TUBALI COMPLETE BY AYSHA ALIYU GARKUWA

TUBALI COMPLETE  BY  AYSHA ALIYU GARKUWA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

GEMBU MEMBILA Taraba State.

Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako 

wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami.

Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina.

Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, 

kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da kaɗawa da ƙarfi.A dai-dai ya irin wannan lokacin kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci 

kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota.

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani ne 

ko wane, ta faso kai.

Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama. 

Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba.

Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake 

cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da 

rayuwar duniya ba.

Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran. 

Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi.

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya 

ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi.

Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu 

wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye.

Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za.

Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, 

magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana.

Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan.

Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi.

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna 

wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato.

DOWNLOAD COMPLETE HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *