TAWA TA SAMENI CHAPTER 28 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 28 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya

Jin wannan lIbr sai wani sabon kuka na saki dan lokacin sai naji wani son Adams din ma
nakeyi,yaynmu ya daka min tsawa yi mana shiru ko na
tsaya na bubbuge ki, wannan bakin ya yi tsit nayi shiru har mukaje gidan anty yagana.
Washe gari ina kwance anty yagana ta shigo ta

Washe gari ina kwance a gidan anty dubeni
tashi Iman kiyi wanka ko kya ji dan dadi nace dan Allah anty ya zanyi wannan lallen ya fita ne?na tsaneshi tace ba zai fita ba sannan ke da kike Amarya ya za’ayi ki goge lalle da sauri na tashi Adams din ya dawo yace zai aureni ne?Anty tace ni dai ban sani ba Babanki da Alhj sun ce a ci gaba da shirye shirye biki ba fashi sai dai ina zaton ba da Adams din ba ne nan na koma na Www.bankinhausanovels.com.ng
kwanta na dora sabon kuka nace TAWA TA SAMENI ni
iman aure ban san mijina ba?na_ shiga uku,Aunty yagana tayi ta bami hakuri gami da lallashi.. Ashe abinda ke faruwa shine boka yayi aiki sun hada Adams da aljani ya juyar mishi hankali dan haka da suka samu Ibr zancen aure ya rushe da Adams sai murna da farin ciki hatta Aunty Mimi tayi murna dan dama tace bata

son in auri Adams dan kar mu zama abokai,a cewarta in auri abokin mijinta taci baya(hahhhah lallai a gaisheki mimi)ita tana auran mai kudi nima na auri mai kudi ba zai yiwu ba..Zaune gaban boka Haj Yaya ce da Haj Laure suna murna gami da godiya boka ya katse su to ynxu kunsan wanda za ta aura ko?Haj yaya tayi sauri tace duk ma wanda zata aura Allah gafarta boka taje ta
tayi ta aura tunda dai ta rabu da abokin dana ai shi
kenan dama bani son ta rabu dana kusa da dan nawa
ne bare shi kansa,ta cigaba dan haka tun da duk
kanmu….Haj Laura ta karasa da cewa ya fada kan
kowa,sun bashi kudi da alkawarin in wata matsala ta
taso zai gansu. Yaune juma’a kuma yaune lunchn,nace ma anty yagana
nifa ban san wanene mijin ba anty yagana tace inje don kada mutane su gane halin da ake ciki tun da ba kowa ne ya sani ba ki kwantar da hankalinki Babanki yaba Alhj damar ya fidda miki miji a cikin kwana ukun da suka rage shi kuma ya fitar miki da miji dan gaske ki dauka haka Allah ya tsara,cikin kuka nace Aunty
wanene?tace nima ban sani ba dan ko mamanki bata
san kowa ye ba sai dai tace tasan ba zai miki mugun
zabe ba shi yasa ma kikaji nace dan gaske.Ina ji ina
gani ta shirya ni suka zuba min dubai less da gwala
gwalai nace anty ni dai kayan Adams ne ku cire
min,tace a’a ba nashi bane ai ke yar gata ce wannan
cikin kayan da babanki ya hado maki ne daga dubai
sannan mamanki da Alhj sun maki gwala gwalai shima
Adams ya bar maki akwatuna,dan haka in kinje gidan
ango sai kiyi ta kwaliya,na share hawayen idona,Anty
Saudatu ta miko min kayan shafa nan na kuma yin
wata kwaliyar. Gurin lunchn yayi guri ko ina ya Www.bankinhausanovels.com.ng tsaru mutane kamar kasa har abin ya bani mamaki ni da kawayena muka hau high table shalele ya cashe sosai su Mami da Amira da sauram kawayena sun yi min kara wajen buga abubuwa,na sha liki gurin dangi da yan uwa sun min liki baran ma Kabir har nace a raina kodai da Kabir din aka hadani ne?yaynmu ne ya bani mamaki ko leke duk yanda muke dashi shine ko yazo bikina niko a na shi
nayi rawa nayi tsaki ba komai duniya ce.Bakwai aka
tashi daga gurin lunchn, gidansu Anty Yagana muka
koma kuma can aka min kamu sai dai banga dangin
miji ba kamar yanda naga ana yi a al’ada Washe gari daurin aure tun safe direban babana yaxo
ya daukeni ya maidani gidan Babana nan na samu
gidan cike da yan garinmu har da tsohuwa jikinta na
fada na soma kuka tace kuji mun sakarai ai ni murna
nayi da dan Ball yace baya yi dan Allah ya sani tunda
akace Adamu Ball yake sai naji bana sonshi ynxu da
babnki ya mana bayani yace ya fasa nace gara haka
kila ma yace ba zai iya rike ki bane yace ba yayi tunda Ball ai ba sana’a bace, duk da halin da nake ciki sai da nayi murmushi a raina nace to shi wannan baki san ta sana’ar ba kila ma gara Ball.Karfe biyu gidan
babana ya soma cika da yan daurin aure niko ina can dakin Babana na kudundune sai kyarma sanyi nake zazzabi ya rufe ni ba wanda ya san inda nake ban sani ba har an daura aure su Amira sunzo muje gurin sai nemana ake gidan cike yake dam da jama’a can babana ya shigo bedroom dinsa yana cewa bari ya karoma baki dabino sai ya sameni kwance ina ta rawar sanyi da sauri ya isO gurina,uwata menene?dama kina nan?ya dago ni jikina zafi rau ya shigo falo ya shiga kiran Anty Maijidda a waya data zo yace mata gani nan ba Ify shi kuma ya fita ya sallami baki ya dawo,Anty Maijidda ta dagani ta zaunar dani ta dubi babana tace to baban Www.bankinhausanovels.com.ng
Iman ya za’ayi ynxu?ga gidan dinke da mutane ko zaka kira likitan mu ne?yace a’a bari na kira wata likitar kin san tana da matsalar zuciya ya dubeni kin san number Doc dinki na girgiza kai alamar a’a yace to bari na kira yaynku ai shi yana da no dinsa ko?nayi alamar eh,ya shiga neman layin yaynmu Anty Yagana ta yowa Anty Maijidda waya wai inzo yan walima sun soma zuwa Anty Maijidda tace yagana ga Iman nan kwance babu Ify ynzu ma likita muke kira,Anty Yagana tayi salati tace gamu nan zuwa babana ya samu yayanmu ya sanar dashi yazo da likita gani nan ba Ify yayanmu cikin rikicewa yace ba dai ciwon ta bane ko,babana yace shi
yasa nace kazo da liktan ta dan kar abin yayi nisa,jim kadan sai ga yayanmu shida likita daga dakin babana aka daukoni zuwa falo kan doguwar kujera aka kwantar dani likita ya shiga dubani can ya dago ya dubi su babana da yaynmu yace ba ciwon ta bane damuwa ce ta saukar da zazzabin sai dai ayi kokarin ganin ta rage damuwar dan tana iya kawo barazana ga ciwon nawa,ya rubuta magunguna yace zaije da kansa ya siyo sannan yace da yaynmu asamu tawul karami mai kyau asa cikin ruwa mai tsafta a dinga goge min jikina nan da wasu yan mintuna daga kafa har zuwa goshina Na zaci tare da yaynmu zasu fita sai naga yaynmu ya
zauna Babana da Anty Maijidda suka fita Anty tace
bara na dauko tawul da ruwa a zatona anty ce zatayi min gugar jikin sai naga yaynmu ya amsa ita kuma ta fita har da kulle kofa.. yaynmu ya iso gabana ya tsugunna sanye yake da rigar
boyel fara tas kamshin turare sai tashi yake a
jikinsa ya cire farar hular shi ya ajiye sannan yasa hannuwanshi Www.bankinhausanovels.com.ng
ya jawoni yaja zif din rigata kasa gabana sai faduwa
yake tsoro da mamaki suka cikani a raina nace yaya
zasu ce yayanmu ne zai min wannan aiki to ko
dakinmu daya ai bai dace ba inaji ina gani ya cire min
riga da breziya ta daga ni sai zani iya cibiya sannan
yajuyo dani naso in sa hannu in kare kirjina amma
kasancewar jikina babu kwari sai na kasa dan haka sai
na runtse idona ina jiran naji ruwan a jkina sai naji shiru a hankali na bude idona yaynmu na gani a gurin da yake idonshi kyam a kan Kirjina da sauri nasa hannu na rufe ya dauko tawul din ya soma goge saman cikina zuwa kirjina sannan fuskata duk da yayi kokarin kamewa dan kada na gane na fuskanci ya dimauta da ganin halittar kirjina haka yafi goge min gurin can aka
kwankwasa kofa ya yi sauri ya samin riga sannan yace a shigo, likita ya shigo da magunguna yace a bani abinci naci sai nasha ynxu,bayan tafiyar likitan ne yayi ma Anty Maijidda waya a kawo min ruwan Tea, su da yawa suka shigo Anty Maijidda da Anty Yagana,Mami Amira harda tsohuwa kakata sun min sannu sannan suka fita,a raina nace a rasa mai bani tea dinma sai yaynmu kadan na sha nace ya isheni ya harare ni karbi da sauri na karba na kafa kai na shanye yace ko kefa,kafin ya rufe baki sai amai na wanke mishi jiki tas da amai yana rike dani sai da na gama sannan tsoro ya kamani na tuna Mami ta taba bani lbr wai wata rana Bilkisu bata da lfy tayi amai a dakin Haj Yaya ya shigo ya taka sai da ya mareta duk da bata da Ify wai ya zatayi amai a daki da sauri na dube shi cikin tsoro nace yi hakuri dan Allah……shiiii ya katseni sannan ya dubeni yace kin gama na daga kai yace Anty Maijidda
ta shigo tana ganina tace ya kika ma yayanku amai kin bata mashi jiki Iman yace ba komai ta kuskure bakinta ta sha maganin yanxu zanje gida na dawo anjima, bayan na sha maganin na kwanta kawai sai barci, bani na farka ba sai magriba Anty Yagana suka sani nayi wanka sannan naji suna cewa tun da jikin da sauki a kaita tayi sallama da mamanta,na dubi Www.bankinhausanovels.com.ng Anty nace dan Allah Anty Maijidda bani da Ify kar ku kaini wani gurin suka ce naje naji sauki a dakina ina kuka ina komi suka kaini gurin mamana tayi min nasiha mai ratsa jiki sannan ta kara da cewa tsafta da girki suma manyan makamaine na kara karfin zaman aure dan haka ki kula,yan uwan mama da suka zo da yan uwan Maska,dangin Alhj suma sunyi min tasu nasihar amma har ynxu banji wanda yace min ga mijin ba gurin Alhj aka kaini shima yayi min nasiha sosai har ya kara da cewa duk wanda kika gani a matsayin mijinki to kiyi mishi biyayya haka Allah ya tsara ni dai sai kuka nakeyi,mun taso tsakar gida,gidan cike yake da mutane yawanci dangin mama ne da kawayenta daga nan sai gidan kawu malam shima yayi min nasiha sosai kuma yace min na rike mijina haka Allah ya Www.bankinhausanovels.com.ng hukunta,Bamu shiga cikin gidan ba da yake su Baba suna can gidan mamana gidan babana muka koma a gurguje kafin motar daukar amarya tazo suka kuma min wani gyaran na dubi Amira da Mami nace ina wayata suka ce tana gurin Saudat suka kirata ta kawo min na kunna ta ina
budeta text ne ya fara shigowa na bude shi naga ansa “dama nace miki i am always lucky gashi kuma.. kaina

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *