NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 6
Www.bankinhausanovels.com.ng
______dawo da kallan sa yayi izuwa gare ni ya wurga min harara kana ya kalli Zuby da take cika tana ba tsewa saida ya saki fuskar sa ya fad’ad’a ta da Murmushi yace “uwar gida sarautar mata duk kishin ne haka ko gaisawa kin ki bari muyi ki kwantar da hankalin ki akan wannan abar”. Ya nuna mata ni da hannu kana ya cigaba da cewa “ina da ke mai zanyi da ita ko baki kare mata kallo bane? Ko matan duniya sun kare bazan so wannan abar ba danni kallon na miji nike mata”.
Muryan Zuby a dakushe tace “to halakar ka da ita da zaka zo gurina sai kazo da ita, ni wallahi har kasa naji na tsane ta saboda ko macen kuda bana son tare beka bare kuma macen da da halakar aure zai iya shiga tsakanin ku, ina kishin ka ina yi maka son da bazan iya kwatan ta maka ba idanuwa basa iya ganin sa dan Allah Sadeeq kada ka ci amana ta ka soni koda rabin san da nike maka ne “. Idan Zuby har ya cika da kwalla, Sadeeq kuwa jikin sa yayi sanyi a ransa yake shawara “shin ya fad’a wa Zuby matsayin Siddeeqah a wurin sa ko kuwa yayi mata karya”. saboda ya hango tsantsar kishin sa da ‘kiyayyar Siddeeqah acikin ‘kwayar idanun ta gwauran numfashi ya sauke yace “Baby ki kwantar da hankalin ki ‘diyar mai gadin mu ce fa”.
Kallon sa Siddeeqah tayi suka had’a ido ta tin tsire da dariya tace “saboda ka wulakanta ni zakace diyar mai gadin gidan ku ce ni?, to badiyar mai gadi bace kadai fadi wani”.
A fusace ya daga hannu zai kwada min mari, Zuby tai saurin ce masa “abinda ta fad’a gaskiya ne shiyasa zaka dake ta na shiga uku Ni Zubadah Sadeeq mai kake nufi dani?”.
“ki saurare ni baby wannan yarinyar da kike gani munafuka ce idan kuma kin yarda da abinda ta fad’a shikenan amma ni iyakar gaskiya ta na fad’a miki”.
“haba Sadeeq da ganin wannan yarinyar ba d’iyar mai gadi bace jibe ta fa da larabawa take kama fatar jikin ta luwai luwai, wai ka ta’ba kare mata kollo kuwa dan Allah Sadeeq ka kalle ta yanzu”. Wai gowa yayi ya kalleni na tsawan wasu yan sakonni kana ya cigaba da kallon Zuby, mi’ko masa wayar ta tayi tashiga camera tace “kaima kalli kan ka ka gani”. Sadeeq bai fahimci inda Zuby ta dosa ba shidai kawai biye mata yake yi bayan ya kalli kansa ya mi’ka mata wayar, tace “ina fatan ka fahimci inda na dosa yanzu?”.
Kai ya girgiza mata alamar bai fahimci komai ba tace “ina son ka fad’a min maye Alakar ka da ‘yar mai gadi har kake kama da ita? Wallahi ko alqur’ani aka bani zan dafa ita d’in jinin ka ce Sadeeq maiyasa kayimin kar…”.
Tsawa ya daka mata gami da cewa “ke ashe bakida hankali? ni zaki duba tsabar ido na kice min makaryaci tabbas zan nuna miki kuskuren ki”.
Sai yanzu Zuby taga rashin dacewar abinda tayi a fusace Sadeeq yayi ribas Zuby na kwala masa kira ya amma ina ransa ya riga ya baci figar motar yayi sosai yake gudu akan titi saura kiris ya daki wata mota da ta fito daga wani layi zata hau titi sai Allah ya takaita abun yayi sauri ya ci burki idanuwan Siddeeqah sun yi kulu kulu tsoran ta kada yaje ya kashe ta tasan ya kashe banza wayar sa ce ta fara ringing amma ko ta kanta bai bi ba koda yazo bakin get din gidan su sosai yake danna horn mai gadi a tsoroce ya leko ganin yallabai ne yasa yayi sauri ya wangale masa get din acikin ran Habu yake cewa “ko waya tabo yallabai yau?”.
Bayan Sadeeq ya sulala motar sa cikin gidan yane guri yai faking da sauri Siddeeqah ta kai hannun ta da niyar ta bude murfin ta fita sai taji sa a kulle game alokacin Sadeeq ya hada kansa da sitiyarin mota tsoro ne fal acikin zuciyar ta, tana jin yadda zuciyar Sadeeq ke harbawa da sauri da sauri ahalin yanzu tasan ko sunan sa ta kira shake mata wuya zaiyi komawa tai ta zauna itama tayi tagumi hawaye na saukar mata da batasan dalilin zuwan su ba