TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 13 KARSHE
In da Dee da Amatullah su ka yi kwanan farin ciki, Saifullahi da Ayush a nasu ɓangaran kwanan tashin hankali su ka yi, Dan kuwa Saifullahi ranar kamar wanda aka yiwa mutuwa, wani bakin kishin yau Amatullah za ta kwana da wani ba shi ba ne ya addabi rayuwar sa. Matar shi da ta gane yanayin da ya ke ciki ba ta saurara masa ba, ba ta yi la’akari da jama’ar biki da ke gidan ba haka ta ringa neman sa da tashin hankali ta na mai daga murya. Sai barin ɓangaren sa yayi, ya koma falon Baban Sasa, nan ya sha kukan sa ya koshi kamar yaro dan goye. Yanda ya ga dare haka ya ga rana.2 **** Sai da Amatullah ta yi kwana uku a gidan ta, a daren na hudu su ka raya sunnar manzon Allah SAW, cikin aminci da yardan juna, so da kauna tare da tausayi. Farin cikin da Amatullah ta ji ko rabin sa ba ta ji ba sanda ta kasance da Saifullahi a daren su na farko. Dee ya mata alkhairi babu adadi, ya Kuma mata albishirin zuwan su umarah da za su yi wata mai zuwa. Tun da aka yi auren Dee da Amatullah Ayush ta dena ganin Saifullahi da gashi, musammam yanda ta ji labarin gidan Amatullah bakin jama’ar gidan. Kullum cikin gorin takaici ta ke yiwa Saifullahi, da ta kira shi bagidaje, sai ta kira shi local. Babban tashin hankali gare shi shi ne yanda in za ta yi kwatancen Mijin da ya hadu sai ka ji ta ambato mijin Amatullah. Wanan shi ne babban dalilin da ya kara lalata zaman auren su.2 Kafin su tafi Umarah Dee ya kai Amatullah Abuja wajan mahaifiyar su, so da tararraya babu wanda ba ta sha ba. Ita kan ta Amatullah ta san ta yi dace, ba ga mijin ba, ba ga surikar ba. Dee ne ke kai ta makaranta ya ɗauko ta, shi ya tsaya tsayin daka akan karatun ta, su na gama exam su ka keta hazo zuwa kasa mai tsarki. *** A kwana a tashi haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin Ayush ya tsufa sosai har ta wuce EDD ɗin ta sannan aka yi inducing din ta, har an fidda rai ana shirin shiga da ita Cs Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗan ta namiji. Sai dai Allah da ikon sa yaron ya zo da matsalar down syndrome, irin wannan yaran masu halitta daban, wanda sukan dalalar da yawu haka kuma hannun sa daya shanyayye ne.2 Tun da aka nuna mata ɗan da ta haifa ta ke kuka, haka ma Saifullahi wanda ya hau ta da faɗa, a cewar shi ita ta jawo musu masifar haihuwar nakasasshan ɗa, sanadiyar cikin da ta yi kokarin zubarwa, ta cuce shi ta zalunce shi.6 Sai da su ka yi kwana huɗu a kwance gadon asibiti saboda yaron bai da isasshen lafiya, wata tsohuwa aka turowa Aysuh daga Kano domin kula da ita dan Hajiya ta juya mata baya. A kwana na biyar ne da kyar Amatullah ta lallaba Dee ya yarda ya kai ta asibiti ta duba shi, kasancewar Baban Sasa na ta tambayar ta ko ta je ta duba Ayush, bai san ita ma fama ta ke da laulayi ba. Najaatu da Baba Anas ya tilasta mata zama da Ayush ce su ka gani a harabar gaban ɗakin. Gaishe su tayi a mutunce tana mai cike da fara’a, nan Amatullah ta ce ta shiga ta musu iso. Tashi tayi ta shiga ɗakin fuska ba yabo ba fallasa. “Yaya Amatullah ce da mijinta su ka zo gaida ki” Wata irin zabura da Ayush ta yi sai da ya firgita tsohuwar da ke zaune mata “Kutmesi, watau don munafunci zuwa su ka yi su ga abin da na haifa su min dariya ko, toh wallahi ubansu yayi kaɗan” tace cikin hayagaga.2 “Haba Aisha, ina laifin wanda ya gaishe ka, ai sau dubu ya fi wanda ya zage ka, ce musu su shigo yarnan” ta ce tana ƙarewa da isar da sakon ga Najaatu. Tun da su ka shigo Ayush ta ɗaga idanu ta kalli Amatullah gaban ta yayi mummunar faɗuwa, ta ga yanda ta yi kiba ta yi kyau, abin ka da mai yaron ciki nan har wani sheki ta ke na musamman. Da ya ke dare ne Amatullah sanye ta ke cikin bakar abaya da aka yiwa ado da shuɗin duwatsu, Daya daga cikin abayar da Dee ya siya mata zuwan su umarah ne, ta naɗe kanta da shudin mayafin kamar diyar larabawa, haka kuma bakar safar da ke sanye kafar ta bai hana shudin takalmin ta mai tsayi haskawa ba. Hankalin ta bai tashi ba sai da ta ga wanda ke biye da Amatullah ya yiwa mijin ta tazara a komai nesa ba kusa ba.4 STORY CONTINUES BELOW Sanye ya ke cikin kananan kaya, shudin riga da bakar wando, kusan ma anko su ka yi. ‘kar dai wannan shi ne mijin na ta?’ Tambayar da ta yiwa kan ta kenan. Yanayin kallon da ta ke masa ya sanya Dee riko hannun Amatullah. Amatullah na gaishe da tsohuwar tare da yiwa Ayush ya mai jiki, amma ina gaba ɗaya hankalin Ayush na kan Dee. Namiji har namiji, kyau, kwarjini da wayewa wane Saifullahi, bare nakasassan ɗan shi da ta haifa. Amatullah da idan ta lura da halin da Ayush ta shiga sam ba ta nuna ba, ta karɓi dan ta na mai faɗin “Allah ya raya mana” Tsohuwa ta amsa da “Aameen” Ana haka sai ga Saifullahi, wanda kamar Ayush, shi ma ɗin ganin Amatullah ba ƙaramin firgita shi ya yi ba, ashe haka Amatullah ta ke da kyau bai taɓa sani ba, lalle ya yi asara babba a rayuwar shi.2 Shi kuwa Dee shigowar Saifullahi da kuma yanayin da ya ga yana kallon Amatullah ne ɓata masa rai. A murtuke su ka gaisa da Saifullahi, ya ce da Amatullah “Madam mu tafi ko?” “Amatullah ta amsa da toh Mijin so”10 Ta sa hannu a jaka ta ɗauko kudi dubu ashirin ta ajiyewa Ayush bisa gado. Ayush ta bi kudin da kallon takaici, wai ita Aysuh tsohuwar matar Saifullahi ke yiwa kyautar kudi tsabagen lalacewar mijin ta. Amatullah ta musu sallama, hannun ta cikin na Dee su ka fice in da Ayush da Saifullahi su ka bi su day kallo cike da sha’awar ina ma dai su ne. Zuwan Amatullah ne ya haddasa masifa tsakanin Ayush da Saifullahi, don cewa ta yi tir da bagidajen miji irin shi, dan Allah ya kama kafa da mijin Amatullah ko ya dan waye, abin ya masa yawa ga talauci ga gidadanci shi ya sa Allah ya bashi nakasassan da daidai da shi6 Wannan maganar da Aysuh ta yi ba ƙaramin daci ta masa a rai ba, dan ko sallama bai mata ba ya tafi, ashe karshen ganin shi da ita kenan. Washagari da sassafe ta haɗa nata ya nata, da kudin da Amatullah ta bata, ta tsallake dan jinjirin da ta haifa ta gudu gida ita da tsohuwar da aka aiko mata, wacce da ƙyar ta hillace ta, ta amince su ka gudu. Ƙarfe goma ta musu a gidan su Ayush, kallon mamaki iyayen ke mata, har cikin ransu baƙi da ramar da tayi ya taɓa su. “Wai idanunki kenan? Kin gama shanye romon Saif din ne kika dawo?” mahaifiyarta ta ce cikin tsananin ɓacin rai. “Ummah!!” Ayush ta ce cikin hawaye. “Ai tuni muka yafe ma Saifullah ke, ace don kin yi aure ba zaki waiwayo iyayenki ba, ko sau ɗaya baki zo ba, ko talaucin ya kai kun rasa na mota ne” tace ranta a ɓace “Ummah ku yi haƙuri” Ayush ta ce cikin tausayin kai, haka dai suka haɗu suka wanke ta tas, sannan aka tabbatar tayi wanka ta ci lafiyayyen abinci, daga nan sai bacci ba tare da tuna wani ɗa da ta haifa ba. Naja’atu ce ta ka kira Saifullahi ta shaida masa Ayush dai ta cika rigar ta da iska, bayan ta zauna ta jira ta ga in da za su ɓullo har ta gaji. Saifullahi bai yarda ba sai da ya zo ya ga zahiri, da gaske ta tsallake ta bar masa jinjiri. Nan ya tabbatar kiyayyar da ta ke masa kiyayyar gaske ce, tashin hankalin da ya shiga baya musaltuwa.2 Daukan jaririn yayi in da yake kuka wiwi jinjiri na kuka, dan kuwa lokacin da ya kamata a bashi nono yayi, duk dama dai bai iya sha da kan sa sai dai a tatsa masa. Tun da har ta na uwa za ta iya tsallakewa ta bar ɗan da ta haifa ya san lalle Ayush ta kai matuka wajan rashin mutunci. Saboda haka ya lashi takobin kin waiwayar ta har illa mashaAllah, duk sanda ta yi shirya ta turo ta karbi takardar ta.2 Gun Hajiya dai ya koma, ya nemi yafiyar ta da kuma rokon ta da Allah ta koma asibiti ta na kula masa da Muhamad Jamoh, da ya ke sunan Emjay jinjiri ya ci. Hajiya ta ki yafe masa, sai da Baban Sasa ya sa baki sannan ta amince ta ce ya ci darajar masu daraja. Baban Sasa na mai duban Saifullahi ya ce “Saifullahi duk yanda na so na tausaya maka, yau na kasa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, ka ga dai yanda ta kasance da kai, ka ga kuma yanda Allah ya sakawa Amatullah, duk sanda yaran nan Dan Yusuf ya zo gare ni sai na yi da na sani , ina ma tun farko na yi imani da hukuncin Allah na aura masa jika ta, da yanda ya ke faranta min yanzu tun daga lokacin zan fara mora, wannan yaron Dan Yusuf ya koyar da ni ilimi a shekarun da na riga na tsufa, ya wayar min da kai cewa babu wani tazara tsakanin ni’imar ubangiji da dan adam, muddin ya kasance mai tsoran Allah, Allah yayiwa Dan Yusuf albarka, amma ka sani, yanda ba ka ci riba ba itama matar taka babu riban da zata ci, dubu sunyi kafin ku wani riba suka sami?”6 Kai Sunkuye Saifullahi ya gaza motsawa ya yin da hawaye ki fita daga idanun sa cike da nadama, Nadama a lokacin da shi kanshi ya san ya makara.4 ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH