TAWA TA SAMENI CHAPTER 25 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 25 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

tashi ba sai da aka soma liki sannan ne na shiga nima
na bada tsoro da kudi na fito,anty mimi tayi kyau sosai
cikin farin tattausan leshinta rigar fitet ce don haka cikinta ya dan fito dan das daga mun hada ido Sai ta dalla min harara har Amira ta lura da ita tace ke kefa matar can take harara nace tayi ta gama abinda yasa
ma bata neme ni da rigima ba dan tasan yanxu bama
shiri da mijinta ko ince an samin rana shiyasa Amira
tace haka ne kam,wayata ta soma ringin na duba sunan
yaynmu na gani gabana yayi mummunan faduwa na
dauka yace ina jiranki a falon gidan nan cikin in ina na Www.bankinhausanovels.com.ng
ce ban san hanya ba ki tambaya sai ya kashe wayar na dubi Amira kinji yaynmuda rikici ko wai na sameshi
falonsu bayan dazu da ya ganni sai ya wani daure
fuska Amira tace kije mana nace to ai tana kallona
matarshi Amira ta ce to zauna ina ruwana,na mike na
nufi hanyar waje nan na kirashi nace ban gane hanyar

ba gani a gurin bakin gate,yace ni kenan kike nufin in
zo ko?sai ya kashe,gun mai gadi na nufa nace mishi
dan Allah ina kofar falon,ya nuna min sannan na nufa
sanyi da kamshi da kuma laushi su naci karo dasu ina


shiga falon,yana zaune yana shan coke na isa gurinshi
har ya canza kaya daga bakin jeans zuwa blue da yar Www.bankinhausanovels.com.ng
shirt,na dan rusuna gefenahi yace tashi ki zauna kan
kujera na tashi nabi umarninsa yana kallona kamar hoto ko TV yana shan coke na gaji kar matar shi tazo sai
nace gani yace na ganki sai yaci gaba da abinda yakeyi da danne dannen waya,can sai yace ke kamar ni nazo garin nan ace ki gagara zuwa ki gaisheni? sannan da muka hadu sai kika wani dauke kai ke kin girma wai
shekarar ki nawa ne?nayi shiru dake nake na dubeshi
fuskata a daurena kauda kai,ba kya jina nace sha
takwas yace to me na miki kika kasa gaidani? nace ban gane kaba ne shiyasa shi yasa kika manta dani ko?baki taba yi min waya ba tun da natafi me yasa?nayi shiru can nace to kayi hakuri,aikin ki kenan bada hakuri to na hakura menene shirye shiryen na ki bikin? na dubeshi ni bani da wani shiri yace ki dai fada tun da wuri kinsan ance mai kwarmin ido da wuri yake sa ma kuka nine uban Amarya kuma nine abokin ango,haushi ya kamani nayi kicin kicin yace to menene na bata ran kamar ba ke kika zabi mijinki ba?sai ya canza magana baba kwana biyu ban kirashi ba kuma tun da nazo banje ba amma zanje mu gaisa nace dama kana kiranshi ne? sai ya share zancen,kun zana jarabawar?munyi,to Allah ya bada saa amin ina yan waige waige yace me kike kallo ne ki saki jikinki gidana kike ba na wani ba ni ko Www.bankinhausanovels.com.ng
yaynki ne,Amira da Mami sai doko min waya suke ina
cewa gani nan yaki sallamata,har suka tashi sai ga
mutane na mike da sauri harara ya sakar min ba shiri
na koma na zauna a raina nace kai dai kana shaawar
kowane biki sai ka sani a problem,sunyi mamakin
ganina sosai fuskar anty mimi a kaina,Nace don Allah
zamu tafi shi kuma sam ya ki sai da yayi raayi sannan
yace to wa zai kaiku?nace mashin yace bana son kina
hawan mashin fa nace to nabi motar Nasir ni da
Amira,to sai yaushe nace ai yanzu kuna nan zamu yi ta gaisawa ko yaushe yace shi kenan,washe gari lunchn tun safe ba hutu sun tafi gyaran gashi ni kam da bani kona gashi sai na tafi kitso biyar daidai kowa ya shirya sai mu kawaye da Amarya ake jira dan har an soma dibar kawaye bayan na shafa mai sai inner wears na dakko less wanda ya amsa suna less kalarshi ba zaa kirashi milk ba kuma ba zaa kirashi yellow ba shi kuma
ba light brown ba yana dai tsaka tsaki na saka shi
sannan nayi shafe shafe kai ni kaina nayi mamakin
kyan da nayi sai da na gama shiri tsaf sannan na fito
kai Iman inji Mami gsky ko ni amarya kin fini haduwa
gsky cire inji Mami nayi murmushi nace ba wani kyan
da nayi,kafin tayi magana sai ga su Amira da sauran
kawaye kowacce sai da ta raina kwalliyarta ynxu burina inga yaynmu shima inji ta bakinsa mun fita harabar
gidan mu yan mata ne tsantsam nan kallo ya koma
kanmu Adams ne tsaye suna magana da sauran abokan Www.bankinhausanovels.com.ng
ango yana hango ni sai kawai ya wani washe baki yana kallona amira tace iman ji mutuminki nace naganshi share kawai,ya iso gurinmu Amarya gsky ba tare da ango zamu kaiku ba sai dai ya haura ma kanshi daga baya,Mami tace saboda me kace haka Adams? Ya nuna ni yace ga yar gidana da Amira ku zauna tare a motata
don ni ne zan tuka ku na juya zan mishi magana sai
wata masifaffiyar hadaddiyar mota ta kunno kai
harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja’a ga
ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta ni kam
shashancewa nayi ina duban motar dan tunda nake ban taba ganin mota irin wannan ba,Adams ne yace sai Maska dai dai lokacin da yayanmu ya fito cikin wata shadda galila yar gaske sai maiko take,hatta
numfashina sai da ya dauke na yan dakiku sannan ya
dawo daga nesa damu yake amma kamshin sa har
gurinmu,Adams ya ce sai Maska yaynmu ya dago mishi
hannu ya mishi alamar yana zuwa ‘yan mata suka bishi
da kallon birgewa yayin da wasu suka kyasa
A hankali nayi ajiyar zuciya sannan nace Adams kun
damu mu fito ga mutane ba’a gama kwashe su ba ya
za’ayi mu tafi?ya ce to ynxu ya za’ayi kenan? Amira
tace don Allah ku gama kwashe su mana sauran
abokan suka ce to,yaynmu ya kuma fitowa gurin
motarshi ya nufa Adams ya bishi ya bude mota suna
magana da Adams ko me suke cewa oho?sai Adams ya
dawo shi kuma ya shiga cikin motar sai kuma ya fito
ya dubi gurinmu da hannu ya yafito ni gabana ya fadi
nace Amira yayanmu yana kirana mami tace karki dade Www.bankinhausanovels.com.ng
fa banko iya magana ba na nufi gurin motar sai na
samu kaina da canza salon tfy cikin isa da kaSsaita na iso gurin motar gefen kusa da dryva ya bude dan haka sai na Zagaya nayi magana sai naji yace shigo ba musu na shiga kamshi da sanyi sukaimin sallama cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dubeni ba cikin gwaninta ya fusgo motar da gudu sai da muka hau titin Bako Road sannan ya kara sautin wakar p square cikin
wakar su ta no one lyk u,na jingina da kujera ina
sauraro wakar na zata gurin lunchn zamu je sai fa naga
mun dau wata hanyar ban ankara ba sai gamu gaban
gidan yaynmu dake Yakubu Avenue gabana ya fadi
sannan tsoro ya bayyana a fuskata yaynmu ya dube ni Sai ya fito da waya yana yan danne danne shi ban sani ba ashe hotona yake dauka ban sani ba,na rufe wayar sannan yace bisimillah mu shiga nace me zan yi
yaynmu?kasan fa gurin Lunchn zamuje,yace nima
bazaniba dan haka kema ki hakura da sauri na dubeshi
cikin damuwa nace mami ba zata ji dadi ba fa yanda
muke da mami ban kyauta mata ba,dubana kawai yake
sannan yace to mimi taje mana ni dake dan haka ynxu
ma ni yunwa nake ji mu shiga ki min abinci na dubi
fuskar shi ba alamun wasa amma duk da haka sai da
nace bai dace matar gidan ba ta nan ba na shigar mata gida ya daka min tsawa gami da cewa tsaran ki ne ni kike yi min musu?bayan mun shiga ya tsaya da motar na fito shine a gaba ina binshi a baya har falo ya zauna nace inane kicin din bi nan ya nuna hanyar,na tafi komai na kicin da ake bukata akwaishi dan haka na shiga aiki gasky na raina tsaftar matar gidan banyi karambanin gyra mata kicin ba nidai nayi iya aikina farar taliya da miyar kwai da hanta nayi mishi gabanshi na jera komai na koma na zauna ya dubeni zo mu ci kai kawai na girgiza dai dai lokacin da naji ringing a cikin jakata na ciro wayar har ta katse na duba 11 miss call na duba su Mami ne da Adams na dubi yaynmu dake faman cin abinci nace su mami na jirana ya dubeni kin san bana son nacin magana ko? ya kamata ki rike wannan ya cigaba da cin abincin shi sai Www.bankinhausanovels.com.ng
da yayi dam sannan ya shige dakinshi wanda an rubuta master bed room a jikin saman kofar dakin da yellow din kala kamar minti biyar ya fito zo muje
A ranar haka muka yi ta yawo a gari dan mugunta har magariba kuka ne kawai banyi ba dan haushi wai ace biki kamar na mami bana guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe na rasa irin wannan ikon,
gidan shi muka koma ya tafi masallaci ya barni
wai nayi sallah cikin dardar na zauna sai bayan ishai ya dawo ko sallar ma banyi ba ya kuma daukata ya shiga gari sai tara ya maidani gida lokacin an tashi daga lunchn din dan haka dakinmu na wuce na fada gado ko da mami ta shigo da fushi ganin ina kuka sai ta sakko tana tambayata menene?cikin kuka nakece mata yayanmu ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin lunchn dinki tace ba komai kila shima yana da dalili nace wanne dalili?shidai burinshi ya ga raina a bace nan dai ta shiga lallashina. Washe gari aka daura wasu mami aure, da daddare aka kai mami gidan Nasir dake unguwar sarki tun fara bikin sai yaune muka sake nida Adams dan yayanmu ya kasa ya tsare yaki barina na cashe ashe shi yana can suna yinta da anty mimi yace ba zata zo ba ita kuma tace sai ta zo ya gama shirinshi tsaf ta taso har gun mota ta biyo shi tana cewa Sai taje,ta shige mota itama tata kama murfin motar yace sake min tace sai fa naje yace ke kina fa cin darajar cikin jikinki ne bayan haka dakin san ina fada kina fada ba zata yiwu ba amma zaki haihu ba zan dau wannan iskancin ba wata macen arziki ce zata bar gidan aurenta karfe goma kuma bata san sanda za’a tashi ba to tunda lallashi baya miki zan biki da zafi yaja
murfin motar ya rufe sannan yaja motar,muna tsaka da fira sai ganinshi mukayi tsakiya suka sani shida
Adams,Adams ya dubeni mun zata ba zaka zo dinner
kanwa ba?yace kasan mai iyali saida na lallameta tayi barci Adams yana yayi kyau muma dai Allah ya kaimu ga jarawa ,ni kam kumallon ya motsa don haka duk haushi suka bani Adams ya dubeni yar gidana kina
gaya min kince zakuyi lunchn da mene?nace sai mun
zauna dasu Amira menene na sauri Adams da sauran
lokaci fa,yace ba wani lokaci gara ki fada min don in na tafi sai ana sauran kwana daya biki zanzo in Www.bankinhausanovels.com.ng nasan komi tun yanzu zaizo da sauki,na dubi yaynmu wanda yake ta aikin danne dannan waya tamkar baya jin mu nan ko yana sauraren komai nace to kafin ka tafi zamuyi zancen, gobe fa zan tafi cikin kosawa da
maganar nace to baga waya ba Adams yace to shi
kenan ya canja zancen da hajiyata tana son jin
muryarki bari na kirata ku gaisa,nace haba dai daren
nan?ka bari sai da safe yace to na bari kinsan ni ba dai cikin gimbiya ba nayi dariya nace to Allah yasa ka dore ba sai naje gidan ba a canza min yace haba aini din nan ko bawa kika samu kinsan yanda nake son ki
kuwa?kin san nutson da nayi a kogin kaunarki?

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *