TAWA TA SAMENI CHAPTER 21 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 21 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI


                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Adams ya bashi mamaki sai naga ya dauke fuska a
daure,hannu yaba Adams suka gaisa sannan yace dama naso daga nan gidan Nasir zan sameka muje ku gaisa da Amarya sannan mukai ku airport,ina su john suke?sun fita da Nasir nima ynxu naje sallama da yar gidana shine na samu su mami sukayi min bayanin tana nan sai mukazo amma fa ina ganin ba zamu tafi tare da su john ba,because of what?yaynmu yayi saurin tare shi da tambaya,Adams yace kana son sani ne?to saboda sister dinka yaynmu yace yana da kyau ka san su ma ta lagos zasu tafi dan haka muje mu sallamesu,Adams ya dubeni zan dawo yar gidana kinji ko?gira na daga shiko yaynmu harara ya sakar min ya wuce abinshi,mun jima dasu mami sannan mukayi sallama,sukan su yaynmu suna fita sai gidan Nasir inda rigima ta sarke tsakanin yaynmu da

Adams yaynmu ya nunashi kai Adams kana mantawa da
halina kasan fa in har nace no ba mai canja min ra’ayi ko?kasan haka kafi kowa ma sanin hakan amma kana bata ma kanka lokaci ne a banza,Adams ya dafa yaynmu Maska na maka alkawarin barin kanwarka akan sharadi guda biyu na farko in tace bata sona na biyu kuma in ka gaya min hujja mai karfi da ba ka son na

nemeta ka fahimta?yaynmu yace don so bata sonka maganar hijja kuma babu kasan baka isa in maka karya ba baya ga tana da wanda takeso da na tsaya maka ka aureta amma ynxu am sorry to say bazata aure ka ba in kuma zaka bata lokaci ne to shi kenan,Adams ya kule Maska na
gama sanin cewa kaima son yarinyar nan kakeyi tun
lokacin da nasamu Ibr ba dadynka ya haifeta ba,yaynmu yayi wata dariya mai kama da yake sannan ya dubi su nasir wayanda sukayi cirko cirko suna duban abokan juna Www.bankinhausanovels.com.ng
mafi kusanci da juna a england suna rigima a kan yar
yarinya kamar yanda maska ke kiranta,kunji shi da wani magana kai kanka ka san in ina sonta baka isa ka
nemeta ba bayan haka ba ni da ra’ayin auran kananan yara don bana son raini so please and please kabar maganar nan ma dan zamu iya rabuwa da juna,Adams yace and so what idan mun rabu?na shirya,Nasir yace dan Allah ku saurara haka kai Maska kayi hakuri mana tunda ka san ko shi wane ne in yana da wata matsala ne sai ka mishi bayani ga matsalar ka shi yasa kaga in da gyara sai ya gyara,yaynmu yace Adams yace namiji ne,bashi da wata matsala sai dai ya nemi matarshi a gaba Adams yace ai na samu yanxu kai kuma baka isa ka hana ba,Ok! zamu gani kana proud din baka taba neman abu ka rasa ko?to zaka fara akan wannan inji
Maska,su John dasu Nasir sune suka bada baki kafin
sukayi sallama amma banda Adams yace sai ya kara
kwana biyu,sun kaisu airport sannan suka wuce gidan
amarya wacce ta cika fam da fushi,yaynmu ya dubeta
madam kimin afuwa kinsan ina tare da baki yau zasu tafi ko shiyasa ya fada lokacin da yake zaunawa kusa da ita su Nasir da Adams ma suka zauna,ta dan yatsina fuska sannan ta gaishe su yace yunwa fa mukeji fa,ta dube shi baku ci binciba?ayya gashi nayi bakin kawaye momina ne ta rako su shine suka cinye Dukda,ranshi ya sosu amma bai nuna ba sai yace shi kenan kawo masu wani dan abin sha mana,ta mike tana karairaya Nasir ya bita da kallo sannan ya dauke kai shima irin matan nan basa Www.bankinhausanovels.com.ng
birgeshi sam bata son mutane yaci ace yanda suke
abokan Maska ace sun saba amma ita sai girman kai
kamar yar wani da wata gashi daga gani za tayi rowa kai shi kyanta ma bata birge shi mace a bushe haka?fari ne da hanci kawai shi kuma bai ma cika son dogon hanci ba,tunanin shi ya katse lokacin da ta aje musu da robar ruwan Cway da kofuna,kunya ta kama yayamu ya dubeta ke ba wani mai dan zaki ne?bana yiwa Kabir waya ya kawo drinks ba?ta dan yatsina fuska zata tashi Nasir yace no yi zamanki don ni dam nake sai dai ko Adams, Adams da ya zuba tagumi yana tunanin Iman ya ce am ok nima a koshe na ke,sun dan yi hira sama sama ita bata sa masu baki ba TV kawai take kallo ko da zasu tafi ba tayi musu magana ba sai Nasir ne yace mu mun wuce,to kawai tace suka fita yayi masu rakiya ya dawo su kuma
su ka nufi gurinmu a Asibiti. Washegari aka sallame ni na dawo gida da kudirin cusa son Adams a zuciyata don haka duk sintirin da yaynmu yake yi bai burgeni ba duk da in har inna ganshi sai gabana ya fadi, kuma sonshi na nan daram a raina,daren
ranar sai ga Adams ya zo mani sallama yana min
bayanin dan dai zasu yi wani wasa ne a club dinsu kuma wasan yana da muhimmanci sosai da ba zai tafi ba gashi ba Maska bai kamata kuma shi ba ya nan ba,nace ba komai naji sauki kuma ga waya ai,ya ce to bani no naki in yaso in naje sai na dinga kiranki sannan ki bani tabbacin kina sona dan Maska ya gaya min kina da wanda kike so,haka ne?nace batun wanda
nakeso dai bai taso ba dan babu sai dai game da kai,in mun waya zan sanar da kai ina jin kunya ne yanxu,yayi murmushi shi kenan yar gidana a zuciyata nace kunyar karyar da zan maka ne ya sa ba zan iya fadama baki da baki ba dan na san ba wani sonka nakeyi ba ne burgeni kawai kakeyi,kyautar wani kyakkyawan agogo da turare ya yi min nayi mishi godiya mukayi sallama sannan yace min Www.bankinhausanovels.com.ng
idan ya sami sukuni zai zo ba da jimawa ba kuma jiya ya gabatar da kanshi a gurin Alhj,da sauri na dubeshi me yace maka?ya ce yace kar na damu gurin su manya ba matsala in dai sunyi bincike sun gano asalina a Ghana,nace yauwa Adams kana da yare ne?ya ce eh yace mu asalinmu fulanin yola ne yan Adamawa zama ne yakai kakaninmu suka haifi iyayenmu muma aka haifemu a Ghana,nayi karatuna duka zuwa Degree wasan kwallo kuwa ina primary nake zakara kuma ni ne babba a kaf gidanmu kanne na hudu maza da mata,matan babana biyu ne kuma har ynxu muna zuwa Adamawa kuma suna
zuwa babana yana da sarautar matawalle dan haka duk salla familynmu a can muke yi ko ni in ina gida tare muke zuwa,kin fahimci takaitaccen tarihina? nace na gane yace to muna da yawa sai ki shirya in munyi aure duk sallah zamu zo daga England Adamawa zamu sauka haka nan in kin haihu a can zaki zauna ko in baby yayi kwari sai nazo na tafi da ku dariya nayi nace Adams kenan har ka tsara komai yace yes haka kullum nake mafarki nace to ba ka fadamin me kayi Degree a kai ba sannan cikakken sunan ka,yace nayi Degree akan engineering,cikakken sunana shine Adamu Salisu Adamu, Abokaina su suka sa min Adams sai ya zama har JC na Adams suka samin kinji yanda abin yake,sai naji Adams ya kara bani sha’awa kuma zan iya kukutawa in aure shi,mun yi sallama dashi nayi mishi rakiya har wajen gate mukayi sallama akan sai naji shi a waya. Ni,Mami da Amira tafe muke kan hanyar mu ta zuwa Www.bankinhausanovels.com.ng
kasuwar unguwar Rimi zamu raka Mami ne amsar dinki muna tafe muna hirar Adams,nace mami ni fa yanxu Adams kawai na tsaida ma zuciyata duk da na san cewa bashi ne zabin zuciyata ba zai fi min kwanciyar hankali,Amira tace na goyi bayanki Mami tace sam ba zata yiwu ba kina tunanin shi ba wata matsala daga dangin shi?sannan ba shi kike so ba in kika jure wani abu wani ba zaki jure ba musamman ma da yake ba shi kike so ba gara wanda kake so zaka hakura da wani abun albarkacin son nan shiko daban ne,nace Mami Haj Yaya da Haj Laure ba zasu bari na zauna Ify ba sannan
da wanda na ke sonshi baya so na gara wanda nake ki
yake sona zan lallaba da Adams,mun tsallaka daidai
shagon Ubale zamu shiga cikin kasuwa sai ga wata mota ta tare mana gaba baka ce wuluk Mami tace motar nan tayi min kyau,kafin nayi magana har mai motar ya fito wani mummunan duwar gaba naji yayin da muka hada ido da mai motar,shima ni ya tsura ma ido yana kallona mami ta ce kin sanshi ne?nayi karfin hali nace a’a naja hannun Amira jikina ba karfi sai mutumin yace uwata ni zaki gani ki wuce uwata?kin bani mamaki uwata zo karki tafi ina Habiba? Sai na soma kuka mai karfi mutane kallona sukeyi ya bar jikin motar ya nufo ni da gudu na tsallaka titi na nufi layinmu ina jiyo muryar shi yana fadin
uwata kar ki kuma tfy ki barni zo mana mamana,ai sai gida ina tafe ina kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu ban damu da kallon da mutane suke min ba jikin Mama na fada tana zaune a firgice ta tashi tana fadin Ify?menene? Ina sai kuka ruri nake Mami da Amira suka shigo a sukwane Mama tace Amira me ya faru? hankalinta a tashe ta ke magana Amira tace mama muna tfy zamu shiga kasuwa sai muka ga wata mota har muna cewa kai motar ta hadu kawai sai mai motar ya fito yana ganin Iman kawai sai mukaji ya hau cewa uwata dama kina nan uwata?zo nan kawai sai muka ga tana kuka ta rugo shine mutumin yace mun san gidansu? mukace eh shine ya dauko mu ynxu yana nan waje wai WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
mu kiraki mama tace baku da hankali daga ganin mutum sai ku nuna masa gidanku?dama ya tafi daku,ta daka masu tsawa maza kuje ku ce masa ba zan fito ba a ina ya sanni,Amira da Mami suka kada baki wilh mama yayi kama da Iman sosai mama tace ba shi bane nace kuje ku sallame shi mana,cikin kuka nace mama baba nefa,mama tayi shiru dama nasan ta gane can sai tace Amira kije kuce mishi mijina baya nan dan haka ba zan iya ganinshi ba su Mami suka sameahi ya kifa kai jikin sitiyarin mota mami tace baba da sauri ya juyo yaushe rabon da yaji wannan kalmar yana kishin jin kalmar nan ga zatonsa Iman ce amma sai yaga yaran dazu,ya
dubesu ina Habiban?suka ce tace mijinta baya nan shi
yasa ba zata iya ganinka ba ba.
Na idar da sallar magriba ina zaune a takure duk
tausayin mahaifina ya cika ni Alhj ya shigo da sallamarsa ba sosai yake shiga dakin matanshi ba sai in bukatar hakan ta taso ya karaso gurina yaya dai Iman? Ify dai ko? nace lfy klau ka dawo Ify ya kasuwa?Amalhmdl Iman kuma Ify lau muka dawo ina Habiban fa?nace tana cikin dakinta,ya nufi dakin mama yana fadin Habiba sarkin hidima hala wani aikin takeyi,sun jima sannan suka fito naga fuskar mama murtuk babu alamar dariya ta zauna kan kujera shima ya zauna kan daya kujerar dake kusa
dani yana fdin ban sanki da fushi ba ba halinki bane
ruko,kuma ba kya gaba,uhm kuskure mutumin nan yayi ya kuma gane har kasuwa ya sameni shi da wani
Ibrahim ban san wanda ya nuna musu ni ba sai dai
ganinsu nayi nace miki har kuka yayi gabana yanzu kiyi hakuri ki zo muje suna falona ku gaisa,mama ta ce cikin fushi Alhj Mukhtar na taba yi maka musu?yace a’a tace to tin da kaji nace ba zani ba itama ni na haifeta ba zata ba to,ko kukan jini yakeyi ba zamu ba,yanzu ne ya san damu?ba zan iya ba wllh in kuma ya matsa min sai na
maka shi kotu da sauri na dubi mama kalmar ta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *