TAWA TA SAMENI CHAPTER 35 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
ranta kar na kusanci yarinyar kuma ba zan iya ba tunda
ina tsananin sonta na zabi ba zata haihun ba to ynxu
tun bamu je ko ina ba gashi ta samu ciki,Dr Salihu yace
kaima ka san dole ne tayi cikin tunda ba wani mataki
ka dauka ba sannan zaka cutar da ita in har kace ba
zata haihu ba akwai nau’in zalinci,yaynmu yace naso a
dan dauki lokaci ne sannan na san yanda zanyi na
shawo kanta na san bai kamata nabi son rantaba na
saba ma Allah, amma ina son na ganar da ita a
hankali,Dr ya ce gashi ka soma magana a gabanta yace
wannan ba wani abu zan shawo kanta, ni kam lokacin
na kifa kaina a tebir din likita sai kuka nake yi, cikin da
Www.bankinhausanovels.com.ng
na kwallafa rai shi ne yaynmu yace a cire min ko da
yake ba mamaki tunda dama yaynmu ba wai yana sona
ba an dai bashi ne,soyayyar da yayi ta nuna min don ya
mori albarkatun kirjina ne,ina wannan tunanin suka
shigo yaynmu ya zo gurina ya kamani muka ida
komawa kan wata doguwar kujera,Na dubeshi fuskata
taf da hawaye nace yaynmu ciremin za’’ayi yace kiyi
hakuri kinga cikin na baki wahala nace ynxu ai naji
sauki ina sonshi dan Allah a bar min yace ba ki isa
haihuwa ba ki bari sai nan gaba, nace zan iya dan Allah
ku barmin ina sonshi yace nima ina so to
amma dole
ne a cire ai bana so in rasaki ne Iman,na dube shi ya
soma ban haushi nace yaynmu kona mutu in dai gurin
haihuwa ne nayi shahada pls kar ku cire min ina son
babyna,sai na ga yaynmu ya daure fuska gami da
hararata gashi in ya sha mur ko kai wanene dole ka
Www.bankinhausanovels.com.ng
saurara dan haka sai nayi shiru ya kira likitan ta waya
da yake fita yayi ya bamu guri yazo yace to kazo ka
mata inaji ina gani yaynmu ya kwantar dani a jikinshi dr
Saluhu ya danna min Allura har biu sannan yace mu
dan zauna dan tana da karfi ,lokacin duniya ya isheni
na mike nace ni gida zanje sai jiri duhu ya mamaye min
ido na sulale kasa daga nan ban kuma sanin komai ba
sai dai na farka naga Mama da Haj Maska,sai Yaynmu
dake gefen gadon jina nayi sharkaf da lema ko ban
duba ba na san jini ne na soma kuka yaynmu
yazo ya rike min hannu ina ne yake miki ciwo?ban kula shi ba
mama da Haj Maska suna min sannu nace Mama me
Www.bankinhausanovels.com.ng
yake zuba a jikina?ta dubeni yau me zan gani ni
Habiba?wannan ai jini ne haka jini ya tsinke sai zuba
kan kace kwabo har na fita hayyacina likitan kanshi ya
rude da ganin jinin dake zuba daga jikina ya ma wani
likitan waya yazo sun hadu su biyu a kaina suka ce su
Mama da Yaynmu su fita,Yaynmu hankalinshi a tashe
yama rasa me yake mashi dadi sai safa da marwa yake
yi a kofar dakin tunanin shi in na mutu shine
sanadi,dana sani da nadama kawai yakeyi dan da ya
san hakan zata faru da bai bi san ran Hajiyan shi ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Awa daya,awa biyu,har awa hudu basu fito ba sai da
aka kira magriba Mama ta matso gurin shi tace
Abdulrahman kaji masallaci ana kiran sallah yace mmn
Sagir ba zan iya salla cikin nutsuwa ba gara in sun fito
Sai nayi tawa,Mama tace ka daure ka je sai kayi addu’a
kaji ko? Haka nan ya tafi ,yana dawowa sai yaci karo
da Dr Salihi,yace yawwa Maska dama kai na fito nema
ynxu mun shawo kan matsalar da kyar sai dai jini muke
so leda hudu zamu duba,yaynmu yace a’a gani ka
gwada nawa in yayi sai ku diba ko laida nawa kuke so
Dr yace biyu zamu diba a naka yaynmu yace Allah duka
za’a diba haka kuwa akayi Mama tayi ta yima yaynmu
fada wai ya zai kwanta adibi jini har leda hudu?yace
mmn sagir mu dai yi fatan samun lafiyarta haka aka sa
min jini hannu biyu sai da na kwana biu bansan inda
kaina yake ba sai da na farka jinin ya kare sai
Www.bankinhausanovels.com.ng
ruwa.Dishi-dishi nake gani ban san su waye a dakin ba,
hasalima dakin shiru sai karar fanka a hankali idona ya
soma washewa naga Mama da anty Yagana,sai Babana
da Alhj, sai kuma Malam. Nakai dubana kusa da kaina
Yayanmu ne daf dani da ganin shi yasa komai ya dawo
min sabo a raina nace abin da kake so shi yake
wahalar da kai,hawaye suka shiga yimin zarya sannan
ne yaynmu ya gane na farka da sauri yace Iman kin
tashi ne?ya kamamin hannu su Mama suka zo suna
min sannu gami da yiwa Allah godiya,wasa wasa kwana
na sha daya, Yau monday na fito wanka ina zaune a kan
gado yaynmu ya shigo Mama da Haj Maska suka fita
bayan sun gaisa ya dubeni Iman ya jiki?nace da sauki
fuskata babu walwala yace iman ki min afuwa na san
nine sanadin sakaki cikin wannan halin amma ki min
hakuri bana son rasa ki ne shi yasa,ni dai shiru na
mashi nasan duk dadin bakine yake min yanxu na gane
in mutum yace baya sonka tun farko ba zai taba sonka
ba,sai dai wani abu to shima yaynmu na gane
albarkatun jikina kawai yake so ba wani ni ba dama
nasan ni ba ajinshi bace shishshigi nayi
Ya tabani Iman tunanin me kikeyi ne?na zame na
kwanta hawaye ya soma min zarya abin da yafi bani
haushi yanda har ynxu zuciyata take matukar son
shi,har ynxu son na nan ba zan iya fdama wani ainahin
Www.bankinhausanovels.com.ng
abinda ya sameni ba,Likita ya shigo bayan dube dubene
aka sallameni sun yanke shawarar Mama ta wuce dani
gida don haka gida muka tafi shi kuma yaynmu su
babana suka ce ya koma,ranar da zai tafi ya shigo
tunda na gaishe shi ban kuma magana ba, ba yanda
baiyi ba in yi magana naki daya matsa min sai na sa
kuka, ya kifa kanshi akan gwiwoyinshi na dube shi duk
ya rame a raina nace duk kai kaja ni ynxu don son da
nake maka zanci gaba da zamada kai baya ga haka da
sai dai ka sakeni ya mike to Iman na tafi sai kin jinia
waya ko motsi banyi ba bare na tashi nace Allah ya
kiyaye hanya yadan dubeni sai kuma ya tafii,Tunda ya
tafi kullum zai min waya sau uku,amma daga galsuwa
bana kuma magana har mama ta gane sai fada take
min tanacewa ai ba shi ne ya dora min ciwon ba in
kuma cikine ai Allah ke badawa dan ya zube sai na
zargi mijina.Na warke sarai jikina ya dawo nayi kiba
mama tace na koma dakina nace nidai tunda Haj Maska
ta koma Maska sai su yaynmu sunzo zan
koma,watanshi uku da tfy suka dawo saboda zuwan
watan Ramadan nan da sati daya, ina falo ina kallo naji
ana masu oyoyo duk da son ganin yaynmu da zuciyata
takeyi sai naki tashi,dakin Haj Yaya suka yada zango
sai daga baya yaynmu ya shigo dakinmu, na dube shi
kullum dai yana nan dan gaye dashi jikin nan sumul,
Www.bankinhausanovels.com.ng
yace gimbiya ina gajiya nace kunzo lfy,yace lafiya,ina
mmn Sagir?nace tana Sallah mama ta fito suka gaisa
da har nace ni ba ranar zan koma ba mama ta bude
min wuta dole na bisu, Yaya Kabir yasa an gyara gidan
an share shi,na zauna a falona ya shigo kusa dani ya
zauna nayi kamar ban ganshi ba yace Iman kin canja
min sosai yanzu ba kya kula dani kamar da shiru na
mishi ya jawoni jikinshi tashi muje dakina mu kwanta
nace kayi hakuri ba zan iya kuma kwana dakinka ba,
yace kina hauka ne ko? nace ba hauka yace ya zaki ce
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG