TATTALINTA CHAPTER 13 THEND KARSHE

TATTALINTA 




CHAPTER 13 THEND KARSHE





    Bayan wasu watan ni lokacin cikin Nadiya yayi girma sosai girman da ciki be ta6a yi mata ba. ajiye aikin asibitin ta tayi ta dawo gida ta zauna, komai sai dai ayi mata dan babu abinda take iya yi. Zaune take tana karatun wani littafin addu’o’i, yayin da su humaira da Islam ke ta wasa sai ga Balqees ta dawo daga gidan hajiya, zama tayi a parlor’n tare da kallon Nadiya tace. 

“Sannu ya jikin..!” 

“Sai godiyar ubangiji kawai, ya kika baro hajiya kakan da kuma k’afar ta ta…?” 

“Lafiya lau can na bar ta ina shiga gidan ta din ga min fad’a wai na taho na barki, shine nace mata zuwa nayi na ganta dan kar ta mutu ba’a sani ba, shine wai toh sai na riga ta mutuwa dan ita sai taga auran takwarar ta (Islam).” 

Nadiya ta kyalkyale da dariya, tana cikin yin dariyar ne taji ana tsikarin ta a marar ta, nan da nan tayi saurin rik’e ciki tana furta kalmar “innalillahi wa’innailaihir rajiun.” Balqees najin haka ta yi saurin zuwa gurin ta tana tambayar ta menene Nadiya ta nuna mata cewar haihuwa ce, tashi tayi da sauri zata bugawa sultan waya Nadiya tayi saurin rik’o ta tana kad’a mata kai bayan ta rintsa ido, murya k’asa-k’asa take magana. 

“Rabu da shi karki d’aga mai hankali, Bilkisu ki yafe min duk laifin da nayi miki na fili dana 6oye, kin san ance zo mu zauna zo mu sa6a dan Allah ki yafe min ki kuma kular mana da Ahmad, Balqees Ahmad nagartaccan Namiji ne wanda samun kamarsa sai an tona a cikin al’umma. Ki kula dashi yana sonki na san da haka koda be fito ya nuna ba a zahiri amma nasan soyayyarki a cikin jininsa take, Ahmad ya iya *TATTALIN MACE* zaki ji dad’i a tare dashi, kullum fata na da addu’a ta Allah ya baki haihuwa mai sauk’i da kuma ‘ya’ya masu albarka, na gwadaki baki da wata matsala kawai dai Allah ne beyi ba sai kuma wannan azababbiyar ciwon marar da kike yi amma karki yi fushi Allah shine yake badawa yake kuma hanawa a….” 

Ta kasa k’arasawa domin yadda taji cikin ta ya murd’a jikin Balqees duk yayi sanyi har ta fara hawaye ganin yadda Nadiya ke ta salati tana cewa ta kular musu da Sultan ko zan cen ‘ya’yan ta bata yi sai ta wannan k’aton, Balqees ke fad’a cikin ranta. Wani irin nishi taji Nadiya nayi hakan ya k’ara gigita ta domin bata ta6a ganin hakan ba, hannun na rawa ta d’auki waya ta lalubo numban Sultan ringing d’aya ya d’auka zai fara kashe ta da dad’ad’an kalamai yaji muryarta na rawa tana cewa. 

“Ya…ya Mommyn Islam… na shiga uku gata nan Yaya kana ina…??” 

“Subhanallah baby on my way, but please kin san me zaki?…karki kuka ta gani kije ki dinga yi mata addu’a ganin zuwa…” 

Kashe wayar tayi ta kuma komawa gurin Nadiya wadda a lokacin ta fita a hayyacin ta, suna nan zaune sai tasbihi suke yi tare a haka Sultan ya shigo ya tarar dasu, kallon Balqees yayi cikin tashin hankali yace. 

“Baby jiki d’akko trolley d’in da aka shirya kayan haihuwa, ki d’auki su humaira ki kaisu gurin Umma sai ki gaya mata ku taho asibitin.” 

Be jira cewar ta ba ya ciccibi Nadiya wadda keta faman kalmar shahada suka nufi motar shi. 

“Sannu Nadi…sannu Allah ya rabaku lafiya.” 

A baya ya sata yana k’ok’arin fita ya koma drive seat yaji ta yi mai wani irin wawan rik’o idanunta kur a kansa tana murmushi tace. 

“Ina sonka miji na ina kuma neman afuwarka gareni ka yafe min…” 

“Enough Nadi meye hakan? Yau kika fara haihuwa? Ko yau kika ta6a ganin irin hakan? Me yasa kike son d’aga min hankali? Please ki sake ni na kaiki asibiti karki karyar min da zuciya.” 

Story continues below


Da kyar ya kwakule hannunsa a jikin nata yaje ya kunna motar, sam bakinta yak’i mutuwa akan neman gafarar sa tun yana yi mata magana har yayi shiru jikin sa ya mutu zuciyar sa ta din ga harbawa tamkar zata fito a haka suka k’arasa aka kawo gado aka d’ora ta sai kallonsa take tana murmushi har aka shiga da ita lebour room. 

Yana nan tsaye sai ga su Balqees da Umman sa suma duk sunyi wujiga-wujiga, duk zama suka yi suna jiran a fito da ita amma shiru har fin awa d’aya dan haka Dr Omar ya fito tare da kallon Sultan wanda yayi shiru ya tallafo ha6ar sa yace. 

“Malam Ahmad gaskiya sai anyi wa Hajiya Nadiya c.s coz ta wahala k’arfinta har ya k’are tana cikin mawuyacin hali gara a samu a cito koda rayuwar babyn ne…” 

Cikin rud’ewa da gigicewa sultan ya fara magana yana rik’o hannun Dr Omar yace. 

“No… No Dr kuyi k’ok’ari wajan ganin kun cito rayuwa Nadi koda na rasa d’an/’yar ba damuwa dama bamu saba ba amma ita kuwa Nadi wani 6angare ce a jikina please Dr do something dan Allah karku bari na rasa Nadiya dan Allah…” 

Zaunar dashi Dr Omar yayi cikin tsananin tausayi, lokacin daddyn Nadiyan ya k’arasa yana zuwa suka yi mai alfarma ya shiga. Ya dad’e shima a ciki kawai ya yanke shawarar yi mata aiki kwai, fitowa yayi da takardar da Dr Omar ya bashi daddyn Nadiya yazo gurin Sultan cikin kwantar da hankali yasa shi yayi singing sannan suka sake komawa ciki. 

Cikin ‘yan sakanni aka gama aikin, su Umma na zaune a reception suka jiyo kuka har biyu nan da nan suka fara murna sa6anin Sultan daya koma tamkar wani gunki ko motsi bayayi bare yaji abinda suke cewa, kalaman Nadiyan kawai yake tunawa. 

“Ka yafe min abunda na yi maka ni dai na yafe maka abban humaira, duka duniyar nawa take dama dole ko wane bawa sai ya d’an’d’ani d’acin mutuwa, abban humaira idan na mutu dan Allah karka dena yi min addu’a da neman min yafiya a gurin ubangiji zai je gari ni kuma zanyi alfahari da hakan, Allah ya bud’a maka k’ofofin samu ka ci gaba da temakon alummar annabi..” 

Jinsa kawai suka yi ya fashe da kuka mai k’arfi yana cewa. 

“No…. No… Nadi karki min haka, munyi alkawari zamu rayu tare haka ma zamu mutu tare please don’t…don’t…” 

“Ahmad! Haba kana namiji kana abubuwan irin na mata wawayan nan? Ga yaranka nan zuka-zuka lafiyayyu dasu Hassan da Hussain tashi ka gansu.” 

A hankali kamar wani sakarai ya kalli Dr Omar idanunsa sun yi tamkar gar washi yace. 

“Dr basu nake son gani ko ji ba ina matata take..?!” 

Kallon sa Dr Omar yayi sannan yace, 

“Ku d’an bamu lokaci malam Ahmad ana can ana mata d’inki sai kuma kun taya mu da addu’a dan neman nasarar aikin kasan sumar da ita aka yi yanzu farfad’owar ta zamu jira.” 

Ai Sultan yana jin haka ya mik’e, wani mugun kallo ya dinga watsawa Dr Omar tamkar wani rud’add’e yace. 

“Sumar da ita kuka yi? Toh kayi fatan ta tashi idan kuma ba haka ba kaine mutum na farko da baxan iya yafewa ba a nan duniya, baka san wacece Nadiya ba shi yasa zaka sumar min da ita, ya Allah ka dubi baiwarka mai yawan ibada a gurinka ka tashi kafad’un ta…” 

Gaba d’aya ya fita a hayyacin sa yaran ma yaki d’aukar su hasalima haushin su yake ji sabida gani yake yi sune silar daya sanya Nadiya cikin wannan halin da take ciki na rai ko rayuwa. Sun dad’e sosai kafin daddyn Nadiyan ya fito lokacin ‘yan uwa da abokan arzik’i duk sun zo sun cika asibitin kai kace wani d’an k’aramin taron ake yi ko kuma ace ranar ne suna. K’arasawa daddyn Nadiya yayi gurin Sultan sam besan ma yaje ba ya riko hannunsa yana k’ok’arin fisgewa sai yagansa hakan yasa shi sunkuyar da kai shi kuma yaja shi zuwa cikin room d’in. 

“Ahmad be a strange man, from Allah we come and from him we are return..dan haka ka dena sanyawa kanka damuwa kowa da ka gani a duniya toh da ranar da zai koma, zauna anan yadda hankalinka zai kwanta kafin ta farfad’o.” 

Story continues below


Kujera ya samu ya zauna a kusa da ita tare da kura mata ido tayi fayau da ita hasken ta ya kuma k’aruwa fuskarta kamar tana murmushi sai kawai shima ya samu kanshi da murmusawa duk a ganinsa itama yi takeyi. Ya dad’e a zaune a gurin ko motsawa baya yi har sai da yaga ta fara motsi, kura ymata ido yayi sannan yaga ta yi hamma yayi saurin sanya mata hannunsa a bakin, ido ta bud’e tabi shi da kallo da sauri kuma ta kalli cikin ta sai taga wayam sai wani alamu da taji, hannu tasa zata shafo gurin Sultan yayi saurin rik’e hannun ta yana girgiza mata kai. 

“Alhamdulillah Sannu my Nadi me kike ji yanzu?” 

“Ba komai abban humaira mai aka yi kake kuka?ko na haihu Allah ya k’ar6i abin sa ne?!” 

“No Nadi aiki aka yi miki, na shiga tashin hankali ne ni ban ma san me kika haifa ba hankali na yana kanki na sani ba cikin ba.” 

Kwankwasa k’ofar aka yi daddyn Nadiya ne tana ganin shi ta fara k’ok’arin tashi yayi murmushi yana kallon Sultan kamar ba siriki ba yace. 

“Ahmad ka dawo normal ko?!” 

Shafa keya yayi kurum tare da fita daga d’akin, zaune yaga su Umma da sauran mutane ya k’arasa gurin Umma ta kallesa tace. 

“Ta farfad’o ne?!” 

Murmushi yayi sai kuma kallon hannun Umman yake yi dana Balqees, so yake ya tambaya amma kunya ta hanashi sai faman bin yaran yake yi da ido, Umma na lura dashi ta kuma gane me yake nufi dan haka ta mik’a masa su bayan ta k’ar6i na hannun Balqees. Kar6arsu yayi yana jin wani farin ciki a zuciyar sa, ko a mafarki be ta6a kawowar zai samu twins ba domin wannan ma da aka yi secarning d’aya aka gani nan yayi musu hudu ba tare da yi musu addo’o’i ya k’ira Balqees da ido suka shiga room d’in da Nadiya take. 

“Aunty Nadiya…!” 

Balqees ta fad’a tare da k’arasawa gurin Nadiya ta rik’e mata hannu, ita kuwa mamakin ganin yara biyu ne ya cika ta, cikin sanyin murya ta kalli Balqees tace. 

“Mamin Humaira da har an fidda rai dani ko?!” 

Balqees har kuka tayi ita bada haihuwa ba amma duk an sanya sunan iyayen ta, kaunar Sultan da Nadiya ta kuma shiga cikin zuciyar ta ta tabbatar Nadiya ba kishiya bace tana rokwan Allah ya kawo hanyar da itama zata faranta mata a cikin rayuwar ta. 

Rayuwa suke yi cikin kwanciyar hankali da jin dad’i, Balqees na bawa Nadiya girma sosai kamar yadda take bata muhimmanci itama, komai yanzu tare suke yi hankalin Sultan ya kwanta, zaune yake yana cin abinci Balqees kuma tana rik’e da abbanta wato Hussain d’an watanni bakwai Sultan ya kalleta cike da so kafin ya kalli wayar shi da ake ta faman Kira, katsewa yayi sannan ya kalleta yace. 

“Baby wai ina wannan k’awar taki wadda na ta6a kora anan gidan??” 

“Yaya wai Asma’u kake nufi? Ta6 ai yanzu bama tare tama dena kulani…” 

Jin-jina kai yayi sannan ya d’akko wayar sa, nuna mata taxts massage’s d’in ta da  take turo mai, zaro ido Balqees tayi lokacin da take karanta wani massage wai _”Toh ni ina sonka kuma a shirye nake da na kashe aure na sai na aure ka naga wannan matar taka ta yi maka k’ank’anta, uwar gidan kuma bata zama.”_ haka Balqees dai ta din ga karanta sak’wan nin Asma’u zuciyar ta na harbawa kanta na mugun sarawa bata gama katanta su bama ta ajiye wayar tana jin ranta na kuna. 

“Ni dama tun da na ganku tare naji sam ba ta yi min ba a k’awancen ku, kiji wanda taci amanar mijinta shine zan kwakuso nima tazo taci amana ta…” 

“Yaya kayi hakuri ka yafe min please.” 

“Zo nan.” 

Tashi tayi taje ya kalleta tare da cewa, 

“Jeki kwantar da shi sai kizo.” 

Kan kujera ta kaishi sabida tana part d’inta kasan cewar duk sun tare a sabon gidan su, k’arasawa tayi ya d’ora ta akan cinyar sa, kallonta yayi yana ja mata hanci tana lumshe ido yace, 

“Ni baki min komai ba baby fatana da buri na kisan irin k’awayen da zaki din ga yi, kinga yanzu service zaki tafi dan Allah ina son ki kare kanki ki kuma kare martabar auranki kinji baby na..? Idan ma ni kike buk’ata kiyi min waya sai nazo na d’auke ki, ni naki ne ke kuma tawace domin akwai wani *BABBAN SIRRI* a tsakanin mu I love you baby forever zan zauna dake.” 

Kwanciya tayi akan k’irjin sa tana shafawa murya a sanyaye tace. 

“Nima haka Yaya zulkallain, kai d’in mutum ne jajir tacce mai kula da duk wani hakki da Allah ya d’ora masa, Yaya ka iya *TATTALIN MACE* ta ko wacce siga dan haka nak’e sake godewa Allah da ya bani kai a matsayin miji ina kuma addu’ar Allah ya bani zuri’a masu Albarka a tare da kai, me to love you forever *RUWA KO ISKA* baza su sanya na rabu da kai ba sai randa ta Allah ta kasan ce..” 

A hankali cikin salonsa ya rik’o hannun ta yana faman kashe mata ido tare da lasar lips d’insa, kunshin yatsunta yabi da kallo kafin a hankali in a romantic way zura su cikin bakinsa yana tsotsa yana kuma kashe mata ido hannunsa d’aya yana yawo dashi a jikinta a hankali yace mata. 

“Baby na zan yi bacci please muje ki lalla6ani coz bazan iya yi ba sai da temakwanki..” 

Tashi tayi duk da ta gano wayan shi, suna shiga d’akin ya rufe k’ofa dan yasan zai iya ganin humaira da Islam ya jata suka fad’a kan gadon, kamota yayi jikinsa ya rungume ta, wasu zafafan kalamai ya shiga fad’a mata Balqees na jinta tamkar ita kad’ai ce a gurinsa har mantawa take tana da kishiya, ji tayi yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnanta, ai kuwa nan da nan Balqees ta hargitse sai ta kuma shigewa cikin jikinsa tana kai mai nata tallafin a sassan jikin sa, shi kuma a hankali ya cafko mata baki ya had’a da nashi yana tsotsa tamkar ya samu chocolate. tare suka yi wanka bayan sun fito suka dunguma zuwa sasshen Nadiya bayan ya goyo ta suna zuwa k’ofar ya direta suna dariya suka shiga ciki. 

Gadan gadan Nadiya ta fara aiki a sabon asibitinta cikin d’in bin nasara, daddyn ta ya samo mata manyan likitoci hakan yasa asibitin ya kuma samun d’in bin al’umma ya kuma yi albarka.

          *£^∆* 

   Balqees kuma ta wuce services garin gombe in da ya fara gina mata wani k’atan botic na gani na fad’a a cikin kwaryar kano. kud’in ta na gado kuma tasa aka bud’e mata wata gidauniya mai suna *SulBal Foundation* in da take tallafawa gajiyayyu da marayu ta hanyoyi da dama da masallaci a wani k’auye shima tasa aka sanya sunan mahaifanta *Lates Papa-Ummi mosque* Allah ya kai lada mizanin iyayan ta. 

Rayuwa suke yi su duka mai cike da ingantacciyar kulawa, kauna, yadda da kuma soyayya. Shirye-shirye suka fara yi wanda sam Sultan be san suna yi ba, kasuwa suka shiga suka siyo kayan cefane da kansu duk wani abun da suke da buk’ata suka siyo Nadiya ce tayi tuk’in Balqees na gefenta duka yaran kuma suna bayan mota daga masu wasa sai masu fad’a. Suna komawa gida suka shirya lafiyayyun girke-girke suka shirya shi a parlor’n shi tsakiya kuma cake ne mai kyau d’an k’arami sannan ko wacce ta koma side d’inta suka ciyo kwalliya yaran ma aka shirya su dai-dai lokacin ya dawo misalin k’arfe 8:00pm, direct side d’insa yayi yana shiga yaga duk glops d’in a kashe ya fara laluban wayansa dan ya haska kawai yaga haske ya bayyana harda me walwali kanshi ya d’aure karaf kuma idanunsa suka sauka akan center table d’insa yana k’ok’arin k’arasawa yajiyo kukan Abba (Hassan) can kuma yaji Islam tana cewa. 

“Mommy mun gaji.” 

Dole tasa suka fito daga ma6oyar su suna dariya, tsayawa yayi kawai yana kallonsu yaran da iyayen suka ruga suna mai oyo-yo bayan sun rungume sa dukan su Balqees da Nadiya suka fara mai wak’ar birthday ya kalli cake d’in wanda aka sa mai *Ahmad birthday* sannan suka jashi zuwa gurun Nadiya ta bashi wani kyakyawan card ya kar6a ya fara karantawa. 

_”The best way to enjoy your Birthday each year is to keep getting more gifts but never remember your age. Happy Birthday…”_ 

Murmushi yayi yana shafa quarter million d’in fuskarsa, Balqees ma ta mik’a masa nata tare da rungume hannunta a k’irjinta suna binshi da kallo. Bud’ewa yayi ya fara karantawa harda su kiss a jiki. 

_”You are the most amazing person I have ever met in all my life. I just wish that you be blessed so much that all who see you, learn that good people are always rewarded. Have a very Happy Birthday…”_ 

Lumshe ido yayi tare da ware hannunsa suna gani suka nufeshi dukkansu suka rungume shi ya rungume su tare da d’ora kanshi a kan Nadiya kasan cewar ita ce dai-dai inda zai iya muryar sa shar da ita yace musu. 

“Allah yayi muku albarka ya bar min ku har k’arshen rayuwata…” 

“Amin….” 

Suka amsa baki d’ayan su sannan suka jashi yaje ya yanka cake d’in ya sakawa kowa a baki shima ko wacce ta bashi sannan suka ci gaba da bidirinsu zuciyar Sultan fes yana jin babu abinda yake damunsa a rayuwar sa kullum bud’i yake samu ta hanyoyi da dama babu abinda zai cewa Allah sai godiya. Bayan anci anshi yaran har sunyi bacci suka d’auke su suka wuce dashu d’akin Nadiya dama haka suke yi duk ranar da wata take da miji sai yaran su koma gurin wadda ba ita ke dashi ba, suna kaisu Nadiya tayi musu sallama suka tafi bayan yayi kissing d’inta ba tare da Balqees ta gani ba sannan suka wuce side d’inshi bayan ya sungume ta dan baya jin wahalar hakan. 

Kan gado ya direta tare da kwanciya a kan cikinta, nishi ta fara yi tana ture shi cikin shagwa6a take cewa. 

“Wayyo Allah Yaya kayi nauyi please d’an d’aga ni.” 

Story continues below


“Baby yau ni nayi nauyi?!” 

“Yaya kaji ka kuwa?wayyo hajiya kaka..!” 

K’in d’aga ta yayi sai ma k’ok’arin cire mata doguwar rigar jikin ta yake yi cikin wani sabon salonsa. 

“Boy wonder bacci zanyi.” 

Ta fad’a tana lumshe idonta. 

“Toh yi mana baby ni babu abinda zanyi miki naga sai wani zille-zille kike yi kamar yau zan fara, amma baza ki kwanta ba baby sai kin cire kayan jikin ki dan zasu takura min wajan yin bacci.” 

Cak ta tsaya da kanshi ya cire mata yana bin surar jikinta da kallo cikin wata matsanan tacciyar buk’atarta, tsam ya d’akko ta suka koma tsakiyar gado ya kwantar dasu, a hankali ya dinga bin sassan jikinta da hannunsa yana shafawa ita kuwa tayi lif tana kar6ar sakwaninsa zafafa kafin ya ja musu bargo yana manne da ita murya k’asa-k’asa yake cewa. 

“Baby sleep…sleep I love you irin soyayyar da baki da gangar jiki baza su iya furtawa ko bayyanawa ba, kisa a ranki baby da soyayyarki zan bar duniya ina sonki ina son komai naki ina kuma alfahari dake…” 

Itama ta kuma shigewa jikinsa tare da rik’o hannunsa ta d’ora akan kirjinta tana kuka tace. 

“Baby wa yace miki dan baki haihu ba hakan zai sa kaunarki dake cikin zuciya ta?karki sake fad’ar haka domin sonki a jinina yake I love you forever.” 

Suka rungume junanasu cike da shauk’in so da kaunar juna, so sone kun san dole ne idan namiji ya had’a mata fiye da d’aya toh dole a cikin su sai yafi karkata akan wata, annabi (s.a.w) idan ya shigo gidansa matansa sunce baya iya ganin Nana Aisha bai ta6a ta ba, wato ma’ana duk lokacin da annabi ya shigo inda Nana Aisha take baya iya mallakar kansa, dan haka ke zaki san wane matsayi kike a wajan mijinki ta hanyar yi masa biyayya. An rawaito cewa akwai lokacin da Annabi (s.a.w) bashi da lafiya amma kullum cikin tambaya yake, yau a ina nake? Idan ance kana guri kaza sai ya kuma tambaya yace gobe fa?kana guri kaza, sai yace jibifa? Abin da kawai yake son ji yaushe yake gurin Nana Aishi, sabida itace wadda a duk lokacin da yazo kusa da ita za’a same shi yana cikin nisha d’i fa farin ciki sabida duk abinda tasan yana sashi farin ciki tana yinsa. 

Allah ya bamu ikon kyautatawa mazajen mu da tsarkakakiyar niya, yasa muyi kishi irin na gidan maxon Allah (s.a.w) Amin. 

      Alhamdulillahi
Allah na gode maka daka bani ikon kammala wannan novel d’in lafiya, Allah kasa a amfana da abubuwan dake ciki masu amfani, Allah ka nuna mana watan Ramadan muyi shi cikin d’in bin nasara dajin dad’i Amin. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *