TATTALINTA CHAPTER 8

TATTALINTA





CHAPTER 8






Yayi ball da ledar dake ajiye gabaki d’aya kayan ciki suka tarwatse Balqees da Nadiya suka zaro ido suna yi mai kallon mamaki da al’ajabi.

Sake bin kayan yayi d’aya bayan d’aya ya dinga ball dasu kamar wani zararre, Balqees ta bi kayan da kallo domin kayan costmetiec ne, kuma daga gani zasu yi tsada masu kyau dasu harda spray suma kusan guda biyar haka ya bisu yana wulli dasu sai da yayi musu filla-filla ko wanne ya samu guri sannan ya juya ya kalleta idanuwan shi sunyi jawur yace,

“A gidan uban wa kika yayubo mana wannan sakaran wawa me shegen surutun tsiya ah…?!”

Ta yatsina fuska wannan karan ba kuka ta fara magana ciki-ciki tana cewa.

“Gaskiya ni Yaya Sultan na gaji, ya za’ayi ka dinga korar min masoya? Nazo da Adam kace yayi kankanta na samu Salman a makaranta ban kawo shi nan ba ka dakatar dashi yanzu na samo wannan kazo kace wai ya fiye surutu ai surutu baya hana aure bare soyayya.”

Ta fad’a tana fari da idanuwa tare da cono baki tana murgud’a shi yace,

“Oh ni kike kallo kina gaya min wannan maganar sabida yanzu wuyanki yayi kauri ko?!”

Wannan karan Nadiya ce ta kar6e zancen ta hanyar kallon Balqees tace,

“Jeki d’aki daughter rabu dashi.”

Juyawa tayi tana cewa,

“Ni gaskiya gidan hajiya kaka zan koma na gaji da nan gidan.”

Kallonshi Nadiya tayi fuskarta a sake tace.

“Yarinyar nan ta fimu gaskiya fa, shin yanzu idan bata fara kula samari ba mine a gida zata zauna a dinga kallonta ne? Ko kuwa baza tayi aure ba a haka zata k’are rayuwarta? Ko ka gaya min Kaine zaka aureta?!”

Da sauri ya kalleta kawai yaji wani gumi yana karyo masa sannan bugun zuciyar shi ya k’aru a hankali ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta tsawon lokaci be ce komai ba kafin ya samu damar yin magana yace,

“No! Nadi me yasa har yanzu kema kika kasa gano abinda nake hangowa baby?”

Nadiya ta kalleshi cike da mamaki tare da kulawa sannan tace,

“Ba wai fahimtar kane banyi ba, a’a kaine ka kasa fahimtar inda take son ka gano, daughter ga dukkan alama tana son aure ka gaya min idan bata bawa samarin dama ta yaya za’ai har ta samu wanda ya kwanta mata? kaga kenan sai tana basu fuska tana kulasu kai kawai abinda ya dace da kai shine duk wanda kaka tarbiyar shi bata da nagarta sai ka tsawatar mata akan ta dena kulashi mu kuma muna taya ta da addu’ar Allah ya dubi maraicinta ya za6a mata miji nagari wanda zai kula da ita…”

Sultan ya sauke ajiyar zuciya tare da rungumu Nadiya jikin shi yana sanya mata albarka, sai dai shi kanshi wani sa’in be san abinda yake warware mai control d’in jikin shi ba idan yaji wani yazu tun da ta nuna bata yi da Yazid amma duk da haka yaji baya son Imran ya tsaneshi ma. 

Suna nan a zaune sai ga Balqees ta fito niki-niki da kayanta cikin trolley ba tare da ta kallesu ba tazo zata wuce Nadiya ta zame jikinta daga na Sultan ta k’arasa wajanta tare da rik’o hannunta tace, 

“Haba daughter ya haka? yanzu sai ki tafi kibarmu ciki harda humaira ma?” 

Balqees ta yatsina fuska yayin da shi kuma Sultan yake bin ta da kallon mamaki tace, 

Story continues below


“Aunty Nadi gaskiya  bazan iya zaman cikin gidan nan ba naga alama kun fison na zauna kuyi ta kallona ni kuma yanzu gaskiya ina son nayi aure toh shi kuma Yaya sai korar min samarin yake yi, kinga kuwa dole na bar gidan naje inda baza a hanani ba sai dai ma ayi min sam barka.” 

Kar6ar trolley d’in Nadiya tayi tare da cewa, 

“Kiyi hakuri shi yayan ki har yanzu be ga kin kawo wanda zai iya barin ki ku dinga tsayawa tare ba bare har kuyi aure, kin san kuma shi aure dole sai anyi bin cike akan wanda za’a aura, dan haka kiyi hakuri kema kuma kisan irin maxan da zaki dinga bawa fuska dan karki je ki jajibo karabiti.” 

Turo baki tayi tana k’ara had’e fuskarta kamin ta juya ta koma d’aki, taso Yaya Sultan d’in yayi magana amma ta gano cewar bashi da abin da zai ce mata ne yasa shi tsuke bakin shi yayi shiru. 

**** 

Shirye-shiryen tafiya ethopoeia ta fara yi dan halattar bikin Yayya Aamanee, shiryawa suka yi su duka kasan cewar Umma baza ta samu damar zuwa ba yasa tace Nadiya ta wakilce ta dama already Yaya Sultan yayiwa Aamanee alkawarin zuwa bikin nata. 

Ranar talata suka d’aga zuwa k’asar ethopoeia Balqees murna fal cikinta. 

Suna sauka Ahmad yaje ya d’auke su, sosai aka yi ta murna da zuwan nasu. D’aki guda aka basu Balqees da Nadiya shi kuma Sultan yace hotal zai kama dan sai yafi nutsuwa, sai da suka ci abinci suka huta sannan Ahmad ya raka Sultan hotal d’in da zashi, sai da ya tabbatar ya gama har ma yakai kayanshi room d’in sannan suka koma can gida. 

Da dare lokacin da zai tafi hotal d’in cewa yayi dole Nadiya tazo su tafi ba yadda ta iya haka ta bishi suka tafi kunya fal cikinta sai dai Balqees ta hana su Humaira dan haka anan suka barta kasan cewar tafara cin abinci. 

Suna kwance da dadare a d’aki Aamanee ta kalli Balqees tace, 

“Wai har yanzu kina nan akan wannan son guy d’in Balqees?!” 

Balqees ta had’e rai cikin 6ata fuska tace, 

“Gaskiya yayya Aamanee ki dena min irin wannan abun, kefa ba wata shawara kike bani ba amma ko waya muke dake sai kin wani tambaye ni.” 

“Allah sarki dan ma na tambaye ki yanzu?, dama ji nayi su uncle Habeeb suna cewa zasu had’aki da broth Fahad yadda zaki dawo kusa dasu su dinga ganinki shi yasa ma kikaji na tambaye ki yanzu ma .” 

“Na shiga uku..!” 

Balqees ta fad’a tana dafe kirjinta tare da zaro manyan idanuwanta masu zara-zaran eyelashes mai d’auke da fararan kwayar ido tamkar madara amma tashin hankalin da ta shiga yanzu har sun farayin kallar ja kirjinta na lugude tamkar ana yi mata kid’a a kanshi Aamanee tace. 

“Kinga kwantar da hankalinki dan shima broth Fahad d’in be amsa ba cewa yayi sai kinzo ya ganki idan kin cika type d’in shi sai ayi idan kuma yaga baki mishi ba shikenan kin sanshi da rashin mutunci.” 

Balqees ta sanya kuka tare da rungume humaira, Afrah dake gefenta tace. 

“Ke meye na kuka kuma? kema fa Balqees kina da baki kuma a family d’in nan ba’a yiwa kowa auran dole dan haka kema idan kinga beyi miki ba ki fito ki fad’a karki cuci kanki.” 

Balqees ta numfasa cikin takaici da bak’in ciki tace, 

“A’ah watakila idan anga ni banida kowa ba majingina sai ayi min dolen, ni yanzu kuma ta ko’ina babu dad’i, amma nayi alkawarin zan hakura da duk wanda Allah ya bani tunda shakara da shakaru Yaya Sultan ya gaza gano inda zuciyata ta nufa.” 

Afrah ta kuma kallon ta cike da tausayawa tace, 

“Karki haka Balqees ki samu Yaya Sultan ki sanar dashi da bakinki yaji sai kiji ra’ayin shi a kanki.” 

Balqees ta share hawaye tace, 

“Bazan iya ba sister Afrah, domin ina hangowa kaina zubar da mutunci a gurin shi, karku manta na gaya muku sau da yawa ina fad’a a cikin mutane cewar shi nake so zan aura, karkuga yadda yake nuna min sai dai daga baya na ce mishi ai da wasa nakeyi sannan ne zamu shirya dashi sabida shi jinshi yake kamar wani uncle d’ina…” 

“Toh ki rabu dashi mana Balqees sai kace shine kawai namiji a duniya. kuma wallahi da alama wannan matar tashi ce tayi duk abinda zatayi har ta cire mishi son auranki a zuciyar shi.” 

Da sauri Balqees ta kalli yayya Aamanee cikin mamaki, kai ta fara kad’awa cikin rashin yadda da maganar tace, 

“Ban yadda ba gaskiya domin tun kafin na santa na san yadda Yaya Sultan yake matukar sonta, yayya Aamanee suna san juna fiye da yadda bakina zai sanar muku, so karku sanya min wani zargi ko shakku akan aunty Nadi, koda nake son Yaya sultan wallahi yanzu ina jin kunyar ranar da zata gano hakan ban san da yadda zata kalleni ba.” 

Aamanee ta ta6e baki cikin ko’in kula ta fita zuwa d’akin da kawayenta suke domin duk ba sa’annin su Balqees din bane. 

Washe gari Amarya suka bi zuwa wajan lalle anan duk aka yi musu harda Nadiya ma domin ita matace da bata da girman kai ko nuna cewar tafi wani gata da kwarjini dan ba kasafai mutum zai iya tsare ta da idanuwa ba. 

Sai yamma lik’is suka koma gida, a cikin motar Ahmad suka ga Sultan duk suka gaida shi ya amsa cikin sakin fuska sannan suka wuce yayin da Balqees da Nadiya suka tsaya a gurinshi Nadiya ta mik’a mai hannunta tana murmushi tace, 

“Mine kalla ka gani yayi kyau?!” 

Mik’a hannu yayi ya riko nata yana kallon kunshi yace, 

“Wow! gaskiya wannan kunshi dole yau a nuna irin jin dad’in kyawun da yayi, baby kema anyi miko ko??” 

Ta yatsina fuska tare da cewa, 

“Eh.” 

Ya kai hannun Nadiya saitin bakinshi tare da sumbatar kunshi, kallon Balqees yayi karaf suka had’a idanuwa sai yaji gabanshi ya buga da karfi amma yayi fuska yace, 

“Baby ke bazaki nuna min naki bane?!” 

Kallan kofar parlour tayi sai ta ruga tana cewa, 

“Wait Yaya ina zuwa….?” 

Kallon bayanta yayi sannan ya kad’a kai tare da janyo Nadiya jikinshi yana sunsunar wuyanta ita kuma tana kokarin kwacewa sabida duk a takure take ganin tun wankan safe ne a jikinta amma shi sai  mannata yake a hancinshi. 

“Mine dan Allah ka barni naje nayi wanka mana.” 

Ya sake matseta tare da d’ago fuskarta ya had’e da tashi yace, 

“Wanka kike son yi?” 

Nadiya ta sargafo wuyanshi da hannunta tare da cewa, 

“Eh wallahi kai bakaji sai tsami nake yi ba, amma sai nanikata kakeyi.” 

Ya zare ido domin shi sam beji ba hasalima kamshin turaran wuta kayan jikinta suke yi kasan cewar bata sanya kaya sai ta turarasu, fatar ta kuwa kamshin kwaleqca yake da humra hakan yasa duk beji tsamin da take tunanin tana yi ba. 

Bakin shi yakai saitin kunnanta yace, 

“Toh bari muje masaukin mu sai na kara miki wani abun wanda zai sa kiyi wankan dole ma bana tsami ba..” 

Dariya tayi sabida ta gane abinda yake nufi ta kwace jikinta da kyar sannan ta kalleshi tace, 

“Toh ina zuwa.” 

Ciki ta shiga be sake jinta ba sai da zasu koma masaukin su, aikuwa tashi mita da korafi ita dai dariya kawai tayi Balqees kuwa be sake ganinta ba bare yaga lallenta. 

Washe gari aka shirya wani party wanda za’ayi a wani special event da aka  tanada za’ayi, me taxi yana sauke su sultan ya wuce wajan wani ruwa dake bayan gidan ita kuma ta wuce ciki fuskarta cike da walwala. 

Tana zuwa dai-dai d’akin dasu Balqees suke zata shiga kawai kunnuwanta suka jiyo mata wani mugun…….

    
    Mugun labari, cikin sauri ta juya ta fita tana neman sultan amma bashi qwata-qwata a wajan, wayarta ta ciro a cikin ‘yar pos d’inta ta hau kiran layin shi amma cikin takaici babu network hakan yasa ta komawa cikin gidan lokacin taga duk an fito daga cikin d’akin. 

A kwance ta tarar da Balqees rannan nata a 6ace gefenta humaira ce take bacci, ra6awa Nadiya tayi kusa da ita ta zauna tana kallonta. 

“Daughter ba magana?!” 

Nadiya ta tambayi Balqees tana mai kura mata idanuwa, tashi Balqees tayi kawai ta fad’a jikin Nadiya sai kawai ta saki kuka nan da nan hankalin Nadiya ya kuma tashi ta kuma nuna mata kamar ba taji komai ba cikin kuka Balqees ke cewa. 

“Aunty Nadi basa sona, wallahi kowa d’anshi yake so yake kuma tarairayawa yanzu meye daga zuwa na biki za’a wani za’a had’a dani ayi min aure da wanda ban rayu dashi ba? Ban san halinshi bafa aunty Nadi sannan bana son shi, ni kenan bani da sa’a a duniya kenan dan anga duk gatana sun mutu shine ake min haka..” 

K’irjin Nadiya na bugawa bakinta sai faman rawa yake yi sabida tsananin tausayi da tashin hankali tayi k’ok’arin cewa. 

“Ki dena kuka daughter Allah yana tare da ke, insha Allahu baza ki dinga yin kukan rashin iyaye ba bari na kira yayanki.” 

Sake kiran layin Sultan Nadiya tayi amma wannan karan busy, d’an jirkintawa tayi kafin ta sake bugawa ringing d’aya sultan ya d’aga cike da barkwanci yace. 

“Komawa zamuyi ne madam?!” 

D’an murmushi Nadiya tayi kafin tace, 

“Zaka iya shigowa ciki mine? Please daughter na kuka sabida ana shirin yi mata abinda bata so.” 

Cikin tashin hankali Sultan yace, 

“Ok gani nan amma ki fito sai ki shigar dani d’akin dan ban san inda kuke ba.” 

Yana wayar ne yana tafiya dan haka lokacin da Nadiya ta fito sai ta tarar dashi tana gaba yana bin bayanta a baya cikin damuwa har suka k’arasa cikin d’akin duk kuwa da d’in bin mutanan dake gidan. Kwance suka tarar da ita tana faman yin kuka jikinta sai faman rawa yake yi suka k’arasa wajanta Sultan ya d’agota nan yaji wani zazzafan zazza6i a jikinta ya kalli Nadiya cikin tashin hankali yace. 

“My Nadi bata da lafiya fa, muje asibiti.” 

K’ok’arin d’agata yayi Balqees tayi saurin rik’e mai hannu tana gir-giza mai kanta ya kalleta da mamaki duk da idanunta a rufe suke yace, 

“Meye baby? Asibitin ne bazaki je ba ko yayya ne?!” 

Tace, 

“Eh Yaya karka wahalar da kanka ba zani ba.” 

“Me aka yi miki toh waye ya ta6aki?!” 

Kuma rushewa da kuka tayi, kawar da kanta tayi murya a dakushe tace, 

“Yaya aure za’a min.” 

A cikin tsananin razana yace, 

“Mene..?!” 

Sai kuma yayi murmushi cikin takaici yace, 

“Dama dangin uwa ne suke bada aure? Toh ma wai tsaya wa za’a aura miki? Kina sonshi ne? Ko ke kika ce kina so?!” 

Story continues below


“A’ah Yaya amma zan hakura na k’ar6i za6insu tunda ni dama ba wani tsayayye garini ba duk korarsu kake yi.” 

Mtwww yaja tsaki tare da gyara zama, Nadiya ta kalleshi ganin yana son maida abin wasa tace, 

“Wai kai meye haka dan Allah, kana ganin wai abun wasa ne ko mene yasa kake wani murmushi haka..?!” 

“Toh kuka zanyi? Abun ne ni naji shi wani banbarakwai namiji da suna hajara, idan banda hauka daga zuwan mu biki sai ace za’a yiwa yarinya aura kuma ma wai a 6angaran uwa bayan na ubanta suna nan kuma a hannunsu take kinga kuwa dole nayi dariya.” 

Tashi yayi ya fita ba tare da yasa cewa komai ba cikin sa’a kuwa suka had’u da uncle bashir yana k’ok’arin shiga mota zai tafi, da sauri Sultan ya k’arasa gurin uncle bashir yana ganinshi yayi murmushin jin dad’i dan dama yasa a nemoshi ba’a ganshi ba sai yanzu ya ganshi. 

“A’ah Ahmad dama tunda nazo nake nenanka aka ce min baka dawo daga masaukinka ba, ya mutanan gidan naku dasu hajiya.” 

Sultan ya tsuguna yana amsa mai da cewar duk suna gida Lafiya lau, sannan ya kalli uncle bashir wanda shima kallonshi yake yi yace, 

“Ammm uncle naji ana cewar wai za’a had’a da baby a bikin kuma naga mu bamu zo da shirin yin hakan ba.” 

“Kagane ko Ahmad abinda yasa muke son yin haka shine dan mu k’ara kulla alak’armu ne shi yasa, sannan kuma anyi sa’a shima Fahad d’in yana ganinta yace yaji ya amince tayi mai shi yasa muka yanke cewar kawai a had’a dasu ayi gabaki d’aya daman yanzu nake son naje office sai na kira abban naku na sanar mai.” 

Daram dam yaji kirjinshi na bugawa kanshi a k’asa nan da nan jikinshi ya hau rawa uncle bashir ya bishi da kallon mamaki kafin kace meye har ya fara zufa, ya shiga uku me yake shirin faruwa dashi ne a yanzu har yake neman rasa tunanin shi, kodai ya fara son baby?no fahad d’in ne beyi mishi ba shima, amma a ina ya ta6a ganin shi da zaice beyi mai ba?kawai sunan ne yake tunanin beyi mai ba shi yasa yaji ya tsaneshi. 

“Ahmad lafiya dai ko??” 

Sultan yaji muryar uncle bashir yana tambayar shi, kasa kallonshi yayi shi kuma uncle ya d’ora da cewa. 

“Insha Allah duk abubuwan bazasu gagara ba karka damu, dama shi fahad d’in yayi gininshi idan yazo nan ethopoeia ma acan yake zamanshi sabida akwai komai a ciki, zancen kayan aure wannan duk ba matsala bace za’ayi daga baya indai har wannan ne damuwarka karka damu.” 

Jiyayi hankalinshi ya kuma tashi jin abinda uncle bashir ya fad’a, share zufar ya fara amma tamkar sake koromai ita akeyi da kyar ya samu ya dafa motar yana daga tsugonne cikin rud’ani ba tare da yasan da faruwar hakan ba yace, 

“Uncle ai da mun riga da ni da ita munyi alk’awarin aure, what I mean is ni nake sonta zan aureta….” 

Zaro ido uncle bashir yayi jin abinda Sultan ya fad’a, fitowa yayi daga cikin motar yana gyara malun-malun yana cewa, 

“Subhanallahi ai Ahmad mu bamu da labari kwata-kwata shi yasa ma muka za6i bata fahad ashema ‘yar gida za’ayi? Ah taso-taso mu shiga daga ciki dan Masan suma basu sani ba sai a canza ai duk d’aya ne kaida fahad d’in.” 

Uncle Bashir ya fad’a tare da rufe motar ya wuce cikin gidan, shi kuwa Sultan gaba d’aya ji yayi garin yana juya mai tamkar sama zata fad’o mai ya rintsa ido a gurin ya kasa tashi, ji yayi an dafa shi gabanshi ya kuma bugawa jin kamshin turaranta a kusa dashi sai ya kuma yin k’asa da kanshi, shi wallahi abinda ya fad’a yayi ne dan irin yadda Balqees d’in keyi idan taji Yusif na cewa zai aureta, toh ko dai shi be iya yin da barar bane har yasa ya fad’i haka gashi tana nema kwa6e mishi?kai a’a yana fa jin zuciyar shi yadda takeyi idan yaji wani yazo neman auranta, ji yake kamar zata fashe mai, yanzu ya zaiyi me zai cewa Nadiya da ita kanta babyn da wane idoma zai iya kallonsu musamman Nadiya!tabbas yana cikin tashin hankali. 

Muryar Nadiyan yaji tana mai magana cikin damuwa ganin halin da yake ciki, Nadiya ta kuma rik’e kafad’unshi tace. 

“Wai mine me yake damunka ne ka tsuguna anan gurin?!” 

Da sauri ya waigo yana kallonta da jajayan idanunshi gabanta ya fad’i ta sake kallonshi sai ji tayi ya janyota yana cewa, 

“Kina son kice min wai bakiji abinda uncle Bashir ya shiga yana fad’a ba?!” 

“Wallahi banji ba naji dai ya kira daughter hakan yasa ni kuma na fito kasan ai ba zama zanyi naji abinda zai ce mata ba shi yasa nayo waje. Gaya min meya ce?ko cewa yayi dole sai sun aura mata wanda bata son…” 

Da sauri ya jata jikinshi ya rungumeta tsam a jikinshi, wani tsananin kaunarta yaji yana yawo a cikin ranshi kafin ya d’ago fuskarta daga kan kirjinshi murya a sark’e yace mata. 

“My Nadi ke a ganinki ko a zatonki zan iya cin amanarki ko na tozartaki ko wulak’antaki…?” 

Kallonshi tayi jikinta a sanyaye duk da bata san ko meye ba haka kurum jikinta ya bata cewar akwai matsala wanda ya shafeta, cikin k’arfin hali dana zuciya tace tana shafa mai fuska, 

“La’lah mine, ko a mafarki ban ta6a kawowar wai zaka min duk wad’annan abubuwan daka lissafo kuma har abada ina addu’ar kar Allah ya nuna min ranar da zaka yi abu nace ka cuceni ko something that reletated to irin wannan abun da ka fad’a.” 

Sake rungumeta yayi cikin jikinshi yana faman matseta, ya rasa ta inda zai fara mata bayani can dai tace. 

“Wai menene yaka faruwa ka gaya min domin wannan yanayin maka yafi komai d’aga min hankali, please dan Allah ka gaya min kabar zuciyata cikin zullumi da fargaba.” 

Sake janta yayi jikinshi duk sai taji wani iri nan da nan ta fara sake-sake cikin sanyin muryar shi yace, 

“Wai…wai..wai in..inji uncle Bashir cewa ya..yayi ni…ni zan auri bab..bab….baby, please ki gaya min my sweet Nadi ya zanyi? Yama za’ayi ace nine zan aureta dan kawai nace bata son Fahad..?!” 

Ras!.. Ras!! Ras!!! K’irjin Nadiya ya buga kafarta tayi sanyi tayi luuuu zata zame ta fad’a daga jikinshi yayi saurin rik’ota ya rungumeta sai kawai yayi waje da ita ya tari taxi suka nufi hotel d’in da ya Kama hankalinshi a mugun tashe… 

A can gidan kuwa uncle bashir ya same su duka a parlour yace a kira mai Balqees, fitowa tayi a sanyaye guskarta jage-jage da kuka ta k’arasa ta zauna kowa sai kallonta yake ana tambayarta ko lafiya amma tak’i cewa komai uncle bashir yayi murmushi yace, 

Ku rabu da ita ashe Fahad ne bata so sabida sun riga sunyi agreement na aure ita da yayanta Ahmad yanzun nan yake sanar dani.” 

“Yaya Bashir wane Ahmad kuma…?!” 

Aunty sa’adatu ta tambaya cikin mamaki shi kuma uncle bashir yayi dariya yace, 

“Ahmad dai yayan ta wanda suka zo tare.” 

Ai razane Balqees ta mik’e idanunta a waje hannunta dafe da kirjinta tana shirin yin magana Aamanee tayi tsagal tace, 

“Tabbas kuwa uncle haka ne ni d’innan sheda ce wallahi Balqees tana mutuwar sonshi.” 

Sai kuwa guri ya kaure kafin Maman fahad d’in ta fara fad’a wai an raina mata hankali mafi yawa kuma murna sukeyi musamman da akaji cewar suna son juna. 

Da gudu Balqees tayi gurin uncle bashir ta rungumeshi tana kuka uncle bashir ya bata hakuri tare da yi mata alkawari masu yawan gaske Afrah da Aamanee sai dariya suke mata. 

Daga nan uncle bashir yana fita abban sultan ya buga ya sanarwa Abba yayi murna sannan yace zai sanarwa da hajiya kaka duk abinda ake ciki zai sanar mai da haka suka ajiye wayoyin. 

Tunda suka tafi hotel d’in Sultan yake faman…..

    Tunda suka tafi hotel d’in Sultan yake faman kakkafewa kan nunawa Nadiya cewar shima cewa aka yi ya aureta ba wai dan kanshi bane, ita dai bata ce mai komai ba tana dai jinshi zuciyarta sai addu’ar nenan tsarin yi mai abinda be dace ba take yi, bata son yin magana dan k’ila ayi 6atacciya ita dashi dan haka tayi shiru tana hawaye yayin da ya makaleta a jikinshi ji yake gabaki d’aya ya tsani kanshi. 

Basu k’ara magana ba musamman ma ita Nadiyan, kayanta ta shirya duk yana kallonta gabaki d’aya ya kasa cewa komai harta gama shirya kayan sannan ta zauna kusa dashi tana kallanshi tace. 

“Temaka min dan Allah kaje ka d’akko min Humairah ba dan niba, ina son komawa Nigeria ne yau.” 

Cike da mamaki yake kallonta tayi mai wani d’an guntun murmushi wanda iyakarshi saman leb6anta ya rungumeta cikin tashin hankali yace. 

“My sweet Nadi tafiya zaki ki barni bayan tare muka zo kuma ina matsayin mijinki amma ki tafi ki barni a lokacin da nake tsananin buk’atarki? karki min haka ki bari mu tafi tare kamar yadda muka zo karsu zargi wani abun, sannan kuma zan gyara abun kafin faruwar hakan dan baxan iya auran baby ba jinta nake tamkar ni na haifeta please…” 

Hawayan da take 6oyewa sune suka zubo mata sannan ta kalleshi cikin kuka tace, 

“Kayi hakuri abban humaira amma bazan iya zama a garin nan ba, idan har baka son nayiwa Allah butulci da kuma nuna cewa ban yadda da tsarinsa ba to kabarni na tafi gida bana son abinda zai zamo sila a sanadina ace wani mumunan abu ya faru, tunda kaji an furta zancen aure tsakaninku toh haka Allah ya kaddara bani da ikon canza wa, kuma ban ta6a saka ran cewar dani kad’ai zaka zauna ba tunda mukayi aure dan haka yanzu ma banaja da ikon Allah, but ka barni ka kuma lamince min na tafi.” 

Haka Sultan ya dinga aiyanawa cikin zuciyar shi, kallonta yayi yaga itama still shi take kallo yayi saurin kawar da kai, domin wata muguwar kunyarta yakeji a cikin zuciyar shi da gangar jijin shi. cikin sanyin jiki yace mata. 

“Toh ki had’a mana kayan tare sai mu wuce gabaki d’aya ni dake d’in.” 

Mik’ewa tayi tsaye ta k’arasa wajan trolley d’in sannan ta d’akko mayafinta ta kuma komawa wajanshi, hannunshi ta kamo zata fara magana sai hawaye suka fara zirarowa ya kamota jikinshi ta daure cikin kukan tace. 

“Dan Allah karka bini mu koma tare, karka sanya suyi mana wani zargin kaji? Kayi zamanka har nan da sanda zaku dawo, abban Humaira wannan karan ne zaka kare min mutuncina da martabata tare da kare hakkina a wajansu, kasan duk abinda zaka gaya musu bayan na tafi ta yadda baza su gane cewar nice na buk’aci yin hakan ba. Yau ne zaka nunawa duniya cewar ga irin soyayyar da kake min ta hanyar rufamin asiri a idon duniya nayi maka alk’awarin kare maka naka kaima a duk inda naji ana neman cin zarafinka.” 

Ta k’arasa magana cikin kuka ya kuma rungumeta a jikinshi har tsawon wani lokaci, zame jikin nata tayi tana sharar kwalla tace, 

“Dan Allah ka d’akko min humaira mu had’u da kai a airport zanje na samu veser a yanzu koda kuwa ta dare ce.” 

Story continues below


Sam Sultan kasa tashi yayi ya fita ganin haka yasa Nadiya jan trolley d’inta tayi waje hakan yasa shi biyo ta da sauri ya tari gabanta tak’i kallonshi domin zuciyar ta tafasa kawai takeyi da kyar take samun damar yin hailala sabida rad’ad’i da tsabar bugun da takeyi. 

“Dan Allah my Nadi karki tafi ki bari mu koma tare kinji?!” 

Yayi maganar yana dafo kafadunta tayi murmushi me zafin gaske kafin tace, 

“A’ah idan muka tafi mu duka bamuyi adalci ba sannan ko ba komai Balqees tamu ce kayi zamanka kawai.” 

Ya kura mata ido cikin mamaki dan yau sai kashe shi take yi da abubuan da batayi take, a yaune ta kirashi da abban humaira sannan a yaune yaji ta ta6a kiran sunan Balqees d bakinta lallai anyi mata abinda bataji dad’in shi ba. Da kyar ya samu zarafin yin magana yana mai kar6ar jakar hannunta yace. 

“Ki koma ciki tukunnan kafin na kar6ota.” 

Ba musu kuwa ta koma cikin d’aki ya shigar mata da kayan sannan ya fita jikinshi duk a sanyaye, waya ya ciro ya kirawo Ahmad yana d’agawa ya rok’eshi alfarmar ya kawo mai humaira hotel, yana nan a tsaye kuwa har wani lokacin sai ga shi ya kawota anyi mata wanka da kwalli ya kar6eta yayi mai godiya sannan ya wuce ciki. 

Yana zuwa dai-dai k’ofa ya bud’e, tarar da ita yayi tana sallah ya zauna yana kallonta cikin zuciyar shi yana tunanin gara yaje ya gayawa baby gaskiyar lamari cewar shifa yayi irin yadda takeyi ne amma ba gaskiya bane zancen dan kila itama tana can tanajin haushin shi akan yace zai aureta tunda yasan yadda take son imran. 

Saida ta idar sannan tayi addu’a suka shafa a tare kafin ta mik’e ta gyara mayafin jikinta, kallonshi tayi humairah sai mik’o mata hannu take ta k’arasa kusa dashi ta k’ar6e. 

“Bari na fara bata tasha kar sai mun shiga jirgi ta fara min kuka.” 

Kallonta kawai Sultan yake ganin yadda take abubuwa cikin nuna k’arfin hali, harta gama bata babu wanda ya iya magana a cikinsu. 

Mik’ewa tayi tana kallonshi tare da sakar mishi wani marayan murmushi tace, 

“Muntafi sai kun taho, Allah yasa ayi taro lafiya a kuma gama lafiya.” 

Trolley d’in taja ta fita shi kuma duk ya sandare yama rasa abinda zai yi, tashi yayi da sauri yabi bayanta lokacin har ta fita harabar hotel d’in yaje ya k’ar6i trolley d’in nata suka k’arasa bakin titi, me taxi ya tarar musu ganin ta shiga shima ya shiga ne yasa ta zaro ido cikin mamaki tace, 

“Ya haka abba humairah kardai binmu zakayi?!” 

Da kyar ya samu bakin yin magana, shi tunani ma yake idan ya zauna me zaiyi amma idan ya tafi nan ma akwai zargi gashi yana son ganin Balqees dan ya shaida mata cewar da wasa yake yi. 

“Zanje na kaiku airport d’inne sai naga tafiyar Ku tukunna.” 

“Godiya muke yalla6ai.” 

Ta fad’a tana gyarawa humaira gyaran gashin da akayi mata, suna zuwa airport d’in suka fara cuku-cukun yadda zasu samu jirgin da zai je Nigeria a lokacin cikin sa’a suka yi komai yana ji yana gani Nadiya ta tafi shi kuma ya koma hotel d’in dan nemawa kanshi mafita. 

***** 

Su kuwa su Balqees ana cikin farin ciki a take tana komawa d’aki ta kira kawarta sdy ta shaida mata nan suka hau murna suna farin ciki. Da yamma suka shirya suka tafi partyn da aka shirya amma har lokacin fa basu sake ganin Sultan ba, rabonta dashi tun daya bar d’akinsu tayi nema tayi cigiyar harta gaji bashi ba Nadiya ba humaira. 

Misalin k’arfe 10:00pm na k’asar dare ne amma tamkar rana dan yadda mutane ke harkokinsu tamkar suna yi da rana Sultan yaje gidan su Aamanee, kiran Balqees yayi ta d’aga sannan yace taxo ta sanar mai bata gida amma gasu nan sun taho, guri ya samu ya zauna yana jiransu aikuwa tana zuwa ta ganshi fuskarta cike da tsananin farin ciki yaja hannunta suka koma inda baza’a gansu ya kalleta yace. 

“Baby kinji abinda uncle bashir ya fad’a ko? Toh dama….” 

Be k’arasa ba yaji ta fad’a jikin shi tana kuka cikin kukan yaji tana fad’in, 

“Yaya zulkallain naji, naji abinda uncle ya fad’a ashe dama kaima kana son ka aureni? Ashe Yaya bani kad’ai bace nake haukan sonka ba? Yaya nasha wahala akan kaunarka da kullum nake kukan rashin samun yadda nakeso daga gareka? Yaya Sultan I so much love you, wallahi ban ta6a son kowa a duniya ba kamar yadda nake sonka ashe kaima kana son ka aureni Alhamdulillah ko yanzu Allah ya kar6i rayuwata zanyi alfahari da wannan ranar a kuma wannan gurin cikin wannan lokacin…” 

Gabaki d’aya jijiyoyin jikinshi suka nannad’e hankalinshi yayi kololuwar tashi tunaninshi ya tsaya cak a hankali ya sauke kwayar idanunshi a kanta kirjinshi na tsananin bugawa har tsawon wani lokaci sannan yayi k’arfin halinyin magana yace, 

“Fahimtar dani baby! dama wai kin dad’e kina min so irin na aure…?!” 

Balqees ta hau kad’a mai kai alamar eh fuskarta fal hawaye kafin ta d’ora da cewa, 

“Na dad’e ina sonka Yaya tun lokacin da kana zuwa min visiting hakan yasa nak’i bawa kowa damar shiga cikin zuciyata, mun samu matsala sosai da Abdul-malik d’an gidan A.A marafa wato gidan da na zauna a can k’asar da nayi karatu sabida nace bana sonshi, bayan na dawo Nigeria na dinga nuna maka amma Yaya sam ka kasa ganewa inda na nufa daban kaima yadda kake d’aukata daban har na samu matsalar broth Yusif amma still ka kasa ganewa, a yau kuwa da na hakura da kai zan yadda na auri broth fahad badan ina sonshi ba sai kuma aka zo aka sanar min cewar ashe kaima kana sona duk kuwa da cewar ina matukar jin nauyin aunty Nadiya amma nakanyi tunani cewar kawai shigar sauri tayi min na rasa yadda zan 6ullo muku ganin yadda koke son juna.” 

“Innalillahi wa’inna’ilaihir rajiun how…why…na kasa gane hakan? But baby kinsan mene nifa…” 

Be k’arasa fad’a ba yaji ana kiran ta, 

“Balqees uncle Bashir yana kiranku keda angon naki.” 

Cewar Afrah yayin da kirjin sultan ya kuma bugawa ita kuma Balqees ta k’arasa wajan Afrah suka k’arasa d’akin shima sultan yana binsu a baya har suka shi jikinshi duk yayi wani sukuku kai da ka ganshi kasan yana cikin rud’ani. 

Be samu zarafin sake magana da ita ba gashi uncle bashir yace masa gobe su abba zasu zo shida daddyn Yusif dan su halarci taron d’aurin auran wanda za’ayi washe gari. 

Hotel ya koma gabaki d’aya Duniya tayi mishi zafi, gashi sai faman kiran Nadiya yake amma not available sai kawai ya kira Ummi wato mahaifiyarta suka gaisa yaji batayi mai zancen zuwansu Nadiyan ba har suka yi suka gama gashi muryarta faran-faran a sake alamar har lokacin bata samu labari ba nan fa hankalin shi ya k’ara tashi ya dinga tura mata text message no reply gabaki d’aya sai Sultan ya fara…..😉

    
    Ya fara sambatu duk ya rasa inda zai saka rayuwar shi, tashi yayi ya fita domin zuciyar shi bata cikin nutsuwa ya tari taxi ya wuce airport dan jin abinda ke faruwa. 

Yana zuwa ya tambaya nan aka sanar dashi cewar tuni jirgin ya sauka Lafiya a abuja tare da fasinjojin nan sultan ya fara tunanin ina Nadiya ta shiga, ba yadda ya iya haka ya koma hotel a ranar be rintsa ba har akayi sallar asubahi. 

Ita kuwa Nadiya suna sauka taxi ta tara ta wuce gidan yayar Ummi, tana zuwa suka tarbeta cikin murna da jin dad’i aka kaita d’aki tayi wanka tayi sallah tayi duk wasu addu’o’in da takeyi sannan tabi lafiyar gado ko abincin da aka kawo mata bata kallar ba. 

Wayarta ta ciro tana kallon wallpaper d’inta hotan sultan ne hannunshi rik’e da humairah gabaki d’ayan su sunyi dariya wawulan humaira a waje shi kuma fararan hakoranshi sun fito bata san lokacin da tayi murmushi me sauti ba kafin ta shafi screen d’in, contact ta shiga ta nemo sunanshi be mine sannan ta girgiza kai a take ta goge ta saka abban humaira tana share hawaye sannan tayi switch off d’in wayar ta kwanta amma sam bacci ya gagareta har wajan 2:30am hakan yasa ta mik’e ta kuma tada sallah dan ci gaba da neman yardar ubangiji da samun nutsuwar zuciya. 

Sultan kam yana idar da sallah wayar shi ya d’auka ya dinga kiran Nadiya amma sai ace arufe take kafin kace mene wani zazza6i mai tsananin zafi ya kamashi da ciwon kai tamkar zai fad’o mishi ko kwakwaran motsi baya iya yi. 

Misalin k’arfe 4:30pm na k’asar ethopoeia su abba suka sauka, direct gidan uncle bashir suka nufa sai da suka yi sallah aka kawo musu abinci suka ci sannan uncle bashir ya sake korowa su abba labarin abinda ya faru, abba yayi farin ciki yayin da daddyn Yusif ya kalli abban Sultan ranshi a 6ace yace, 

“Zancen banza zancen wofi kenan ni za’a wulakanta? Banda wulakanci ansan cewar ga yaron daya jima yana sonta tun kafin tasan hankalinta yake fama da ajiyar kaunarta shine ni za’a yiwa rufa-rufa sai ankawoni wata k’asar tukunna za’a sanar dani? Toh wallahi an min ba dai-dai ba musamman ma kai yaya tunda kasan yadda mukayi dakai…!” 

Mamaki da al’ajabi suka kama abba jin abinda kaninshi gudan jininshi yake fad’a a gaban wani, kallon shi ya sake yi cikin karyar da kai yace, 

“Amma na d’auka yanzun nan muna tare da kai ake sanar mana yadda abin ya kasance? Habba Abdul-jalal me yasa wani sa’in kake yin abubuwa kamar na yara? Please dan Allah ka bari muyi komai cikin kwanciyar hankali, mace bata ta6a auran mijin da banata ba haka zalika namiji ma baya auran matar da batashi ba, ni a ganina Ahmad da Yusif duk d’aya ne babu banbanci tsakaninsu.” 

“Gaskiya ne haka ne Alhaji.” 

Cewar uncle bashir yana faman jijjiga kai alamar tabbatarwa, 

Mtwww daddy yaja wani dogon tsaki, bazaka ta6a tunanin cewar namijine yayi shiba bare kuma a ce maka magidanci ne suka bishi da kallo ya mik’e tare da karkad’e babbar rigarshi ya kallesu cikin tsananin 6acin rai yace. 

“Ni baza’a raina min wayo ba kun had’a baki zaku yaudareni, kunga tafiya ta Allah ya had’a kowa da rabansa…!” 

Yana kaiwa nan yabar sitting room d’in zuciyar shi na zafi abba sai kiranshi yake amma fur yaki kulashi jikin shi yayi mugun yin sanyi ji yake tamkar ya kurma ihu ganin cewar jininshi d’an uwanshi shine yayi mai wannan cin fuskar a gaban mutane wanda yake ganin girma da mutunci. 

Story continues below


“Kayi hakuri alhaji bansan da wata maganar wani akan ta ba kuma ni Ahmad d’in ma be sanar dani ba kawai nuna min yayi ai shine yake sonta kuma sun sasanta, danaje mata da zance kuma alhaji karka so kaga yadda farin ciki ya wanzu azuciyarta wanda ban ta6a ganin irin shi ba, sannan karka so kaga yadda take a yanzu tafi kuwane lokaci murna da nishad’i.” 

Uncle bashir ya fad’a, murmushi abba yayi sannan yace. 

“Ba komai tunda dai mahaifiyar mu ta amince toh duk wanda zai nuna 6acin ranshi akan hakan ai a banza ne dan hajiya dana gaya mata cewa tayi ko mutuwa tayi a lokacin toh kar a sake a d’aga ranar d’aurin auran nan toh kaga dan yayi hakan bazai hana ayi abinda za’ayi ba Allah ya nina mana goben lfy.” 

Uncle bashir ya amsa sannan suka ci gaba da hirarar su, kiran Sultan d’in suka dinga yi amma tak’i shiga sai da abba ya dad’e yana kira sannan yaji an d’auka. 

“Ina ka shiga ne Ahmad??” 

“Abba ina hotel d’in dana sauka kazo ne…?!” 

Ya buk’aci ji duk da cewar muryarshi na rawa, cike da zargi abba yace. 

“Ok toh amma dai bakada lafiya naji muryarka haka?!” 

Zuciyar Sultan ta Kara shiga cikin rud’ani yace. 

“Ah abba ciwon kaina kuma yayi sauk’i yanzu ma zanzo gida.” 

Abba yace, 

“Toh shikenan ina Nadiya ko tana gidan bikin?!” 

Sultan ya rintsa ido ya rasa me zaice sai kawai ya katse kiran da nufin beji maganar da abban keyi mai ba. 

Sai da aka yi magrib sannan sultan yazo lokacin gidan yayi dank’am da mutane maza da mata, a can wajan wani gurin shak’atawa Sultan yaga su abba nan ya k’arasa jikinshi duk a sanyaye, gaida su yayi sannan suka yimai ya jiki abba ya d’ora da cewa, 

“Ina Nadiya ne Balqees tace ita sam bata ganta ba tun jiya ina ta shiga…?!” 

Cikin da kiya sultan yace, 

“Eh abba tun a jiyan da taji zancen tace toh baza akai k’anwarta babu kayan lefe fa dan haka ta wuce London tun ajiyan wai ita zata had’o mata.” 

Cike da mamaki su abba suka dinga sanya mata albarka dan duk sun d’auka zata yi irin borin nan irin wanda mata keyi idan za’a musu kishiya. 

Hotel d’aya suka kwana abba da Sultan washe gari kuwa aka shaida d’aurin auran Aamanee da alhaji Tukur sannan akayi na Ahmad da Bilkisu wanda abba yayi wakilcin na Balqees yayin da uncle bashir yayi na sultan akan sadaki dubu d’ari cif na Aamanee kuma d’ari uku Sultan ba aboki ko d’aya dan haka ana gama d’aurawa ya tafi hotel ya fad’a kan gado ya rasa a wane yanayi yake jinshi farin ciki ko akasin hakan. 

Yana kwance dafe da kanshi yaji k’arar text message kamar karya duba sai yaji zuciyar shi nasan ganin ko meye dan haka ya janyo wayar take yaga sunan Nadiya jiki na rawa ya bud’e ya fara karantawa. 

_”I wish your married life be filled with love, happiness and everlasting romance. Happy married life to the newly wed’s._” 

Yana gama karantawa ta sake turo mishi wani na ban hakuri sabida tasan ya nemeta be samu ba ya sake dubawa jiki a sanyaye. 

Kiranta ya hauyi amma tak’i d’agawa dan haka shima ya tura mata nashi text message d’in. 

_”My Nadi you are the one, whom I think about while I go to bed, and the reason I blush while listening to love stories. When you hug me, it makes me forget the world outside. I feel so special and so loved. No one in this world can make me feel this way Nadi. I love you_.” 

Yana turawa sai ga kiran Balqees ya shigo rasa yadda zaiyi yayi sai dai bazai iya k’in d’auka ba, cikin sanyin jika ya kara a kunnen shi yana sauraranta. 

Daga can 6arin Balqees ce sai faman kuka takeyi yana daga kwance sai gashi a tsaye kan k’afafuwanshi cikin tashin hankali ya fara tambayar ta, 

“Baby lafiya? Menene?!” 

Cikin kukan ta fara magana tana cewa, 

“Yaya menayi muku ne haka dakai da aunty Nadiya? Ko auran ne yasa kuka d’auke min k’afa ko kunma koma gida ne ban sani ba? Me yasa kasan zaku yi min haka kace zaka aureni? Shin ko dama dan ku…” 

“Ya isa haka baby ki nemi Ahmad na nan gida kice ya kawoki masauki na idan kinzo mayi maganar.” 

Haka aka yi kuwa tana gama wayan ta fita waje da kyar ta samu aka gano mata shi ta gaya mai yana tayi mata tsiya  tayi mai shiru fatanta kawai akaita wajan su taji dalilin daya sa basa zuwa gidan tunda aka ce zata aure shi, suna zuwa Ahmad ya kaita har bakin k’ofar d’akin sultan d’in sannan yayi tafiyar shi. 

“Yaya ina su aunty Nadiya, duk da cewar nasan k’ila yanzu babu wanda takejin ta tsana a duniya sama dani. Yaya nima haka na d’and’ani wannan rad’ad’in ranar da aka d’aura auranku, sai da….” 

Kasa k’arasawa tayi jin cikinta ya tsira mata tayi saurin rintsa ido tana cizon le6anta, shi kuwa sai faman kallon ta yake yi domin maganganunta kullemai kai suke yana kuma mamakin yadda akayi shi duk be gano hakan ba sai yanzu da take warware mai zare da abawa. 

“Washh Allah nah nashiga uku..” 

Ganin yadda take faman rik’e ciki ne yasa Sultan saurin k’arasawa inda take ya rungumota wani fitinannan kamshi yaji ajikinta mai sanyaya zuciya ya lumshe ido a hankali yace, 

“Baby menene…?!” 

Balqees ta damk’i hannunshi tana faman cizon lips tace, 

“Yaya mara ta, marata ke min ciwo wayyo Allah…” 

Nan da nan ya kuma rud’ewa cikin tashin hankali ya….🤪

    
    Ya d’ago ta amma sai sake nakewa take yi a jikinsa kasan cewar ita kad’ai tasan yadda take ji, zame jikinta tayi daga nasa ta zame k’asa tayi gohu kamar me yin sallah duk ta rasa yadda zata yi. 

“Baby dama kina irin wannan abun ne..?!” 

Ya tambayeta yana daga tsugunne a kusa da ita jikinshi duk yayi sanyi, a hankali Balqees tace. 

“A’a Yaya amma daga last month na fara bana sonshi wallahi ji nake tamkar zan mutu.” 

“Sannu baby me kike sha ya dena yi miki zafin?!” 

Sake mik’ewa tayi tana faman zuk’ar iska ta cikin bakinta ta koma kan kujera tana yarfa hannu tace, 

“Wallahi Yaya ban sani ba, lokacin da nayi aunty Nadi ce ta bani wani magani kamar ruwa nasha amma ban san ko meye ba nima.” 

Zaro ido yayi yana kallonta jin abinda tace, cikin zuciyar shi ya fara tunanin. 

_”Yanzu ya zai yi? Ai da tsagwaran kunya ya tambayi Nadiya ya gaya mata cewar baby na ciwon Mara wane maganin zai bata ba zai iya ba dan zata iya yi mai wani zargin.”_ 

Yana can yana tunani ya rasa mafita yaji Balqees d’in na cewa. 

“Yaya dan Allah maidani gida bazan iya zama anan ba please.” 

Tashi yayi ya koma kusa da ita tare da janyota jikinshi amma ta kwace sabida sam bata jin dad’in rik’on da yake mata, kai ya shafa yana kallonta yace. 

“A hakan zan fita dake na kaiki gida Kina faman durkushewa k’asa? No sai kin bari ya dena yi miki sannan zan rakaki yanzu dai ki bugawa Nadi ki tambayeta meye maganin da ta ta6a baki.” 

Wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauk’e tana cizon le6anta da hakoranta can kuma tace, 

“Hmmm Yaya yaushe rabona da ita..sam wayanta baya shiga ita kuma  bata nema na nasan kuma duk wannan abun ne ya janyo hakan.” 

Nan Sultan ya rasa yadda zai yi, kallon shi Balqees tayi da kyar sannan tace, 

“Yaya wai ina suka tafi ne dan Allah ka gaya min.” 

“Baby Nadi taje London had’u miki kaya tace da kanta zata yi wannan aikin, nace tabari sai mun koma gida wai a’a har humaira ta d’auka tace wai karta dameki…” 

Murmushi Balqees tayi cike da farin ciki, mik’ewa tayi ta koma kan hannun kujera sannan tace, 

“Allah sarki aunty Nadi wallahi nasan baza taji dad’i ba duk da cewar wata rana idan muna hirar kishiya takan ce min _daughter ni bana gudun kishiya sai dai kawai ina tsoran a kawo min wadda zata rabani da mijina, kishiya ai Allah ke bada ikon ayota kamar yadda aka auro mutum.._ ina jin kunya wallahi yanzu ace nice kishiyar ta wallahi Yaya ina jin kunya a yanzu.” 

Kallonta yayi yadda yaji tana zuba uban surutu wanda be tambayeta ba, ita kuwa Balqees azabar ciwo ne yasa ta wannan surutun ya mik’e ya fita zuwa waje, wani pharmacy yaje ya gaya musu nan suka bashi magani ya koma yana zuwa yaga bata parlor’n hakan yasa shi wucewa ciki sai ya ganta ta kwanta akan gado amma duk rabin jikinta yana k’asa ya d’an lek’a fuskarta idanunta a lumshe da alama bacci ya d’auketa a haka. Maganin ya ajiye akan bedside drawer ya fara k’ok’arin gyara mata kwanciyar aikuwa yana ta6ata ta farka ta fara shure-shure tana cizon le6anta sabida azaba cikin wahala tace. 

Story continues below


“Yaya why (Yaya meyasa)..?!” 

Tsayawa yayi yana kallonta cikin mamakin tambayar da tayi masa, komawa tayi ta kwanta yace. 

“Baby tashi kisha magani gashi na siyo miki.” 

Shiru tayi dan yanzu ko magana batasan yi, parlor ya koma ya zauna yayi shiru yana mamakin yadda yanzu abubuwa suka sauya mai wai yau shine ya auri baby yayin da Nadiya ta tafi ta barshi bayan hakan bata ta6a faruwa ba tunda suka yi aure. Wayar shi ya zaro ya kira layin nata cikin sa’a kuwa ta d’auka sai da ya sauke wata k’atuwar ajiyar zuciya lokacin da yaji ta kira sunan shi kuwa kawai kan kujera ya fad’a yana shafar kanshi idanunshi a lumshe yace, 

” My Antibiotic’s, my chocolatynah, bae of life kin wahalar dani my Nadi kin sani cikin damuwa da zullumi why kike kashe wayarki bayan kinsan bazan ji dad’in hakan ba…?!” 

“Yi hakuri abban humaira banyi hakan dan na kona maka ko 6ata maka raiba, afuwan karka yi fushi dani kaji mijin mu.” 

Murmushin yayi mai had’e da jin waya azababbiyar kunya da jin nauyinta sannan ya kuma lumshe idanuwa cikin sanyin muryar shi yace, 

“Na hakura kinsan bazan iya fushi dake ba amma meyasa yanzu kike kirana da abban humaira a memakwan mine dakike fad’a..?!” 

Yanajin tana murmushi shima sai ya tsinci kanshi da yi yana zagaye bakin shi da ‘yatsun sa guda biya, jin baza tayi magana bane yasa shi kuma cewa, 

“Ina jinki me yasa kika canza min suna?!” 

Kuma yin murmushi yaji tayi mai sauti sannan tace, 

“Kayi hakuri abban humaira amma karka tsaurara bincike, kawai hakan zan dinga ce maka daga yanzu.” 

“Toh ban yadda ba bana so ki sake wani.” 

“Yalla6ai shi kenan yayi maka?!” 

“A’ah ai da wannan gara ki koma baya ki barni a abban humairan meye wani yalla6ai sai kace wani tsoho….?!” 

Dariya yaji tayi sosai kamar yadda yasan Nadiyarsa nayi idan suna cikin nishad’i, ji yayi zuciyar shi nayin sanyi yanajin wata muguwar soyayyarta tana kara shigar sa ya fara ayyana kyawawan halayanta lallai Nadiya ‘yar halak ce yana kuma fatan ta d’ore a haka karta sauya halinta mai kyau. 

“Shi kenan toh my cherrypie sai anjima zanyi sallah bye-bye.” 

Yace, 

“Woww ina son wannan, bye ayi min addu’a.” 

“Insha Allah cherrypie.” 

…… 

Sai wajan k’arfe biyar na yamma sannan Balqees ta farka lokacin ciwon marar ya lafa mata sosai harma al’adarta tazo nan kuma wata shahararriyar kunya ta lullu6eta ko fita parlour ta kasa yi. Sultan ne daya shigo a lokacin ya dawo daga wajan abban shi dan a ranar zai wuce su kuma ya basu umarnin dawowa ranar litinin. 

Shiga cikin bedroom d’in yayi tana jinshi ya shigo ta rufe ido mamaki ya kamashi duk a tunaninshi har lokacin bacci take ya lek’a fuskarta nan yaga idanuwanta suna motsi gashi kamar tana son bud’esu ya zauna a gefenta yana danna waya yace, 

“Baby tashi akwai abinci a parlour kije kici baccin ya isa haka.” 

Dif ta sake yi baxata iya tashi ba sabida duk ta fara 6aci ya kuma kallonta murya k’asa-k’asa tace. 

“Dan Allah Yaya zani gida yanzu.” 

“Kifara tashi kije kici abinci tukunna.” 

“Na shiga uku.” 

Ta fad’a sultan yayi saurin kallonta cike da mamakin jin abinda da ta fad’a. Ajiye wayan yayi a gefen gado sannan ya mik’e tare da wulk’itota idanunta rufe tasanya hannu wad’anda suka sha jah da bak’in lalle a ‘yan gudil-gudil d’in yatsunta amma sai da yaji wani dam abinda be ta6a jiba tsakanin shi da ita tunda suke tare ba yayi saurin kauda kai tare da mik’ewa tsaye yana cewa. 

“Baby kifito nace fa.” 

Ganin ya takura sai ta fita ne yasa ta juya mai baya tace, 

“Yaya fa wanka zanyi kuma duk banida komai anan.” 

“Oh wai kina nufin abin yazo ne…?” 

Balqees ta d’aga mai kai alamar eh sannan ya juya ya fita, be dad’e ba sai gashi da leda ya shiga bedroom ya bata sannan ya koma parlour yana jiran ta gama taci abinci yaje ya mayar da ita gida. 

Bayan fitar shi Balqees ta janyo ledar taga English wear’s riga da skirt sai pad da pant da kuma have vest tayi murmushi sannan ta mik’e ta shiga bathroom Allah yaso bata 6ata bedsheets d’in ba dan haka tana fitowa ta shirya tasa kayan kamar ya aunata duk da cewar dama yasan size d’inta ta d’auki turarukan shi dake kan mirror dressing ta fesa sannan ta yafa mayafin da ta cire ta fita parlour kamar ba Balqees da ta gama walainiya a kasa ba ta fito shar da ita. 

“Yaya ina yuni..?” 

D’agowa yayi yana kallonta sosai tayi kyau duk da cewar ba ko powder a fuskarta, kusa dashi ya nuna mata taje ta zauna yaji wani diran bak’on al’amari ya kuma ziyartar zuciyar shi, ido kawai ya rintsa ya fara tunanin wai daman son Balqees yake yi irin wannan da har yake jin shi cikin wani yanayi, kallon fuskar shi Balqees tayi cikin sanyin murya tace. 

“Yaya bacci zaka yi?!” 

Ya bud’e idanuwan ba tare da ya kalleta ba yace, 

“A’ah baby je kici abinci na maidake anata nemanki tun d’azu.” 

“Yaya banajin yunwa.” 

Kallonta yayi da mamaki ganin tun dazu take kuma ko ruwa bega tasha ba yace, 

“Me kika ci da kika koshi?!” 

“Ba komai amma bana sha’awar komai.” 

Tashi yayi yaje ya d’ibo abinci ya dawo kusa da ita dan baya san ta koma bataci abinci ba ga olser d’inta dan haka da kanshi yaje ya zauna ya dinga bata tanaci kamar zata yi kuka, sai da yaga ta kusan cinyewa sannan ya kyaleta ya zuba mata juice tasha sai da ta huta sannan yace ta fito su tafi. 

Taxi ya tarar musu suka nufi gidan bikin shi har yama manta da cewar ana biki sai da suka shiga unguwar duk da cewar anata kiran magrib ai kuwa ko daga motar be fito ba tana sauka yace da me motar ya maidashi inda ya d’akkosu. Sai da yayi sallan magariba sannan ya koma room d’inshi yana shiga kiran Umman shi na shigowa cikin wayar shi, nan da nan hankalin shi ya tashi yayi picking tare da karawa jikin kunnanshi yasan yau sai Allah…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *