TAWA TA SAMENI CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
…..tsawa ya daka mata ke shiga hankalinki
ni sa’anki ne?uban wa yace da zaki makaranta ki biyo
ta nan?me zan miki?karki sa ma_bakinki kwado zaki
sha mamaki duk sanda ana min magana kika tsoma
baki ya nuna kofa da hannunsa yace see your way,fita a nan ta mike jiki na rawa mama ki daina min fada a gabanta kin manta ita ce matar da kika zaba mani na aura?zata raina ni ne hajiya in kina min haka a gabanta har tana sa baki dan raini,wllh taci albarkacinki ne da sai na mata dukan tsiya,ya cigaba da cewa bata san cewa ni saboda ke ni zan aure ta ba ba wai don tayi mani ba?haj yaya tace tsaya tsaya ba na son cin fuska ka manta ni da uwarta nono daya muka sha? bayan haka ma mimi bata da makusa ubanta balarabe ne ka kuma sani inma ilimi ne akan nema take gashi tana sonka sosai amma kai sai faman goce goce kake yi shi yasa na canza shawara kafin ka tafi sai an sa ranar aurenku,ya dubi haj yace ki dai yi hakiri na dawo don kar aje ana dagawa tace sam ban yarda ba yace to shi kenan ta juya zancen dake cewa wacece take kuka kuka tsaya kai da Kabiru?yace waccan yarinyar da nake aike ce,nan ta hau bala’i da masifa tace dama in banyi da gaske ba sai Habiba ta shanye min yara yanda ta shanye babanku kallonka kawai nake yi wannan mummunar yarinyar yanzun itace abincinka gyaran dakinka,aike yanzu itace tunda haka kafi so ai sai kayi sauran ka ka soma kai shawara gun Habiba haka tayi
ZAMU TASHI
ta sababi yana bata hakuri har dai ta sauka,Niko tuni nakai dinkinmu gun yaya Sulaiman nan da nan kuwa sai ga kaya ya kawo,na rakoshi zai hau mashin nan mukayi kicibis da yaya Kabir suka gaisa da yaya Sulaiman ga mamakina sai naga yaya Kabir ya daure fuska ya dubeni yace na lura baki jin magana ko Iman? me yaya Abdulrahim yace maki?na dibe yaya kabir nace ai to wannan ba yayan da ya bani waya bane wannan wani ne bai saurareni ba yayi cikin gida muka fita ina ta mamakin wannan abu da yaya Kabir yayi na dubi yaya sulaiman da nufin nayi magana sai kawai shima naga yayi fuskar shanu(wato ya hada rai)yace wannan kuma wanene?nace yayanmu ne Www.bankinhausanovels.com.ng yace ni ba wani yayanku na kula ke sam baki ma san halin da nike ciki ba ko? gabana ya fadi nace me kake nufi?yace ina cikin mayen sonki,na dade da yin nutso cikin kogin sonki don Allah ki taimaka min da ganin wannan da ya wuce sonki shima yake yi,nan take hankalina ya tashi na gudu nayi cikin gida dakinmu na fada na kwanta a kan gado rigingine nayi fuskata na kallon silin na soma tunani, yaya Abubakar sona yake,yaya Ibrahim sona yake, yau ga yaya sulaiman da wannan zancan har kuma yana tunanin wai shima yaya Kabir sona yake, ban ganeba? na mike zumbur tamkar an tsunguleni nace da na shiga uku ni Iman muddin Haj Yaya taji wannan Ibr na Ciji yatsana na soma sintiri a tsakar dakin tabbas da zan so yaya kabir ko ba komai yana dan yanayi da yayanmu wata zuciyar tace min in yana yanayi da yayanmu shi kenan sai ki soshi a matsayin da yayan naku ya taka a
zuciyarki?shin kina neman ma kanki rigima da mahaifiyarki?menene laifin Abubakar da ba zaki soshi ba?ya jima yana maki dawainiya dake in ba ki son shi
ga Ibrahim nan shima dan uwanki ne sannan in dama
za kuyi adalci to da Sulaiman kika zaba ki tuna shine
yake maki hidima ta fannin dinki tun kina karama har
yau dinnan shi ke maki dinki, **hhh! Lallai yariya taki tasameki,duk cikinsu Www.bankinhausanovels.com.ng
blood ne***** ban san shigowar mama ba sai dai naji an girgiza ni sannan nayi sauri na jiyo cikin tsoro naga tana kallona tace iman me kike tunani haka?na shiga uku ni Habiba na soma in ina,ina cewa ba komai ta girgiza kafaduna da karfi cikin daga murya murya tace kinsan tsawon lokacin dana dauka ina maki magana nan kuwa baki sani ba,na jima a nan ina kallonki kina safa da marwa tamkar wadda abin duniya ya dama,ta ja hannuna muka zauna a bakin gado ta sanyaya murya tace Iman sanar
dani matsalarki don baki da wanda ya fini kuma na jaki a jikina don irin wannan ranar wato don neman
shawara kar kiji komai sanar dani ta fada tana kallona nayi shiru ina tunanin mama gaskiya dole ne ma na sanar da ita sai dai ba zan gaya mata maganar kabir ba, na dubi mama nace yayyena duka uku sune suka sani shiga wannan tunani,tace kamar yaya?na dukar da kaina kasa sannan nace yaya Abubakar da yaya Ibrahim da kuma yaya Sulaiman kowanne yazo wai yace yana sona,Mama tayi shiru kamar ruwa ya cita tace ke me kika gani?ta cigaba da cewa Abubakar da ne ga yayar mahaifinki cikinsu daya,Ibrahim kuma dan kanin mahaifinki ne da suke uba daya shi ko Sulaiman dan wana ne nima cikinmu daya sai ki fadi min wanda kika zaba?nayi shiru tunani ya dawo sabo mama tace ba tunani zakiyi ba sanar dani abinda kikace masu kekin amsa musu dukansu ne?nace aa duk hakuri na basu,nace ni karatu zanyi amma tamkar sun hada baki kowa sai yace zai jirani yaya Sulaiman ne ma ban tsaya yi mishi magana ba,mama ta dafa ni sannan tace
yanzu gaya mani a cikinsu wa kikafi so?sai na baki
shawara nace gsky mama ni cikinsu bana son kowa,ta
mike tana fadin alhamdll gara hakan don dama ko da
dole sai na zabi daya ne,to nace gara Sulaiman yaron
na da mutunci,kuma naji ma ina fuskantarshi game da
ke ma na dade da gane cewa sonki yake nayi kwadayin
dama shi kadai ne yace yana sonki taci gaba da cewa
yanzu in naceki amince dashi sai ace don yaron Www.bankinhausanovels.com.ng danuwana ne shi yasa don haka ki kwantar da hankalinki kinga jarabawa na matsowa kar ki yarda na kuma samunki kina wannan tunani ba yarda za ai ki auri wanda bakiso ba mai matsa maki don karatu ma zakiyi,haka mama tayi ta lallashina har dai na saki jiki sai dai a raina maganar yaya Kabir itace a raina. Tun ana saura kwana uku bikinsu anty mariya dangi suka cika gidan,fannin Haj Shuwa da yanuwa Haj Yaya,sai yan uwan Alh Mukhtar wato yan maska Aunty Mimi ma a ranar tazo don ranar ne za’ayi
dayis,yayanmu ranar bai wuni gida ba sai yamma dama ni banje masu wurin da suke yin lalle ba nida Amira mukaje mukayi kitso sannan mukayo namu lallen a can don dama mu ba ma saka mai a kanmu. Misalin karfe biyar na yamma yayanmu ya aiko Kamal ya kira ni nazo yace na kawo masa wani abu tabawa in akwai dan yinwa yakeji na koma ba wani abin kirki sai na rana kuma ya huce nasan ba zai ci ba,don haka sai na dafa mashi indomie da kwai na kawo mishi natarar da Aunty Mimi a dakin sai naji raina ya baci na ajiye zan juya yace ke kizo ki zuba mani mana na dawo sai tace ka barta sai na zuba maka ,bai dubeta ba yace min samin mana kina kallona baki sanni bane?nayi kasa da kaina sannan na zuba mishi na dauko mishi coke da ruwa sannan na juya zan fita sai naji yace shiga bedroom ki dauko wayarki tana nan a kan katifa,na dauko sannan nayi mashi godiya,washe gari a command quest za’ayi kowa ya shirya cikin anko nima na sanya nawa ankon nayi kyau sosai na fito harabar gidanmu a nan ne ake daukan yan matan tuni kowa ya tafi sai Amarya da kawayenta wadannan kuma bana tunkare su ba itako mami tuni dama tana can don sune masu shirya gurin dasu bilkisu da sauran kawaye,ina tsaye na jingina da
bangon dakin yayanmu ina kallon kawayen amarya suna ta kai da kawowa kowacce na rike da waya Www.bankinhausanovels.com.ng tamkar masu gasarta nan na tuno da tawa mama tace na aje sai mun gama zana jarabawa ina wannan tunanin naga anty mimi sun fito itada yayanmu itama anko ne a jikinta irin nawa tayi matukar kyau dama anty mimi ba dai kyau ba gata fara yanda mami ke gaya mani mahaifinta balarabe ne zamanin da Haj Laure mahaifiyarta suke zuwa kano to jidda a can Allah ya hadata da wani balarabe ta aura shekarunsu ko goma ne da aure ya rasu lokacin Anty Mimi na shekara shidda shine ta gudo da ita ba tare da sanin dangin babanta ba,sannan ta sake aure shine ta haifi yaya uku sanda naji wannan Ibr a raina nace ashe jirgi daya ya debomu ni da ita…
Garama ni ubana yana nan, haka danginshi, nayi nisa
cikin tunani na ji horn ba karewa na juya can wajen da ake horn din bakin gate sai naga ashe su yayanmu ne zasu tafi ban fahimci wai ni suke ma horn ba sai da anty Mimi ta bude gaban mota tace ke na dubeta na dafa kirjina nace ni?eh da Allah zo nan ana maki horn kinyi banza da mutane, na nufi gunsu ina zuwa naga yayanmu ya sako hannu ya bude baya yace shiga,gabana na faduwa na shiga motar don nasan ba wanda ya taba shigarta a yan gidanmu sai yaya Kabir na zauna sannan na rufe sanyi da kamshi sune suka ziyarceni tamkar wata munafuka haka na zauna a motar kaina a kasa, suko suna ta labari bana jin dai muryar yayanmu sai ta anty .Mun yi nisa sannan na dago idona sai kawai muka hada ido da yayanmu ta madubi nayi sauri na sunkuyar da
kaina kasa har mukaje ban tanka ba,ban kuma daga
idona ba,sai da naji an tsaya sannan na dubi gurin yan mata ne cike na buda zan fita sai naji yayanmu yace karba,na juyo sai naga yana bani kudi ne sababbi yan naira hamsin na amsa nace Allah ya saka da alkhairi,anty Mimi ta shaka sosai da na kalli fuskarta ni dai nayi ciki ko zan ga Mami, ana cikin hidima shalele suka kira don haka gun ya cika da karan kidan police band Sa’a tazo tace kije ana kira gabana yana faduwa nace inji wa?ta harareni dole sai kinji? ki zo mana na bita can baya mukaje ganin Anty Mimi da Amare da kuma kawayensu yasa wata faduwar gaba ta sameni na dai daure na isa Www.bankinhausanovels.com.ng wurin,Anty Mimi ta kai mani rankwashi akai tace ina jakarki?nace tana gun Mami tace nawa yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau
zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji
biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi
kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin, Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina kuka tace Iman menene?Bilki tace ba’a sani ba
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG