TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 11

Gaba ɗayansu bin sa su ka yi da kallo har ya fice, nan ne Baba zubairu ya ɗan muskuta ya ce+ “Nifa ban ga laifin yaron nan ba, na tabbata da ace shi mu ka gani a wannan hali ba zamu taɓa waiwayensa ba balle mu taimaka masa, bayan mu ne addininmu ya koyar da mu kyautatawa” yace yana mai kallon ƙanensa zuciyarsa cike da Nadama. “Gaskiya ne, don wallahi ba ruwan bambancin addini a kyautata mu’amala ko sauke hakkin makotaka. Yanda ya wajaba a kan musulmi haka ya wajaba akan wanda ba musulmi ba, sannan a ko ina cin fuska haramun ne” Baba Anas ya ce yana mai goyon bayan Baba Zubairu. “Amma kuma aka ce kada mu riƙe su aminai” Baba hamza ya ce a ɗan hasale.. “Eh an ce kada ka rike su aminai don za su cutar da kai amma ba a ce kada ka rike su da amana ba, kun manta zamanin Annabi SAW sau da yawa kafirai na zuwa da niyyar kashe shugaban halitta amma su ɓige da musulunta ba su kaɗai ba har mutan garin su, duk saboda kyakkyawan mu’amala da musulunci ya koyar da ayi ga kowa ciki har da wanda ba musulmi ba.” Baba Anas ya ce kai tsaye. ” Ni dai babu wani kame kame da za ku min, kun ci amanar Babanmu, kun sani sarai yanda yake ƙyamarsu don su ɗin najasa ne, da kuke maganar na siya ba a sanin ko nawaye me yasa kullu. Muke addu’a muke faɗin RABBANA LAA TU’AKHIZNA INNA SINA AU AKHƊA’ANA toh shi Ubangiji ai mai Rahma ne, ba zai kama mu da laifi ba amma kuma yanzu fa? Haba! Haba!! ” faɗin Baba Hamza ransa a ɓace. ” Kunga matsalar Bahaushe kenan, shi a duniya gani yake babu wanda ya kai shi zama kusa da Allah, haka kuka dinga tada jijiyar wuya lokacin da ɗan wajen madina ya auro Gara, a bakin bahaushe za ka ji yana kaskantar da wani jinsi in dai ba yarensa ɗaya ba da kiransa ƙabila. Shi bahaushe shi dai wanda bai cikata farillansa ba amma a duniya ba wanda yake nuna wa Yatsa sai wanda ba musulmi ba, shi ne zai kalli malamin addini ya kira shi da tubabbe matukar daga baya ya musulunta. Da haka manzo SAW yayi da ya tara manyan sahabbai da yake da su? don dukkansu tubabbu ne a fassaran bahaushe.” Baba Salihu ya faɗi kai tsaye. ” Shine ai nagani, gashi kiri kiri wanda kuka zaɓa akan arnen yana shirin kashe muku mahaifi. Na gwammace a ce Arnen can ne ɗa na in dai zai tuba ya musulunta akan wancan sakaran” Baba Anas ya sake fadi cikin takaici. “Ko me zaku ce muna dai jin ku ne kawai don ba zai wanke cewa baku kyauta ma babanmu ba kunci amanarsa ba ko kaɗan ba, Jinin Arne fa ke gudana a jikin Baba, mutumin da yayi rayuwar sa kaf cikin musulunci” Baba Mahmuda da tun farko bai maganta ba ya ce yana mai tsananin jin takaici.4 Tun da suka fara magana Baban Sasa ya dawo hayyacin sa, idanunsa a rufe sai yake jin zantuttukan su kaf a kunnensa inda yake ji kamar mafarki yake yi, so yake ya fahimci me su ke faɗi amma ya gagara, idanun sa sun masa nauyi dan haka ya kasa bude so, bubu abin da ke motsi jikin sa face yan yatsun hannun sa. Baba Idris wanda tun da aka fara magana bai tamka mu su ba, shi ne ya lura da halin da ya ke ciki. Cikin hanzari ya tashi ya na fad’in “Ina ga fa Baba ya motsa, yi maza kira likita! Baba Muhammadu ne ya fita cikin sauri sauri gudu gudu, in da gaba ɗayan su suka zagaye shi suna masu faɗin “Sannu Baba! Allah ya tashi kafadar ka” *** Faɗin Damuwar da Amatullah ta shiga ba zai misaltu ba, don gaba ɗaya kanta ta ba laifi don gani take damuwar rashin komenta ne ya kwantar da Baban Sasa. Addu’a kam ta yi sosai akan ya samu lafiya.2 Zaune take tana tunanin zuwa shika Amma wa zai kai ta? Lokaci take kallo tare da tsimayen kiran sallan la’asar domin ta ba da farali. Ɗumi ta ji ya fito mata wanda ta dan razana tare da gyara zama yayin da taji fitowarsa a karo na biyu. STORY CONTINUES BELOW Ajiye littafin ‘Ina Darajar take?’ da take karantawa tayi ta shiga bayi don gane ma idanunta. Abin da bata zata bane ta gani, wani irin yanayi ta shiga don gaba ɗaya ba za ta ce murna kaɗai ta ke ba. Gyara kanta tayi ta isa ga mama da ke ɗaki tana hutawa tace “Mama abin ya zo, na kusa fita idda” tace cikin farin ciki. Kabbara mama tayi tana mai gode ma Allah sannan ta ce “Kiyi shiru da bakinki, ba za su ji ba sai kin yi wankan na ukunki, kai Alhamdulillah Alhamdulillah” mama tace cikin farin ciki.4 **** Ayush kuwa tunda garin Allah ya waye take cika ta na batsewa musammam da ta ji Baban Sasa ya farfaɗo daga bakin su Naja’atu. Gaishe da Hajiya da ta ke zuwa kowacce safiya ma yau ki ta yi.2 Hajiya da ta ji ta shiru, tunanin ko lafiya ya sanya ta shiga bangaran Aysuh din. A falo ta tarar da ita, sanye da wando wanda ko gwiwa bai kai mata ba, da riga damammiya mara hannu. Ta yi dai dai bisa doguwar kujera, ƙafa ɗaya kan ɗaya, yayinda ta ke cin gashesshiyar kaza ta na korawa da lemo mai tambarin five alive. Yanayin shigar Ayush ya sanya Hajiya tsayawa bakin kofa ta ɗan yi Jim, ganin Ayush ba ta da niyar tashi ta rufe jikin ta bare ma ta nuna ta san da zuwan Hajiya, Hajiya ta ɗaure ta karasa cikin falon da fara’ar ta ta ce “Assalamu Alaikum, Aisha sannu”2 Sai da ta kora kazar bakinta da lemo, sannan ta amsa da “Yauwa Hajiya barka da maraice fa, da fatan dai lafiya ko? Dan dai yau ko fita ban yi ba inan dakina bare ku ce na fito mu ku cikin tsiraici!” Jikin Hajiya yayi sanya kamar wacce aka zubawa ruwan sanyi, ta ce “Haba yar nan, kar ki ce haka ai gyara kayan ka ba zai zamto sauke mu raba ba, rannan da ki ka ga na tanka shi ma ai da dalili, yanzu na ji ki shiru ne ba ki zo an gaisa ba ya sa na biyo sahun ki na ji ko lafiya” “Lafiya lau na ke, gudun kar na fito ku ce na fito mu ku zindir ya sa na yi zama na ɗaki, gidan ubana ba a takura min ba, ban ga dalilin da zai sa a takura min a nan ba, ehe!”2 Ba ta damu da yanayin da Hajiya ta shiga ba, ta kara kora lemun ta, sannan ta ƙara da “To Hajiya ma fisabilillahi ɗan ki ya ajiye ni a gida kamar bukka sam babu ventilation kuma you guys are still expecting me to dress like the local woman you’re?” “Iyye? me ki ka ce? Na ji kina turanci kin san ba ji na ke ba” “Aw haka fa, yi hakuri hajjaju ashe ba boko, dama cewa na yi tunda ɗan ki ya aje ni gida irin wannan dole na ke shigan shan iska, na saba da AC gidan uba na” Kai Hajiya ta girgiza, sannan ta ce “Eh da gaskiyar ki, mun takura ki zaman gidan nan tun da ba ki saba ba, amma kar ki damu komai zai wuce, za ki koma na ku gidan daga ke sai mijin ki” Hajiya ta faɗa ta na mai kallan kazar da Ayush ta ke ci. Ganin in da idanun ta ke kallo ta ce “Ragowar kazar da Saifullahi ya saba siyo min ne duk dare, na ga kamar ran ki ya biya, za ki iya ɗauka Hajiya”6 Ran Hajiya ba ƙaramin motsawa yayi ba, dan kuwa rabon da alkhairi ya shiga tsakanin ta da Saifullahi tun sanda ya ke auren Amatullah, lokacin su kazar nan babu laifi ya kan kawo mata, yau gashi sai dai ta gani ɗakin matar shi, har ta na mata tayin wulakanci. Hajiya na mai kokarin ɓoye bacin ran ta tace “Ah ah madallah, na gode, idan yayi niya shi Saifullahi zai kawo min tawa ai” “Eh toh nan fa ɗaya , kun fi kusa ai ɗa da mahaifiya, na gode Hajiya, Allah ya huta gajiya” Jiki sanyaye Hajiya ta ce “Ameen” Har ta juya za ta fita ta kara dawowa ta ce “Baban Sasa ya farfaɗo, sai ki shirya da anjima kaɗan in za a je duba shi a tafi da ke ko?” STORY CONTINUES BELOW “Saboda mai ya sa!” Cewar Aysuh ta na mai aje lemon hannun ta kasa, ta kara da “Miji na bai ce na je ba, duk sanda na sami lokaci zan je dan Allah Hajiya kar ku matsa min! Ai da ya na so na je ai da ya faɗa min ko?”4 “Eh gaskiyar ki yar nan, Allah ya sa mu dace” Hajiya ta ce yayinda ta juya da sauri ta bar dakin zuciyar ta na tafasa, ba dan Aysuh Amarya ba ce, kuma ta na shakkar zuri’ar da ta fito da yau sai ta sanya Saifullahi ya saba mata! Tunanin da Hajiya ta ke yi kenan, har ta kusa buge Amatullah ba ta sani ba.4 Amatullah sanye cikin hijab din ta har kasa, ruwan kwai dan kyau har sheki ta ke, dauke da Emjay. Fuskar ta cike da fara’a ta ce “Afuwan Hajiya ban gan ki ba ne” Takaicin yanda Amatullah ta yi bulbul ta yi kyau, wanda kallo ɗaya za ka manta ka tabbatar da kwanciyar hankalin da ke tattare da ita, ba ƙaramin baƙin ciki ya karawa zuciyar Hajiya ba.2 Amatullah ta kara da “Barka da maraice, ina wuni?”1 “Lafiya lau” Amatullah ta wuce abin ta, da yake dama fita za ta yi, za ta je asibiti duba Baban Sasa. Ta bar Hajiya da bakin ciki fal zuciya.2 Da fitowar ta, da tsayuwar motar Saifullahi lokaci guda ne. Tun kafin ya fito daga motar ya kura mata idanu, gani yayi ta zame masa sabuwa gal, dan ko sanda ta ke buduwar ba ta taɓa masa kyau da kwarjinin da ta masa a yau ba, abin mamakin shi ne ba wai ta yi ado ba ne, wannan hijabin nan dai da ya tsana shi ne sanye jikin ta. Fitowa yayi ya tsaya jikin motar, ganin ta nufo in da ya ke bugun zuciyar sa ya karu, bai taɓa tunanin ganin Amatullah zai sanya shi cikin mawuyacin yanayi da shiga ba. Ya sakankace gun shi ta nufo, in da murmushi ya bayya fuskar sa, wani daɗi ne ya mamaye zuciyar sa. Amma da Amatullah ta zo dab da shi sai ya ga ko kallon sa ba ta yi ba bare ma ta nuna da wani ɗan adam nan tsaye, wucewar ta tayi ta, in da ya bi ta da kallo tamkar sa ƙara’i.2 ‘ashe Amatullah za ta iya ganin sa ta ki gaida shi?’ Tambayar da yayiwa kan sa kenan cikin zuciya, a zahiri kuma bin ta yayi da sauri ya na kiran sunan ta “Amatullah! Amatullah! Amatullah!” Amatullah ta tsaya, juyowa ta yi fuska ɗaure ta na duban Saifullahi fuskar ta ɗauke da alamun tamabaya. Saifullahi na duban ta kamar zai haɗiye ta ya ce “Haba Amatullah, yau ina ɗa’a da tarbiyar na ki? Ko babu komai ai ni yayan ki ne ko Amatullah? Ya kamata ana gaisawa”2 Ta na mai ɗan sakin fuska ta ce “Ban san kai na wuto ba ai, na dai san akwai wani tsaye jikin mota. Da fatan ka na lafiya” Amsar da ta ba shi ba ƙaramin sosa masa zuciya ta yi ba. Ya ɗaure ya amsa mata da “Alhamdulillah, ya Emjay? I missed you guys ..” “Lafiya lau Alhamdulillah, sai anjima ko?” “Ina za ki je ne, ai sai na ajiye ku kin ga yamma na yi” Cewar Saifullahi ya na mai fatan Amatullah ta yarda ya ajiye ta, dan har ga Allah ba ya so ya dena magana da ita.2 Kai Amatullah ta girgiza tare da faɗin “Thank you, we are very fine, we can manage” Ta na faɗin haka ta yi gaba. Nan ya tsaya ya na duban ta, har sai da ta ƙurewa ganin sa sannan ya hakura ya shige gida. Ɗaki ya tarar da Hajiya tana matse kwalla, ganin Saifullahi ta fashe masa da kuka, wai ta na da ɗa kamar shi a cikin gidan nan sai dai ta ga kaza ɗakin matar shi, ya na neman albarka kuwa? Saifullahi kallon ta kawai ya ke har ta gama kukan ta, ta share hawayen ta dan kan ta. Sannan ya ce “Hajiya da kin san abin da ke damuna da kaza ba ta saki kuka ba Hajiya, tun ba a je ko ina ba, zuciyata ta fara konuwa da barin Amatullah, Allah ya sa ba dana sani zan yi ba Hajiya!”6 STORY CONTINUES BELOW Nan fa ta haushi da faɗa, ta in da ta ke shiga ba nan ta ke fita ba, ta kare da “Idan ni na haife ka Saifullahi maganar wannan bakar yarinyar ta fita bakin ka! Ina tunanin dai ba haka uwar ta ta bar ka ba!” Saifullahi ya tashi zai fita ba tare da ya sake furta komai ba, har ya kai kofa Hajiya ta tsayar da shi ta hanyar faɗin “Kuma ka tabbatar kazar yau da ni za ka siya! Na dai faɗa ma ka! Wanda ba ya neman albarka!” Takaici ya sanya shi girgiza kai ba tare da ya furta komai ba. Ya wuce bangaran sa. *** Sai da Baban Sasa ya kwana biyar kafin ya dawo cikin hayyacin sa, babu wanda bai zo ya duba shi ba, hatta Saifullahi ya samu ya lallaɓa ya je ya duba shi, Amma ban da Aysuh. Dee Yusuf kuwa duk sanda ya je wajan supervisor din shi ya kan yi kokarin leƙa Baban Sasa, duk da har lokacin ba su gana ba, kullum ya zo sai su Baba Hamza su ce bacci Baban Sasa ya ke, ba ma sa bari ya shiga. Shi kuwa dama ya na zuwa ne saboda Baba Salihu, waje su ke zama su ta hirar mahaifin Dee, kasancewar ya faɗa masa makaranta daya su ka yi. Hakan ba karamin fahimtar juna da sabo su ka yi ba cikin kankanin lokaci. Baba Salihu kan yi tunanin ina ma Dee musulmi ne da tabbas sai ya ba shi auren Amatullah, dan kuwa ya yaba da nutsuwa da hankalin Dee, babu shakka ya gaji mahaifin sa, haka kuma bai fidda ran zai musulunta ba dan hakan ma ya sa ya ke jan sa a jiki sosai. Kamar yanda su ka saba, yau ma da yammaci, sun shafe wajan awa ɗaya suna hira da Baba Salihu, kafin Dee ya ma sa sallama, ya ce ya na so ya koma gidan sa. Baba Salihu ya ce “Ka tafi hakan nan ba ku gaisa da Baban ba?” Ya na mai sosa kyeya ya furta “Ai ina ce har yanzu bai tashi ba Baba, wani karan na zo ma gaisa” “Ah ah yau kam za ku gaisa, mu je ku gaisa” Ba a san ran shi ba, amma ba ya so yayiwa Baba Salihu musu haka ya bi shi. Baba Salihu na tafe, Dee na biye da shi har su ka isa dakin kwanciyar Baban Sasa. Baban Sasa kishingide kan gadon shi, Alhamdulillah jiki yayi kyau, a kasa kan tabarma Baba Anas, Baba Hamza, Baba Idris da Baba Muhmuda ne zaune, in da su ke zantawa Baban Sasa na ɗan sa mu su baki jifa jifa. Ganin Baba Salihu da wanda ke biye da shi tuni kowannen su ya tsuke fuska. Baba Anas ne ya yiwa Dee iso cikin sakin fuska. Gaban gadon Baban Sasa Dee ya tsuganna, yanda Baban Sasa ya haɗe rai bai hana Dee murmusawa ba, cikin girmamawa ya furta “Baban Sasa sannu da jiki? Ya saukin jiki?” Da kamar ba zai amsa ba, dan har Dee ya fidda rai, sai kuma ya amsa masa da “Lafiya, asibitin ma sai ka biyo ni yaro? Wannan naci har ina?”2 “Yo ai Baba tun randa ya ba ka jini kullum sai ka gan shi asibitin nan, na kasa ganewa ko jinin na sa ya ke so a biya sa……” Cewar Baba Idris cikin dacin rai. Maganar ta shi ce ta firgita Baban Sasa, ya na mai rike kirji ya ce “Waye ya ba ni jini? Eye?”5 Shiru ne ya biyo baya, dan kuwa takaicin furucin Baba Idris ne ya hana su magana. Baba Anas na mai duban Baba Idris ya ce “Yanzu Idris menene amfanin kalaman ka?” “To to ai gwara ya sani, dan dai kun san da Baba ya na cikin hayyacin sa ba zai yarda a kara masa jinin arne ba!” Baban Sasa da hankalin sa ya gama tashi ya kara da “Yo ‘ya’yan nan kwa min shiru? Na ce jinin wa aka karamin!” “Jini na ne Baba, kuma har leda uku ma kuwa!” STORY CONTINUES BELOW Cewar Dee cike da tsokana, dan kuwa ya gane Baban Sasa irin wannan tsofaffin nan ne ma su kafiya, tun kalaman na sa na bata masa rai, har ya dena.2 “Jinin ka aka kara min yaro?” Cewar Baban Sasa ya na mai fidda idanu, Shi kuwa Dee ya gyada masa kai alamar “eh”. “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Shikenan ni Jamoh yara sun kashe ni da rai na! Yanzu Anas ka na ina aka karamin jinin arne! Yanzu da ku za a ci amana ta?”5 Kunya ne ya cika Baba Anas da Baba Salihu, su Baba Idris kuwa da ma abin da su ke so kenan, Baba Sasa ya san abin da aka masa dan an ga ya na kwance rai a hannun Allah. Ganin yanda Babab Sasa ya rikice, idanu na fidda kwalla hannu bisa kirji ya na faɗin “Jinin arne ke gudana a jiki na, an ci amana na, an cuce ni!” Dee ya ce “Kwantar da hankalin ka Baba, ni ma ɗin aro na ba ka ai ba kyauta ba, ka dawo min da kaya na, shi yasa ai kullum na ke zuwa duba ka, in ba haka ba ina ruwan arne da kai”2 Jin haka Baban Sasa ya tsaya ya duban Dee, irin wannan kallon na kar ka maida ni shasha mana. Su kuwa Baba Anas da Baba Salihu dariya ce fal bakin su ganin kallon da Baban Sasa ya ke yiwa Dee, amma su ka kunshe gudun bacin ran Baban Sasa. “Ku ji mu da yasasshen zancen! Ta yaya zan dawo ma ka da jinin na ka?” “Ai wannan abu ne mai sauki, da ka warke duka jinin jikin ka za a zuke, in ya so sai a tace min nawa daga na ka, dan ko nima ba na son jinin tsoho ya gwarwaya da nawa, hakan nan da kuruciya ta!” Cewar Dee da mayar da zafafan maganar Baban Sasa zolaya. Baban Sasa na mai duban Baba Anas ya ce “Anas ka ga ɗan butan tsiya! Da ka samu ma aka sanya jinin ka jiki na mai daraja! Sai ka zo ka zuke jinin na ka na gani! Dan tselan uwa kai!”4 Daga Baba Anas har Baba Salihu kasa rike dariyar su ka yi, dariya su ke sosai, cikin wannan yanayi likita ya shigo. Ganin yanda su Baba Anas ke cikin nishadi ya ce “An ya kuwa Baba ana bari ka huta?” “Ina za su bari na huta bayan sun kashe ni da rai na? Sun gaji da ni so su ke na mu su huta! Jinin arne su ka ƙaramin, gashi nan gaban ka ya na faɗa min wai biyan sa zan yi bayan na warke?” Ya na maganar ne ya na mai nuna Dee da ɗan yatsa. Ko da Doctor ya kalli Dee su ka hada ido sai ya fadada fara’ar dan kuwa ya san Dee tun suna makaranta. ” Ah Dee Yusuf! Har da kai ake daga hankalin Baba?” Dee na murmushi ya tashi ya na mai bawa Doctor hannu su ka gaisa, kana ya ce “Dr Abba Ai tsohon nan da ka ke gani ran karfe gare shi, mun yi kaɗan mu daga ma sa hankali, kawai dai jina na ne sai ya biya ni!” Dr Abba shi ma ɗin dariyar ya ke yiwa Baban Sasa ya ce “Dr kada ka daga ma Baba hankali, Baba rabu da shi, shakiyanci ne irin na jikoki…..” “Kai ni ba jika na ba ne! Ina ni ina jika da arne ne!” “Toh Allah ya ba ka hakuri Baba, Dee ko za ku fita daga waje? Ina so na duba Baba” Kai ya gyada, in da yayiwa Baban Sasa sallama, maimakon ya amsa masa sai ma kawar da kai gefe yayi. Aka bar Baban Sasa da Doctor. A waje Baba Salihu yayiwa Dee godiya, tare da bashi hakuri bisa lafazan Baban Sasa. Dee ya ce da shi kar ya damu, ai babu komai shi ɗin yanzu ya gama fahimtar Baban Sasa, ai shekaru sun ja. Cike da sha’awar hali irin na Dee Yusuf su ma yi sallama, bayan tafiyar sa Baba Anas ya ce da Baba Salihu zai so ace Dee musulmi ne, ko zai musulunta, da ko shakka aure tsakanin shi da Amatullah alkhairi ne, ya kare da “Ka ga fa yanda ya iya tafiya da Baba cikin sauki da lumana, duk da cin fuskar da mu ke masa, ina ma Saifullahi ke da wannan halin” Kai Baba Salihu ya gyada tare da faɗin “Yusuf sak, haka uban sa marigayi ya ke wallahi, Allah ya masa rahama” STORY CONTINUES BELOW Baba Anas ya amsa da Aameen. Su Baba Idris kuwa ba su fasa tuhumar su Baba Anas ba, dan kuwa wannan karan laifin biyu ya zama, wai har da na rashin kunyar sa su ka bari Dee yayiwa mahaifin su. Haka kan baffanin Amatullah ya rabu biyu, masu son Dee, wato Baba Zubairu, Baba Anas da Baba Salihu, sai kuma masu nuna masa kiyayya karara, Baba Hamza, Baba Mahamuda da Baba Idris. **** Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, sai da Baban Sasa yayi sati uku kwance gadon asibiti kafin a sallame shi, cikin satin ukun nan kuwa Dee Yusuf na yawan kai masa ziyara, acewar shi dubawa ya ke ya ga ko ya warke dan kar Baban Sasa ya warke ya cika rigar sa da jinin sa. Tun idan ya zo ya na kin amsa gaisuwar shi, har ya zo ya na amsa sama sama, Har dai ya dan saba da ganin sa. Haka duk sanda Dee ya tashi zuwa ya kan zo masa da kayan marmari, kamar ‘ya’yan itatuwa haka. Amma fa duk ran da ya zo ba sa wanyewa lafiya, hakan ya sa Su Baba Idris su ka yi kokarin hana shi zuwa ba tare da sanin Baban Sasa ko su Baba Anas ba. Ganin an sallame su, kuma kusan kwana uku kenan bai ga Dee Yusuf ba ya sanya Baban Sasa raba idanu. Kayan sa ake kwasa ana sanyawa cikin mota, cikin masu kwasar kayan har da Saifullahi. Baban Sasa zaune kan kujera, tun da aka sallame su aka ce ya zo a kai shi mota, ya ce ah ah a fara kwashe kayan tukun. Amma a zahiri jira ya ke ko Dee Yusuf zai zo. Baba Anas da Saifullahi ne su ka dawo tafiya da shi bayan Baba Hamza yayi gaba da ragowar kayan. “Wai lafiya yaron nan ya daina zuwa?”2 Cewar Baban Sasa yayinda Baba Anas da Saifullahi su ka riko hannun sa suna mai sanya shi tsakiya. “Wani yaro fa Baba?” Baba Anas ya amsa masa da tashi tambayar. “Wannan arnan mana! Dan Yusuf” Gaban Saifullahi ne ya faɗi jin Baba na maganar Dee Yusuf, shi kuwa Baba Anas darawa yayi ya ce “Ah Baba yau kuma kewan sa ka ke kenan?” Shiru yayi, sai da su ka isa mota kafin ya shiga ya amsa masa da “Ka san zuciya ba ta da kashi Anas, yaron nan duk da arne ne na gane ya na da hali mai kyau” “Ko dai kana jin tsoran kar ya zo a zuke masa jinin sa da ya ba ka ne” Cewar Baba Anas cikin zolaya yayinda ya taimakawa Baban Sasa ya shiga mota ya zauna. Shi kuwa Saifullahi wani malulun kishi ne ya taso ya tokare shi a kirji jin ana yaban tsohon saurayin Amatullah, dan kuwa duk duniyar nan idan akwai wacce ya ke so ta bi bayan Amatullah, so ya ke Baban Sasa ya sami sauki sosai ya lallaba shi ko Allah zai sa a mayar da auren su. Wai kuma har jinin sa aka sanyawa kakan sa! Wannan abu ya tsaya masa a rai, ya na kuma daga masa hankali. Daga cikin mota Baban Sasa ya dan leko, kana ya ce “Anas ba na son shakiyanci, amma dan Allah idan da hali a shaida masa an sallame ni, ka ga yana yawan zuwa duba ni, kar ya zo ya ga ba na nan” “Toh Baba za a sheda masa kuwa” Baba Anas ya amsa zuciyar sa ɗaya ba tare da ya lura da halin tashin hankalin da Saifullahi ke ciki ba. Haka su ka koma gida Baban Sasa na yaban Dee Yusuf, ihu ne kawai Saifullahi bai kurma mu su cikin motar ba tsabagen kishi.2 ***** Ranar da Baban Sasa ya koma gida murna gidan kamar sallah. Ayush kuwa ranar wuni ta yi cikin taikaci. Ko da Amatullah ta je gaishe da Baban Sasa, nan ma sai da ya mata maganar Dee Yusuf, cewar shi “Jinin Dan Yusuf aka kara min Amatullah, kin ga rayuwa kenan, na ki hada jini da shi sanadiyar sabanin addini, ashe akwai lokacin da jinin sa zai ratsa nawa, har ya ke gudana a jiki na!” Mamaki ne ya cika Amatullah, dan kuwa ko da wasa ba ta ji maganar nan ba, ba ta ji ko Mimi ma ta sani da ta fada ma ta. Haka su ka sha hirar su, nan ya jara jaddada mata ta shedawa wannan yar uwar Dan Yusuf din, cewar an sallame shi fa, dan Allah ta fada masa dan kwana biyu ya rabu da lekowa. Amatullah ta amsa da toh. Da haka su ka yi sallama. STORY CONTINUES BELOW *** Sai da Baban Sasa ya kwana uku a gida su Amatullah su ka fara Lectures gadan gadan. Jin Dee shiru Baba Anas da kan sa ya tambayi Baba Salihu number Dee, dan ya tambayi Amatullah ta ce ma sa ba ta da shi, kuma da gaske ba ta da shi din. Kamar daga sama Dee ya ji kiran Baba Anas, ko da ya gane Baba Anas ne sai gaishe shi cike da girmamawa, in da Baba Anas ya ce ya Kira yayi biko ne, kwana biyu sun ji shiru, ko dai ya fasa karbar jinin na sa ne? Baban Sasa ma ya na kyewar sa. Dee ya masa alkawarin zuwa tare da bashi uzurin komawar makarantar da dilibai su ka yi ya sanya hidama su ka yi masa yawa, ba tare da ya sheda masa su Baba Idiris ne su ka ja masa kunne akan zuwa gun Baban Sasa ba, a cewar su ya na hana shi samun kwanciyar hankali. Kamar yanda yayi alkawarin washagari sai gashi kofar gidan su Amatullah. Baban Sasa bai iya ɓoye farin cikin ganin sa ba, duk da kuwa har lokacin bai fasa zolayar sa ba. Dee sanye ya ke cikin shadda ruwan toka dinki buba, kan sa dauke da hula zanna bukar mai ratsin ruwan toka da kore. Waje gaban sa Baban Sasa ya bashi ya zauna, ya na mai duban sa ya ce “Kai Dan Yusuf sai kawai ka ɗauke kafa mu dena ganin ka haka ake yi?” “Sunana Dee Yusuf Baba, ka ce Dee ba Dan ba” Cewar Dee cikin zolaya. “Kai tafi can! Wannan ruwan ka ne ba nawa ba! Yaro na gode fa, ashe dai za ka min rana? Allah ya saka maka da alkhairi” Cewar Baban Sasa idanun sa na mai kawo kwalla. Ganin haka Dee ya ce “Ah ah Baba godiyar me ka ke min? Sai fa ka biya ni jini na? Haka za ka zauna da jinin arne?” “Yo to da haka sai ka kashe ni ai ka huta!” Dariya Dee ya saka. Nan su ka cigaba da hirar su tamkar jika da kaka, dan kuwa wasa da tsokanan shi da Dee ya ke ko Saifullahi ba ya yi. Sai da su ka gaisa da Baba Anas da Baba Zubairu sannan yayi musu sallama. Ya na shirin shiga mota ne sai ga Amatullah dauke da Emjay sun dawo daga makaranta. Ganin ta ya sanya Dee tsayawa ya na kallan ta yayin da zuciyar sa ke dada kamuwa da soyayyar ta. Sai da ta zo dab da shi sannan ya mayar da kallan sa ga Emjay wanda ke kwance kan kafadar ta. Kamar kullum yau ma hijabi ne jikin ta, fari kal. Zuciyar ta ke harbawa tun da ta yi tozali da Dee bai hana ta murmusawa ba yayinda da ta furta “Sannu da zuwa, ashe ka zo” Shi ma dai murmushin ya ke, ya na mai mayar da kallan sa ga fuskar ta, in da ta yi kasa da na ta idanun. Shi kan shi ya san Amatullah ta canza, Amma ba ya ce menene takamamman canjin ba. “Amatullah how are you? Ya babyn ki!” Ya tsinci kan sa ya na fada, dan kuwa ya biyewa zuciyar sa zai shagala ne nan tsaye ya na kallan ta. “Alhamdulillah, gashi nan bacci ya ke yi ya gama rigima” Ta juya masa fuskar Emjay, hakan yayi daidai da fitowar Saifullahi. Ran shi idan yayi duba ya baci ganin Dee da Amatullah, musammam yanayin da Dee ke kallan ta fuskar shi ɗauke da murmushi. Bai san sanda ya tunkare su ba, kamar daga sama sai gashi gaban su. “Amatullah ba ni yaron nan ba ki ga ana rana ba za ki tsaya da shi haka?”2 Cewar Saifullahi ya na mai kokarin karbe shi daga hannun Amatullah ba tare da ta ankare ba. Ganin haka babu shiri ta sakar masa Emjay, fuu ya wuce ciki. Daga Amatullah har Dee bin sa su ka yi da kallo cike da mamaki, musammam Amatullah da ta san tun da ta bar gidan Saifullahi bai taɓa nuna wani kulawa ga Emjay ba. Kallon Dee ta yi ta na mai murmushin yake dan kuwa hankalin ta na kan Emjay, shi ma Dee ya lura da hakan dan haka sai ya mata sallama ya tafi. Saifullahi kuwa bangaran sa ya wuce da Emjay, ya na shiga tsakar gida ya ci karo da kwanukan wanke wanke fal tsakar gida, daga gani an san kwanukan tun na jiya ne, kudaje ke bi gashi warin ruwan wanke da ke aje cikin kayan wanke wanke ne ke tashi. Dama ya kwaso bakin cikin Amatullah da Dee Yusuf. Jikin sa har rawa ya ke tsabagen bacin rai, STORY CONTINUES BELOW “Aisha! Aisha! Aisha!” Ya shiga kwalla mata kira da ƙarfi har sai da Emjay ya tashi daga bacci ya sa masa kuka. Amatullah da ta biyo sahun ɗan ta da sauri ta nufi bangaran Saifullahi jin kukan Emjay, shigar ta yayi daidai da fitowar Aysuh sanye cikin rigar bacci, wanda hakan ke tabbatar ma sa har lokacin ba ta bar gadon ta ba, bare a yi maganar yin niyar wanka da gyaran gida, bare uwa uba girki. Wani irin kallon tsana karara ta ke yiwa Saifullahi da Amatullah, yayinda Amatullah ke kokarin karbar Emjay. hannu bisa kugu Ayush ta ce “Malam lafiya? Wannan wani irin wulakanci ne za ka shigo min da tsohuwar matar ka gida ka na kwalla min kira haka kamar sakarai?” Bakin ciki da kunyar yanda Aysuh ke masa magana gaban Amatullah babu da’a bare tarbiya, ya ce “Aisha ni ki ke yiwa magana haka?” Amatullah da ta samu ta karbe ɗan ta gaba ta yi ta bar su nan tsaye Saifullahi na mai kumfar baki, ta na jiyo Aysuh na faɗin “An maka din! Akan wani dalili za ka kawo min tsohuwar matar ka gida? Ka kawo ta ne ta ga yanda ka ke kuntata min?” A fusace ya ce “Waya ya damu da ke da har zai kawo wata gurin ki? Why? Me ya sa ki ka cika lalaci ne? Why are you so dirty? God ban taba ganin kazamar mace kamar ki ba Aisha! Ace tun safe rigar bacci ne jikin ki? Kalli tsakar gidan ki kaca kaca! Wanke wanke fal guri! Kin mike kafa ki na ta baccin asara!”2 Yatsune ta yi, cikin halin ko in kula ta ce “Gidan da ka dauko ni ko tsinke ba na daukewa, diyar hutu ce ni ka sani sarai ka san in da ka ɗauko ni! Ni ba baiwa ba ce bare yar aiki! Nan su Naja’atu suna shigowa suna taya ni aiki kai da Hajiya ku ka haɗa baki ku ka hana su, saboda haka idan ya maka ciwo kai ma kana da hannu ka gyara! In kuwa ba ka iyawa sai ka yiwa Hajiya magana ta zo ta gyara ma…..” “Shut up!!! Mahaifiyar tawa ce za ta zo ta gyara mi ki gida? Ashe ba ki da mutunci Aisha?”2 Ya katse ta cikin tsawa. Kallon sa ta ke a wulakance ta ce “Wallahi na yi da na sanin auren ka Saifullahi, dan haka a yau da za ka sauwake min ba ƙaramin farin ciki zanyi ba…..” “Na sauwake mi ki? Haka ki ce?” Ta na murguda baki ta juya da niyar komawa daki, wani irin wari ne ya buso su sanadiyar iskar da ta kado ruwan waken da ke wajan wanke wanke, Saifullahi yayi saurin ja da baya yana mai toshe hanci, ita kanta Ayush sai da ta rufe hancin ta, murya kasa kasa ta ce “Hmmmm Hajiya ta yi hamma!”11 Hakan ya sa Saifullahi harzuka dan kuwa ya so ya ji abun da ta ce “Ke! Me ki ka ce? Me ki ka ce Aisha?” Daki ta shige ba tare da ta amsa masa ba, cikin masifa da bambami kamar wanda ya zautu Saifullahi ke faɗin “Da mana ki maimaita! Ashe ke maraya kunyar karya ce! Ki maimaita mana! Da yau na tattaka ki, sakarya wacce ba ta san darajar iyayen ta ba!” Baba Anas ne ya zo wucewa, jin muryar Saifullahi ya na bambami ya sa ya ɗan tsaya, ya lekoshi tare sa faɗin “Saifullahi a na yin hakuri, zama da mata ai sai da hakuri, amafanin dace da kamular mace kenan ai Saifu”2 Yana maganar ya wuce abin shi ba tare da ya jira amsar shi ba, dama shi ma Saifullahi da ya san magana ya faɗa masa bai da niyar amsa masa. Ciki ya shiga ya nemi su Naja’atu ya ce su zo su gyara masa gidan dan ko ruwan gidan ba zai iya hadiya ba muddin ba gyarawa aka yi ba. ***** Washagari a makaranta tun safe Amatullah da Mimi su ke fafutukan lectures, duk da tun safe jikin Emjay ya ki dadi, kuka ya ke mata na babu gyara babu dalili gashi ya ki shan nono. Sai da ta goya shi yayi bacci sannan ta samu sauki. Kusan minti ishirin yayi ya na bacci, suna gaban notice board suna kwafar timetable da aka canza kawai ta ji ya na mimmike mata a baya. Cikin damuwa ta ce da Mimi “Mimi kin ga yanda Emjay ya ke mimmike min a baya, ina ga yaran nan be da lafiya dan Allah kama min shi na kwanto shi” Mimi ta amsa da “toh” yayinda Amatullah ta sauko da Emjay da tuni ya gama mimmikewa kamar mai shirin suma. Ganin haka Amatullah ta “Na shiga uku me ke damun yaron nan haka!” Mutanan da ke kusa da su duka hankalin su ya koma kan Emjay, nan aka zagaye su in da aka basu shawarar kai shi asibiti da gaggawa. Dan ajin su Amatullah ne ya karbi Emjay, ya wuce gama Mimi da Amatullah na biye da shi. Allah ya so nan cikin department ya aje motar shi, ko da su ka shiga motar Mimi ta karbi Emjay dan kuwa Amatullah jikin ta har rawa ya ke tsabagen tashin hankali, ba tare da bata lokaci ba su ka wuce asibiti. Yanda Emjay yayi wata mika tare da sauke numfashi ya sanya Mimi ta san rai yayi halin sa, amma ta kasa faɗawa Amatullah. A haka su ka isa asibiti. Haka shi ma ɗan ajin na su da ya dauki Emjay bayan da su ka isa, ya ji ya kara nauyi ga idanun sa sun kafe ya san Emjay kam ya kare, kallan Mimi yayi in da ta gyada masa kai. Haka jiki babu sanyi su ka shige asibitin, Amatullah da ba san halin da ake ciki ba tuni ta yi gaba da saurin ta. Suna isa emergency tun kafin Doctor ya taba shi ya ce da su “Ku yi hakuri, yaran nan ai ya cika…..”4 Cak Amatullah ta tsaya ta na kallon Doctor, kafin daga bisani ta mayar da kallon ta ga gawar Emjay da ke kwance gaban su, a hankali kamar mai rada ta ce ” Ko taba shi ba ka yi ba ka ce ya cika? Haka ku ke aikin asibitin? Bai cika ba Doctor, duba ka gani ai suma yayi fa, dan Allah ka tayar da shi……” “I’m sorry Madam” Ganin yanda Amatullah ta dauki gawar Emjay ta na mai rungume shi a kirjin ta, ya na kallan Mimi ya kara da “ina ga zai fi kyau ku tafi da su gida, she is in shock”. Shi kan shi dan ajin na su ya tausayawa Amatullah, bare Mimi da Emjay ya zame mata tamkar dan cikin ta. Dan ajin na su ne ya ce zai kai su gida, amma har lokacin Mimi ta kasa tabuka komai, bare uwar gayya Amatullah da ta rungumi gawar dan ta tana mai raba idanu. Mimi na share hawaye ta ce da Amatullah “Amatullah” Karo na farko da ta Kira sunan ta kenan, maimakon ta amsa mata, kawai sai ta zuba mata idanu. Mimi ta ce “Tashi mu tafi gida” “Mimi bai mutu ba, Emjay bai mutu ba, dana bai mutu ba, ku kai ni wani asibitin wannan ba su san abun da su ke ba” Hawaye ne me zuba daga idanun Mimi, ta ma kasa magana sai kawai ta ruko Amatullah ta na kuka. Da kyar dan ajin na su ya shawo kan Mimi, ta taimaka su ka samu Amatullah ta shiga mota. Mimi ce ke nuna masa hanyar zuwa gidan dan kuwa tun da Amatullah ta shige gidan baya dauke da gawar Emjay, ba su kara jin ko tarin ta ba, idanu ta tsurawa gawar har su ka isa gida. A kofar gida ta tarar da Saifullahi, daga ganin alama fita zai yi. Ganin shi Amatullah tun kafin su faka mota Amatullah ta bude murfin motar, dan haka dole dan ajin na su ya tsaya nan tsakiyar hanya, da sauri ta fito gun Saifullahi ta nufa ta na mai nuna masa gawar Emjay ta ke faɗin “Ya Saifullahi ka ga wannan Doctor din sam be san abin da ya ke yi ba, ya kalli tsabar idona ya ce min Emjay ya cika!” Kallan ta ya ke tamkar ba hausa ta ke masa ba yayinda yayi kokarin karbar Emjay daga hannun ta amma ta hana shi. Cike da alamar tambaya ya ke duban Mimi da ta biyo bayan Amatullah. “Me ke faruwa ne? Me ya same shi? Saifullahi ya shiga jerowa Mimi tambaya. Cikin sanyin murya ta ce “Sai dai ku yi hakuri, Emjay ya koma ga Allah” Wani irin razana Saifullahi yayi ya na mai kokarin duba gawar Emjay. Amatullah kuwa cikin gargadi ta ce da Mimi “Ina ganin mutuncin ki Mimi, kar da ki sake cewa dana ya koma ga Allah! Emjay na nan tare da ni!”6 *** how? Menene ya same shi? Me ya faru?” + Saifullahi ya sake tambaya jiki na rawa. Amatullah ta wuce ciki rugume da gawar Emjay, ɗakin Baban Sasa ta shige nan ta tadda shi kwance. Ganin shigowar ta ko sallama babu ya sanya shi tashi zaune, ya na mai faɗin “Amatullah lafiya?” Gaban sa ta shimfide gawar Emjay, ta ce “Ka ga Emjay Baban Sasa, lafiyan sa lau mu ka tashi, Wai dan kawai ya ɗan yi mika mu ka kai shi asibiti, likitan ya ce wai ya mutu!” 2 Kallo ɗaya Baban Sasa ya masa ya san ko shakka babu tabbas babu rai jikin Emjay. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ya faɗa da kakkausar murya. “Baban Sasa karya su ke, dan Allah ka tada min shi, Emjay tashi, tashi ɗan albarka” 5 Ta shiga jijjiga kafadar gawar. Ganin haka Baban Sasa ne ya mike tsaye, hannun Amatullah ya kama, ya na mai janye ta daga jikin gawar, ta na cijewa, faɗi ta ke “Baba Sasa tsaya mu tashe shi” Fitowa yayi da ita, ya na rike da hannun ta su ka nufi cikin gida, Amatullah ba ta fasa waigawa ba tana cewa “Baban Sasa kar mu bar shi shi kaɗai cikin ɗaki, idan ya tashi bai ganni ba kuka zai yi” 4 A haka su ka isa har ɓangaran Gwaggo, in da ganin Amatullah da Baban Sasa ya sa duka ahalin gida su ka biyo bayan su. A tsakar gida su ka su ka tarar da Gwaggo, cikin alhini Baban Sasa ya ce “Yaro ɗan wajan Saifullahi dai Allah ya amshi abin sa, sai ki masa addua Allah ya masa rahama, yanzu za mu shirya shi a kai shi” Salati Gwaggo ta saka, haka ma sauran jama’ar da ke gurin. Amatullah har lokacin ba ta fasa karyata maganar mutuwar ba. Gwaggo ce ta shiga da ita ciki, in da yanayin gidan gaba ɗaya I ya canza, daga masu kuka sai masu salati da sallallami. 4 Baban Sasa ya koma ɗakinsa bayan ya shaidawa su Baba Anas a yi shirin yiwa Emjay wanka, a shirya shi cikin gaggawa, su Baba Idiris kuwa su ne su ka tafi makabarta domin haka kabari. Saifullahi zama yayi dirshen a ƙasa in da Amatullah ta bar shi tare da Mimi. Surutai ya ke mara kan gado tamkar wanda ya zare. A haka Baba Anas ya zo ya same shi, ya ce da shi maza ya zo a shirya ɗan sa tare da shi. 2mSai da Mimi ta nemi wayar Dee har sau wajan uku ta na Kira ba ya dagawa, daga bisani ta masa text, dan kila ya sa wayar a chaji ne ya shiga aji ya na bawa dalibai karatu. Gab da la’asar aka shirya Emjay tsaf. Kafin a fita da shi aka ce da Amatullah ta zo ta masa sallama. Mama ce da Mimi su ka kai ta dakin Baban Sasa.2 Sai da ta ga an rufe Emjay cikin lin kafani sannan ta yarda lalle da gaske mai raba ɗa da mahaifiya yau ta mata yankar ƙauna. Gaban gawar ta zauna, hannun ta bisa gawar ta furta “Yaro na? Ka na jin Maman ka? Yaro na naso ka, Ina son ka, Amma Allah ya fini son ka, ya karbe ka, na yafe ma ka, Allah ya rahamshe ka Emjay…..Allah….Alllah….Allah……” 4 Kukan da ya ci karfin ta ya sanya ta kasa karasa maganar, kawai sai ta sunkumi gawar ta na kuka ta na faɗin “Ya Allah….Allah…..ya Allah!” Daga Mimi har Mama duka kuka su ke, shi kan shi Baba Anas hawaye ke gudana daga idanun sa, bare Baban Sasa, wanda ji ya ke dama shi mutuwar ta ɗauka ta bar masa ɗan jikar sa. 5 Saifullahi wanda tun shigowar Amatullah kan sa ya ke sunkuye, ya taso daga in da ya ke, cike da tausayawa ya shiga kokarin karɓe Emjay, shi ɗin ma hawaye ya ke. Da kyar ya iya karɓan shi, su Mama su ka janye ta ciki. Nan ɗin ma su duka su ka shiryo cikin alwala don halartar sallah gareshi. Ba tare da ɓata lokaci ba aka sallaci Emjay, amma tun a kabbarar farko Saifullahi ya gaza, sai kuka haka har aka idar da sallah. Mata su ka koma cikin gida yayin da maza su ka doshi hanyar maƙabarta. Saifullah ya ɗauki gawar cikin tabarma lullube da zanin goyan sa, ya ki bawa kowa har su ka isa makabarta. Baban Sasa kadai aka bari waje bisa tabarma kasancewar jikin sa ba zai bari ya iya zuwa makabartar ba. 2 Ganin har la’asar ta gota sosai ba su dawo ba ya sanya Baban Sasa tayar da sallar la’asar, hakan yayi daidai da isowar Dee Yusuf wanda bai sami sakon Mimi ba sai bayan da ya fito daga aji, kai tsaye ya nufo gidan su Amatullah. Ganin babu kowa wajan ya tabbatar ya makara an tafi kai Emjay. Dan haka gudun kar shi ma ya makara ya ɗora alwala, Baban Sasa ya kai raka’a biyun farko ya zauna tahiya shi ma yayi yi harama, ya na mai kabbara ya zauna gefen shi in da ya shiga mika tashi sallah ta hanyar bin Baban Sasa. 14 Sai da su ka zauna tahiyar karshe sannan jama’ar da su kai Emjay su ka shigo layin. Sam babu wanda ya lura da wanda ke bin Baban Sasa sallah, sai da su ka zo dab da su, wato daga Baba Mahmuda, Baba Anas, Baba Idris, Baba Hamza, har zuwa Saifullahi tsayawa su ka yi cirko cirko suna duban su, hakan kuma yayi daidai da lokacin da Baban Sasa yayi Sallama, ganin yanda su ka yi tsaya kamar sokwaye ya sanya shi waigawa gefensa, me zai gani? Dee ya tashi tsaye ya na mai kabbara ya shiga rama raka’oi biyun da ya rasa. “Lahailaha illallahu!” Cewar Baban Sasa! “Kai Dan Yusuf dama ka na sallah?” 5 Ya faɗa tsabagen mamaki ya ma manta ba a yiwa Wanda ya ke sallah magana. Shi kuwa Baba Idris hargiza yayi cikin nuna bacin rai ya ce “Isgilanci ne irin na arna! Mu za ka yiwa shakiyanci! Karya ya ke yi ba ya sallah! Yaudarar ku ya ke so yayi, dan ni wallahi babu arnan da zai yaudare ni!” 2 Baba Anas na mai taɓa kafadar Baba Idris ya ce “Bari mu idar da sallah kila ma iya sauraran yashesshen zancen nan na ka!” Ya na mai duban sauran jama’ar ya ce “Ni dai ina da alwala, Idan da mai alwala ku zo mu yi jam’i ko? Lokacin sallah ya riga ya kure” Ya na gama faɗin haka ya cire takalmi ya bi bayan Dee, haka ma Baba Mahmuda da wasu makotan su biyu da su ma din su ka ce suna da alwala. Takaici ya sa Baba Idiris shigewa ciki. Shi kuwa Saifullahi sallah Dee zame masa ta yi tamkar an sake masa wani rashin, lalle lokacin komawar Amatullah yayi ko da kuwa da tsiya da tsiya tsiya ne sai ya sake mallakar ta, ba zai yiyu ya na ji ya na gani ya rasa Emjay ya rasa uwar Emjay ba. Kasa zama sallahn yayi, shigewa cikin gidan yayi kamar mai shirin tashi sama. Koke-koken mata ya ke ji zuciyar sa na ƙara tsinkewa. Haka ya lallaɓa ya shiga sasansa ya zauna a kujerar falo. Ba komi ke masa yawo a idanu ba sai yanda da hannunsa ya cusa ɗansa a cikin rami, sannan yana kallo aka maida ƙasa aka rufe shi. Tiryan Tiryan komi ya dinga dawo masa kamar mai bita, tun daga kai ta asibiti don a cire cikin, zuwa haihuwar da tayi bai dire a ko ina ba sai inda ya sheganta ɗansa. “Yaa Rabbi ka yafe min, Emjay ka yafe min” ya ce yana mai dafa kansa.4 “Ai da bin sa ka yi ƙarshen soyayya” Ayush da tun shigowar sa take kallonsa tace tare da jan tsaki. Sai a sannan ya ɗaga ido ya kalle ta haɗe da kula da zaman ta a wajen. “Ayush Muhammad Jamoh yaro na ya rasu” ya ce mata cikin sigar neman ɗauki, kallonsa take cikin yanayin rainin wayau, ba ta san sanda ta kece da dariyar rainin wayau ba haɗe da ɗiban dambun naman da take ci tare da kai shi baki. “Wai dama kana da ɗa ne? Ina ce tuni ka yar da kwallon mangwaro” tace masa cikin tuna masa Kalamansa gareta lokacin da ya faɗi mata ya saki Amatullah.4 “Aisha!!!” yace cikin daka mata tsawa, ita kuma tattara kwanon dambunta tayi, ƙara kallonsa tayi ta saki dariya kafin ta shige ɗaki ta rufo ƙofa har da saka makulli.2 Ɗumin da yaji na sauka a fuskar sa ne ya sanya shi sharewa, sai a lokacin ya tabbatar da kuka fa yake, kuka akan mutuwar yaron da ya ce ba nashi bane.4 *** Dee Yusuf na idar da sallah ya kauce zuwa gefen Baban Sasa saboda sallah da su baba Anas ke yi. Azkar ɗin da annabi ya koyar na bayan sallan farali yayi, cikin natsuwa wanda hakan ya zama masa jiki tun bayan da aka koyar da shi. Fara’a sosai Baban Sasa yake yi yana mai jin ƙauna Dee na ƙaruwa a zuciyarsa, Godiya ya shiga yi ma Allah da ya sa hakan ya tabbata.2 A kan idonsa Dee ya yi Raka’a biyun da zai cika na sallah, mamaki sosai ya cika Baban Sasa ganin sallah yayi a natse cikin kwarewa.2 “Dan Yusuf jika na” Baban Sasa ya ce yana mai shafo shi cike da ƙauna.6 “A’a fa, ka ji min tsoho, ni dai jini na kawai zaka bani” yace cikin shaƙiyanci.2 “Ja’iri!!!” Baban Sasa yace yana mai kai masa duka. A wannan gaɓan su ka idar da sallah, baba Zubairu tsam ya tashi ya nufi Dee ya miƙa masa hannu.2 “Allah ya ƙara ma rayuwa Albarka, mene sunan” yace masa bayan sun yi musabaha.2 “Dawood!” Dee ya amsa cikin farin ciki. “Dauda dai ko?”4 Baban Sasa ne ya tambaya. Dee na girgiza kai ya ce “Ah ah fa tsohon nan kar ka ɓata min suna, Dawooda ne, haka sunan ya zo cikin alqur’ani, inda Allah ya jero sunayen annabawa 25 acikin suratul An’am, haka kuma suratul Saba’i inda Allah yayi magana akan falalar da ya bawa annabi Dawood, haka suratul Namli in da Allah yayi magana akan ilimin da ya bawa annabi Dawood, haka kuma suratul Saad inda Allah yayi maganar Khalifancin da ya bawa annabi Dawood a doran ƙasa, haka da sauran wajajen ma”9 “Ummmmm” “ummmm” Abin da ke fita daga bakin su kenan jin yanda Dee ke musu bayani cikin nutsuwa da tsari. Dee ya kare da STORY CONTINUES BELOW “A cikin Bible kuma sunan a David ya zo…..” “Allahu akbar! Allah shi ne mafi girma! Allah ya sa mu cika da imanin mu! Allah ya maka baiwa yaro, ka gode masa!” Cewar Baba Anas cikin sauki da kaunar Dee.2 “Bamu labari ma” Baban Sasa ya ce yana mai riƙe masa hannu cike da ƙauna. Dariya Baba Anas da Baba zubairu su ka yi, yayin da Baba Mahmuda ke yaƙe, Baba Idris da Baba Hamza kuwa zama su ka yi don jin ƙarshen ƙarya. “Bayan zuwa na gidan nan, na taradda auren Amatullah, lokacin gaba ɗaya na amince da babu addinin gaskiya sama da musulunci. Zuciyata ba ta karye ba, amma ina barin gidan nan na samu saƙon rasuwan uban riƙo na mijin mahaifiyata, haka na isa gida na tsaya mata a lokacin da ta fi bukatata sannan aka yi makoki da ni.2 Bayan kammala karatu na, duk lokacin ina cikin waswasi tsakanin amsar addinin musulunci ko kuma maida hankali wajen gyara rayuwata ta duniya. Na koma gida a wannan halin, ban ɓoye ma mahaifiyata komi ba game da halin da nake ciki. A bisa umurnin ta na isa Haɗeja, ban sha wuya ba wajen gane gidanmu, kamanni na da mahaifi na ya sa ba su gardama kasancewa na tsatsonsu ba. Sun min tarbo na musamman ba tare da sun damu da sanin addini na ba, sun yi farin ciki ainun sannan na ƙara da musu albishir din son amsar musulunci.2 Sai da nayi wata ɗaya a Haɗeja sannan na kai ma mahaifiyata ziyara a lokacin na iya izifi huɗu daga tabara zuwa nasi. Ko da mu ka tashi zuwa bautar ƙasa na yi yanda za a tura ni jihar Jigawa daga nan na nemi hanyar yi a Haɗeja, a nan na yi amfani da shekara ɗayan nan na nemi ilimin addini sosai, nayi fiqhu na yi tauhidi ga Hadisai duk na nemi ilimin su. Muna kammalawa na samu gurbin aiki a ABU saboda fita da sakamako mai lamba ɗaya da nayi, sannan na cigaba da masters dina, bayan dawowan ne na fara zuwa ɗaukan karatu wajen Ustaz Yunus inda nake haddan Ƙurani, yanzu Allah cikin ikonsa na haɗa izifi Arba’in, daga Nasi zuwa Tauba”6 Ko da ya kai ƙarshe hawaye sosai Baban Sasa yake, imani na ƙara ratsa shi, ya san cewa akwai wainda aka haifa a cikin musulunci da basu samu ilimi mai zurfi da Dee ya samu ba.4 Ko a zaria da yake matattaran ilimin addini, inda duk in da ka zaga ina ka fito islamiyya ina zaka majalisi ne akwai da yawa da suke da shekarun Dee kuma ba su samu gatan ilimin ba. Kenan ba ruwan sanda ka shiga addini da yanda za ka riƙe shi.2 “Dawooda Ɗan Yusuf, Na maka murna, lallai kai din mai tsananin rabo ne, Ubangiji Allah ya baka dukkan alkhairi duniya da lahira”4 Baban Sasa ya faɗi zuciyarsa cike da Nadamar abin da ya aikata a baya. Nan dai Su baba Anas su ka haɗu suna masa fatan alkhairi. Sai wajen ƙarfe biyar da Rabi ya nemi Mimi ta fito su ka tafi. A hanya ya ke tambayar ta halin da Amatullah ke ciki, ta amsa “Sai ka tausaya mata Dee, she is in pain, wallahi ta na ganin rayuwa” “She will be fine in Sha Allah, I will give her the best I can when we unite”4 Baki washe jin maganar Dee Mimi ta ce “Yessssssss! That’s the spirit!” Dariya yayi, cikin ran sa ya na mamakin yanda Allah ya haɗa jinin Mimi da Amatullah.2 ***** Dee bai sau damar yiwa Amatullah gaisuwa ba sai da aka yi uku. Daga soro ta fito sanye cikin hijabi. Muryar ta dashe saboda murar da ya kama ta. Ya na mai tsura mata idanu ya ce “Amatullah, ki yi hakuri, Allah zai musanya mi ki da alkhairin sa, Allah na sane da ke” Kai ta gyada masa ala’amar “eh” sannan ta kara da “Ina wuni?” “Lafiya lau Alhamdulillah, ya hakuri?” Cewar shi cike da tausayawa. “Alhamdulillah” “Allah ya masa rahama, ya sa mai ceto ne”2 “Allahumma Aameen” Shiru ne ya biyo baya, daga bisani ya mata sallama ta koma ciki shi kuma ya koma wajan Baban Sasa. Duk wannan hidimar da ake yi akan idanun Saifullahi, idan akwai wanda ya tsana duk faɗin duniyar nan ya bi bayan Dee Yusuf.2 Nan ya kara shan alwashin tsananta tazara tsakanin Dee da Amatullah ta hanyar tunkarar Baban Sasa da maganar komen Amatullah, da zarar An yi bakwai din rasuwar Emjay.4 **** Ranar da aka yi bakwai da daddare Saifullahi ya sami Baban Sasa, Nan ya kalallame shi har ya na fitar da kwalla ya ke faɗin “Baban Sasa ka rufa min asiri ka mayar da aure na da Amatullah, wallahi na yi kuskure na yi nadama, ka duba girman zumunci ka min wannan alfarmar Baban Sasa, ka bani damar gyaran kuskuren da na yi, na ma ka alkawari zan zamo abin alfahari a gare ka”5 Ganin yanda Saifullahi ke fitar da kwalla, da kuma yanda ya rame yayi baki gaba daya ya fita daga hayyacin shi ya sanya zuciyar Baban Sasa karyewa. “Saifullahi” Ya kira sunan sa a sanyaye. “Na’am Babab Sasa” “Amatullah ta ce saki uku ka yi mata, ka yi hakuri” “Wallahi Baban Sasa daya dal na mata, ina ga zafin sakin ya sa ta dage a ukun na mata, Baban Sasa Amatullah na jin maganar ku, yarinya ce mai hankali, ladabi da biyayya, na tabbatar muddun ka ba ta umarni za ta bi, ka taimaka min Sasa” Ya kare cikin shasshekan kuka.6 Shiru Baban Sasa yayi ya na mai ɗan tuntuntuni, kafin daga baya ya furta “Kar ka damu Saifullahi, zan yi iyakan kokari na in Sha Allah, idan Allah yayi da rabo za ta koma, ka kwantar da hankalinka kar ciwo ya kama ka” Cikin jin daɗi Saifullahi ya riko kafafun Baban Sasa, faɗi ya ke “Na gode! madallah, na san za ka min rana, Allah ya saka da alkhairi, yanzu zuwa gobe za ta komo min ko?”7 Kai Baban Sasa ya girgiza ya ce “Nan fa daya, ka yi hakuri zafin mutuwar nan ya ɗan bar ta, nan da sati biyu haka sai a mata magana” Murna sai ta koma ciki, ran sa ya ki ya motsa dan kuwa gani yake in har ya tsaya kallon ruwa kwado zai iya masa kafa.2 “Amma Baban Sasa ba ka gani jinkiri na iya haifar da fitina?” “Fitinar me kuma? Ah ah kar ka damu in Sha Allah”4 Jiki sanyaye yayi masa sallama. Kai tsaye dakinsa ya nufa. Ya na zancen zuci ya manta bai yi sallama ba, kan gado ya tadda Ayush ta yi daidai cikin shigar nan nata da ta saba ta na bacci har da mun shari, shigar da take rikita Saifullahi da shi a da, Amma yanzu kuwa sam ba sa burge shi, bare ta ɗaɗa shi da kasa. Ya na mai girgiza kai har zai juya ya fita idanun sa suka sauka kan ɗan karamin kwalin magani gefe a ƙasa, haka nan ya ji ya na so ya ga maganin menene. Ko da ya ɗauka ya duba sai gashi an rubuta “emergency contraceptive”2 Ya faɗa , ya maimaita! Wai shi Saifullahi matar shi, matar ma ta so ce ke shan Emergency contraceptive? Wato tsabagen dan kar ta haihu da shi? Ɓacin rai ya sanya ya manta makoki ya ke, dan kuwa idanun sa sun kada sun jajur. Nan take ya karasa wajan Ayush. Sam be damu da baccin da ta ke ba cikin nuna isa, ya shiga neman hakkin sa. Duk yanda ta so ta kaurace masa ta kasa har sai da ya biyawa kan sa bukatan sa. Ta na samun ta kan, ta tashi cikin sauri naɗe cikin bargo, cikin tashin hankali ta shiga binciken maganin ta kwali daya dal da ya rage, domin kuwa ta sa a samo mata cikin unguwar ba a samu ba sai Jamila ta yiwa waya, ta mata alkawarin turo mata da shi nan da kwana biyu. Ya na daga kan gado ya ke kallon ta, ta ƙaraci dube duben ta, Amma babu magani babu alamar sa. Ganin babu sarki sai Allah ta dubi Saifullahi ta ce “Malam menene haka za ka far mani ina bacci kamar dabba! Wannan wani irin gidadanci ne! Kai wani irin bagidaje ne! God Saifullahi you so local! Too local for my liking! Wallahi da na san haka kake bagidaje da ban aure ka ba!”2 Yanda ta ke maganar ne, da kalaman ta da ke shigar sa kamar kibiya tsabagen ɗaci ya sanya shi tunawa da lafuzzan sa ga Amatullah,4 ‘bagidaje? Shi Saifullahi ne matar shi ta aure ke kira bagidaje? local? Shi Saifullahi shi ne local?’32 Abin da zuciyar sa ke faɗi kenan, azahiri kuma kallon ta ya ke cike da tsana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *