DR MUHSEEN CHAPTER 25 KARSHE BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………….Haka bayan kwana biyu su Hajiya Mariya suka Kara dawowa inda suka nemi yafiyarta ta Kuma yafemasu.
Dakyar ta yarda tabi Muhseen zuwa Abuja dan cewa tayi ita kam ta gaji da yawon bin garuruwa,gwamma ya barta anan ya rinka zuwa end of month.
Anan ya badawa idonshi toka akan inhar taki yarda ta bishi to ba makawa sai dai ya kara aure tunda shi ba waliyi ba ne,Ai Seeyerma tana jin haka ta rude harda su kukanta ita bata yarda ba,har so tayi ta bashi dariya,Amma dan karta fahimci wani abu haka ya gimtse ta shiya suka kama hanya, Bayan Ummeey ta yimata hadi na kaya masu kyau da gyara jiki.
Ameerah tunda ta dawo zaman gidansu Bata da sukuni,ga laulayin ciki Yana damunta duk tabi ta rama tamkar ba Ameeerah Yar kwalisa ba.
Sosai su Muhseen ake Shan soyayya haka suke aje Jenior yayi ta bacci abinshi kasancewar baya da rigima sosai.
Su Safna an shiga Jami’a sai rawar kai ake yi,itako Khadijah sai bana ta zama jamp tana jiran sakamako.
A Abuja kuwa tuni Muhseen ya saka Seeyermar shi a babbar Jami’a Mai kyau da tsada dan tuni ta yaye jenior,tayi kwawar duniya ya bari ayimata planning ya ce sam baisan wannan ba,dole ta hakura ta ci gaba da zuwa karatu a haka,Amma tana ta zullimin kada ta samu ciki ga hidimar karatu,tunda Ummeey ta amshi jenior daga kawo shi a yaye shi sunki mayar masu,suko Kara suke yi kada suce a basu aga sunyi rashin kunya,Amma suna kewar yaron sai Khadijah ce take turomasu pictures dinshi.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau su Seeyama har an shiga ajin karshe a jami’a, inda a katsina kuwa su Aunty Hindatu da Rukayya sun Kara haihuwar,Rukayya yan biyu ta haifa,ita Kuma Aunty Hindatu ta haifo diyarta mace.koda Seeyama ta zo suna haka sukayi ta yimata tsiya Wai taki yarda ta Kara haihuwa sai dirka kiba take yi abinta.
Ranar tunda taga jenior ta kankame kayanta baccima tare suka yi,Aunty Hajara sai dariya take yimasu Wai baza’a bata shi ba sai dai tayi zuciya ta haifo wani.ita dai bata cewa komai dan tasan yanzu da kwanika ma take yi a jarabar Muhseen batare daya sani ba take planning dinta so take ta kammala karatunta kafin a dora daga inda aka tsaya.dan shi kanshi ta fahimci ya fiye yimata zancen haihuwar nan,ko jiya kafin ta taho saida Suka yi rigimar Wai ko wani abu take Sha.
Bayan suna da kwana biyu aka gudanar da family meeting kamar yadda aka Saba,inda aka cire kudade domin a tallafawa su Hajiya Mariya na rashin lafiyar Balaraba ga Ameerah da tunda aka yimata theater jikinta yaki dadi,sai faman yawo asibiti ake yi,kosa ya tausaya masu.
Saida ta Kara kwana biyar akai kafin ta koma Abuja kasancewar da driver ya hadota a motar daya siyamata sabu ta zuwa school.
Ranar kuwa Muhseen ya shirya danya yi alkawarin saiya gano metake yi,tun Bayan tafiyarta da kwana biyu ya fara binciken dakinta dakyar ya gano maganin da take Sha ba tare daya sani ba,dauke shi yayi ya boye.
Saida ta zo da dare kafin ta shiga dakin shi ta nemi magani ta rasa,sosai ta shiga tashin hankali Dan tasan ba Wanda zai dauke shi sai Dadyn Jenior,yau kam ta shiga ukku ita ya zata yi.
Haka Seeyerma ranar tayi mirsisi a dakinta taki fitowa har kusan karfe shadaya da rabi na dare,gashi idonta biyu Amma ji take bazata iya fita ba,somin sauran semester daya ta kammala kafin ta fara bautar kasa,tasan yanzu idan ta samu ciki to tana da sauran aiki a gabanta dukda itama tana bukatar beby kasantuwar an kwacemata jenior.
Shiko Muhseen a dakin shi ya dade zaune Yana jiran shigowarta,Amma shiru kake ji babu alamarta.
Saida ya shirya tsaf kafin ya nufi dakinta. Cikin sa’a ta manta bata rufe kofar ba ya tura,da sauri ta rufe idonta dan tasan ba Wanda zai shigo sai shi.
Hasken wayar shi ya kunna ganin dakin yayi duhu,can karshen gadon ya hangota ta kudundine wuri daya,yasan idonta biyu Dan haka ya haura saman gadon.
Duk tana jinshi,Amma a zuciyarta neman mafita take yi na karyar da zata yi danta kwaci kanta,saboda doctor ya sanar da ita ta dole ta Sha maganin before ta kasance tare da mijinta,ta Kuma Sha bayan nan.
Da sauri ta mike zaune tana zare idonta jin wasu abubuwa da yake yimata.
Da sauri ta rungumeta jikin shi Yana shinshina wuyanta tare da cewa “Maiya faru kika tsorata haka,kada ki damu ba abinda zanyimaki kawai haƙƙina nake nema”.
Rasssssss ta ji gabanta ya fadi,tasan ba hanyar guduwa dole ta sadakas tun kafin ya ganota.
Haka ta hakura badan ranta ya zo ba, shiko addu’ar shi Allah yasa ya ijiye twince a wurin.
*Bayan shekara Biyar*
Da saurin yaron ya nufo bakin motar Yana Kiran “oyoyoooo my papa”ya fada jikin Muhseen Yana kyalkyala dariya.
Itama Yar kyakykyawar yarinyar data biyo bayan shi da gudu ta fada kansu tana cewa “Ni Papa Ina biskit dina”
Dukarta yayi Yana cewa “Umhm kaga Mai bakin Shan Zaki ko?”
Cike da taku irin na manyan mata Seeyerma ta fito daga bakin kofar falon jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta leshin green anyimai touching da milk na zare,sosai ta Sha kwalliya sai sheki take yi.
Nifo inda suke tsaye tayi tana murmushi.
Saida ya shafa kana yaran kafin ya ce “Uhmmm you luck so beautiful my wife”.
Saida ta Kara fadada murmushinta kafin ta dauko jakar daya zo da ita tana yimai sannu da zuwa.
Da haka Suka karasa falon gidan daya gaji da tsaruwa.
Saman kujerun dinning Suka baje suna cin abinci cike da kaunar juna.
A bangaren su Hajiya Mariya kuwa tuni Ameerah ta samu sauki tana auren wani dan sanda anan cikin layin unguwarsu,matanshi biyu ita ta ukku,Amma kasancewar Yana da rufin asiri kowacce gidanta da ban ne.
Ita ko Balaraba kwana ya Kare,yau watanninta biyu da rasu,sosai Hajiya Kaka tayi kukan rashinta koba komai yar’uwarta ce.
Haka itama Hajiya Mariya ta auri wani Dan kasuwa tana zaune lafiya da Matar shi daya sai yara tara.
An saka bikin su Khadijah da safna,sai su Sadik da isma’il.inda aka yi hadin gida kamar yadda Suka saba yi.
Yanzu Seeyerma nada yara ukku,biyu maza daya mace mai sunan Ummeey kenan.
Sai Hindatu mada yara hudu,Rukayya nada yara biyar.
Sosai familyn ya Kara yawa da samun zaman lafiya,inda suke Kara samun ingattaceb ilimi na addini dana zamani,Shiki Jenior tuni ya zama dan gidan Ummeey yaron sosai yayi wayo kamanin shi da Muhseen suka Kara bayyana.Sosai suke zaman lafiya,dukda ya hana tayi aikin gwamnati Amma Yana kokarin ganin ya tsaremata komai na yau da kullum.sai soyayyar su suke Sha cikin aminci da hakuri.
Wayyyyyyo Allah na gaji 😥
Tammat bihamdlillah.