TAWA TA SAMENI CHAPTER 17 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
jim kadan wayata tayi kara na duba sai naga lambar
yayanmu da sauri na dubi gurin da yake bashi nan sai na dauka nace hello ya katseni ki sameni a wajen hall din nan gurin wayoyin nan ta kofar baya na fita da sauri can bayan wasu furanni na ganshi na isa cikin fargaba ya dubeni fuskarahi ba annuri yace me gayen nan yace miki?nayi shiru ba zaki gaya min ba?ya daka min tsawa jikina yana rawa nace yace ne yana sona,da sauri ya dubeni sonki?.
Na gyada kai alamar eh yace oh my God bana sanar
dashi krt zakiyi ba?to naji me ke kikace mishi?nace nima haka nace mishi ya dunkule hannunshi ya naushi dayan hannun sannan ya dinga kai kawo a filin gun mamakin shiga damuwar dayayi na tsaya yi a raina nace ya bar amaryarshi yana yin abin da bai dameshi ba,kamar ya san tunanin da nakeyi sai naji ya dawo gabana daf dani
yasa hannuwanshi ya rike kafaduna yace kar kiga na
shiga wannan halin kiyi tunanin inayin shishigi ne a cikin abinda bai shafeni ba,no yin karatunki shine kwanciyar hankalina kuma muddin na yarda wannan dan iskan ya soma cusa maki ra’ayin sonshi to zai min illa domin nasan Adam ba sanin yau ba yana da sa’a a rayuwarshi zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba tamkar ni yake,so bazan yarda da huldarku ba,nayi shiru ina tunanin wannan iko na yayanmu tunda yace tamkar shi yake sai ma naji ya burgeni na dubi yayanmu nace to in dai zai bari na gama karatuna why not na aureshi in kasan yana da hali mai…..kafin na karasa sai saukar mari naji cikin firgici na dube shi shima ni yake kallo ranshi a
bace,hawaye ya zubo min a kan fuskata yace kina hauka ne?kike kiran wani ya aureki?sai kuma naga yayi shiru ya juya min baya,Aminatu yaja sunan kafin na amsa Sai ya juyo da sauri ya zo guna ba zato sai gani nayi ya rungume ni tsam tsam a jikinshi gabana yana faduwa jikina na kyarma amma na kasa kwacewa ,nama kasa kokarin kwacewar gwaggwarona kaina ya fadi gashina ya bayyana a waje kitsona ya sauka a kan kafaduna ni kam
tamkar an jona ni a lantarki haka nake jina,cikin sanyin murya yake magana,Amina bana son ki saurari Adams zaiyi ma rayuwata illah nafi son sai kin gama karatu ne kafin ayi maganar auranki,ki fahimceni ba ina nufin hanaki aure bane a’’a ina son kiyi krt ne,wani haushi naji ya kamani domin a lokacin nayi zaton zai ce min yana sona ne,yanda naga yayi mugun shiga damuwa sannan ya kamani ya wani rungume yana faman ajiyar zuciya tamkar jinjirin daya kwana uku ba tare da ya sha nonon
uwarshi ba ina fama da sonshi tamkar na mutu shi kuma ya nan yayi aurenshi sannan ya zo ya wani rungumeni yana min maganar banza nasoma kici kicin kwacewa ya girgiza ni yace come on my sister ki…..kafin ya karasa maganar da zaiyi sai jin salati mukayi akanmu,cikin tsananin tsoro na juya su dayawa daga cikinsu akwai kannanshi da Amarya da Haj Laure uwar Amarya da wasu daga cikin danginsu,duk tsoro ya kamani,Amarya tasa kuka na dubeshi shi kuma ko ajikinshi duban su ma
yake yi na tattare zani zan gudu sai naji ya sa hannu ya riko ni……. Masha Allahu Alhamdulillah, mun Kammala littafi na daya Mu hadu a littafi na biyu
Tawa Tasameni 2-01
NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Cikin tsoro nake dubansu dukkansu ni suke kallo cikin
mamaki da sauri na dubi yayanmu shi kan murmushi ma
yake yana rike da hannuna muka isa gunsu Haj Laure ta Www.bankinhausanovels.com.ng
sakar mishi harara gami da cewa Abdulrahim kana da
hankali kuwa?fuskarshi a sake yake cewa me ya faru
momi?naga kun zo nan kuda yawa kuna faman rafka
salati,haushi ya kara kamata tace kai fa ka iya rainin
hankali rungume fa muka ganka da wannan bakar
yarinyar amma dayake ka iya duniyanci sai ka nuna ko a jikinka ita kuma tana wani kikkifta ido dama an saba da bin maza ai ka kyauta a kunnan uwarka in ni ka raina ni ka gamu da uwarka,ta juya fuu!sai kawai ya daga kafadunshi gami da fadin ke ya shafa ya juya ga sauran kannanshi uban me kuke jira?cikin sauri suka juya kowa yana yar kunkuni Amarya kadai suka bari tana faman rafsa kuka,ya saki hannu na yaje gunta ya dafa ta yana mata magana,ban dai san me yake ce mata ba, na san dai ba zai wuce lallashi ba har ya ciyo kanta ta fada
jikinshi ya rungumeta ganin haka sai kishi yataso min
kirjina yasoma nauyi sai na dauki Gwaggwarona da ya
fadi na tafi cikin takaici,na dubi wayata da take ta faman ruri a kan teburin robar dake gabana,ban dauka ba bare naga kowaye har ya tsinke,zaune nake kamar gunki ina tunanin rigimar da za’ayi idan zancen nan ya isa kunnen Haj Yaya?sannan in mama taji cewa yaynmu ya rungumeni na ma kasa komawa cikin hall din,kukan wayar nema ya kuma dawo dani daga tunanin da nakeyi cikin rashin kuzari na yunkura na dauki wayar,sunan
Mami na gani akan screen din na dauka ina fadin ya dai Mami?tace yaynmu ne yake nemanki,na danyi tsaki gami da fadin me zaiyi min?ni fa ban son a dameni,tace sai ki kirashi ki tambaye shi ni ban sani ba,ta kashe wayar nasan taji haushin tsakin da nayi mata ne Assalam ya yar kyakkyawa na zauna?da sauri na juyo Adams ne nayi ajiyar zuciya sannan nace zauna mana ya
zauna gami da fadin ya kike zaune anan ke kadai,nace
na gaji da hayaniyar ne shi yasa na fito nan,yace is good nima na nemeki ban ganki ba gashi bani da numbarki so daga baya sai nayi tunanin fitowa shine na fito gashi nayi WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
sa’ia baby tunamin sunanki,Amina sunana amma Iman
ake ce min ya gyara zama sannan yace sunan yayi min duka biyun yanzu ya maganar mu?nace wacce maganar kenan fa?yace ina sonki gane nifa ina sonki kuma aure ki sannan zaki yi krt ki a England domin can zan tafi dake ki yarda dani Iman ni mai sonki da dukkan gskyta ne,dubanshi kawai nakeyi dan gayan black beauty ne idanunshi masu kyau salon maganarshi da yan da yake kiran sunana sai ya kara burgeni kuma na ji zan lya yin uwar daki a rashin uwa wato zaniya auran shi a rashin
yaynmu….ya katse min tunani look Iman bani zuciyarki in dan shiga nasan zaki soni lokaci kadan ba mai yawa ba am yar kyakkyawa kinji?ya kura min ido nayi dariya shima sai dariyar ya keyi,nace kaci gaba da neman fada gurin yayanmu yanxu in yace ya yarda na aureka ni a gurina ba matsala yayi shiru na yan dakikai sannna yace nafiki sanin waye Maska din don in yace abu baya canjawa ni dai zan nemi so gareki tare da yardarki kuma tun da na ganki jikina ya bani kece madam dina da na dade ina nema ashe tana Nigeria,dariya ya bani sosai muna ta hira bamu ankaraba jin hayaniyar mutane mukayi ashe har antashi,yaya kabir ya maida mu gida
bayan munyi sallama da Adams akan sai gobe,kafin
lokacin kamun Amarya tuni lbr ya bazu yaynmu ya
rungumeni na idar da sallar ishai mama ta kirani wane Ibr naji ana faman riritawa a gidan nan,cikin in ina na gaya mata abinda ya faru amma bance mata ya rungumeni ba ce mata nayi don ya kirani zai bani sako ko sakon bai riga ya fada min ba sai gasu haj laure shine suke ta surutunsu mama tace ance wai har rungume ki yayi?cikin sauri nace aa bansan wannan ba shiru na dan lokaci sannan ta juya ta fita,washe gari da safe misalin karfe tara ina ta faman yiwa mama gyaran daki ita kuma
tana dakin Alhj tana mishi gyara kasancewar yaune
daurin aure,karar wayata na juyo daga dakinmu na nufi dakin sai muka hadu da Jamila zata kawo na amsa ina fadin Jamila har ynxu baku wuce haddar ba,ina sagir? tace gashi can yaki yayi sauri ya saka kayan tacigaba da cewa anty don Allah dama mu zauna kinga yau fa bikin yayanmu daidai lokacin dana kara wayar a kunnena nace to anki din maza ku wuce
Hello yaynmu ne yace kina jina nace eh yace ban fa
karya ba bayan haka ina son ki hada mani kayana guri
daya kin gane?nace wanne kaya?yace ki dai sama min
abin da zan karya tukunna in kin zo sai ki gansu nace
to,bayan na gama sai na fito kamar munafuka don tun WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
jiya da abun nan ya faru ban fito ba tun da na shiga
daki,ina kicin ina hada mashi breakfast sai ga mami tace
wai shin jiya mai ya faru ne?naji wasu surutai itama
yanda na fada ma mami haka na fada mata tayi tsaki
sannan tace shine aka canza magana surutu kala kala
ana tayi ba dan Baba ya taka borki ba da sai anyi
rigima,gabana ya fadi nace waye ya gaya ma Baba
wannan lbr?tace oho kila yaynmu ne dan sun rasa wanda
ya gaya mishi. Nayi sallama a dakinshi da tire a hannuna
shi kadai ne zaune kan kujera na ajiye tiren sannan na gaisheshi ya bude kula me kika kawo min?nace gashi nan dai duba,yace to sauran ki hada min kayana nace wane kayan?yace gasu can kinsan yau zanyi kaura shine
nake aon insa kabir ya kai min kayana haushi ya kamani
ban ce komai ba na shiga dakin a raina nace me shegen
zumudin tsiya kawai,ba karamin gajiya nayi badahada
kayan nan akwati hudu na cika banda wata jaka babba
wasu kayan ma ina ganin bai taba sa su ba,yawanci
kananan kaya ne manyan akwati daya na cika ga kuma sauran nan cikin durowar kayan shi itako babbar jaka duk JC ne da sauransu,na gama ina shirin fitowa naji
sallamar Haj yaya can cikin falon ya amsa sannan ta
shigo tana fadin kai da waye naga takalmin mata?
gabana ya fadi a sauri na shige bayan labule na boye ya amsa mata da cewa ni kadai ne ta leko bedroom din tana
fadin wannan kayan fa?yace ina shirya su ne don inason WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
kabir ya kai min can gidan yakubu avenu,ta karasa
shigowa cikin bedroom tana fadin matsalarka kenan baka
son manyan kaya sai aukin dinkasu tazo kusa dani ta
tsaya tana kallon kayayyakin ni kam jikina rawa yake a
bayan labule gashi bata magana a hankali don tunda
dama haj yaya mafadaciya ce don haka ko maganar
arziki takeyi sai kaji tamkar tana fada ne, Yayanmu yana
tsaye a bakin kofa yace Haj menene kike nema ne tace
magana zamuyi yanzun maganar kayan nan fa ba kace
komai ba?yace kaya gasu nan ki diba dama inason rage
ma kabir ne don sun min yawa sosai kinga fa ko abikin
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG