me?” Oho, ina ruwanki.” 

“Zaid Abdur-Rahman, idan ka kuskura ka yi abinda ba daidai ba…” 

“Iye? Allah, yarinyar nan kin raina ni.” Dariya ta saka mai shiga rai ta ce, “Kai fa ka dauki girman dungurgum ka bani a cewar Hajja Ku.”
“Oya, sai dafe ki yi barci ki bar ni na yi aiki, ki daina jin maganar tsohuwar can kuma za ta kai ki ta baro ki.” “Tam, dama na kira na yi tsokana ne.” Murmushin nishadin nan dai ya Ki barin fuskarta.


“Zan mayar miki da martani kuwa, ki zauna cikin shiri. Twinkle. Yawwa sannan ba…” Na’’am?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba ki taba gushewa a tunanina ba, bare na samu sararin kewarki. So, I don’t miss you. You are always here with me. A tunanina, a zuciyata da mafarki na. Sauran wuraren. I can’t say, tunda kin gujeni, kin ga dole na yi maneji.”Yaya Zaid!” Ta fada cikin Karaji, yana dariya ya kashe wayar, kada kai ta yi tana
nata murmushin hade da rungume wayar a Kirjinta.

**********

Kullum sai sun yi waya, kuma kullum suna cikin farantawa juna da daddadan kalamai,
da kuma nuna asalin kulawa. Rayuwa ta yi masu kyau, ba su da buri illa na ganin farin-cikin juna.
Umm Adiyya ta Kagara Yaya Zaid ya dawo don ta ba shi kyauta ta musamman,
baran ma yadda ta yi biris da sha’anin binsa Turkey, sannan ya yi hakuri, ya biye
mata. Ta tabbatar wannan kyautar da za ta ba shi, ta wuce komai kima a wurinsa.
Don haka tun saura kwanaki shida, dawowarsa ta hau shiri, ta fara da gyara masa
gida, gyara kanta har da ‘yan Kayatattun kyautuka masu sauKi.
Amira dai duk komai matar Kawun nata ta yi, sai ta yaba, ita kam burgeta take yi ta kowani bangare. Shi ya sa duk wasu shiryeshirye tare da ita ake yinsu.
Saura kwanaki uku ya dawo ne, ta tafi gidan Abba ta wuni masu a can, ta ji dadiin
wunin sosai, don Maami tana gida, sannan ta samu Yaya Saadik sun iso da amaryarsa Saudat, don haka can suka kule abinsu, suka sha hira, har ma Saudat
din ta yi mata alKawarin za ta zo su kwana. Washegari su sha hirarsu. Www.bankinhausanovels.com.ng

*******

Wajejen Karfe biyu na dare ne, ta sulale a Kasan tayil din bandakinta, wanda nan da
nan sanyin ya rabeta, duk da zufan da ya shiga tsattsafo mata. Numfashinta ne ya
shiga fita sama-sama, dai-dai lokacin da wani gigitaccen ciwo, ya soki Kasan mararta.
“Inna-Lillahi’ wa-Inna-[laihir-Raji’un! Umm Adiyya ta fada cikin cije lebenta, tabbas za
a kuma ne, nan da nan hoton ilahirin rayuwarta ya shiga giftawa a idanunta, a take
Yaya Zaid ya zo mata a ranta. Shin akwai ranar da za ta iya ba shi kyautar da ya fi
so sama da komai? Shin Maami za ta rike jikokin da suka fito daga jikinta?
Yaya Zaid! Ba ta fada masa batun cikin ba ma, a tunaninta ya kasance zance mafi daci da zai samu da zarar ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Kasar TurKiyya.
Idanunta ne suka sake runtsewa lokacin da wani sabon ciwon ya nuKurkusheta, duk
abin da ta fuskanta a rayuwarta da mafarkan da take faman cimmawa, suka cika
mata KwaKkwalwa har sai da wani ciwon ya Kara kai mata damKa.
A hankali ta ja jikinta cikin matsanancin azaba zuwa tsakar dakinta, a saman durowa
ta Gauki wayarta, ta danna lambar Amira, wacce take dakin baki a Kasa. Amira ta
tsorata Kwarai ganin yanayin da Umm Adiyya take ciki. A Cikin KanKanin lokaci ta kira wayar Fa’iz, ya taho suka wuce asibiti, sai dai irin
yadda ta rinKa zubar da jini ta san cewa wannan karon ma ta rasa gudan jininta.
Shi kenan bazatan da take da shirin yiwa Yaya Zaid ya ma rushe, tun kan Allah ya yi dawowarsa.
Haka dai suka isa asibiti wurjanjan! Can komai ya yiwa Adiyya dif! Sai nesa-nesa take jinsu, kafin komai ya koma mata baki wuluk! Www.bankinhausanovels.com.ng

***********

Hankalin Zaid ya yi matuKar tashi lokacin da ya samu labarin an kai Umm Adliyya
asibiti. “Ciwon wuyan nata ne ya tashi?” Ya tambayi Amira.
“Ciwon wuya? Uncle Zaid fa na ji Doctor tana fadawa su Maami Miscarriage ta sake
samu.” Shiru ne ya biyo bayan maganar Amira. Wani jiri ne ya ji yana neman ya debe shi. “Hello, Uncle Zaid ka na ji na?” Gyarar murya ya yi ya fito daga zurfaffen tunanin da ya fada. “Idonta biyu yanzu?”
“Eh, ina ga ta tashi. Bari a kai mata wayar.” “No, kashe zan kirata.” Bayan sun kashe wayar. Zaid ya yi kusan minti biyar bai san inda kansa yake ba, a
take a lokacin ya ji wasu hawaye masu zafi suna bin fuskarsa. Yanzu ya fahimci me ya sa take Kin binsa tafiyar nan. Wato tun kan ya taho ma tana dauke da cikin kenan ko kuwa sai bayan ya taho ta gane?
Sannan ga shi yanzu ya taho ya bar ta ita kadai abubuwa sun mata yawa ba tantama, har ta kuma samun kanta a wani irin mawuyacin hali. Allah ne masanin wane irin hali take ciki a halin yanzu, sam baya son ya kwatanta ganinta a irin
wancan yanayin. Ranar yadda ya ga rana haka ya ga dare bai runtsa ba.
Ya koma dakin sa na cikin otel din da ya sauka, ya natsu sannan ya danna lambar
Umm Adiyya. Ko wani Kara yana Kara masa gudun bugun zuciyarsa ne. Har lokacin
da ya ji zazzaKar muryarta a raunane daga daya Dangare, wani abu ne ya toshe
masa maKoshi, ta yaya za ayi ya zare mata wahalar da take ciki? Twinkle, yaya jikin naki?”
Yana jin shasheKar kukanta daga daya ban
gare, “Ya isa haka, ki yi hakuri, kin ji?
Allah Ya ba ki lafiya. Ya Kara miki juriya, da hakuri. Ina dawowa ni ma gobe idan Allah ya kai mu.”
“Ameen, ka yi hakuri, ban fada maka ba. Nayi tunanin… Na yi maka bazata ban San…
Shi kenan, ki yi haKuri, ki bar kuka, kar wata matsalar ta taso, kin ji? Ki kwanta ki Www.bankinhausanovels.com.ng
huta. Maami ce a gunki ko Aunty A’ isha?” “Maami ce.”
“To zan yi magana da ita. I love you my Twinkle. Sai da safe.”
Wani abu ta hadiya sannan ta ce “Allah ya kai mu.” Dukkan dauriyarsa ce ta dauke
shi kar ya zubar da Kwalla, jin halin da Twinkle ciinsa take ciki, ya san ba Karamin
tashin hankali take fuskanta ba, ga zafin da yake a zahiri ga kuma na cikin zuciyarta.
A take a wannan lokacin ya yanke shawara, baya ma jin zai iya jira safiya ta yi bai ganta ba.
Amma ba yadda ya iya, dole ya haKura. Salloli kawai ya shiga yi cikin daren, don ya rage lokaci, ya kuma miKawa Allah kukansa.
A safiyar ya yi KoKarin kammala duk wani abin da ya rage masa, domin ya kama jirgi na gaba mai komawa Najeriya.

*********

Lokacin da ya iso asibitin, ya gama kimtsa kansa ya yi fes! Ba mai cewa jiya a jirkice ya yi kwanan zaune ba, saboda ya samu barci ya sace shi a cikin jirgi. Cikin dare ya iso asibitin. Bai damu da su Maami da Faruk da Innayo da suke dakin ba kai tsaye
bayan sun gama gaisawa da Maami, ya wuce gadon Umm Adiyyarsa, ya riko
hannayenta cikin nasa, yana mata lallausar kallo. Ita kuwa daga ganinsa, kawai sai Www.bankinhausanovels.com.ng
ta fashe da kuka, ta jinginu a jikin kafadarsa, sa hannu ya yi ya zagayeta cikin jikin
sa, sai su Maamin ne suka zille daya bayan daya. Ganin lamarin ya fi Karfin ganinsu.
“Shhh! Ya isa Adiyyata, na sanki da dauriya
da hakuri. Inshaa-Allah rabonmu na
gaba, ki yi haKuri kin ji? Allah ne ya san daidai, shi ke kuma badawa ya karbe, a
duka lokacin da ya so. Kuma kin san an ce Kaddara ta riga fata. Mu gode masa da
Ya bar mu da numfashinmu da ni’imomi masu tarin yawa, ashe kuwa shi abin godiya ne ko?
Ba lallai bane sai mun samu abin da muke nema lokacin da muke so, haka ba lalle
bane. Allah ba ayi masa dole. Rayuwa shirin Allah ne, zai mana wani arziKin, amma
idan kin ga haka ta faru, to idaa bawa ya dauki Kaddara akwai tanadinsa gare shi a
gaba, Kila ma mafiyin na farko.”
Wani shassheKa ta sake yi, wanda bai sauka a ko ina ba sai tsakiyar zuciyar Yaya
Zaid, “Za ki daina kukan, ko kin fi son ni ma na yi ne. Iye?” Ya fada yana leKa
fuskarta da ta manne cikin Kirjinsa. Kada kanta ta shiga yi. Tana goge hawayenta.
“Na daina.” Ta fada cikin shagwababbiyar muryarta da idan da sabo ya saba, amma
duk lokacin da ya saurari wannan zazzaKar amon muryar matar tasa sai ya ji
zuciyarsa ta amsa, abinda yake ji wa Adiyya daga Allah ne kawai, domin shi kansa bai san iyakarsa ba.
“Inshaa-Allah ba za ki sake fuskantar wannan halin da ki ke ciki ba. Allah Ya ba ki Www.bankinhausanovels.com.ng
lafiya matar H.” “Allah Noorie, ka daina, zan fadawa Maami.”
“Da ma Abba ki ka ce sai ya kwace miki fadan.” Hannu ta sa za ta ture shi, ya riKo
hannun cikin nasa, ya gyara zama a bakin gadon asibitin. “Iye, har an yi min lallen oyoyo ne?”
“Noorie a asibiti muke fa.” Ta fada tana zame hannunta daga nasa. Yi haKuri, na ga wai ya yi kyau ne, kuma duk ki na bata gayun da hawaye, shi yasa. “Na fa daina kukan.”
“Yawwa ko ke fa.” Kanta ya sumbata a hankali, sannan ya mike daga gadon, “Bari
na fita, kar su zaci har yanzu ba mu gama gaisawar bane.” Sun san me ka tsaya yi ai.” “Don kuma ni ne Sarkin likewa mata ko?”
“Yau ka fara ne?” Dariya ya yi, ya ji dadin yadda ya sa ta fara sakewa, don haka
nauyin kirjinsa ya ragu akan mizanin da ya shigo da shi dazu, can ya fita yana
murmushin rashin gaskiya, sai ya ji ya kasa tsayawa, su Kara gaisawa da Maami, har kunyarta ta kama shi. Dazu shigarsa bai damu da ko ma su waye a dakin ba, shi dai kawai matarsa da lafiyarta da kuma damuwar da take ciki, su ne matsalolinsa. Allah dai ya sa bai yi wani abin na zarce kima ba? Da wannan tunanin ya fita wurin su Abba, a can
farfajiyar asibitin, inda suka gaisa da kyau, suka kuma jajantawa juna. Wannan karon kwanakinta biyu a asibitin, saboda irin yadda ta yi ta zubar jini. An sallameta bayan an tabbatar babu wata Www.bankinhausanovels.com.ng matsalar, banda wanda ba za a rasa ba.

**********

Gidan Maami ta koma, saboda rashin jin Karfin jikinta. Innayon ma can ta bi ta suka
tare, sai da suka shafe sati biyu. Duk iya zamansu a can. Zaid yake Karashe
wuninsa, daga ya taso aiki, baida wurin hira illa gidansu, dakin matarsa, ko falon Abba ko falon sama.
Maami kam ta kawo idanu kawai ta zuba akan wannan ikon Allah, idan ta tuno borin
da Adiyya ta rinka kantama masu akan ita an cuceta da aka aura mata Zaid. Wani abin dariya ma, duk dadewa da ya yi yana sintiri a kanta yana zuwa kullum dubata, fitarsa goma da ababensa na armashi yake tahowa, ko babban kyauta ko
Kanana ko na sawa ko na ciye-ciye.
Ranar Alhamis da ta shud, ta kula da yadda Ummun ta bi ta diririce, ita kadai sai fada take yi, tana cin magani, har ma ta sauke akan FaruK shi da bai ji ba, bai gani

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *